WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 19

33K to 36K   out of 57K words

cikin kuka ba.
Ya lumshe ido yana bude su dukka a kanta, sun kada sun yi jawur. Wannan karon sautinshi ya
yi kasa very cool! Ga dukkan alamu tunanin mutuwar matar ya tava zuciyarshi.
A hankali ta ce, “I’m sorry”.
Ya ce, “Na gode”.
A marairaice ya ce, “Ki yi hakuri ki karve ni LAILAH”. (Ya ga sunan ne a jikin passport dinta). Ko
da a matsayin abokin tafiya ne, bana nufin komai dake sai alheri Lailah. Lailah ina so na

taimaka miki ne, ta wani fannin in taimaki kaina. Kin amince dani Lailah?”
Ta karaya, amma bata son nuna karayar tata a kan MAZA. Tana da tabon su, tana da danyen
mikin su cikin ranta, tana da mummunan kullaci a kan al’amarin su;
Sune suka rabo ta da iyayenta da basa hada kaunarta da ta kowa. Sune suka rabo ta da
mijinta da aurenta. Sune suka rabo ta da ‘yan uwanta da aminanta...... Sune.....sune.....sune
suka yi wa zuciyarta gyambo da har abada ba zai warke ba.
Sune suka yi mata miki mai rudani, suka sanyata cikin rudanin rashin sanin sahihanci da
ingancin addininta......
In haka ne ita wace irin wawuya ce da za ta amince ta sake fadawa a tarkon su haka ‘so early?’
(da wurwuri?)
Ta girgiza kai ta furta mishi da karfi, “Never! (Fau-fau). Babu ni babu Da Namiji!”.

Ya yi saurin juyowa idanunshi sun kada sun yi jawur, yana son tantance sanadin wannan
ANGER (fushin) da ke cikin muryarta.
“Why Lailah (me ya sa)?” Ya bukata.
“Ai ba duka muka taru muka zama daya ba. Kowa sunan shi yake amsawa. Kada kiyi mana
jimilla a rashin kirkin, wannan rashin adalci ne!”.
Ta soma kokarin kwatar jakarta tana magana, wannan karon cikin kuka.
“Am not your wife (ni ba matarka ba ce), so why the disturbance? (meye dalilin wannan
takurawar?)
Ka kyale ni in yi tafiyata, ka kama hanyarka in kama tawa, ka yi wa Allah ka rabu dani........”
Kuka ya ci karfinta.
Karfinta ya kare domin ta kasa kwatar jakar. Karfin mace, da karfin namiji. Balle zabgegen
mutun irin ABBAS. Wadanda irin su tsiraru ne a cikin al’ummah.
Sai ta tsuguna a nan kan kafafunta ta sa mishi kuka mai gigitarwa, tana rokon shi Allah da
Manzon shi ya ba ta jakarta ya yi tafiyarsa ya kyale ta.
Shi ma sulalewa ya yi nan a gabanta a kan gwiwoyinsa idanunshi a rikide, amma ba kukan yake
ba.
Numfashinshi ke gwagwarmaya da sauri da sauri. Ji yake in duk duniyar nan za ta taru a kansa
ba za ta raba shi da Lailah ba!.
“Hanya mai hadin zumuntar dole….”, in ji ‘yan Magana. Lailah ta gamu da gamonta. Ta ci
kukanta ta koshi, ta tabbatar ba zai rabu da ita ba sai dai su kwana a nan. Ta yi tunanin hada
shi da ‘yan sanda kawai su yi masu katangar karfe. Daga baya wata zuciyar ta ce da ita, “A kul,
shi din kin san wane ne?” Bai yi kama da irin mazan da mace za ta wulakanta ta kwan lafiya ba,
bai yi kama da wulakantaccen mutum ba. Haka bai yi kama da wadanda ‘yan sanda za su
girgiza ba, tun da kasa ce da kowa ke da ‘yancin kansa.
Ba ta da zavi ban da dangana, ta yi gaba tana huci ya bi ta a baya yana murmushin cin nasara.
Suka gangara ta liftar kasa zuwa ‘Rail-Station’ na Heathrow, suka yi amfani da katunan Abbas
na hawa jirgin kasa suka hau jirgi mai zuwa cikin ‘Central-London’.
***
12/SAFAR HIJIRIYYAH
Cikin jerin gwanon masu saukowa daga matattakalar jirgin ‘Royal Air Moroc’ har da Engineer
Mohammed Bauchi, fari sol da shi bafulatanin Jama’are, ga dukkan alamu babu tambaya, cikin

