Chapter 9 Reading IDAN KAYA YA GAJI Farashin cin amana By Mrs BUKHARI HN Novels

IDAN KAYA YA GAJI Farashin cin amana By Mrs BUKHARI

Author :  Mrs BUKHARI Category :  KDP NOVELS

Chapter   9 / 15

24K to 27K   out of 42.4K words

da gas kuka na da silinda haka. In ya dawo mayo cefanen kayan

abinci dan wallahi kayan abincin Sarayina sun haramta a gareni da ragowar kab abinda ke cikin Sarayin nawa su Adama zasu tafi da kaya rigi _rigi kuwa. Nasan dai zaiyi wuya ama gas kuka asiri da tukunya baya ga su ban yadda da komai ba. Ga babbar sar™ar gwal Wina tana gidan Allah ya soni azurfar wajen

Goggo tana cikin han bagi na Wayan gwal Win na wuyana.

Maigogul na kira a waya ban rufe mishi komai ba kamar yadda kuka sani.

"""Kinyi kyan kai. Nima dani za'aje Wiban wannan kaya Sabuwa tun a cikin gidan za'a watsa musu fitsari"

kafin a taSa. Na haWo miki itatuwa da zaki daddafa ki dinga shansu tsarine da izinin Allah babu fa shirka ko kaWan a lamarin. Kinsan dai ba'a faWama Bararo magani ba ko?

Shi kanshi gas kuka ki tottofeshi da adda'a kafin kiyi amfani dashi. Babu komai.

"Ita kuwa Hauwa akan wannan Abun kinji na rantse saina saketa ta WanWani zafin zawarci, ina na dena"

barinsu Kayi nayi kaWaima ta isheta Allah.

Ita kuwa Shuwa taje dan kanta ruwa cikin cokalima ya ishi mai hankali.

Abinda nake sonki dashi shine kinga tunda kin matsa gefe to sai fa dagewarki tafi ta baya Lolo. Sabida

"kafin mijinki ya dawo gidanki tsab za'a iya wanko mishi kai yama fitittike yace bai sanki ba, koma yace ya sakeki bafa komai bane."

Bacci bai gammu ba Lolo dole mu dage muita faWama Allah muci gaba da tuba a bisa laifukanmu na baya.

Hajiya Balaraba gobe da safe zata tawo ita da ma'aikata ai miki sabon jere ni zan biya kuWin Lolo in sha

"Allah."""

Mun daWe muna waya kafin mukai sallama.

Sai na shiga aikace_aikacen gida kuma.

"Alhaji Zaidu bashi ya shigo ba sai bayan isha ya tawo mana da gashasshiyar kaza, sai kayan shayi da"

biredi da ruwan gora da lemun gora.

"Kazar muka ci muka baje mukaita hirarmu, kana muka soma karatu da koyon ba™i sabida yace so yake in"

fahimci karatu ta yadda bazan sha wuya ba. Hanya mafi daWi itace in iya ba™i.

Bayan mun gama karatu kuma muka shiga raya dare muka wayi gari cikin farin ciki.

"Kuma banji wannan irin abunda na ji jiya ba da daddare na sha rubutuna na shafe jikina dashi, kuma sai"

dana tsarkake jikina na kwanta ina daga kwance inata ambaton Allah har bacci yayi gaba dani.

Wannan kenan.

Gaga_gaga da safe muka wuce sabon gidana gas kukan ma ko sakko dashi ba'ayi ba. Ruwan shayi na

dafa mana a butar shayi na wuta dake Kitchen Win. Na Sare sababbin kofuna a leda na Waurayesu da tafashasshen ruwa muka sha shayi da biredi sai ragowar kazar da muka bari.

Muna gamawa muka tattara komai muka wuce.

Mun yi waya da Hajiya Balaraba ma suna hanyar zuwa can sabon gidana dake unguwar Tarauni.

Kusan minti sha biyar ne a tsakaninmu mun iso suka iso.

