Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
ce, “Haba Abbas, ya za ka jikani? Yanzu na yi wanka fa”.
Bai saurare ta ba ya saukaka kayan jikinta ya manne bakinta da nashi da wasu irin matsiyatan
‘kisses’ da ba ta tava sanin akwai irinsu a duniyarta ba.
Ya saki ‘shower’ a kansu, cikin wani sabon al’amari da Lailah ba ta tava tsintar kanta a
kwatankwacin sa ba.
Ashe dai wannan ita ce soyayyar, na baya duk shirme ne? Wane Sa’idu wane Yayansa!?
Wadanan MANYAN MAZA ke magana…., wadanda basa furta SO ko I luv u a fatar baki, sai dai
ZUCIYA da GANGAR jikinsu ya nuna.
Fatan alkhairi gare ku ABBAS DA LAILAH! -Takori
Washegari ta kama Lahadi, Abbas kam yau sallar asuba a gida aka yi ta, Lailah ta samu kanta
da kasa hada ido da angon nata. Shi kuma hakan bai hana shi gudanar da amarcin shi ba,
soyayya ruwan zuma gangariya ake gunadarwa cikin kwanaki biyun da suka biyo baya.
Ya kasa amincewa wai ya tafi ya bar Lailah, har na tsayin watanni uku. Ga ayyuka ya bari masu
dimbin yawa. Ita kanta Lailar ta baro nata ayyukan a makaranta don haka ta karfafe shi da su
daure su tafi, lokaci kankani ya rage mata ta kammala gaba daya sai su tsara mai yiwuwa.
Sai da ya kaita har Madinah tamkar ba za su rabu ba, hakan dai aka daddaure aka ciccije aka
rabun da alkawarirrika masu yawa da ma’ana.
Ya biyo Ajrah (tasi) ya dawo Jiddah, karfe goma na daren ranar ya bi British-Air zuwa London.
Tana canza kaya a dakin su Dhuha ta yi sallama ta shigo, kallon mamaki ta yi mata tare da
tsoro, ta ce cikin harshen Larabci.
“Ke kuwa ina kika shiga Lailah har tsayin kwana biyar? Yanzu haka daga kai ‘report’ din vatanki
nake ga ‘security’ din makaranta. Hankalina ya tashi sosai”.
Lailah ta yi dariya ta ce, “Kai Dhuha? Ana yankan kai ne a Saudi-Arabia?”
Ta ce, “Ina na sani, tun da na ga wani ya zo neman ki kuma tun daga ranar ne ban kara ganin ki
ba, ba dole in yi zaton ya sace ki ba?”
Lailah ta kara yin dariya ta ce, “Sai ki koma ki gaya musu gani na dawo”. Ta juya tana cewa,
“Yanzu kuwa”.
Lailah ta kwanta a gadonta ta lumshe lumsassun idanunta tana tariyo rayuwarta filla-filla tun
daga kuruciya har girma.
Ta tuno Mohammed da rayuwar ta dashi, ta tuno Sa’idu. Sai ta samu kanta da yi musu addu’a.
Ta kuma gode Allah da ya musanya mata da miji na gari dai-dai yadda take buri a rayuwarta ta
duniya.
****
Bayan shudewar watanni uku suka samu hutu ta koma gida Egypt, ta tarar da haihuwar Sujood,
ta haifi kyakkyawar yarinya mai kama da Momi Najla. Wannan ne ya sa take yanayi da ita
Lailan, don duk cikinsu ta fi su kama da Momi. Duk yadda ta so ayi shagalin suna da ita hakan
ya faskara, sakamakon rashin isasshiyar lafiya, komai ta ci sai ya dawo ba ta ko son ganin
abinci ko kamshin sa.
Daga rowan lipton din ‘Tetley Tea’ sai gugguru, su kadai ne in ta ci ko ta sha ba ta amansu. A
matsayin Sujood na cikakkiyar likita, a take ta gane abin da ke damun Antin tata, ciki ne na
watanni biyu ko Momi ba ta gane ba.
Sujood ta rubuta magungunan da za su taimaka mata aman ya tsaya ta ba wa Isma’il ya siyo
mata ba tare da ya san na wace ce a cikin su ba, tun da ba ranar ta fara aiken shi siyan magani
ba.