caftan na ‘ash colour’ shadda mai taushi da walkiya. Agogon (RADO) baki sai sheki yake cikin
tattausar fatar hannunshi da bakin lallausar gashi ya baibaye.
A very serious person (wanda babu alamun wasa cikin al’amarinsa), wato irin mutanen nan
masu wuyar sha’ani da rashin walwala. Sai dai fa in ka san wata kalma wai ita ‘aji’ na karshe, to
Mohd. ya mallaki dukkanninta.
Dan kimanin shekaru 35, Mohammed, yana da tsayi sosai da lange-langen jiki na fulanin usli,
wadanda suka jiku suka zurfafa suka gogu cikin ilimin addini da na boko.
Ga wanda duk ya san Mohammed Jama’are, ya san shi da wannan halayyan nashi na
(seriousness), watau daukar abinda ke gabanshi da muhimmanci a kan komi. Babu abin da
yake bai ma lokaci kamar aikinsa da abubuwan da ke gaban shi, na ci gaban rayuwar shi.

Tun kan ya idasa saukowa daga matattakalar ya zura hannu cikin aljihun kaftaninshi ya fiddo
wayarshi ya kunna, yana kiran kanin shi Sa’idu ya zo ya tarbe shi.
“Big Bro. isowa haka unexpected?”
Ya fada cikin kasalalliyar murya.
“Da tun jiya ka sanar damu, yanzu haka ina cikin Jama’are, Inna ba ta jin dadi”.
“Ow.k, ba matsala, bari in kira Lailah, ai tana gida ko……?”
Shuuuu...... ‘network’ ya katse, don haka bai ji amsar Sa’id ba.
Ya lalubo lambar ya kira, sunan ‘eclairs’ ya soma yawo a ‘screen’ din. Ta yi kara har ta gaji babu
agaji.
A karo na biyu ya sake kira. Wannan karon ma ta yi ta vurarinta har ta gaji, ‘eclairs’ ba ta agaza
mata ba.
Cike da kosawa ya sake kira a karo na uku, ta yi har ta gaji ta tsinke don kanta. A serious
person, abinki da dama ya ya lafiyar giwa? Nan da nan ya kufula, gaba daya ya kashe wayar
don haushi, ya figo jakarshi zuwa harabar ‘air-port’ ya samu achava ya dane, mai machine ya
rike jaka a gabansa, bai tambayi ba’asi ba ya figi babur, ga dukkan alamu wannan oga a kule
yake, don haka bai tambayi inda za a ba sai da ya mula don kansa ya fada mishi.

​ Gidan na daga jerin farko-farko na gidajen unguwar (Fati Mu’azu Links) cikin Bauchin
Yakubu, gida ne ‘flat’ karami hawa daya ma’abocin wadatar shuke-shuken furanni masu launi
daban-daban da kamshi daban - daban. ​Karamin gida ne da ya kunshi duk wasu nau’o’in
abebaden jin dadin rayuwa cikin tsari da sanin ciwon naira. Abin nufi, babu almubazzaranci, babu fariya, haka babu son nuna isa. Komi ka gani cikin gidan
mai amfani ne, haka ba a yi dakuna rankatakaf ba adadi ba.
Kwata-kwata dakuna ciki uku ne da makeken falo, sai (boys quater) daga waje da (study room)
mai kunshe da littattafan da suka shafi mazauna gidan.
Maigadi ya saki baki bude, ganin maigidansa na sauka daga kan dan achava da jakar kayansa.
Ya ciro kudi ba tare da ya kirga ba ya mika mishi ya wuce yana godiya.
Malam Surajo bafullatanin garin Dambam ta jihar Bauchi, kuma amintaccen maigadin maigidan,
ya karvi jakar uban gidansa ya yi ciki da ita ba tare da ya jira ubangidan ya gama kiraye-kirayen
wayar da yake yi ba.
Ya yi matukar mamakin ganin motar matar gidan na nan. Rufe cikin tamfol, sai dai ga dukkan
alamu an jima ba a yi amfani da ita ba, sakamakon kura da ta yi futuk ita da tamfol din.