"""Wazirat to ni zan wuce office kawai Hajiya tace zan kawota amman sai da daddare. To zan zo in kawota"

"in sha Allah. Me da me kuke bu™ata na cefane tunda su Yaya Adama suna hanya? """

"To shikenan Allah ya kaimu, ashe fa yau a wajen Hajiya kake. Allah sarki ni, yau daga ni sai fulo kenan"""

Murmushi yayi mun ya kalleni sosai.

"""Shalele rigima kenan. To su kayan da su Yaya Adama zasu Webo yaya za'ayi dasu ne uhm? Naga ga"

"sababbin kaya kince Alhaji Baba ya baki uhm"""

Hakane. To su Adama ne zasu raba a tsakankaninsu gaskiya kaji yadda za'ayi dasu. Kayan abinci kuma

"kayan miya nake bu™ata da su nama dai haka sai ruwa da lemo"""

Bana so ince harda su shinkafa da mai ne ya soma zargin wani abun in kirama kaina ruwa inya fita na

saka a siyo tunda akwai kuWi a wajena.

"""To shikenan Abinda za'ayi zansa yara su kawo muku Shalele ni na tafi sai mun yi waya"""

Da haka mukai sallama ya ja motarshi ya tafi.

Gas kuka kuwa kamar yadda Maigogul yace sai da na tottofeshi fes kafin na wankeshi tas da ruwa a

tsakar gidan.

Hajiya Balaraba kuma tana ciki tare da ma'aikata tana basu oda. Ma'aikatan nata na tura kasuwa suka

siyo mun kayan hatsi komai da komai. Da yaran Alhaji suka kawo cefane sai na tashi girki.

Gaga_gaga cikin awa Waya da rabi aka gama komai falo ya Wauki fasali har turarukan B4B gidan ™amshi ta

kuma kawo mini box guda kuma tace dani show glass yana tafe.

"""Naji labarin komai. Kinga munubiya tun muna makaranta macace mai son mulki da son kanta sosai,"

gata da mugunta hatta a kalaman bakinta babu alkhairi sam. Wannan dalilin yasa bana cikin sabgarta kwata kwata ai na faWa miki.

Adda'a zaki ri™e babu mamaki wa'adinta ne yayi. In kuma da rabo sai kiga kin haihu dashi ke Win. Allah

"Ameen da munyi farin ciki Hajiya Sabuwa"""

Gaga_gaga da misalin ™arfe biyar na yamma sai ga motar kaya tare da motar su Maigogul. Mu muka

buWe musu get aka zube kaya kwatsar a tsakar gida harda suturun dake sib dana akwatinan da Hajiya tayi mun dan ba kayan ciki kaWai ba har akwatin banso wallahi.

"Sai dai fa sar™ar gwal tayi layar zana basu ganta ba sam. Magazin da Ma'aru ma sun biyosu, a mata"

"Kuma Adama, Labbai, Rahama, Uzairu muzuru da Gaza yace ayo gaba dashi harda sar™a aka saka mishi a wuya sabuwa. ³an uwa masu daWi sai naji sun zabtare mun rabin damuwata."

"""Wannan kayan gado dai zasu koma show Room in da ciko sai in yi ma Hajiya. Ragowar karikicen Kitchen"

"da suturu, da kayan abinci, da waWannan kayan fulawa na biki kuma rabon su Adama ne sai su wauwanke su shanya duk su bushe dan fitsarine linkib a jikin suturun. Kuma harda laya gata a ™ar™ashin gadon lolon muka tarar harda sunan lolo da sunan Alhaji Zaidu a cikin baka kun ganta"""

Maigogul ya ciro ba™ar leda a aljihunshi ya warware mana muka ga layarnan jikina yayi sanyi ™alau

"wallahi."""

Sai da suka gama wauware kaya suka kasafta tsab suka wanke hannuwansu muka shiga ciki muka baje

aka soma liyafar cin abinci sai santin gidan suke yi dan gaskiya gidan yayi ga falon yayi biyun wanda na baro haka ma Wakunan tabka tabka komai a yalwace.

