Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
ji
alamar shigowar sa sai da suka kammala.
Ta runtse idon ta kadan, a kan wannan kalma da ya kara ambata mata, ta yarda Mukhy,
mutum ne mai tsananin riko, irin wadanda da wuya a cuce su su yafe, ba tare da sun rama fiye
da abun da aka yi musu ba ko mafiyin sa, ko da zasu huce din ma kenan.
A ranar ta nemi jin ta bakin Maman ta kan komawa mahaifin ta, ta ce for my sake Mammah!
Ta hada hannayen su wuri guda tana rokon ta. Har da hawayen ta.
A karshe Jalan ta amince zata komawa Baban Amani, albarkacin Amani da Mukhtar don su
yi zaman aure na jinyar Alhaji, koko zaman auren zuba ruwa a buta da kai ruwan wanka kamar
yadda Amani ta kira auren.
Wata biyu bayan nan Mukhtar ya yiwa Baba Idirisu da su Kamilu da Baba Sahura shirin
tahowa Kenema, shi kadai ya tsaya tare da Alhaji da kamfani, cikin kwana uku da zuwan su aka
maida auren Ahaji da Jalan, farin cikin da Amani ke ciki ne yasa ita da kanta ta hada musu
kayan su don su taho Katsina tare da su Baba Idi, wai biki zata yi wa Daddy da Mammah, biki
na kece raini, hararar ta Jalan ta yi ta ce,
ki fara shirin naki bikin dai, ni ba saar wasan ki bace.
Baba Idi dake wurin yace ai in suka isa Katsina ba zama zasu yi ba, mika ta wajen mijin ta
zasu yi, zasu dunguma ne su wuce wajen iyayen sa a Diffa region, ta kasar Nijar. Kuma
Mukhtar yace in sun tafi bazata dawo ba, sai ko da ganin gida.
Maganar sai ta tunowa Jalan da Yayar ta Aisata dake Nijar. To ai kamar a Diffa din ne ma
dan aiken dake tsakanin su yace take aure. Tsakanin ta da Aisata sai aike, don bata taba fita
daga gidan mijin ta ba tun ranar data shige shi. Ta sa a ranta zata nemi jin hakikanin inda take a
Nijar din in sun je, bata dai tabbatar da inda take a can din ba don taba zuwa ta yi ba, zata
nemo mutumin ya bata adireshin Aisata ko don ta yi wa Amani Uwa a can da jinin ta kuma uwar
ta.
**** **** ****
B
a karamin shiri Mukhtar ke yi na isowar Maman su Jalan ba. Ya sa an fente gidan gabadaya da
sabon farin fenti mai feshi, an shirya mata dakuna na alfarma da furnitures yan uban su.
Sannan ya sa an shirya dakin Fajur kusa dana Amani, Safwan ma yasa na fidda masa daki
daga waje kusa da na Kamilu. So gida ya zama full house, family house don hatta Baba Idrisu
sun bashi dakin sauka a gidan duk lokacin da ya zo. Gidan Hon. Usman babban gida ne da ya
lamushe dukiya mai yawa wajen ginawa a matsayin sa na Architectural Engineer, har gobe
kuma kullum kara kyawun gidan ake da gyara shi yadda zai tafi daidai da zamani da duk wani
sabon abun kawata da ya shigo da shi daga waje.
Rakiya na ta hidimar dawowar uwar dakin ta, bata sama bata kasa don tabbatar da ta ajiye
ma Amani komai na bukata, yadda suka saba. Ta ji labarin auren Amani da Mukhy a bakin
Malam Tajudden tun kafin su dawo, tayi mamakin ta ita kadai ta bari. Yanzu kuwa Kamilu ya
gaya mata har Babar Amani mahaifiya zaa dawo don haka girke-girke na musamman ta yi
musu, zuwa yamma kuwa sai taji dirin motocin da suka je debo su sun shigo, wato dai sun iso
gidan lafiya.
