Author : Sumayya Abdulkadir Category : Romantic Hausa Novels
wasu ne an bar wasu. Ya yi kira da murya mai karfi....
“LAILAH!”
Kiran ya dauki amon da ya karade ilahirin gidan. Ya sake bude iyakar muryar da Allah ya halitta
masa.
“LAILAHHH! LAILAHHH!!!”
Shi kansa sai da amsa kuwwar ta hargitsa cikin kwanyarsa.
Davas! Ya sulale ya zauna da mazaunansa bisa carpet.
“Me ke faruwa ne? Ina ta tafi? Babu sallama balle neman izini? Wannan ba halayyarta ba ne, ba
ta tava ba, ba ta da kowa a nan sai shi, sai iyayenshi da ke kauye wajen wa za ta je?”
A sukwane ya kara zaro waya ya kira dan’uwansa. Ta yi ruri har ta gaji, ta yi gunji ta yi vurari
mamallakinta ya ki dagawa. Da ya sake kokarin kira a karo na biyar, mai abar ya kashe ta gaba
daya.
Cike da mahaukacin mamaki ya tattara hankali da kuzarinshi wuri guda, ya mike tare da zuwa
ga lokar gado ya dauko makullan motar sa.
Sai a lokacin tunanin Malam Surajo ya fado mishi. Da sassarfa ya fito ya nufi dakinsa, ya idar
da sallar azuhur kenan bai kai ga mikewa daga sallayar sa ba.
Ya tsaya daga bakin kofa ya tokare cike da jarumtakar voye tashin hankalinsa da gigicewar sa.
“Malam Surajo ina matar gidan nan ne? Ko’ina a bude, kuma a hargitse. Kuma kura futuk, anya
lafiya?”
Malam Surajo ya jinjina kai ya dubi ubangidansa a nutse ya ce.
“Yammacin ranar ta yi min alheri mai yawa, irin wanda ba ta tava yi min ba.
Ta ce, “Watakila Surajo wannan ita ce haduwar mu ta karshe. Na yi tafiya Surajo sai wata
rana”.
Ta dauko damin kudi ta bani, ta kuma bani wannan ‘yar takarda ta ce in baka”.
Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki, da kyar ya mika hannun daman shi Malam Surajo ya
daga buzun sallarshi ya ba shi takarda nannade cikin ambulan.
Daga inda yake tsaye ya warware takardar idanunshi na ganinta dusu-dusu.
Mohammed Dina…..!
Na yi tunani iyaka tunani, bincike iya bincike, na kasa gano tsakanin ni da kai WANE NE MAI
LAIFI?
Da na kasa ganowa sai na bai wa Allah zavi. A daren ne kuma na yardar ma kaina cewa
rabuwar mu ita ce mafi ALHERI.
Domin ba za ka tava yafe min ba......nima kuma ba zan tava yafewa kaina ba.
Idan na yi wa kaina hukuncin da ya rataya ga kuskurena, watakila wata rana mu gana.
Ina rokonka idan ka kuma yin wani auren, Mohammed dina....ka yi kokari kada ka maimaita
kurakuranka.....ka rage ‘seriousness’ din nan naka…. ka bai wa matarka kulawa da dukkan
kaunar da take bukata daga gare ka......
-LAILAH BALLAH!
Kanshi ya daure tam, ya yi zafi rau. Ya kai yatsa baki ya ciza da karfi wai ko barci yake ya farka.
Ya tabbatar idon shi biyu.
A karo na biyu ya sake bin kyakkyawan rubutun Laila ya karance tsaf.
“Me na yi miki Lailah? Wane kuskure na yi miki haka da zafi da kika zavi bari na?”
“Ka manta ne? Sarkin tsokanar? Ta saba ‘trick’ kala-kala, yanzu haka tsokana ce kawai take yi
ba za ta wuce wurin mahaifiyarta ba”.
Wani dan guntun sako daga zuciyarshi ya tunasar da shi.
Don haka cike da kwarin gwiwa ya linke takardar ya jefa a aljihu, ya bar dakin Malam Surajo
yana tafe yana kiraye-kirayen waya domin nemawa kanshi tikitin zuwa Alkahira komi dare.
