Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
ta, shine Mukhtar din ya ce sai an fara dangana ta da mahaifiyar ta
kafin tarewar ta. Wata irin soyayya da kaunar Mukhtar ta zo ta lullube Jalan, sai ta tsura masa ido tana
murmushi tana jin wani irin son sa a ran ta, kwatankwacin yadda ta ji Amani yanzu a ran ta, tace
da Faytoory, tunda haka ne ai ita ce da masaukin su su duka, akwai bangaren maigidan zata
bashi ya sauka, in ya so in zasu koma Katsina sai Malam Abdussalam ya zo ya tafi da su filin
jirgi.
Ai Amani da jin Jalan tace haka ta zaburo ta kuma zumburo baki tace wallahi na zo kenan. Ni
da Nigeria har abada! Daddy ya daina so na, me zan koma in yi? Shi dai ya koma, shine dan sa
yanzu ba ni ba. Ai tun baa je koina ba Jalan ta kai wa bakin Amani mahangurba da hannun
daman ta, ta kuwa same shi a daidai, tana fadin ke kuma ashe baki da kunya? Mijin naki kike
wa magana haka babu ladabi babu ganin girma?
Hausar Jalan bata da karfi sosai amma sun gane abinda take fadi din, duk da cikin yaren Krio
ta karasa fadin bazamu shirya ba ni da ke idan ba ladabi ga babba!.
Mukhtar sai ya dago da kyar don kunya ya ce mata ai shi a gobe zai koma Katsina, sabida ya
baro ayyukan kamfani da yawa ga Alhaji ba lafiya, don ma dai yanzu ya samu dan sa Kamilu na
kula da shi. Amma Mukhtar ya zabi komawa immediately ne don har zuwa lokacin a cike yake
da Amani. Ya san Alhaji bai da matsala yanzu tunda yana tare da dangin sa, ga kuma kanwar sa a
gidan wato Sahura. Ayyukan kamfani kuwa duk yana tafiyar da su ne ta yanar gizo da
kwamfuta, sannan yana da mataimaka na kwarai. Amma so yake yayi nisa da Amani.
Bayan sun ci abinci Faytoory yayi musu sallama ya tafi. Mama Jalan tace bata yarda ba sai
ya yi kwana uku sun gana sosai. Tasa Safwan ya kai masa kayan sa dakin marigayi dake
harabar shigowa gidan bayan fajur taje ta share ta kunna turaren wuta. Fajur da Safwan suna
zaune manne da Amani, sun kasa matsawa ko nan da can kada ta tafi ta bar su. Safwan zai yi
shekaru sha biyar Fajur kuma goma.
Ta umarci Safwan ya raka Mukhtar ya huta, sai suka shiga daki ita da Amani da Fajur.
Ta hada mata ruwan zafi mai kamshi tayi wanka sannan suka zauna suna kara gaisawa.
Sallah ce kawai ta tayar dasu a wannan ranar don kwana suka yi a zaune, Amani na baiwa
Maman ta labarin rayuwar ta da mahaifin ta gabadaya tun daga sanda ta fara wayo har zuwa
yanzu, da yawan matan da ya dinga aura yana saki sabida ita, da artabun su da matar shi ta
karshe Haj. Rabi, da halin da yake ciki a yanzu na shanyewar barin jiki, ta bata labarin haduwar
shi da Mukhy a Paris, da kawo shi gidan su da yayi, ya bashi gida daura da nasu, ya kuma
sakar masa ragamar kamfanonin ta da shagunan ta, yadda ya dinga fifita alamarin sa, da irin
yardar da ke tsakanin su wadda take ganin ta rage mata daraja a gun mahaifin ta, har zuwa
aura mata Mukhtar da yayi ba tareda yardar ta ba wanda shine abinda ya kara sawa ta tsani
Mukhtar ta kuma amince Daddy yafi son sa yanzu a kan ta.
tace Mamma wallahi bana son sa, ko kadan, ko ganin sa bana son yi, kyawun sa ko ilmi sa
ko yanayin kasaitar sa dake burge Balewa bai taba ruda ta sun saka ya birge ni ba, ban taba
son sa ba, kuma har gobe bazan so shi ba, sabida yaron Daddy ne a kasa na yake, kuma mara
kirki mara dadin muamala ba ya girmama ni. Mara asali mara nasaba gashi nan dai shi ba
tsintacce ba shi ba Da ba.