Gidan ya kaure da hayaniyar farin ciki, Mukhtar yana gidan sa yana barci bai san sun iso ba,
don jiya kwana yayi da maaikatan Alhaji ana meeting na amana, kan wanda zai jagoranci
kamfanin Alhaji da gaskiya a cikin su tsofaffin maaikatan Alhaji, sabida shi zai koma gida, bada
jimawa ba. Bai kuma da niyyar dawowa. Boutique din Amani ya koma karkashin kulawar Kamilu kasancewar shima kasuwanci ya
karanta. A karshe Mukhtar ya zabi Alhaji Badaru Matawalle wani tsohon maaikacin kamfanin da
sun fi shekara Talatin suna aiki tare da Alhaji, a shirya a bata, still dai an jure zaman tare na
lokaci mai tsayi, an kuma san halin juna, Alh. Matawalle dan asalin Bindawa ne, shi Mukhtar ya
baiwa kujerar sa karkashin saka hannun mutumin da Lauyoyin Alhaji, suka yi resolution kan zaa
cigaba da gudanar da ayyukan kamfani yadda aka saba bisa amana da gaskiya, Mukhtar ya ce
ko yaya suka fahimci wani abu ya biyo baya na rashin gaskiya a kamfani, to kuwa zasu rufe
kamfanin ne kawai.
Aka yi komai a shariance, sannan ya ce gobe zai ma Matawalle handing over na ofishin sa.
Ba shi ya tashi daga barcin gajiyar da yake yi ba sai ana gab da kiran sallar maghriba. Don
haka a gurguje ya shiga wanka yayi alwallah ya fito yana shiryawa a gaggauce, ya san yanzu
su Amani sun dade da sauka. Ya rasa dalilin dokin da ke cin ran sa sai kace shi aka kawowa amarya ba Alhaji ba.
Murmushi ya yiwa kan sa, wani abu da ba kasafai yake faruwa da shi ba, wato bai da yawan
murmushi, kuma in yayin, shi kan sa ya san ba karamin kyau yake kara masa ba.
Ya ce ma kan sa in haka ne ai shima yana da amaryar, sai dai tasa fitsararriya ce
hamshakiyar shuuma mara kunya, ba irin ta Alhaji mai kirki da sanin ya kamata ba.
Sanda yake fesa turaren sa watau Azzaro Visit bayan ya fito daga wanka, sai da wani farin
cikin son ganin Amani ya darsu a ran sa.
Yana duba wayar sa ya ga missed call din Alhaji dana Kamilu rututu, da sauri ya saka
takalmi a kafar sa ya fita, bayan ya rufo kofar dakin da mukulli ya hau motar sa Bugatti wadda
Alhaji neya bar masa ita zuwa gidan Alhajin, duk da ba nisa da nasa gidan tafiyar kafa ce kawai,
ya kuma fi zuwa a kafan a yawancin lokuta, amma yau da yake cikin saurin isa gidan yake sai
kawai ya hau motar.
Yana parking yana fitowa da Safwan ya fara tozali, yaron ya zo da gudu ya rungume shi,
bakin Mukhtar yau a bude, fararen hakoran sa a warwaje, kai ka ce shi ya mallaki kamfanin
COLGATE, abinda ya baiwa su Malam Tajudden matukar mamaki, sai fara yake yana rike da
hannun Safwan suka shiga gidan, yana ta bashi labarin zuwan su da abubuwan da suka gani
na mamaki a hanya.
Kai tsaye falon Alhaji ya nufa inda ya tadda su su duka a can, har Mamma Jalan, sun hada
kai ana cin abinci tana zubawa Alhaji ruwa a tambulan, wannan abu yayi matukar faranta ran
Mukhtar. Yau rayuwar Ubangidan sa ta koma irin wadda ya dade yana masa fata, rayuwa mai
kyau da maana wadda addinin musulunci yayi koyi da ita, ba irin kazantacciyar rayuwar sa ta
baya ba ta babu wani jinin sa da zai rabi niimar arzikin da Allah ya yi masa. Wadda watakila ita
ta jawo masa yake ta shan wahala a rayuwar sa.
Ya duba ya hanga a cikin su bai ga yar mulkin ba. Wadda tun zuwan su gidan da aka kauraye
da hayaniya ta samu migraine wato ciwon kan barin kai guda wanda gajiya ta haifar mata, sai ta
zame jikin ta ta haye sama dakin ta, ta shige ta kulle kan ta. Har da lika takardar data ke likawa
Rakiya a jikin kofa an rubuta DO NOT DISTURB wato kada wanda ya zo ya dame ta. A duk sanda Rakiya taga ta lika mata wannan a jikin kofa bata kara zuwa kofar dakin sai ta
neme ta don kan ta.