Šakina kaWai aka saka kayan gado ragowar Wakuna ukkun a haka aka barsu sai kafet malala a ciki kawai

dama a ciki muka taddasu.

Bayan magriba sai ga Alhaji Zaidu shi kaWanshi da leda mai zane sha™e da ban™ararrun kaji da jus_jus ya

"shigo, amman shi shi Waya yazo shi banda Hajiya ko me ya faru oho dai."

Haka ya shiga cikin dangina yana ta murnar ganinsu tare da martabasu a yadda sukensu.

Ya Wan jima kafin yayi mana sallama akan sai gobe da safe zai zo. Na bar maganar gwal ne akwai gaSar

da zanyi mishi maganar in ya dawo gidana kafinnan ya nitsa. Ni da Maigogul mukai mishi rakiya zuwa gaban motarshi.

"""Dama akwai wasu sa™e sa™i dana sassa™o muku a jeji da hannuna na haihuwane. Lolo sai ta dafa muku"

"ku dinga sha musamman kai ka zage ka kakkaSa muna sa ran in sha Allah za'a dace. Kasan da nayi harkar bada magungunan kurga, da amagyagya na yara, to bada taimakonma na taSa wallahi denawa dai nayi"""

Ya ™arashe yana dariya.

"""Mungode sosai Alhaji Baba. Matsalar ma daga garenine ina kyautata zato zan kuwa zage in sha in sha"

"Allah. Kuma wallahi naji daWi sosai a baya ma duk na sha daga baya ne na watsar."""

"""Hahahahhh babu komai. Sai dai gaskiya kullum ake so a sha shi babu fashi duk da kullum zaku haWu"

babu matsala tunda wajen aikinku guda ko. Ai hai™an zakai ta sha za'a dace da izinin Allah.

Itama fa mai Wakina Hauwa wallahi na saketa sabida ba ma Babar ³ar shuwa lambarka da tayi. anyi rikici

"a gidan sosai, harma shi babban Wan Hauwa Masa'u wai zai sassareni ko ya turo a sace ni. To ni dariya ma ya bani, Allah na tuba wanne iya shege ne bamu gani ba. To ita Uwar taku dai har gidan uwar ³ar shuwa taje aka raba garin tsiya, mu dai rigima bata lafa ba har yau Winnan. Itama ³ar Shuwan wai ta"

"dawo gida, ko da takadda, ko hutu aka turota tayi ba dai mu sani ba. Ka dai sake ha™uri dan Allah"""

Alhaji Zaidu yace.

"""Ashsha Alhaji Baba. Ko dan albarkacin yaran da an duba ba'a saketa ba. Ayi ha™uri a mayar da'ita dan"

"Allah. Aba Mama Ha™uri itama duk a huce babu komai wallahi."""

"""Ai fa baka sani ba Gaza har gidan Malam Habu ya burma dake ya raka ita uwar tashi, shi dama ba"

"sonmu yake yi ba, ana faWan ya fito yana aibatamu dawa Allah ya haWashi da Gaza.. """

"Maigogul dare yayi ka barshi ya tafi"""

"""Rai a Sace Omri ya dubeni harda hararata, amman ta gargaWice."

""" Toh hakane Alhaji da Alkhairi"""

Maigogul dai ™in bamu waje yayi tare muka koma ciki

Sai wajajen goman dare Maigogul da Hajiya Balaraba suka tafi Uzairu zuchiyata yace a barshi zuwa jibi in

su Adama sun tafi ya dawo.

Ai suna tafiya muka dasa hirar rikicin Hauwa da Maigogul da Kayi nayi.

"""Ke anyi abu. Kayi nayi har waje ta ja Hauwa suka fita dambe da ™yar ma™ota suka raba. Layuza dake"

bata da mutunci tace yau Winnan zata kama ma Hauwa gida su koma gabaki Wayansu ke kiji neman fitina.

