WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 19

39K to 42K   out of 57K words

da kukan, na yau har ya fi na kullum, tamkar
wadda aka yi wa bushara da rasuwar uwa da ubanta.
“Allah-kareem!”
Ya furta cikin zuciyarshi. Ji yake kamar ya dauko damuwar Lailah ya aza ma kanshi don ta huta.
Shi bai ga dalilin da za a cire cikin da yake da uba ba. Koma babu uban shi a haife dan a ba shi
yana so.
Babban burin shi kenan a duniya, ya ganshi da dan kanshi, wanda kuma gurin haihuwar ne
Allah ya karvi ran matarsa.
“Lailah idan ba kya son dan ne ni ki haife ki bani, wallahi Lailah baki san yadda nake addu’ar
Allah ya bani da ba.
Idan Ubangiji ya baka da ya yi maka kyautar komai, wadda wani ko wata bazasu tava baka ba.
Ki tuna ke musulma ce, wadda ko ba dade ko bajima za ta tadda Ubangijinta.
Shin me za ki ce da Ubangiji a bisa wannan muhimmiyar kyauta da ya yi miki kika butulce? Baki
da tabbacin cewa wannan shine kadai kwanki a duniya. Wasu suna nan suna nema ruwa a jallo
koda zasu karar da dukiyoyinsu, amma Allah bai basu ba
A matsayina na dan uwanki musulmi ina mai tunasar da ke cewa, idan kika zubar da ciki kamar
kin kashe rai ne, kuma wallahi Allah ba zai barki haka ba.
Idan laifi uban dan ya yi miki za ki huce a kan dan tayin dake karkashin mahaifa kin yi babban
kuskure, wanda ko ba dade ko ba jima wata rana za ki yi nadama.
Idan bakya so ina mai shawartarki ki daure ki haife, ni Abbas ina so, ki bani. Zan yi mishi uba,
idan bakya son uban shi, ko idan wani laifi uban nashi ya yi miki har ta kai ki ga yin wannan
gurvatacen tunani.”
Lailah ta juyar da kai cikin matse hawayen idanunta. Ga dukkan alamu ranta ya soma sanyi. Ya
ci gaba da yi mata nasiha hadi da ba ta misalai kala-kala, har ta saddakar da tana son
fayyacewa Abbas dalilinta na yin hakan.
A ganinta idan ya ji dalilinta shine mutum na farko da zai goya mata baya ta yi abin da take da
nufin yi.
[12/17/2019, 17:51] Takori: ****
Matsala ta biyu da muka kara cin karo da ita ni da Mohammed, ita ce matsalar rashin haihuwa.
Shekarun mu biyar tare amma haihuwa shiru, babu ita babu alamunta.
Daga baya ma Mohammed ya zo yana zargina da yin ‘planning’ a voye, bayan kuma a zahiri ba
hakan bane.
Muka koma biye-biyen teburin likitoci suka yi ta zakule-zakulen su har suka tabbatar matsalar
daga gare shi ne.
Idan har yana son haihuwa to yana bukatar ai mishi aiki, don haka daga ni har shi muka tattara
maganar haihuwa muka yi watsi da ita. Sai dai duk inda Mohd ya ga ‘ya’ya sai ya karar da
lokacinshi a kansu.
Na lura Mohd na matukar jin dadin yadda alakata take da Sa’eed, domin dan gaban goshinsa
ne, su biyu kacal iyayensu suka haifa kuma mahaifinsu ya jima da rasuwa.
Yana so ya zo ya tadda mu a falo muna ta nishadi, tunda dai shi baya da lokacin mu.

A wani weekend Sa’eed yake yi min zancen yarinyar da zai aura Zaliha, ajinsu daya ne a
makaranta, yana son in fadawa Mohd. don gidan su Zalihan sun takura idan ba zai fito ba za su
bawa wani. Shi kuma yana son yarinyar sosai.
Na ce,
“Sa’eed da rigima kake, kana fafutukar kwalin karatun farko za ka hada ma kanka aure?”
Ya ce,
“Wallahi da gaske nake Antina, ina matukar son Zaliha, idan kuma ban same ta ba ban san ya
ya rayuwata za ta kasance ba, ku taimaka mani”.
Na ce, “Ni don ta ni ai mai sauki ce, amma Yayanka ka fi kowa sanin shi”.