Cikin halayen sa bakidaya babu guda daya da zan iya ce miki mai kyau ne. Ga girman kai ga
fadin rai, baa saka shi baa hana shi, a haka Daddy yake tunanin zan iya zaman aure da shi? A
rayuwata in ba mijin da zan juya kamar waina a tanda ba, bazan taba yarda in aura ba.
Duk mazan duniya Daddy ya rasa wanda zai aura min sai wanda baida asali kuma a karkashi
na yake? Ai karshen kaskantawa Daddy ya gama yi min ita, shi yasa na ce ba zan koma
Katsina ba har duniya ta nade.
Ta fashe da kuka tana cewa ko sadakin su ban karba ba, don haka babu wani auren sa a kai
na ni. Baba Idin ma ya san ban karba ba shi na barwa abin sa, sai dai in Baba Idin ya aura.
Jalan tayi taawizi. Tun baa je koina ba Mama Jalan ta gama karantar wacece Amani, halayen
ta da dabiun ta marassa kyau na girman kai, alfahari da dukiyar uban ta, fariya da izzah na
rashin sanin darajar da Allah yayi wa dan adam. Yawan alfahari da rashin kunya na rashin
mafadi ko tarbiyya mai inganci. Tausayi mai tsanani ya kamata sai ta kasa ce mata komai. Sabida ita ta koina Mukhtar yayi
mata, har tsoron kwarjinin sa da ilhamar sa ta ji, don kwarjinin sa da kasaitar sa cika mata ido
da falo suka yi, ta yi duba don gano makusa a tare da shi da ta sa Amani fadin abubuwan da
take fada a kan sa ta rasa. Sai kawai ta gane cewa Amani wawuya ce, doluwa, gaula kuma goyon namiji. Mai halin yan
fari, kuma wadda gata da kudi ya jika har ya yiwa yawa har ya taba hankali da nutsuwar ta.
Bata samu tarbiyyar uwa da wadatar ilmin addini ba sai na zamani. Sanan bata samu
religious background na musulunci sosai ba.
A yanayin da take magana ma ga kowa, gatsau ba respect ba taunawa tana gatsine baki na
raini ga Mukhy ya tsorata Jalan.
Kamar Mukhtar itama nan take ta gayawa ranta cewa jan aiki ne a gaban ta jawur, don haka
zata roki Mukhy ya bar mata Amani zuwa nan da watanni biyu haka. In hakan ba zai cutar da
shi ba. Yo Allah ta tuba ina wani kwanciyar hankali da miji zai samu a tare da Amani mai
abubuwa irin na zararru? Ai gara ma ya bar ta aga abinda zaa iya a kan ta ko kadan ne, tunda
baa bari a kwashe daidai, kuma icce tun yana danye a ke tankwara shi.
A halin yanzu tana so ta karance ta ciki da bai, don ta san ta inda zata bullo mata, da yadda
zata gyara gurbatattun dabiun ta da halayen ta ko da ba duka ba, kafin ta shiga dakin miji ya
zama ko manner of speaking ta gyara mata. Tunda an riga an baro kari tun ran tubani.
Duk da haka zata yi iya yin ta cikin yan watannin da zasu yi tare, sauran sai ta barwa Allah
mai kowa mai komaia, ta kuma hada da addua da rokon Allah ya baiwa Mukhtar zuciyar dauka
da soyayyar da zata rufe masa ido daga ganin aibun munanan halaye da dabiun yar ta.
Sai bata ce mata komai a kan Mukhtar ba a wannan daren, ta barwa ran ta, don so take ta
gano root causes na matsalolin sangartar Amani da rashin good upbringing din data samu,
sannan ta yi tunanin hanyoyin magance su a ilmance.
Duk da ita ma din ba wai ta samu zurfin ilmin zamani bane amma tayi sakandire kuma tana
da ilmin addini sosai, sannan ga shekaru ga kyakkyawan hankali.
Amani ta nemi ta bata nata labarin. Bayan rabuwar ta da mahaifin ta.
Nan ta gyara zama ta soma bata labari ta gaya mata cewa bayan Daddy ya sake ta a gadon
asibiti basu taho ba sai da ta warke tas, suka dawo Saliyo tare da iyayen ta. Maman ta tayi
mata jego, har ta warke. Mahaifin ta yayi fushi da ita fushi mai tsanani a kan rashin biyayyar
data yi masa na kin zama da Alhaji. Ta hana shi samun makudan kudaden da yake samu a
hannun Alhaji Usman. Yace yanzu gashi ta janyo ya raba ta da diyar data haifa kuma babu
tabbacin yarinyar zata rayu ko aah, ko zasu sake haduwa, tunda babu wanda zai shayar da ita.