Motoci uku ne dama a ma’adanar gasunan. Wanda ke nufi tana cikin gidan, tana ganin kiran
wayarshi amma don iya shege irin nata ta ki amsawa da gangan.
Ya yi kwafa kana ya tura kai cikin gidan. Ko’ina a bude, ba a sanya makulli ko daya ba.
Sai dai fa ko’ina futuk yake da kura kamar babu halittar dan Adam a gidan. Tuni Malam Surajo
ya aje jaka ya fice domin da alama ogan na cikin masifan nashi da ya saba.
Yana tsoron kada bai kar zomo ba a ba shi rataya, don haka ya yi hanzarin daukar buta ya zaga
bayi domin gabatar da alwalar sallar azuhur.
Niyyarshi yau sai Allah kadai zai saukar da shi daga fushin shi, duk dadin bakin nan nata…, duk
kissa da kisisinar nan nata….., duk lailaya da rarrashin nan nata……, duk taushin hannuwan
nan nata........da tausasan levvan nan nata, masu mantar da da namiji duk wani jin kai, takama
da mukaminsa. Yau sun yi kadan su sauke fushin takwaran Manzo. To amma fa ko wajen zama bai gani ba a dai wadannan fututuk din ‘leather’ din masu kama da
an yi wata ba a hau ba.
Babu motsin kowa, babu motsin komi balle ‘yan wake-waken nan nata na zabiya ‘Nancy
Agram’ idan tana ‘yan girke-girke da kaye-kayenta cikin kitchin.
Jikinsa ya soma yin la’asar. Kai tsaye ya fada kitchin babu ita, ya banka dakin barcin su.... a nan
ne idanuwanshi suka gano mai abin al’ajabi.
Kafatanin kayanta da ke cikin ma’adanar kaya gasu nan baza-baza a kan gado. Ga alama an
kwashe wasu ne an bar wasu. Ya yi kira da murya mai karfi....
“LAILAH!”
Kiran ya dauki amon da ya karade ilahirin gidan. Ya sake bude iyakar muryar da Allah ya halitta
masa.
“LAILAHHH! LAILAHHH!!!”
Shi kansa sai da amsa kuwwar ta hargitsa cikin kwanyarsa.
Davas! Ya sulale ya zauna da mazaunansa bisa carpet.
“Me ke faruwa ne? Ina ta tafi? Babu sallama balle neman izini? Wannan ba halayyarta ba ne, ba
ta tava ba, ba ta da kowa a nan sai shi, sai iyayenshi da ke kauye wajen wa za ta je?”
A sukwane ya kara zaro waya ya kira dan’uwansa. Ta yi ruri har ta gaji, ta yi gunji ta yi vurari
mamallakinta ya ki dagawa. Da ya sake kokarin kira a karo na biyar, mai abar ya kashe ta gaba
daya.
Cike da mahaukacin mamaki ya tattara hankali da kuzarinshi wuri guda, ya mike tare da zuwa
ga lokar gado ya dauko makullan motar sa.
Sai a lokacin tunanin Malam Surajo ya fado mishi. Da sassarfa ya fito ya nufi dakinsa, ya idar
da sallar azuhur kenan bai kai ga mikewa daga sallayar sa ba.
Ya tsaya daga bakin kofa ya tokare cike da jarumtakar voye tashin hankalinsa da gigicewar sa.
“Malam Surajo ina matar gidan nan ne? Ko’ina a bude, kuma a hargitse. Kuma kura futuk, anya
lafiya?”
Malam Surajo ya jinjina kai ya dubi ubangidansa a nutse ya ce.

“Yammacin ranar ta yi min alheri mai yawa, irin wanda ba ta tava yi min ba.
Ta ce, “Watakila Surajo wannan ita ce haduwar mu ta karshe. Na yi tafiya Surajo sai wata
rana”.
Ta dauko damin kudi ta bani, ta kuma bani wannan ‘yar takarda ta ce in baka”.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, da kyar ya mika hannun daman shi Malam Surajo ya
daga buzun sallarshi ya ba shi takarda nannade cikin ambulan.
Daga inda yake tsaye ya warware takardar idanunshi na ganinta dusu-dusu.