To yau ma hakan, Rakiya ta zo don ta kawo mata nata abincin, don ta san bata cin abinci da
mutane, nan ta ga abinda aka lika mata tuni ta yi ta kanta. Baba Sahura ta tambaye ta ina Uwa,
ta san in ta ce UWA Amani take nufi, ta ce tana barcin gajiya ta lika kada a dame ta. Sahura ta
ce Inye! Mulki sai mai shi. Wannan da basarake ta aura bansan ind zata kai mulki da iyawa ba. Shigowar Mukhtar falon aka kauraye da yi masa barka da zuwa daga bakin kannen sa Fajur,
Kamilu da sauran yayan Baba Idi dana Sahura da suka zo daga Faskari yau. Baba Sahura na
fadin ango ka sha kamshi, na Uwa farin mutum mai farar aniya alherin Allah ya kaiwa iyayen da
suka haife ka. Sahura ta fadi hakan ne don ta san duk wannan kokarin na gyara rayuwar su
data dan uwan su, kokarin sa ne bana wani ba.
Shima yau ya kasa yin rowar murmushi, sai sakin sa yake gwanin shaawa. Ya zauna daf da
Alhaji yana gaida Mammah, tace Mukhtar ya naga idanun ka sun tasa? Ina fatan lafiya dai?
barci nayi mai yawa Mamma, da yake jiya mun kusan kwana muna meeting ta ce to
madallah, ga abinci ta soma serving din sa burabuskon shinkafa da miyar ganye da naman
tolo-tolo, ya ce Ai Mamma ban iya cin burabusko, shake ni yake yi ta mayar ta zuba masa fried
sphaghetti da romon kaza sannan ya karba ya soma ci ana ta hirar Saliyo. Alhaji ganin kowa ya manta da Amani shi bai manta da ita ba, yar lelen sa tana like a ran sa.
Yace Mukhy, ka gama cin abincin? Ya ce eh Alhaji. Alhaji yace yawwa, to maza tashi ka je ka zo
min da TAFISU yau labarin rayuwar ka zaka bamu dukkan mu. Da abinda ya rabo ka da iyayen
ka tun da ka ce min suna raye, da dalilin da yasa baka ko so a yi maka zancen gida ko na kasar
ku.
Amma ina so ya zama an yi komai a gaban Uwa ta (Tafisu). Don haka je ka zo min da ita.
Kunya ta kama Mukhy, musamman da Jalan ta zuba masa ido, ta rasa mai yasa take jin sa
kamar dan cikin ta, ta yaya zai iya tsallake Uwa da uban Amani ya je inda take a cikin gidan su?
Sai da Alhaji ya sake maimaita umarnin sa, shi ba abun yace a aika Fajur ko Safwan ba,
tunda Alhaji ne da kansa yayi magana. Da kyar ya iya mikewa ya bi matattakala da sassarfa
zuwa sama, wato bangaren Amani.
Yana zuwa kofar dakin ya ci karo da sakon ta na Do Not Disturb. A jikin marikin kofa. Dariya
ce ta kama shi, sai kace a Hotel! Ai kuwa zata ga disturbance yanzun nan. Kofar ya hau
kwankwasawa da karfin sa kuwa. Amani na tsakiyar barcin wahala barcin da migraine ya
sabbaba mata, ta ji ana mata wannan bugun na rashin tsanaki. Ta mike cikin rangaji da sarawar
kai ko kayan jikin ta da suka zo dasu a jikin ta bata cire ba balle dogon hill shoe dake kafar ta,
haka ta afka gadon duka, tana tafe zuwa kofar a fusace, tana fadin mai raba ta da Rakiya yau
sai Allah.....sai tayi kasa-kasa da ita, sai ta ci abu kaza-kazan ta.
Tana budewa dogon baabzinen yana sako kai cikin dakin har yana kusan ture ta, saura
kadan ta fadi don dama jikin ta ba kwari. Ta yi maza ta rike marikin kofar.
Farin gilashin dake idon sa ya zare, yadda zai ji dadin kallon matar tasa rigimammiya Amani
Faskari, ta yi yar kiba kib-kib ta yi jawur ta murje abinta. Mai nuna ta samu kwanciyar hankalin
da bata taba samu ba a zaman ta a Saliyo. Ga wani uban su kunshi mai ja da baki da Mamma
tasa aka yi mata a sawayen ta da zara-zaran tafukan hannayen ta. Ta fito a amaryar ta sosai sai
rashin mutunci fal a idanun ta. Tace a fusace.
Shin baka ga an saka do not disturb bane? Da zaka zo ka tada ni daga barci bayan bani da
lafiya?
Mukhtar ya ce do not disturb, a dakin hotel kike? Ko wata tsiya kike kullawa a dakin banda
barcin asara? Kuma na dauka a gidan mutane kike ba a gidan ki ba, da zaki kwanta kina zuba
iko?
Kallon mamaki Amani tayi masa, ta ce gidan namu ne gidan mutane? Ni da gidan uba na?