Masa'u kuwa saida Gaza ya karza wu™a yaga tayi wal™iya sannan ya fita a gidan. Cacar baki sukaita tatayi

"da Maigogul."""

Rahama ke bamu labari.

Labbai da Uzairu zuchiyata kuwa kun ga dariya wai kuwa haWe kai suka yi sukai ta ™ya™yatawa.

Adama tace.

"""Rakiya ta ™arama rigima maggi. Wai Gaza ne yai nata Rakiya layinmu na da."

Ta faWa gidansu ³ar shuwa shi kuma ya faWa gidansu Malam Habu daya fito yana ™ananun iskanci Suka

"raba abun kunya dai in faWa miki dattijan anguwa dana ma™otan unguwama da ™yar suka raba rikicin. ³ar shuwa dai ana raWe raWin Babangida ya saketa amman babu tabbas gaskiya."""

Kunsan mune har biyun dare muna musu da dariya.

Sai wajajen biyu da rabi Uzairu zuchiyata da Ma'aru suka shige Wakin hagun Wakina suka bi kafet sukai

kwanciyarsu gida to babu.

"Su Labbai kuma gado suka haye, ni kam sai da nayi sallah na sha maganina na shafe jikina kafin na yi"

kwanciyata a ™asa su na basu gadon sai tusa Adama take sakar mana ta cika Wakin fal da wari.

Murmushi nayi na tuno shekaru talatin baya a lokacin duk muna gida muna irin wannan gwamutsuwar

ta bacci muita tusa abinmu.

Rayuwa kenan.

"Gaga_gaga sai da muka kwana biyu cur dasu Adama, washegarin ranar da suka zo suka tafi kasuwa ai"

"kuwa Labbai ma ta samo gyaWa mai sau™i rabin buhu ta siyo, Adama tayi tsince_tsincen kasuwancinta su Rahama kuma suka zama ´an rakiya da su Uzairu zuchiyata daya aro motar Mum ta wajenshi."

A ranar ´an Rano a gidana suka wuni cur mukai zumunci sunata santin waje sosai.

Washegari kwana biyu kenan su Rahama suka tattare kayayyakin dana rabar musu suka kama hanya

Omri yai musu goma sha tara na arziki Maigogul ya kaisu har tasha.

"A kwana biyun na dafa mana magungunan haihuwa da Maigogul ya kawo mana, in Omri yazo da safe sai"

ya cika kofi tam ya shanye nima yace in sha ko babu komai zai gyara mun mahaifa tunda mahaifar dama tana da matsala.

Da yamma ranar da Omri zai dawo gidana a ranar da su Adama suka tafi.

"Na gama komai na gyare gidana na banka ™amshin turare, girkina na kammala na jera komai a ™asan"

kafet ina gaban mudubi sai naji anata doka get wani irin duka da rashin mutunci dai.

Hular dake ajjiye a gaban madubin na saka.

"Ina saye da riga da wando na kanti sun kamani tsam, fuskata na caSa ado ga wannan azurfa a kunne da"

wuyana.

Sanin babu mai gadi a gidan yasa na fita a yadda nake. ˜ofarnan dukanta akeyi.

"Waye yake buga ™ofa haka? """

"Hajiya munubiya ce. Kina ciki anata buga ™ofa bakya ji? """

"Sakatar ™aramar ™ofa na Salle muka haWa idanu da'ita tana tsaye da ™awarta, ga motarsu a bakin ™ofar"

gidan.

HaWa idanunmu sai naji kaina ya sara na Wanji juwa kaWan.

"""Ko zaki iya buWe mana get mu shigo da mota? """

"Inaga sai dai ku barta a wajen bazan iya buWe wannan ™aton get Win ba"""

Hajiya Mansa ke magana cike da ta™amar da zaka rantse itace a matsayin Rakiya ko Maigogul.

Sai ita Hajiyace tace.