[12/17/2019, 17:50] Takori: ***
Tarba ta musamman Momi Najla ta shiryawa surukinta cikin babban birnin Alkahira. Tun da ya
yo waya cewa ga shi nan a filin jirgi a zo a tarve shi, ita da kanta da kannen Laila biyu Sanah da
Najat da kuma babbabn Yayansu Isma’il suka zo taren shi. Isma’il na tuka motar. Autarsu Najat
ta zo da gudu ta rungume shi da ta hango shi yana nufo su tana tambayar shi. “Uncle Pilot za ka tuka ni a jirgi? Uncle Pilot AINA UKHT LAILAHHH?”
Hankalinshi in ya yi dubu to ya tashi, tsigar jikinshi ya mike, ya kidime ya razane. Wannan na
nufin, Lailah ba ta wurin su.
Da wane ido zai dubi Momi Najla da ta danka mai amanar rayuwar marainiyar diyarta?
Gwiwoyi a sage, gavovi a kassare, ya zube a gaban Momi ya kasa ko gaishe ta. Isma’il ya
kama kafadunsa ya mikar dashi, sai ya fashe musu da kuka.
Kan ka ce meye wannan Najat ta shiga taya shi, saboda tsabar haduwar jinin su, yana matukar
son yarinyar ita ma tana matukar son shi. Ba don komi ba si don kwadayin ya tukata a jirgin
sama, wanda shi ne babban burin rayuwarta.
Momi ta matso gabanshi a hankali, jikinta a sanyaye ainun.
“Haba Mohammad, kada ka yi min haka. Me ya faru da Lailah? Wannan ba girmanka bane.......”
Isma’il ya kama kafadunshi, “Abokina Lailah rasuwa ta yi? Ka gaya mana ai mu musulmi ne,
dukkaninmu sane muke da cewa ko ba dade ko ba jima rai zai koma ga Ubangijinsa!”.
Ya girgiza kai, amma ya kasa magana. A karo na biyu Momi ta ce.
“Mohd. idan Laila mutuwa ta yi kwananta ne ya kare..........!”
Ya yi hanzarin tura hannu aljihu ya zaro takardar Laila cikin ambulan ya mika ma Isma’il, don
baya son wannan kalma ta mutuwa da suke ambatawa Lailansa.
A nutse Isma’il yake karanto ma Momi wasikar Lailah, har ya dasa aya. Dukkaninsu suka yi
zuru! Abin tausayi, ba ma ya Mohd. wanda yake jin kansa a victim na duk abin da ya samu
diyarsu.
Kanshi ya yi zafi zau da tunanin wane kuskure ya aikatawa Lailah da har ta zavi barinsa? Abin
da ko a mafarki bai tava kawowa ba.
Bai tava tunanin dai-dai da rana daya Laila za ta iya rabuwa da shi ba, saboda tubalan da suka
gina soyayyar aurensu ba tubala ne da ake amfani dasu wurin yin aure a wannan zamanin
ba......
Shi kuwa Isma’il dage kai sama kawai ya yi bai san me yake tunani ba.
***
Wani abin mamaki shine, Lailah da abokin tafiyarta duk makaranta daya suka zo, wato ‘Muslim
College, London’.
A tsarin makarantar basa ba da accommodation wato muhalli da abinci, don haka bayan sun
gama da registrer din makarantar (Aaliya Arnall), kai tsaye cikin gari suka fito. Suka yi ‘yan
tsince-tsincen dan abin da za su ci, amma basu shiga ‘restaurant’ ba. ‘SAM CHICKEN, chips,
da gwangwanin ‘pepsi’ suka samu suka ci. Suka koma cikin makaranta inda aka hada su da
wanda zai taimaika masu wajen neman muhalli.
Abbas ya zo neman kwalin shi na Ph.D ne yayin da Lailah ta zo neman kwalin masters. Duka a
cikin makarantar ‘Muslim College’.
Babu jimawa suka samu gidan zama na haya na wasu mutanen ‘Lahore’ a (Acton Town), kusa
da makaranta, don daga nan ko basu hau ‘bus’ ba zasu iya zuwa makarantar a kafa. Dakuna
ciki dai-dai, shi yana a saman bene ita tana kasa.
Kuma a washegari suka fara daukar lectures, maimakon biyan kudin haya duk sati sun dunkule
sun bai wa maigidan (Landlord) kudin shekara daya.
Sai ya zamanto wata irin shakuwa na shiga tsakanin Lailah da Abbas, shakuwa mara fasaltuwa.