Ko da Mohammed ya zo, bayan wasu watanni kamar yadda ya saba, na yi mishi zancen, bai
wani ba zancen muhimmanci ba, don haka ya koma ta vangaren Hajiya.
Na ke jin ita ce ta tusa Mohammed din a gaba sai da ya amince aka yi ma Sa’eed baiko da
Zaliha, amma aka ja lokacin sosai zuwa sanda za su kammala karatun su.
Sa’eed ya dauko Zaliha har gida ya kawo min ita, yarinyar kyakkyawa amma ta waye da yawa.
Na yi mishi maganar hasashe na ya ce “haka nan nake son abata”.
Gab da kamawar watan bikinsu muka samu wani mummunan labari, wato hatsarin Zaliha da
iyayenta a kan titin Abuja, duka babu wanda ya tsira.

Hakika Sa’eed ya shiga matsanancin tashin hankali wanda ta kai shi da furucin babu shi babu
aure a duniya.
Shekarun mu biyar da aure Sa’eed ya tafi NYSC jihar Cross-river. Don haka sai na kasance
cikin kadaici da kewa. Da dai kadaici ya isheni sai na tattara na tafi Egypt wajen mahaifiyata,
bayan na nemi izinin Mohammed ta waya.
Zamana da ‘yan uwana sai ya zamo magani ga dimbin damuwar da nake ciki. Momi ta kasa
daurewa don ganin muguwar ramar da nake yi. Ta sani a daki a wani maraice tana tambaya ta.
Ban voye mata komi ba na zayyane mata matsala ta. Momi ta ce,
“Tun farko ke kika kawo yaron nan Lailah kika ce kina son shi, alhalin kin san yanayin aikinsa,
ban ga dalilin da za ki daura ma kanki damuwa yanzun ba.
Idan har kina ganin ba za ki iya ba, to tun wuri ki nemi da ya sauwake miki”.
Na yi jim! Ina tauna maganar Momi, in ce Mohammed ya sake ni? Abune da ba zan tava iyawa
ba, domin dai auren soyayya muka yi, duk da halayen sa na rashin kulawa da soyayya a gare ni
‘still’ ina son kaya na.
Don haka har na koma Bauchi ban yankewa kaina shawarar komi ba, tunda dai 100% na yarje
ma zuciyata ina son mijina.
Ginshikin aure kam ba na samu, wato auratayya. A hankali dai na fahimci jinsin mu ba daya
bane, yana cikin jinsin mutanen da seduality wato auratayya bai dama ba, ya yin da ni kuma
nake a rukuni akasin hakan.
Dole haka na daure ina ci gaba da cin dan uban hakuri. Da dadi ba dadi muna zaune a hakan.
Rashin Sa’eed sai ya zamo min kamar rashin babbar aminiya. Ya shiga jikina sosai, mun
amincewa juna, duk wata matsalar junanmu da junanmu muke shawara, na kuma lura sosai
Mohd ba karamin jin dadin hakan yake ba.

Ta duba agogon ‘swatch’ dake daure a fatar hannun ta, ta dubi Abbas, “lokacin sallah yayi, mu
je mu sauke farali”. Ya sauke tagumin da yayi da hannayenshi biyu yana sauraronta, ya mike
yana duba nashi agogon shima.
****