"""Bari mu bar motar anan. Ai ba zata iyaba"""

Waje na basu suka shigo na rufe gidana nayi gaba suna bayana. Har muka shige cikin falon.

Numfashi naji Hajiya ta ja mai nauyi sosai.

"Ruwa na kawo musu na zauna aka gaisa babu yabo babu fallasa. Sai tambayoyin ina kayana suke to, taga"

na sake wasu yaushe yaushe da Aure.

"Ta le™a Kitchen ta le™a Wakunan dake tsakiyan nawa, zata buWe mun Waki na ri™e abun buWewar nace."

"Nan Wakin mijinane Hajiya"""

Sai ta wayance dai mukai dariya.

"Ko dana basu abinci basu ci ba, bafa su daWe a gidan ba amman a ranar na shiga sabuwar jarabawa kunji"

wata ™addarar ko?

Rimi_rimi Alhaji ya dawo muka tarbi juna cike da farin ciki muka ci abinci akai komai fa.

Wallahi a wannan daren ni dai ™aramar hauka nayi na dinga ihu ina fisgewa zan fita daga ni sai rigar

bacci duk na firgice.

Da Alhaji ya ri™eni sai nayi kukan kura na danna ihu in sha™eshi da ™yar zai ™wace yana yi yana adda'a

yana tofa mun.

Wallahi kafin asuba duk na jij ji mai ciwo ma™ota kuwa duk sun san abinda ke faruwa damu.

Ana ™wala kiran assalatu wallahi Allah sai naji kamar abu ya fita a jikina sai na dawo hayyacina.

Ganin Alhaji duk na yakushe mishi fuska nima duk naji ciwo ga jikina duk tsami sai na fashe da kuka na

faWa ™irjinshi.

Kunji fa wata ™addarar.

"Haka ni dashi muka rufe na ranar farko, ya shirya muka tafi aiki tare, kafin muje aikin sai da muka je naga"

"likita a wani asibitin kuWi, magunguna dai ya bani bayan ya mun tambayoyi da gwaje_gwaje, sai muka wuce wajen aiki muka wuni lafiya."

"Da misalin shidan yamma muka dawo, muna shigowa ban zauna ba na shiga Kitchen. Zuwa bayan isha"

na sarrafa mana shinkafa da miya.

"Muka ci, na sha magunguna mu kai shirin kwanciya. A wannan daren abinda ya faru da irin ihun dana"

dinga yi wallahi saida ma™ota suka fito. Ya fita ya samesu ma ya kasa.

Abubbuwa a haka suka ci gaba da tafiya dole saida Maigogul suka san halin da nake ciki har Baba malam.

Sai aka ala™anta hakan da aljanune suka shafeni nan kuma hankula suka tashi na shiga shaye_shayen

magani afujajan. Sai Rahama ce ta tawo ta zauna dani a cikin gidannan.

"Amman Maigogul da Baba malam basu zauna ba, Baba malam har sau biyu yana zuwa dubani, ina shan"

rubutu

"Ina sauraren Qur'ani, Alhaji Zaidu yanai mun tofi duk kwanan duniya. Ga sa™e_sa™in Maigogul da wasu"

magungunan karya sihiri.

"Amman wallahi ciwo sai girmama yake yi, da safe fa amma babu wata matsala sai da daddare ciwo yake"

tashi.

"Amman da Baba Malam yayo mun wasu rubutu ya kawo sai na dena ihunnan da fisgewa, amman fa nike"

nan firgita da ™an™ame Rahama ko Omri in ranar kwananane yazo ga mafarkai masu tashin hankali.

"Kuma wani ™udurar Allah da Hajiya da dangin Alhaji basu da masaniyar halin da nake ciki, ko da yake ita"

tafi kowa sani tunda ita tayi.