Sannan tsaftatacciya, domin kowanne yana ganin mutuncin dan uwansa. Kuma kowannensu ya
san ciwon kansa.
Idan shi ya rigata dawowa zai dafa musu abinci, haka idan ita ta riga dawowa. Tare suke zuwa
‘shopping’, tare suke zuwa cefane, ‘café’ da sauran su, rayuwar su gwanin ban sha’awa kai ka
ce Yaya da kanwar shi ne.
A cikin gidan ba su kadai bane, akwai mutanen India da wata mata ‘yar kasar Somalia. Idan
Abbas shi ya yi abinci sai ya kwankwasa mata kofa ta bude ya mika mata, haka idan ita ce ta yi.
Duk kokarinta na ta yakice Abbas ta kasa, domin mutum ne har mutum, mai tausayi da kyautayi
mai yawan gaske.
Lokutan daukar lakcarsu ba daya ba, don haka a kullum daya ke riga daya dawowa gida.
Wanda ya riga dawowa gida shi zai dafa abinci.
Rayuwar London mai cike da abubuwan debe kewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali, sai ta
taimaka ainun wajen rage ma Lailah dimbin damuwar da take ciki mai neman janyo mata
‘psychological depression’.
A wajenta Abbas (kawa) ne, wato (aboki) kuma mutumin da za ta iya tutiya da shi matsayin
wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rage mata dimbin damuwar nadamar rayuwar da take
ciki.
A hutu na farko da suka samu bayan share watanni uku suna daukar darasi, Abbas ya same ta
a dakin ta bayan ya nemi izinin shigowa.
Suka yi wa juna kyar da ido kamin su sakar ma juna dariya. Ya ja kujera ya zauna yana mai
fuskantar ta.
“Ko zan samu dan rakiya?”
A sanyaye ta ce, “Zuwa ina?”
“Zuwa ‘Lake-Windermerre’ a Cumbria, picnick nake bukata Lailah. Kwakwalwata tayi zafi, karatu
yayi yawa a cikinta so, ina son samun ‘peace of mind’ (hutu) koda na yini daya ne.”.
Cike da murmushi ta aje littafin da take nazari ta ce.
“Bani minti ashirin na kintsa”.
Ya fita ya ja mata kofar ya ce,
“Plz… hurry”.
Ta jirgin kasa suka bi zuwa ‘Cumbria,’ kauye ne awa ashirin da hudu (24 hours) daga London.
Ga alama hakanshi zai cimma ruwa ya samu Laila ta bayyana mishi tarihin rayuwarta da ta
voye ko zancen, ba ta so.
Domin a ganinta ta riga ta tsere, ta yi nisa da rayuwarta ta baya. Wannan karon ma suka hau
jirgin kasa ta hanyar amfani da ‘oyster’ dinsu. Rataye da ‘picnic bags’ dinsu. Mai dauke da
abinda zasu ci, da wanda zasu sha, ‘camera’ da sauran su.
Lailah sanye take da bakar ‘coat’ wadda ta zo har gwiwoyinta da bakin wandon ‘channel’. Ta
yane fuskarta da kankanin gyale daga ‘pashmina’. Ta saje tsaf da turawan Ingila, ta yadda in ba
fada maka aka yi ba ba za ka iya tsince ta daga cikin su ba.
Yayin da Abbas ke sanye da shudiyar suwaita long sleeve da bakin ‘jeans’ shima, kai da
ganinsu ka ga ‘students’ zaunannun Birnin Sarauniya.
Zaune suke a bakin ‘Lake’ din kafafunsu duka cikin ruwan. Abbas ya dube ta da kammalalliyar
fuska, ta samu kanta da jin wannan mutum kamar Yayanta Isma’il, zuciyarta ta amince da shi.
Ita kanta bata san dalili ba.
Ya ce, “Lailah is high time in ji abin da ya rabo ki da gida, ko zancen wani da ya shafe ki baki
tava yi min ba. Jikina ya bani ba haka kawai cikin dadin rai kika zo karatu kasar nan ba. Is this
friendship?”
Ta ce, “Zan gaya maka Abbas, duk da cewa ban san karvar da za ka yi wa labarin ba”.