Baby ta ci sunan Momi wato NAJLA, suke kiran ta Nawal. Sujood ta dage da kula da Lailah don
duk hidimar Nawal Momi da su Najat ke yi, tsakanin ta da ita sai shan nono wanda sai ta wuni
ba ta sha ba, saboda Momi tana ba ta madara.
Suna wajen motsa jiki Sujood ta dakata ta dubi Lailah ta ce,
“Antinmu ni fa kallon mai ciki nake miki, ki daina edcercise dinnan”.
Lailah ta jinjina kai ta ce,
“Nima na dade da zargin kaina, don watanni uku kenan rabona da al’adata.....”
Hawaye suka zubo mata na tunawa cewa; wannan dan HALAAL ne a jikinta, wanda kowa zai
karva.
***
A yammacin ranar Abbas ya iso. Washegari suka wuce London. Ga mamakin Lailah Abbas ya
tashi daga gidan hayarsu, gida guda Muslim College ta ba shi a cikin gidajen malamai. Aka
koma rainon ciki, tattali da kulawa wurin Abbas wane na baya, wanda ake da shamaki a cikinsa.
Watan ta guda ta koma Ummul-Kura. Ta karasa rubutunta na (project) ta mika, ta amshi kwalin
Dr. of Philosophy (PhD). Suka tattara suka koma Ingila.
Haka rayuwarsu ke garawa cikin nasara da ci gaba kala-kala. A NHS Lailah ta haifi ‘bouncing
baby’ dinta mai kama da ubansa har duhun kalar.
Abbas ya ba shi sunan Isma’il, a cewar shi shine ya shige masa gaba ya ba shi Lailah a lokacin
da ya riga ya fidda rai.
ABBAS da LAILAH, sun zamo manyan-manyan malaman Falsafa a kasar England, a babbar
Jami’ar Musulunci (Muslim College) da ke birnin London.
Akai-akai kuma suna zuwa gida Najeriya gai da Baffaninsu, da yi musu hidima iyakar karfin
aljihunsu. Balle Egypt kuma da ba sa yin watanni uku kwarara ba su zo ba.
MURFI
A'study’ ya same ta tana shirya litattafanta cikin kabinet, a gefe Isma’il ne (Sayyid) da Khalisa
(Sayyidah) tare da autarsu Najwa suna wasansu cikin na’urar koyon karatu mai Alifun-Ba’aun.
Ya yin da babban yaya wato Sayyid ke gefe yana ta rubuce-rubucen sa, dukkansu basu ankara
da shigowar Daddyn ba, kasancewar kowannen su ya mai da kai ga abin da yake yi ko sallamar
shi basu ji ba.
Ya karasa ga Momin ta bayanta ya rungume ta, kamshin turaren shi kawai ta shaka ta lumshe
idonta tana murmushi.
Ya dora habarshi a kafadunta ya ce, “Momy fatawah nake nema”.
Ta ce, “A kan me Daddy?”
Ya ce, “A kan karin aure?”
Ta zumvura baki ta zame shi daga kafadunta ta ci gaba da shirya littattafanta tana cewa,
“Bani da sani a kan wannan sam!”.
Ya juyo ta ya ga yadda ta yi kicin-kicin da fuska sai ta ba shi dariya, ya ce, “At thirty five Momi
kin girma fa, ki barni in dauki sweet sidteen, ta zo daga Muzambikue yin Diploma, shine nake
neman fatawa a kai.
Shin wanda Allah ya yi wa baiwa da mace mai ilimi, kyautatawa, biyayya, tausayi da jin kai ga
mijinta, tare da kular masa da tarbiyyar ‘ya’yansa da gamsuwar sa a shimfidar su, ta tsare masa
mutunci da dukiya idan baya nan, ta zamo mai himma da kokari ga son faranta masa rai, ta
cancanci ayi mata kishiya?” Abin ma ita sai ya ba ta dariya, ba ta san sanda ta ce,
“Idan mijin butulallen Allah ne, ba sai ya yi mata ba?”
Ya jinjina cikin dariya ya ce,
“Kada fa ki manta, Ubangiji (S.W.T) cewa ya yi, “Ku auri abin da ya yi muku dadi daga
daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hur-hudu.....”
Ta zame cikin sanyin murya ta ce,
“Don Allah Abbas ka auri goma-goma.....” Sai hawaye suka zubo.