Kwance yake a mike bisa doguwar kujerar da ke karamin falonshi yana nazarin jaridar
‘Daily-Trust’, sai dai da ganin irin kwanciyar da ya yi ka san ba ta lafiya ba ce, alal hakika yana
cikin matsananciyar damuwa.
A karo na wajen dari da hamsin kenan, ya sake ‘dialling no Lailah, kamar yadda computer ta
saba yi mai vavatu yau ma vavatun ta shiga yi mishi, cikin sanar da shi layin a rufe yake.
Kararrawar shigowa falon ta yi kara, da kamar ba zai kula ba, ya dai daure ya mike ya isa ga
kofar ya bude.
Ya bayyana a falon cikin kyakkyawar shiga ta caftan na farar shadda mirrow, suka yi ido hudu
da dan uwansa da baya da ya shi a duniyar baki dayanta.
Ya matsa kadan ya ba shi hanyar wucewa suka zauna a tare cikin kujeru masu fuskantar juna.
A saluve Sa’eed yake kamar wanda ya sha duka, ya ce, “Yaya har yau ba labari?”
Bai saurari amsar shi ba ya ci gaba da cewa.
“Ni ina ganin a kai zancen cigiya kafafen yada labarai”.
Mohammed bai amsa ba, illa ya mike ya isa ga kitchen ya fiddo ma dan uwanshi abin sha mai
sanyi na’ya’yan itacen ‘tropical juice’ hade da tambulan, don ga dukkan alamun shi a gajiye
yake da uwar tafiyar da ya niko tun daga jihar Cross-river.
Hakika yana tausaya ma dan uwanshi halin da ya shiga a dalilin vatan matarshi, wanda kuma
shi ne sila.
Anya idan Mohd ya ji irin cin amanar da ya yi mishi zai tava yafe mishi? Idanuwansa suka kada
jajir, amma sun kasa tsiyayar da hawaye.
Ya tashi tsamo-tsamo da shi ya nufi hanyar baskwata, don ganin ga dukkan alamu Mohd din bai
son damu yanzu cikin halin da yake ciki.
Wayar shi dake gefe ta yi ruri, ya mika hannu a kasalance ya dauka. Isma’il ne yayan Lailah.
Bayan sun gaisa ya ce,
“Babu labari a nan Bauchin har yanzu? Mu ma nan mun baza cigiya har a sauran kasashen da
ke makotaka damu wadanda take da kawaye a can, ba amo ba labari”.
Mohammed ya ce
“Nan din ma babu, amma yanzun nan Sa’eed ya kawo min wata shawara a kan na baza cigiyar
a nan gida Najeriya”.
Suka yi sallama kowannen su zuciyar kamar-kamar me.

A iyaka tunaninsa, bai san laifin da ya yi ma Lailah takamaimai ba, lafiya kalau suka rabu. Sai
dai da ya yi nazarin wasikarta ya fahimci a kan halayyar da yake mata ne ta gwammace ta yi
nisa da shi, tun da ta kasa magantawa kanta, shima ya kasa maganta mata.
To a yau ga shi a dalilin halayensa aikin ma gaba daya ya kasa a dalilin rashin ta.
Daman an ce baka sanin muhimmanci da amfanin mutum sai ranar da ya suvuce maka. Ya rasa
inda zai sa kansa a dalilin rashin Lailah, ya yi nadama matuka da irin halayen da yake yi mata

wanda ba sau daya ba, ba sau biyu ba ta sha gaya mishi cewa ba ta so, ya daina.
Amma bai dainan ba, sai sanda ya rasa ta. Shi da dan uwanshi suka shiga kafafen yada labarai
na garin Bauchi suka sa cigiyar Lailah har da hotunanta.
Amma har kwanaki suka tura shiru kamar an shuka dusa. To ina ga mahaifiyarta da ta tsugunna
ta haife abarta?

****


Ya kwankwasa kofar dakin a hankali rike da karamin ‘tray’ da ya dauro karamin ‘tea flask’ da
kayan shayi.
Ta zo ta bude cikin nutsuwa ta yi wani irin fari ta rame ta zuge duk a lokaci daya. Ya aza ‘tray’
din a kan wani dan karamin tebir da ke dakin, ya ja kujera ya zauna ya soma hada mata shayin,
ya kammala ya shiga firfitawa.
Kallon shi take cike da tausayin kulawa da taimakon da yake yi mata a matsayinshi na wani
mutum da basu hada dangantakar komi da shi ba, face abokin kan hanya kadai.
“Abokin kan hanya?”
Ta kalubalanci furucinta. A gare ta zuwa yanzu matsayin Abbas ya zarta wannan. He is
someone she respect most!.
Ya shiga zuciyarta da yawa, ta yadda har tunaninta ke canzawa a kanshi, zuciyarta na gayyatar
shi da wani matsayi mai girma. To ita kanta ba ta da ‘standing’, abin nufi. Ba ta san matsayinta
ba balle ta soma tunanin irin wannan, tana da aure ko babu? Ba ta sani ba.
Har ya kammala firfita shayin ya miko mata ba ta farga ba, ta yi nisa a tunanin ta.
Ya ce, “Lailah!”
Ta yi firgigit ta ankara. Ya mika mata shayin wanda ba ko tantama tana sha za ta amayar da shi.
Ya kan ce, “Ya fi babu dai tun da ko ya ya ne wani zai zauna a cikin hanjin cikinta”.

