Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
sa ba.
Ta riga ta dauke shi rival a zuciyar ta, ko kuwa wani wanda ya tare mata gaba ya hanata
rawar gaban hantsi. Sai Jalan ta shiga tambayar kan ta ko yar tata bata da lafiya ne irin ta yaya
mata ko kuma tana da shafar jinnu. Ta lura bayan dolonci, rashin kunya, rashin ilmin addini,
rashin cikakkiyar tarbiyya har da rashin sanin muhimmancin da Allah ya baiwa miji a kan ta, da
rashin sanin hakkin aure.
Kada dai tarihi ne yake maimaita kan sa, tunda itama abunda ta yiwa Uban ta Alh. Usman
kenan, kusan tsayin shekaru biyu tana wahalar da shi a dalilin bata son sa.
Tunda ya aure ta sau daya ya taba samun saar ta, shima ta karfi, wanda daga baya ta gane
rabon Amani ne ya rantse.
Tana kuma lura da cewa tunda suka zo Amani bata je inda yake ba, bata kara bi ta kan sa
ba, bata kara yin zancen sa ko kula da alamarin sa ba a matsayin su na sabon aure, balle ta
damu da sanin halin da yake ciki a masaukin nasa, ko ta tambaya an kai masa abinci ko aah?
Don in an kira shi ya ci ma baya zuwa. Sai ta ji tausayin Mukhy mai tsanani da kaunar sa kamar dan cikin ta ya kamata, bata san
dalili ba amma jin sa tayi ya kwanta a ranta kamar dan ta Safwan, ba banbanci, don in ba
kuskure idanun ta suka yi mata ba ita ta hango kwantacciyar soyayyar Amani maras misaltuwa
a can kasan kasaitattun idanun sa masu sheki da sparkling a duk sanda ya juya su a kan
Amani. Ita a wurin ta Alhaji Usman ya kware shi, da ya hada shi da auren Amani, hakika ya so
kan sa, domin Mukhy data ke faman kira yaron Baban ta ita sai taga ajin sa da kasaitar sa sun
dame na Amani.
Gashi ya san irin tarbiyyar da yayi mata amma ya hada dan mutane nagartacce, kamamme
mai alkunya da wahala, don ya gan shi mai hakuri da biyayya. Ga wata irin nutsuwa da kamala
a tare da shi irin wanda tsayar da addini da kula da sallah ke haifarwa namiji, wanda bata taba
gani a matasa kamar sa ba. Ta shiga hangowa kan ta irin asarar surukin kwarai da zata yi, idan shashashar diyar nan tata
tayi masa rikon sakainar kashin da zai gaji ya yakice ta.
Sai ta yi maza ta mike tana tunanin abun yi na gaggawa, don kankarowa Amani mutunci ka
idon Mukhtar kafin ya karasa zirarewa.
Mukhtar yayi sallama duk suka amsa banda Amani, wadda a lokacin ta kai fork da ta cokalo
dankalin turawa a jikin sa bakin ta, tana wata tauna a yangace kamar bata so. Jalan ta nuna
masa kujerar da zai zauna mai fuskantar ta Amani ya tsugunna har kasa ya gaishe ta, yana ta
kokarin kin dagowa ta ga fuskar sa, amma a kulawa irin ta Jalan, sai da ta hango yanayin da
yake boye mata din, kuma a matsayin ta na babba ai ta san dalilin sa.
Amma sai tace lafiya Mukhtar na gan ka haka babu walwala?
Mukhtar ya ki zama a kujerar don ba zai iya tana kujera shima yana kan kujera ba, sai ya ce
mata Mamma zan koma Freetown gobe da sassafe, daga can zan tashi Nigeria in sha Allah.
Ta kusa ce masa Amani fa?
Don sai ta ji kamar bata kyauta ba in ta rike masa mata har tsayin watanni biyu nan gaba,
bayan bashi da wata matar a can gida Katsinan. Kamar Mukhy ya san me Jalan take tunani sai
yace,
ita Amina Alhaji ya ce ta zauna da ke na dan wani lokaci, ta saba da nan din Jalan ta soma
lalubo idon sa da yake boyewa da nata wayayyun idon na iyaye, ta ce.
Are sure you are okay with her stay here? Cewa nake daurin aure kawai aka yi muku baku
tare ba ko sau daya?
In don ta ni ce ba abunda zata yi min alhalin tana da miji a gefe, gara ta wuce ku koma tare,
zai fi min kwanciyar hankali da kai kan ka.