****
FARKON LABARIN
Haduwata da Mohammed, a babban filin jirgin saman Egypt ne (Cairo International Air-port),
za mu raka mahaifinmu zai tashi zuwa kasar Najeriya. Mahaifinmu dan uslin kasar Najeriya ne,
dan Kano, amma mazaunin Egypt, tun daga zuwa karatu ya samu aiki saboda kyawun
takardunsa. Likita ne kwararre a ‘general hospital’. Ya yin da mahaifiyarmu ta kasance ‘yar
usulin kasar Egypt. Ya aure ta tun auren saurayi da budurwa.
‘Patient’ dinsa ce tana da ‘ulcer’, ya kasance duk wani ‘treatment’ dinta a hannunsa yake.
Suka gina ma zuciyoyinsu wata irin soyayya wadda daga iyayenta basu samu wata matsala ba,
wai don kasancewar shi ba dan kasa ba.
Shi daman maraya ne ba uwa ba uba. Sai Baffanninshi biyu a Kano. Suka yi aurensu a nan
Egypt ya sayi babban gida a can suke zaune cikin soyayya da amana.
Isma’il shine babban dansu, sai ni, sai ‘yan biyun Momi Sanah da Najat. Mohammed matukin
jirgin sama ne, wannan shine babbar matsalar da muka fara cin karo da ita a rayuwar aurenmu.
Shi Mohammed dan asalin garin Bauchi ne, wani gari Jama’are. Su biyu kacal iyayensu suka
haifa daga shi sai kanin shi Sa’eed.
Akwai rata sosai ta shekaru goma tsakanin Mohammed da Sa’idu. A lokacin da aka haifi Sa’id,
girma sosai ya cimma mahaifinsu Malam Yahya, wannan ne dalilin da ya sa Sa’eed ya dawo
hannun mu da zama lokacin yana karatu a Tafawa Valewa University Bauchi.
Mohammed ya ware ma Sa’eed dakin zama a boys kuaters, ya fara karatunsa cikin nasara.
Inda yake karantar ‘Geography’. Wankan tarwada ne mai kyakkyawar sura, yana da
kazar-kazar da fara’a mai yawa, yana da kirki da ladabi ga dan uwansa, da ni da nake matsayin
matar Yayansa. Kirkin Sa’id ne ya sa muka zamo wasu irin aminai, duk abin da ke damuna kafin Mohd ya sani
na fadawa Sa’id.
A ganina shine mai lokacina, saboda mijin bana jin dadin sa. Mohammed, wani irin mutum ne
tough, serious, ba shi da lokacin iyalinsa ayyukanshi na tuki suna gaba da komai.
Sai ya yi watanni uku yana yawo a duniya. Da fari na uzurce shi da cewa yanayin aiki ne, amma
a matsayina na mace mai jini a jika wannan aikin na Mohd. na ci min tuwo a kwarya.
Farkon auren mu ya zamanto ba haka bane, don a lokacin yana fafutukar neman aiki ne muka
gamu. Da ya samu aikin ne abubuwa suka sauya, don haka zuwan Sa’id gidan mu ba karamin
farin ciki hakan ya haifar min ba.
Digirina na farko na yi shi ne daga jami’ar Al-Azhar a kan Falsafa (Philosophy). Ina matukar son
mijina kwatankwacin yadda yake so na. Domin a kan soyayya da kauna muka gina auren, tun
mahaifina yana raye. Mohammed ya dauki son duniya ya dora a kaina, sai dai kuma abin
takaicin ba shi da lokacin da kowacce mace take bukata tare da maigidanta, yana hadawa
kanshi zafi da yawa kamar shi kadai ne matukin jirgi a duniya. Daga baya ne Sa’id ke yi min bayanin ai bayan Virgin Atlantic da yake wa aiki wasu kamfunan
daga ko’ina irin su MEA, KLM, Royal Air Moroc, da sauransu suna daukar shi haya saboda
kwarewar sa.
Amma a matsayina na matarshi abokiyar rayuwarshi bashi da lokacin da zai zauna ya yi min
wannan bayanin, sai dai kullum ya ce bana yi mishi uzuri da yawan ayyukan da ke gabansa.
Sa’eed ya dawo makaranta a wani yammacin Litinin ya same ni a kitchen, yai sallama ya shigo,
ya karve ni a firar dankalin da nake yi.
Ya ce, “Gaskiya Aunty Lailah ya kamata a samo miki yarinya mai aiki mace kina wahala fa, ke
kadai a gidan nan”.