Mohammed Dina…..!
Na yi tunani iyaka tunani, bincike iya bincike, na kasa gano tsakanin ni da kai WANE NE MAI
LAIFI?
Da na kasa ganowa sai na bai wa Allah zavi. A daren ne kuma na yardar ma kaina cewa
rabuwar mu ita ce mafi ALHERI.
Domin ba za ka tava yafe min ba......nima kuma ba zan tava yafewa kaina ba.
Idan na yi wa kaina hukuncin da ya rataya ga kuskurena, watakila wata rana mu gana.
Ina rokonka idan ka kuma yin wani auren, Mohammed dina....ka yi kokari kada ka maimaita
kurakuranka.....ka rage ‘seriousness’ din nan naka…. ka bai wa matarka kulawa da dukkan
kaunar da take bukata daga gare ka......
-LAILAH BALLAH!

Kanshi ya daure tam, ya yi zafi rau. Ya kai yatsa baki ya ciza da karfi wai ko barci yake ya farka.
Ya tabbatar idon shi biyu.
A karo na biyu ya sake bin kyakkyawan rubutun Laila ya karance tsaf.
“Me na yi miki Lailah? Wane kuskure na yi miki haka da zafi da kika zavi bari na?”
“Ka manta ne? Sarkin tsokanar? Ta saba ‘trick’ kala-kala, yanzu haka tsokana ce kawai take yi
ba za ta wuce wurin mahaifiyarta ba”.
Wani dan guntun sako daga zuciyarshi ya tunasar da shi.
Don haka cike da kwarin gwiwa ya linke takardar ya jefa a aljihu, ya bar dakin Malam Surajo
yana tafe yana kiraye-kirayen waya domin nemawa kanshi tikitin zuwa Alkahira komi dare.
[12/17/2019, 17:50] Takori: ***
Tarba ta musamman Momi Najla ta shiryawa surukinta cikin babban birnin Alkahira. Tun da ya
yo waya cewa ga shi nan a filin jirgi a zo a tarve shi, ita da kanta da kannen Laila biyu Sanah da
Najat da kuma babbabn Yayansu Isma’il suka zo taren shi. Isma’il na tuka motar. Autarsu Najat
ta zo da gudu ta rungume shi da ta hango shi yana nufo su tana tambayar shi. “Uncle Pilot za ka tuka ni a jirgi? Uncle Pilot AINA UKHT LAILAHHH?”
Hankalinshi in ya yi dubu to ya tashi, tsigar jikinshi ya mike, ya kidime ya razane. Wannan na
nufin, Lailah ba ta wurin su.
Da wane ido zai dubi Momi Najla da ta danka mai amanar rayuwar marainiyar diyarta?
Gwiwoyi a sage, gavovi a kassare, ya zube a gaban Momi ya kasa ko gaishe ta. Isma’il ya
kama kafadunsa ya mikar dashi, sai ya fashe musu da kuka.
Kan ka ce meye wannan Najat ta shiga taya shi, saboda tsabar haduwar jinin su, yana matukar
son yarinyar ita ma tana matukar son shi. Ba don komi ba si don kwadayin ya tukata a jirgin
sama, wanda shi ne babban burin rayuwarta.
Momi ta matso gabanshi a hankali, jikinta a sanyaye ainun.
“Haba Mohammad, kada ka yi min haka. Me ya faru da Lailah? Wannan ba girmanka bane.......”
Isma’il ya kama kafadunshi, “Abokina Lailah rasuwa ta yi? Ka gaya mana ai mu musulmi ne,
dukkaninmu sane muke da cewa ko ba dade ko ba jima rai zai koma ga Ubangijinsa!”.

Ya girgiza kai, amma ya kasa magana. A karo na biyu Momi ta ce.
“Mohd. idan Laila mutuwa ta yi kwananta ne ya kare..........!”
Ya yi hanzarin tura hannu aljihu ya zaro takardar Laila cikin ambulan ya mika ma Isma’il, don
baya son wannan kalma ta mutuwa da suke ambatawa Lailansa.
A nutse Isma’il yake karanto ma Momi wasikar Lailah, har ya dasa aya. Dukkaninsu suka yi
zuru! Abin tausayi, ba ma ya Mohd. wanda yake jin kansa a victim na duk abin da ya samu
diyarsu.
Kanshi ya yi zafi zau da tunanin wane kuskure ya aikatawa Lailah da har ta zavi barinsa? Abin
da ko a mafarki bai tava kawowa ba.
Bai tava tunanin dai-dai da rana daya Laila za ta iya rabuwa da shi ba, saboda tubalan da suka
gina soyayyar aurensu ba tubala ne da ake amfani dasu wurin yin aure a wannan zamanin
ba......
Shi kuwa Isma’il dage kai sama kawai ya yi bai san me yake tunani ba.