Sai dai duk wanda ya ganni yasan banda lafiya idanuna sun firfito sosai. A haka bikin Uzairu zuchiyata

yazo ina babu dama inaji ina gani akayi shagalin da akayi bana wasa bane. Sabida rashin lafiyata babu wanda ya iya raka Uzairu zuchiyata Canada hankulan dangina yana kaina kacokam

"Ita kanta Mardiyya biki ya ™arato jikina ba daWi sam. Gaza ma gari gari yake zuwa karSo mun magani,"

amman abinda na yadda dashi lokaci Allah ya arama Hajiya. Akwai lokacin da ko ban sha komai ba zan warke da izinin Allah.

"A dangin su Alhaji dai wani biki suna ina daurewa in shiga taron a hakan, tunda ba magashiyyan nake"

"kwance ba, ba dan faWawar da nayi ba babu mai gane ina cikin halin ciwo ma, Goggo Amfana ita ma ciwonta ya tashi bata gane ma wake kanta baiwar Allah. Ita kuwa Hajiya da ka kalli fuskarta sai kaganta a cikin farin cikin ganin halin da nake ciki. Kana kallon makashinka baka da abinda zaka yi mishi wata shari'ar sai Allah. Tazo gidana a ™alla yafi sawu goma tunda ita ba za aci gaba da Soye mata banda lafiya ba. Har ranar da suka haWu da Anty Tani itama tazo Rahama ke sanar mata banda lafiya. Da Hajiya tazo"

sai Anty Tani tace.

"""Koma menene yake faruwa da matan Zaidu mu mun barma Allah ne bawai dan bamu da hankali ba"""

˜us Hajiya tayi ba amsa.

A haka bikin ³an Tagwayen Anty Tani yazo daf dana mardiyya Sadiya ce ta rakani muka je akayi komai

dani a daddafen.

Da bikin Mardiyya yazo Alhaji sai ajjiye aiki yayi ya biyoni muka tare a hotel dan kawai ya kula dani.

Allah sarki bawan Allah baya nuna gajiyawarshi sam wallahi.

Haka akayi bikin Mardiyya a gidansu Baba Malam. A lokacin ma na Wan ciko na sake haske ashe

Soyayyen cikine a jikina babu wanda yasan da bawan Allah. Kunji ™addara a cikin ™addara ko?

To wannan ciki yasa nayi kyau babu laifi haka muka shiga cikin su Sa'a akayi biki. Su Adama ne akan

komai ni sai ido ga ciwo ga laulayi gashi bana son shiga mutane sam.

Su Hameeda sune iyayen Amarya da su Sumy da Hala duk mun haWu dasu gaisuwar mutuncice ta

"rabamu, ³ar shuwa da danginta kuwa babu mutum Waya ma."

Kwana biyu akayi aka gama biki duk abinda uwace ya kamata tayi to Alhaji Zaidu ya fansheni an yi mata

"komai Aure na gata sosai akayi mata. Baba malam yayi rawar gani, haka shima Babangida ya fitar da'ita kunya sosai. Ta tare a gidan mijinta daya gina nan kusa da su Sa'a"

Malama Babba ma naga duk ta rame tayi duhu wannan isar duk babu ita

Rayuwa kenan kayan Allah.

Maigogul dai kusan kullum sai yazo ya kawo magani ko yazo ganina.

Ranar Juma'a ina zaune a falo na gama she™a amai na fito na zauna jagwab sai muka jiyo sallamar

Maigogul ™ur yayi mun.

"""Lolo naga cikin ki kamar ya Waga kumburi yayi ne?"

Sai ni da Rahama mukai saurin duban cikin Rahama ta latsa sai ta zabura.

"""Maigogul ai cikine da'ita"""

"""Tsarki ya tabbata ga Ubangijin kowa da komai"""

Mrs Bukhari ce

"[10/27, 8:49 AM] BADA'AT IBRAHIM: MRS BUKHARI"

9

Kunyi ready ku koyi skill Win da ke kawo kuWi!

"Idan kuna son ku iya yin voice over kamar masu tallace-tallace,"

ko ku iya video editing kamar professionals 

to wannan class Win naku ne!

Za ku koyi:

" Voice

9 / 15