Ni kuma kullum na yi sallah sai na roki Allah ya raya abinda na haifa koda bamu sake
ganawa ba, yasa rayayye ne kuma ya amfani musulunci da alumma.
Daga baya bayan wasu watanni, Luqman tsohon saurayi na dana ke so ya dawo neman aure
na. Da kyar na samu mahaifi na ya yafe mini, yace Yaya ta Aisata tayi mishi biyayyar da ni ban
yi mishi ba, don ita kam sayar da ita ma yayi a Nijar ga wanda bai ko sani ba, don haka kada in
taba tsammanin zai barni in zauna a gidan sa, in kawo miji kawai talakan dana ke so yayi min
aure ya huta. To dama ni da Luqman mun dade tare kuma a kan sa ne naki zama da Alhaji Usman, da
kuma nasa halayen wadanda na san ba sai na fada miki ba, tunda baban ki ne ya kamata ace
kema kin san su.
Muka yi auren kauna da soyayya ni da Luqman, wanda shine mahaifin su Fajur, maaikacin
kamfanin Tama da karafa ne (Steel Rolling Company), wannan gidan, shine gidan da muka rayu
a cikin sa tsayin shekaru goma sha tara ni da Luqman, cikin rayuwar aure ta soyayya da
fahimtar juna wadda mahaifin ki bai iya ko daya ba, shi dai ya yarda kudin sa ne zai samo masa
duk irin matar da yake so a duniya.
Shekara na zagayowa na haifi Safwan, sai bayan shekaru biyar da haihuwar sa har mun
fidda rai sannan daga baya na haifi Fajur, a shekaru ukun baya ne Allah yayi masa rasuwa
bayan gajeruwar rashin lafiya.
Iyayen mu kuwa sun jima basa raye, Aisata ya sayar da ita a kasar Nijar ko zuwa Saliyo bata
kara yi ba tun karbar ta da aka yi aka tafi da ita aka bashi Rakuma masu yawa, wato shi
mahaifin namu a matsayin sadakin ta, lokacin rasuwar mahaifin namu ne ban san ya akayi ta
samu labari ba ta aiko min wasika ta taaziyya ta gaya min watarana zata aiko a kaini inda take
aure a Nijar, kuma tun daga wannan lokacin ne ta soma yi min aiken kudi lokaci-lokaci duk da
bana cikin bukatar komai, ina tare da miji na cikin kwanciyar hankali da rufin asiri lokacin, bayan
rasuwar Baban su Fajur na aika mata ta hanyar dan aiken da ke kawo wasika a tsakanin mu
wanda dan kasar nan ne mai kasuwancin Rakuma a Nijar, shine fa ta bude min asusu, wanda
kai tsaye duk wata take turomin kudade na Saifa masu kauri, wadanda da su ne na cigaba da
daukar nauyin karatun yaran nan, muke kuma cin abinci, na kuma soma sanaar kiwo, ga abinda
mahaifin su ya mutu ya bar mana muna juyawa a gona, muna samun amfani daga noma da
kiwon kaji da kiwon shanu. A takaice kin ji wannan itace rayuwar da muke yi a halin yanzu.
Safwan yana rubuta jarrabawar kammala sakandire yanzu a nan makwabtan mu wato Gambia,
ya zo hutu ne, Fajur tana karatu anan wata karamar sakandire ta kudi a bayan gidan nan,
kullum da kanta take zuwa ta dawo ta huta ta wuce Islamiyya.
**** **** ****
MOTHERHOOD
Z
uwa washegarin ranar, hatta makwabtan Jalan bakidaya sun san da zuwan yar ta dake Najeriya
aka shigo ana yi mata barka, wasu na aiko abinciccikan kwadayi wa Amani, kasancewar Jalan
ta mutane ce mai yawan kyauta da kyautatawa ga makwabtan ta, anata mamakin kamannin su
ita da Amani in ka dauke cewa Jalan mai jiki ce Amani siririya. Duk abokan arzikin iyayen su
dake raye sai da ta kai Amani a washegari suka gan ta. Basu dawo gidan ba sai da yamma lis.
Shima Mukhatr baya gidan tun safe Faytoory ya zo ya dauke shi, sun shiga gari yana nuna
masa wurare masu tsohon tarihi na Kenema, da inda ake Mining din Diamond. Daga can suka
wuce gidan Faytoory suka ci abinci da iyalin sa sai lokacin suka dawo gidan su Amani.
Faytoory ya ajiye Mukhtar kenan suna sallama da cewa gobe in sha Allah da wuri zai zo ya
tafi dashi Freetown, inda daga can zai hau jirgin Lagos.