Na ce, “Da hakan za ta faru da na yi murna”.
Ya ce, “On weekend, (cikin karshen sati) zan je Jama’are zan fadawa Hajiya za a samu insha
Allah”.
Na ce, “Na gode”.
“Yaya bai yo waya ba? Ina so in mishi zancen kudin ‘registration’ ne. Kin san an ce shekarar
kwana gashi har shekara ta zagayo za mu shiga level 300”.
Na ce, “Har nawa ne?”
Ya ce, “Bai kai 20 thousand ba”.
Don haka a daren ranar na kirgo kudin registration na ba shi cikin kudin da Mohammed ke bar
min.
Ban rasa ci ba, ban rasa sha ba, ban rasa suttura ba, amma na rasa soyayya da kulawar mijina.
Sai Sa’id ya zamo wani mutum mai kula da ni da debe min kewa, ta hanyar irin wasannin nan
na kanin miji da barkwanci ga matar Yaya.
Shakuwar mu da Sa’eed din har ta zarta misali, saboda yadda yake nuna min kulawarshi a kan
al’amura na da damuwarshi a kaina.
Idan ka ganmu a kanti muna sayayya ko a kasuwar wunti muna cefane sai ka dauka mata da
miji ne.
A satin muka shirya tafiya Jama’are ni da Sa’eed gaida Hajiyar Mohd. Hajiya ta rasa inda za ta
sani don murna, ta kuma rike ni sai na kwanan mata biyu. Don ita kanta wannan yanayin aikin
na Mohd. na damun ta, don dai ba yadda za ta yi ne.
Da daddare mun yi shirin kwanciya Hajiya ke yi min nasiha cikin hikima na in kara hakuri da
yanayin aikin Mohd. Ita kanta ta damu, to amma yaya zamuyi? Tunda dai hanyar abincinshi
kenan, kowa da inda Allah Ya tsaga mishi hanyar abincinsa.
A raina na ce, “In ban yi hakurin ba ya ya zan yi? Ya riga ya rabani da uwata da ‘yan uwana,
kuma ba shi da lokacina.
Idan dai don kudi ake wannan aikin babu samar ma kai da zuciya, kwakwalwa hadi da gangar
jiki hutu, sai in ce ban san inda Mohammad zai kai kudin da yake samowa ba”.
A kan hanyarmu ta dawowa Sa’eed ya dukufa lallashina, don ko fuskata mutum ya kalla ya san
ina cikin matukar damuwa.
Yake ce min, “wata rana sai labari Aunty Lailah, ki kara hakuri a kan naki na da, shi Yaya da
kanshi zai gane wata rana ba ya kyautawa, ya ragewa kanshi aiki ya rungumi iyalinshi, in kuma
kin amince in yi mishi magana to, duk da yana daga cikin irin mutanen da da wuya ka doshe su
da irin hakan”.
Ban ce komi ba, abin da na sani shine, auren Mohammed ya fice mini a rai, burina tunda ba shi
da lokacina, to ya sallame ni in koma cikin ‘yan uwana gaban mahaifiyata, duk da bai tava
iyakance min zuwa ganin su ba.
Shakuwar mu da Sa’eed sai abin ya kara gaba. Ya zamanto girki ma wannan tare muke yin sa,
kallon kwallon kafa da daddare duk tare muke yi, kamar wasu mata da miji.
Har na kan kissima a raina wani lokacin ni kam da ma Sa’eed aka aura min da na more. Duk da
yake yaro dan shekaru ashirin da bakwai ya sn yadda zai yi ya tafiyar da mace da nuna mata
abin da ta fi so a gidan aure, wato soyayya da kulawa.
Za ka so ganin mu muna kallon ball har da tafawa, saboda shi dan ‘Arsenal’ ne ni ‘yar ‘Real
Madrid’, mu takarkare mu yi ta musu kowa yana kare kungiyar sa.
Mu yi girke-girke mu ci, a karshen mako mu yi ‘sanitary’ mu gyare ko’ina na gidan mu.
Yana da yawan zama a ‘study’, musamman lokacin jarrabawa ba ya wasa. Yaro ne haziki mai
kirkin gaske da saurin shiga rai.
A satin da su Sa’eed suka fara zangon karatunsu na farko a level 300, Mohd ya iso, kai