Abbas gwanin jinya da karfafa gwiwa, Abbas mai kyau, Abbas mai kirki…ya kan nuna mata
wannan ba komi bane, babu wanda baya fuskantar challange (kalubale) a rayuwa. And is up to
us to accept such challenges mu bita da duk fuskar da rayuwa ta zo mana.
Ya ce,

“Ni tashi na yi ba Uwa ba Uba Lailahhh. Haka nai ta gararramba a gidan wan mahaifina, sai dai
na kasance daga cikin hazikan yara, duk da gararramba ta.
Da na kare karatun sakandire gwamnati ta dauki nauyin karatuna a nan Ingila, kin ji abin da ya
rabo ni da gida.
Duk karshen shekara ina zuwa in gai da wan mahaifina. Da na kare karatun digiri na farko ya yi
min aure da diyarshi Hasina, muka taho nan tare, inda ta rasu a ya yin haihuwa.
Na zo gida Najeriya ne gai da Baffan nawa, na hadu da ke a filin jirgi”. Wannan shine
takaitaccen tarihi na.

Ba ta san me ya sa ba hankalinta ya kwanta da Abbas sosai ba, har take jin shine mutum na
farko da za ta kwaye ma cikinta, a kalla ko ba komi zai ba ta shawarar da za ta amfane ta, da

kuma yadda za ta yi ta gyara kurakurenta.
Ya ce,
“Uhm? Ina sauraron ki...?”

****

“A kullum ina tausar Sa’eed a kan rasuwar Zaliha, ina nuna mishi ya yi hakuri haka Allah ya
rubuta musu cewar ba mamallaka juna bane a gidan duniya.
Ya hakura ya nemi wata da ya kare NYSC ya yi auren shi. Duk da ina jin wani dan kishi-kishin
abin a raina.
Shakuwata da Sa’eed har ta kai matsayin da zuciyoyinmu suka soma karkacewa, al’amarin da
bamu tsammana ba (sha’awa). Na fahimci hakan ne daga yanayin kallon da Sa’eed ke min, da
wanda nima nake mayar mishi.
Ya zamanto ko abu Sa’eed zai karva a hannuna sai ya san yadda ya yi hannun shi ya gogi fatan
hannuna.
Muka soma wata irin rayuwa ta daban har ya zamanto Sa’eed babu inda ba ya shiga a dakuna
na ba tare da la’akari da halin da zai iya samuna a ciki ba.
Muka sake muka shantake muna abin da muka ga dama, sai dai bamu tava yin babban aiki ba,
wannan kam muna kula muna jin tsoro. Bamu tava yi ba, kuma bamu da niyya. Amma ‘yan
‘romances’ dinnan bamu dauke su komi ba.
Har ya kammala hutun zangon shi na farko na NYSC ya koma cike muke da kewar juna. Kamar
mu tafi tare.