Ya kai hannu ya shafo hawayen yana murmushi ya ce,
“Ni din me Lailah? Da za ki zub da hawaye a dalilina? Idan kin ga na hada rayuwa da wata, to
sai a Aljannah, idan Allah ya yi min kyautar Hurul-eeni, sai in hada da ke ta zama
kwarkwara........wannan alkawari ne Lailah. You are more than enough to me......and I’m only
yours!” Ya kara rungume ta. Ta yi murmushi wanda ya fito tun daga karkashin zuciyarta, kaunar mijinta ta kara kwanciya
cikin ranta kamar ta hadiye shi don so da kauna. Sai itama ta rungumeshi sosai. Sannan ta yi
mishi nuni da Sayyid wanda ya aje rubutunshi ya zubo musu ido.
Ya sake ta ya koma gabansa ya zauna, ya kama hannun shi kafin ya yi magana yaron ya riga
shi.
“Me ta yi maka ka sa ta kuka?”
Suka kyalkyale da dariya shi da Lailah. Ya dora hannun daman shi a kan yaron ya ce.
“Ban yi mata komai ba, tsokanarta na yi na ce zan kawo muku Aunty, shine take kuka”.
Ya ce,
“To Daddy ai mu muna son Auntyn”.
Ya ce,
“Ban isa ba Sayyid in yi abin da Momi ba ta so, ko ina so kuwa, balle ma wasa nake. Ba na son
kowa sai Momi.....ni mijin ta-ce ne, ku kawai nake so..... I luv you all......” Ya hada su ya
rungume gaba daya.
MASHA ALLAH LAKUWWATA ILLAH BILLAH![12/17/2019, 17:50] Takori: WASAN KANIN MIJI
SHIMFIDA
1/MUHARRAM HIJIRIYYAH
HANYA MAI HADIN ZUMUNTAR DOLE!
Dare ne mai tsananin sanyi, cikin watan Nuwamba. Hazo ya lullube duhun daren ta yadda ya
fidda launi mai haske kamar hadadden hadari, wanda ya takura da yawa-yawan al’ummar birnin
tarayyah.
Za a iya kimanta lokacin da misalin karfe goma dai-dai na daren ranar Alhamis. Dai-dai lokacin
da LAILAH UMAR BALLAH, matashiya ‘yar kimanin shekaru (25) ta iso filin jirgin saman Abuja.
Laila tashe take da ‘yar madaidaiciyar ‘troller’ dinta ruwan toka a hankali, kamar mai tsoron
kada santsin tangaran din takawa (tile) ya tikar da ita. Rataye a kafadunta na dama, jakar mata ce baka mai girma samfurin (vincci) data hadiye
dukkan komatsanta masu muhimmanci.
Laila sanye take da doguwar abaya da mayafinta bakake wul! Kirar Oman, da takalmi rufaffe
maras tsayin dunduniya. Ta karasa ciki a hankali ta hau kan layi domin mika kayanta ga masu
binciken kwakkwafi na cikin gida (customs) kamin a auna su cikin jirgi. Tana daga cikin
(boarding passengers), masu tashi zuwa kasar England, a wannan daren mai tsananin sanyi,
mai kunshe da dimbin tarihi da kuma sabuwar rayuwa a gare ta.
Da ganin yadda Laila ke shige da ficenta, kai tsaye, babu tsoro, babu dari-dari, wajen mika
(passport) dinta mai dauke da Kambun Sarauniya (UK Visa) gami da katin shaida (ID Card), a
duk inda anka bukaci hakan kamar yadda ka’idar matafiya ta filin jirgin ta shimfida, ka san ba ta
da duhun kai; wato dai ba yau ne ta soma keta hazo ba. Sai dai kuma kallo daya za ka yi wa
kayatacciyar fuskar Lailah, ma’abociyar haske, zati da kamala, gami da kwarjini bayyananne
daga sarkin halitta, ka karanto matsananciyar damuwa, tsoro da firgici, har ma da tashin hankali
gami da matsananciyar nadama tattare cikin fararen kwayar idanunta.
Sai dai kuma ta kasance daya daga cikin irin mutanen nan da da wuya ka karanto damuwarsu a
fuska farat daya, kasancewarta ma’abociyar fuskar murmushi. Duk da haka a yau, babu
wannan murmushin, babu wannan annurin. Kamar yadda zuciyarta ke cunkushe da manyan
al’amura masu girgiza zuciyar diya mace, tare da jefata cikin rayuwar ha’ula’i, haka dan
kankanin bakinta ke tsuke tsam! Kamar ba ta tava murmushin ba a tsayin rayuwarta.