***





Wani abin mamaki shine, Lailah da abokin tafiyarta duk makaranta daya suka zo, wato ‘Muslim
College, London’.
A tsarin makarantar basa ba da accommodation wato muhalli da abinci, don haka bayan sun
gama da registrer din makarantar (Aaliya Arnall), kai tsaye cikin gari suka fito. Suka yi ‘yan
tsince-tsincen dan abin da za su ci, amma basu shiga ‘restaurant’ ba. ‘SAM CHICKEN, chips,
da gwangwanin ‘pepsi’ suka samu suka ci. Suka koma cikin makaranta inda aka hada su da
wanda zai taimaika masu wajen neman muhalli.

Abbas ya zo neman kwalin shi na Ph.D ne yayin da Lailah ta zo neman kwalin masters. Duka a
cikin makarantar ‘Muslim College’.
Babu jimawa suka samu gidan zama na haya na wasu mutanen ‘Lahore’ a (Acton Town), kusa
da makaranta, don daga nan ko basu hau ‘bus’ ba zasu iya zuwa makarantar a kafa. Dakuna
ciki dai-dai, shi yana a saman bene ita tana kasa.
Kuma a washegari suka fara daukar lectures, maimakon biyan kudin haya duk sati sun dunkule
sun bai wa maigidan (Landlord) kudin shekara daya.
Sai ya zamanto wata irin shakuwa na shiga tsakanin Lailah da Abbas, shakuwa mara fasaltuwa.
Sannan tsaftatacciya, domin kowanne yana ganin mutuncin dan uwansa. Kuma kowannensu ya
san ciwon kansa.
Idan shi ya rigata dawowa zai dafa musu abinci, haka idan ita ta riga dawowa. Tare suke zuwa
‘shopping’, tare suke zuwa cefane, ‘café’ da sauran su, rayuwar su gwanin ban sha’awa kai ka
ce Yaya da kanwar shi ne.
A cikin gidan ba su kadai bane, akwai mutanen India da wata mata ‘yar kasar Somalia. Idan
Abbas shi ya yi abinci sai ya kwankwasa mata kofa ta bude ya mika mata, haka idan ita ce ta yi.

Duk kokarinta na ta yakice Abbas ta kasa, domin mutum ne har mutum, mai tausayi da kyautayi
mai yawan gaske.
Lokutan daukar lakcarsu ba daya ba, don haka a kullum daya ke riga daya dawowa gida.
Wanda ya riga dawowa gida shi zai dafa abinci.

Rayuwar London mai cike da abubuwan debe kewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai ta
taimaka ainun wajen rage ma Lailah dimbin damuwar da take ciki mai neman janyo mata
‘psychological depression’.
A wajenta Abbas (kawa) ne, wato (aboki) kuma mutumin da za ta iya tutiya da shi matsayin
wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rage mata dimbin damuwar nadamar rayuwar da take
ciki.
A hutu na farko da suka samu bayan share watanni uku suna daukar darasi, Abbas ya same ta
a dakin ta bayan ya nemi izinin shigowa.
Suka yi wa juna kyar da ido kamin su sakar ma juna dariya. Ya ja kujera ya zauna yana mai
fuskantar ta.
“Ko zan samu dan rakiya?”
A sanyaye ta ce, “Zuwa ina?”
“Zuwa ‘Lake-Windermerre’ a Cumbria, picnick nake bukata Lailah. Kwakwalwata tayi zafi, karatu
yayi yawa a cikinta so, ina son samun ‘peace of mind’ (hutu) koda na yini daya ne.”.
Cike da murmushi ta aje littafin da take nazari ta ce.
“Bani minti ashirin na kintsa”.
Ya fita ya ja mata kofar ya ce,
“Plz… hurry”.

Ta jirgin kasa suka bi zuwa ‘Cumbria,’ kauye ne awa ashirin da hudu (24 hours) daga London.
Ga alama hakanshi zai cimma ruwa ya

12 / 19