Ya ce aikin kenan! Alfahari da Uba, ko anan aka binne cibiyar ki baki da ikon cewa kada a dame
ki a gidan nan, tunda ba gidan mijin ki bane gidan Mama Jalan ne yanzu.
Amani tayi kwafa, ta koma gefen gado ta zauna tana fadin har akwai wani gida da ya fiyewa
mace gidan uban ta? Mukhy ya ce sosai ma kuwa, gidan uban nata na wucin gadi ne, gidan da
zata je ta haifi yaya shine comfort zone din ta, shine inda duk mulkin data zuba babu mai
kalubalantar ta. Amani ta zo iya wuya, idan nace maka ni kuma babu wani comfort zone da ya
fiye min gidan uba na muhimmanci zaka yarda?
Idan nace maka baka da gidan da ya isa ka ajiye babbar yarinya iri na zaka yarda?
Idan nace maka Alhaji ya cuce ni iya cuta da ya bada aure na gare ka kaskantaccen bawan
sa zaka yarda?
Idan nace maka kyan ka da ake fadi bai taba bugar da ni ya sa na ji ka da wani matsayi a rai
na ba saboda baka kai matsayin da zan aure ka ba zaka yarda?
Ina bakin cikin abinda ya shiga tsakanin mu ranar nan a Saliyo, saboda kai ba aji na bane, ka
yarda?
Mukhy ya juyar da idanun sa da suka canza launi, yana kokarin hadiye bacin ran da ya taso
masa, ya ce me kuwa zai hana ni yarda tunda na kwana da sanin yar Qaruna ce, Tafisu wadda
tafi sauran mata, kuma a hakan aka bani sadaqar ta, ana roko na Allah Annabi in karba da
hakuri, saboda Alhaji kan sa ya san ba yar kwarai ya haifa ba; ballagaza ce, banza ce,
mahaukaciya ce kuma jahila, wadda ta rako mata duniya!.
Amani sai ta fashe da kukan da baya mata wuya na shagwaba da sakalci, amma na yau iya
gaskiyar ta take yin sa bilhaqqi, domin Mukhy yayi mata cin mutunci da wani dan adam bai taba
yi mata ba, tun baa je koina ba, ai ga irin ta nan, Daddy ya sayo mata gori da rashin daraja a
wajen wanda bai isa komai ba, sai ta kara tsinkewa da kuka.
Mukhy yayi kwafa, yace yarinyar nan ina tausaya miki domin baki san rayuwa ba ko kadan,
baki san Annabi ya faku ba, baki san dukkan mu darajar sa muke ci ba, duk wani rawanin tsiya
ya kare a kan ki, Ubangiji ya laanci shaidan ya kuma fitar da shi daga Aljannah ne sabida
girman kan sa da jin cewa yafi kowa. Baki san Allah ya ce Inna akramakum indallahi Atqakum. Ubangiji yayi alkawarin dankafar
da maabota girman kai dagawa da alfahari, masu girman kai iyalen shaidan ne, ni ina tausaya
miki, ina kuma tausayawa kaina, sannan ina tausayawa yaya na idan kika haife su baki yi
hankali ba. Ke kam ai dadi ne ya yi miki yawa, shi yasa kika kasance mara godiyar Ubangiji; Uwa da
Uban ki na son ki, suna tarairayar ki da ririta ki da son ganin kin zama matar aure ta kwarai,
wani kama na iri na bai samu wannan gatan da kika samu ba.
Don haka in kin gama ki zo suna kiran ki a kasa.
Daga haka ya juya ya fice ya koma wajen su Alhaji. Yana kokarin maida walwalar sa ta dazu,
amma hakan ya faskara, domin kullum Amani ta ci mutuncin sa fita take kara yi a ran sa, baa
jimawa kuma in ya huce zata dawo ta yi masa kaka-gida a rai, ya manta duk wani aibun ta.
Ba jimawa sai gata ta sauko cikin shiga ta kasaita, ta ci hill shoe din ta kamar mai shirin tafiya
dinar babbar aminiya, ta kafe dauri a gaban goshi tana tana taunar cingam rakakas-rakakas. Ita
a lallai ga wadda tafi sauran mata.
Da dane, da tuni Alhaji ya fara yi mata kirarin TAFISU! Amma yanzu da yake yayi hankali sai
cewa ya yi Uwa yaya kika sakko babu mayafi? Maza koma ki yi lullubi ta zumburo baki sannan
ta koma, Jalan tayi fatan a kusa da ita take ta kaiwa bakin da ya sha