Ta daga kanta sama a hankali zuwa ga allon kwamfutar dake manne a saman kanta, mai dauke
da (travel-routine) na ranar gaba daya. (LONDERS-HEATHROW 12:am), kenan akwai sauran
mintuna talatin a gabanta, kafin su tashi.
Don haka ta bi layin sauran matafiya ‘yan uwanta a sansanin da aka ware domin tsimayen
lokacin tashin jirgi, ta samu kujera ta zauna. Ta bude jakarta ta dauko karamar gorar ruwan
(Faro) mara sanyi, ta murde ta kai bakinta tana kwankwada, cikin wani irin yanayi mara
fasaltuwa. Tsabar kishi ne ko ko gigicewa ce? Tun da ta kafa ruwan a bakinta ba ta iya ta sauke ba, sai da ta zuke robar gaba daya. Gardin
ruwan ya ratsa busashshen makoshinta da bakin cikin DA NAMIJI ya busar rayas! Ya saukar da
‘yar kankanuwar nutsuwa a zuci da gangar jikinta. Ta dire robar a kas, ta aje dogon numfashi,
kamin daga bisani ta sanya fuskarta cikin cinyoyinta ta fashe da kuka. Wani irin kuka mai girgiza zuciya Laila ke yi, wanda ba ta tava yin shi a rayuwarta ba, kamar
yadda tunaninta bai tava bata wai watarana irin haka na zuwa da za ta yi shi ba. Balle a kan
MAZA, da ta raina ma wayau. Domin tana ganin ba ta daga cikin irin matan da ake cewa suna
dandanar bakin cikin DA NAMIJI. Tun da babu ta inda Ubangijinta ya rage ta; tana da kyau,
tana da gata, tana da gishirin rayuwa mai tsada (ilimi). Uwa uba nasabar mafi soyuwar jinsi,
wato Arab.
In haka ne to mene ne silar wannan balaguron gare ta? Zuwa inda ba Uwa, ba Uba, ba masoyi
balle dangi?
Har aka yi kiran (passengers) domin bincike na karshe wanda daga shi sai shigewa jirgi Lailah
ba ta ji ba. A gefenta yake zaune, tun shigowar ta, yana nazarin wata takarda mai dauke da
taswirar Birtaniya ciki da bai dinta.
Ya mike tsaye a yayin da kiran ya tsinkaye shi. Ya dauki jakarshi dake aje gefe mai dauke da
kwamfutar (laptop) tare da shafa aljihun bayan shudin wandon ‘jeans’ dake jikinsa domin
tabbatar da zaman tikitinsa da passport. Ya tabbatar suna nan. Don haka ya bi jerin-gwanon
matafiyan dake shiga jirgi bayan an bincike su. Sai dai har zuwa lokacin sautin shesshekar
kukan yarinyar mai taushi da raunana zuciya, ya kasa daina amo cikin kunnuwansa.
Ya yi taku a kalla biyar zuwa shida, amma ya kasa daurewa. Ya rage sassarfa, kana ya juyo. Ya
kai idanunshi ga sashen da ya barta. Har zuwa lokacin tana nan inda ya barta, har zuwa lokacin
kuma kukan take, kanta cikin cinyoyinta. Babu alamar tana da masaniyar cewa kowa ya tashi
daga wajen ya barta, kai babu alama ma ta tsinkayi kiran da aka yi musu.
Wankan tarwada, dogo mai tsararren tsayi, ma’abocin ingarman jiki. Cikakkiyar fuska mai
yalwar dara-daran idanu da wadatar dogon karan hanci zurr! Kai ka ce saita shi a kai a tsakanin
idanunsa.
Ma’abocin yalwar girar idanu kwantacce, gami da gargasa na gashi a kowanne gava mai
bukatar hakan a jikinsa. Dogo ne sosai mai nitsatstsen taku da wasu irin idanuwa masu sheki
da daukar hankali, kai ka ce ruwan zaiba ne aka diga masu (oily-eyes). Fatar jikinshi shine
bayyanannen sirrin kyawun da Allah yai mishi (fata ce irin mai taushin gani a ido). Sai ko wani
irin haske (cool) mai nuni da gogayya cikin zuzzurfan ilimin boko, wanda dole ne ga duk wani
bakin mutum mazaunin yankunan Birtaniya. Da gani babu tambaya, daga duba na farko, kaga
Ba-kanon usuli.