Mama Jalan ta aiko Safwan ya kira shi su ci abincin dare yadda suke yi kullum, a lokacin
yana hada kayan sa a jaka yana tunanin tunda su ka zo rabon sa da kebewa da Amani ko da
da sunan su gaisa, wato ya gama mata amfanin da zai mata, tunda ta dafe uwar ta a gefen ta
shikenan. Sai ya shiga tambayar kan sa na me zai yi wannan tunanin ma? Amani ce fa! Wadda
ya sani ba tun yanzu ba. Ai ya dade da sanin Amani ba yar goyo bace shakiyya ce ya sani
dama, kuma ta fada ta kara haduwar su ta kan hanya ce da zarar ta ga uwar ta babu ita babu
shi.
Ya tuna cin mutuncin data yi masa sa Freetown da zagin fitar hankali na sheganta shi, sai ya
ji zuciyar sa na kara tafarfasa, Amani na kara fita a ran sa. Amma mutuncin iyayen ta a zuciyar
sa na kara ninkuwa.
A ladabce Safwan ya shigo ya gaida shi, sannan ya gaya masa sakon Mamma na ya fito su
ci dinner tare.
Ba tare da ya dago ya dubi yaron ba don baya so ya ga idanun sa, a dai yanayin da suke ciki
yanzu na tsananin bacin ran Amani. Ya ce ya je ya gayawa Mamma cewa a koshe yake, ya ci
abinci a gidan Faytoory kuma yana so zai shigo yayi mata sallama don gobe in sha Allah zai
koma Katsina. Safwan ya je ya dawo ya ce Mamma ta ce ya shigo, a gaskiya a lokacin baya son shiga cikin
gidan a yanayin da fuskar sa ta koma yanzu, wato boyayyen yanayin nan nasa da ba kowa ya
san yana da shi ba ya bayyana, domin baya so Hajiya Jalan ta ga hidden side din sa na rashin
walwalar nan. Gashi idan ya zo baya iya controlling din sa har sai ya bace don kan sa. Sannan haka kawai yake jin muryar Mamma Jalan da accent din ta kamar yadda yake jin
tashin muryar Ummami, wanda hakan ke kara tono bacin ran dake kasan zuciyar sa na kewar
Ummami da jin zafin ta (as well), yana kara bayyana a kan fuskar sa.
Ba yadda ya iya dole bayan yayi wanka ya canza kayan jikin sa zuwa farar jallabiyya kal kirar
Dammam, ya yi sallah a masallacin kofar gidan sannan ya shiga cikin gidan da karamar
tazbaha mai kyau a hannun sa. Nan ya gan su complete family a kan teburin cin abinci abin
gwanin ban shaawa. Amani ta sha ado da laffaya koriya sharr da irin matsatsiyar rigar nan ta
roba mai dogon hannu daga cikin laffayar light green itama. An yi mata wai irin setting din gashi
wanda ya zubo a saman goshin ta ya zarce har bayan kunnen ta. Bakin nan sai shining yake da
Elizabeth Arden Lip gloss kamar ka sace ta ka gudu (looking takeaway), idon nan nata mai
kama da kwan zabo ya sha mascara gashin idon ya fito gazar-gazar.
Rabon ta da yin ado irin wannnan bazata iya tunawa ba. Sai ko yanzu da take jin kanta a
daidai wato bata da damuwar komai, tunda rayuwa ta koma mata daidai, ga ta ga uwar ta a
duniya, ga kanne, sosai take cikin nishadi, barin ma data ji Safwan ya zo ya fadi sakon Mukhy
na cewa gobe zai koma Katsina. Ai kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, yi ta yi kamar ta tashi ta ka rawa, murnar tata har kasa
boyuwa ta yi sai da Mamma ta gane bakin ta ya ki rufuwa don Mukhy ya ce gobe zai koma ya
bar ta a nan. A cikin zuciyar ta Jalan tana mamaki, ko meye aibun Mukhtar haka da matar sa ta
kasa son sa? Mutum son kowa da shi a halitta da dabia, abun alfaharin kowacce mace wajen
kamun kai da kamewa da girmama iyayen ta, amma Amani na neman maraba da shi irin haka
bata ko jin zata yi kewar sa don ko a waya bata ga sun gaisa ba balle text din soyayya.
Kwata-kwata ta gama lura Mukhy baya ran ta, kamar kishin sa take akan Baban ta kamar kuma
zuciyar ta bata taba kimsa mata soyayya a kan