Wasu watanni uku ris Mohammed ya kara a kan wadanda ya saba, suka zama shida ris kafin ya
waiwaye ni.
Bai san zuwa wannan lokacin ni tuni na rufe babinshi na daina kewar shi ba, don haka ya yi
mamakin yadda har ya yi ‘yan kwanakin da zai yi ya kare zai koma bai ji na yi ‘complain (korafi)
ba.
Bai sani ba ni tuni na samu madadin sa ba. Don haka lafiya-lafiya muka rabu wannan karon
yana ta sa min albarka.
Wata ranar lahadi Sa’eed ya zo har kofar dakina ya yi sallama, sanye nake da kayan barci
masu laushi ina shirin kwanciya barci.
Sai ya tsaya kallona galala, shi kadai ya san abin da yake kissimawa a ranshi. Ya kare ya ce.
“Aron wayarki nake so ki bani zan kira Hajiya wayata babu chaji”.
Na dauko waya na taso zan miko mishi ya hada dani ya rungume cikin wata irin rikitacciyar siga.
Na samu kaina da biye mashi, domin nima cike nake da kishirwar abin.
Cikin dan lokaci mune har a kan gado cikin al’amarin da ba zan iya fassarawa ba. Ban tava
samun ‘satisfaction’ (biyan bukata) da Mohammed irin yadda na samu a Sa’eed a ranar ba.
Wannan shine babban kuskuren da na tafka a rayuwata, ya kuma yi dalilin barowa ta gida, don
ban ga sauran amfani na a cikin gidan ba.
Da muka dawo hayyacin mu ne na fahimci aika-aikar da na tafka, ko in ce muka tafka.....”
Ta dakata ta share hawayen da ke kwaranyo mata, ko motsi Abbas bai yi ba, yawun bakinshi ya
dauke, ya kuma rasa wa zai bai ma laifin a cikin su duka ukun.

......Tsoron abin da muka aikata ya shige ni. Tsoron ingancin addinina da aurena ya addabe ni.
Tsoron mahaliccina da abin da za ya tambaye ni ranar da na gamu da shi ya shiga girgiza
zuciyata.
Mohammed kam bai sani ba, amma Ubangijina Ya sani, kuma ni da na aikata na sani. Sai dai
duk na dauki laifin na aza ga Sa’eedu, wanda kuma daga baya da na yi kyakkyawan tunani sai
na ga cewa dukkanin mu muna da laifi.

Na jima da neman gurbin karatu a wannan makarantar ta yanar-gizo ba tare da sanin
Mohammed ba, kuma ‘admission’ bai zo mini ba sai a dai-dai wannan lokacin.
Na duba gabas na duba yamma, kudu zuwa arewa, ban ga inda zan kai nadamata ba, baya ga
tafiya in barsu baki daya.
Don bani da bayanin da zan yi ma Mohd. Bani da bakin da zan fuskanci Ubangijina idan na
cigaba da zama dashi zaman zina. Amma shi din ai mai afuwa ne ga bayinsa. Don haka na
taho, har kuma hakan ya yi sanadiyyar haduwata da kai a filin jirgi.

Sai kuma ga wani sabon al’amarin.... ‘ciki’?” Ta furta cikin tashin hankali.
Bana tantama ciki na Sa’eed ne, don kamar yadda lissafin asibitin ya nuna, ya yi dai-dai da
ranar faruwar al’amarin Abbas........” Ta ci gaba da kuka.

Da da hali, da ya rungume ta ya rarrashe ta, shi kam tun da uwarshi ta kawo shi duniya bai tava
jin irin wannan kwamacalar ba, kuma iya amfani da hankalinsa da tunaninsa ya kasa rarrabe
wane ne mai laifi?
Ya gyara murya idanunshi sunyi jawur, ya zamo daga cikin kujerar da yake zaune, ya durkusa
ya zauna a gabanta, ya mika hannuwa kamar zai kamo hannuwanta sai ya fasa.
Cikin muryar lallashi ya ce, “Lailah! Ni dai shawarar da zan baki kada ki kashe rai. Ki ji tsoron
mahaliccinki, ki bar masa kudura da iradarsa.
Ni Abbas na ji nine uban dan da za ki haifa, ki haife ki bani zan yi mishi uba har karshen
rayuwata.
Babu wanda ba ya yi wa Ubangiji savo, dukkanin mu masu savo ne ta wannan hanyar ko ta
waccan.
Abin bukata shine, tsarkakken tuba da tabbacin ba za a sake komawa izuwa zunubin ba.
Sannan a ganina bai kamata ki yiwa Momin ki da ‘yan uwanki haka ba, yanzu gashi kin barsu
cikin tashin hankali.
Gara da a ce mutuwa ki kai sun san kin mutu,

14 / 19