A sannu cikin nutsatstsen takun shi ya karasa gare ta, ya tsaya dai-dai saitin kanta, ya dau
kimanin mintina biyu a haka kamar mai nazarin, ya kamata yayi mata magana ne ko a’ah? Baya
daga cikin halayyar sa shiga haular da ba tashi ba, kamin daga bisani yayi kundumbala ya yi
mata sallama cikin murya mai taushi. “Kina daga cikin masu tashi kuwa?”
A hankali Lailah ta cira kai, kamar a dan razane. Ta kai duban ta ga sashen da sautin ya fito, ba
tare da duban fuskar mai maganar ba, idanuwan nan farare tas sun canja launi sunyi jawur
tamkar an gumbuda musu barkono.
Ta mai da dubanta zuwa hagunta da damanta, wayam, babu kowa. Ita kadai ta rage, ta yi
hanzarin mikewa ta rataya jakarta ba kuma tare da ta sake duban mai yi mata magana ba. Ta
ce, “Na gode”. Ta wuce babu ko waiwaye.
“Hakika Mallam Nasara kullum kara samun fasahar kirkire-kirkire yake…..”. Laila ta ce a
zuciyarta. “Wato jirgin ma yanzu sai dai kawai ka shige shi, ba tare da ka ganshi ba. Kafar shi
kafar hanyar da ka fito, sai dai kawai ka ganka cikin wani daki wai shi jirgi mai fuka-fukai. Inama
ace yadda yake da fasahar kirkire-kirkire, haka yake da fasahar rungumar kowanne jinsi da
zuciya daya, ba tareda wariyar launin fata ba?
A bayyane yake bature bai tava son baki. Ko ya so shin, akwai voyayyen dalili. Muhimmi shine
idan har ya san zai samu amfana daga gareshi.
An ce an bamu ‘yancin kai amma ba’a daina bautar damu ba. Turawan Ingila basa aiki, kwance
suke a gida, mu din dai har yau mu ke yi musu bauta. Suna kara bunkasa suna kara havaka
muna kara durkushewa. Masu fasahar mu sun tattare a gindinsu suna musu bauta. Suna kara
bunkasa su. Sun ki suzo su gina al’ummar su. Sun kasa ganewa har yau cewa shi dinnan
(nasara) makiyin su ne. Kansa kawai ya sani da al’ummar sa, su ‘bayi’ ya daukesu. A kullum
kara like masa muke muna kara dakusar da kan mu. Bamu da abin koyi sai shi da akidojinsa na
banza, alhalin halakar da kan mu kawai muke yi.
Ta juyar da idanunta ta wulwula cikin jirgin. Daga farkon shi har karshen shi bakaken fata kawai
take hange, musamman kabilar Yarbawa. Suna tururuwar tafiya bauta ma bature. Sun baro
iyaye da kakannin su cikin gonakin kauyuka suna noman Doya, Manja da Cocoa. Don samun
abin kaiwa baki, basa ko tuno su. Jar fatar usli dake cikin jirgin ‘yan kalilan ne, wadanda
yawanci aiki ne ya kawo su Najeriya. Lailah tayi tsaki tare da huci don karin bakin-ciki. To amma
me zata iya a kai? Sai ido sai du’a’i.
Tunaninta ya dawo ga tata rayuwar, da dalilin nata balaguron. Tana da yakinin cewa ba bautawa
Bature zata ba, kamar yadda mutanen mu suka raja’a a kai a UK. Neman ilmi zata. Domin ta yi
wa kanta hukuncin da addini ya tanadar a kanta, wanda ita kanta ba ta sani ba, a yanzun tana
nan a musuluncinta ne? Koko ta fita ne? Bata yarada da cikar imaninta ba….., bata yarda da kanta ba…..! Tana cikin rudani, tana neman
mafita,….. tana cikin nadama, tana cikin tsoron rashin cikar imaninta, tana cikin tsoron
mahaliccinta, tana cikin tsoron anya Ubangijinta zai yafe