Ai jin haka Amani ta soma buga kafa irin wanda takewa Alhaji, tana fadin ita ta zo kenan, ba
inda zata sake zuwa. Alhaji ne yasa take zaune a Katsina kuma ita kam yanzu ta barwa Mukhy
shi halak malak. Sai ji kike gwajab! Mamma Jalan ta gwabje bakin da ya sha lip gloss, tace,
Amina!
Ashe baki da daa baki da ta ido? A gaban kannen ki kikewa mijin ki wannan diban rashin
albarka? Tashi ku je ki bashi hakuri, na ce ki bashi hakuri har sai ya huce, ku yi sallama
cikakkiya, kada in ganki a cikin gidannan sai da safe!.
Tuni Mukhtar ya kai bakin kofa don in ya cigaba da zama a wajen nan Amani ta kara magana
ta rashin amincewa da umarnin ta, ko ta kara furta wani abu akan hakan ya san Mamma Jalan
zata kara kai duka, da alama mai saurin hannu ce.
Sosai dukan Jalan ya samu bakin Amani, tuni leben sama ya kumburo. Zata yi magana ta ji
bakin ta ya mata nauyi, sai ta fara hawayen da baya yi mata wuya, a ranta ta ce shikenan itama
uwa ta yayi sumumu-kasau dinsa na munafurci ya raba mu, Mamma kuma ta yi rantsuwa ta
kara ta tashi ta tafi wajen mijin ta ko ta sassaba mata kamanni yanzun nan. Ko me ta tuna? Ta ja hannun Amani zuwa dakin ta da zafin nama saboda idanun su Fajur da
suka bubbude suna kallon su, suna shiga ta rufo kofar da mukulli, ta dube ta da tausayi, don ta
ga tsanar Mukhtar tsantsa a cikin idon ta. Ita victim ce ta kiyayyar auren dole ta san me Amani
ke ji. Ta ce. Amina, bana so ki zamo daya daga cikin matan da aure da hakkin sa ke kai su wuta. Ba sai
ya ce bai yafe miki ba Allah zai dubi hakkin sa a kan ki ya fidda masa, na san a shekarun ki kin
san aure, kin san maanar sa, amma a dolancin ki kina sa kafa kina takewa.
Shin ya ta ko kin san irin kyautar darajar da Allah yayi miki kuwa da wannan salihin mijin da
ya baki? Ina jiye miki ranar dana sani.... wadda aka ce ..... keya ce, tun da sauran mutuncin ki ki
kankaro shi a idon Mukhtar, kafin ranar da zaki yi nadama mu kuma bama tare da ku.
Jalan ta cigaba da yi mata nasiha iri-iri mai kashe jiki amma banda jiki mai kunnen kashi irin
na Amani. Don nasihar da waazin wani na shiga ne wani na fita ta daya kunnen. Ta kawo wasu
kwayoyin magani ta bata ta ce ta hadiya yanzu tana gani kuma a gaban ta. Sai Amani ta tuno
Haj. Muna, itama hakika ta bata irin wadannan kwayoyin kuma bata yarda ta sha ba, yanzun ma
da Mamma Jalan ta dage sai ta sha a gaban ta, can kasan harshen ta ta kai su ta danne su da
harshen ta ta kora ruwa. Mamma Jalan ta hada garwashin lantarki (burner) nan da nan ta zuba
wani turare irin nasu na musamman tace ta tube ta turara jikin ta. Wanna ba musu ta yi, tunda
turare ne kawai, sannan Jalan ta raka ta har kofar entrance na masaukin Mukhtar, tace ta wuce
ciki tana kallon ta.
Haka ta tsaya daga nesa sai da ta tabbatar Amani ta buga kofar, ta ga sanda Mukhy ya zo ya
bude, da farko kamar ba zai bata hanya ta shiga ciki ba, don ta ga kamar jayayya suke, bata dai
jin me suke fadi sosai kasancewar (by nature) din sa, Mukhy bai da daga murya wannan sai
Amani idan ta so yin rashin kunya.
Mukhtar yana bude kofar ya ga Amani ce, sai ya ki bata hanya, cewa yayi lafiya? Me kika zo
yi wajen dan shege?
Idanun ta suka yi rau-rau, a rayuwar ta bata taba yin maganar katobara ta yi nadama irin
wannan maganar ba.
Da ana amai a lashe da tuni ta lashe ta, ta maida ita cikin ta.
Banda Mamma ta sako ta gaba me zai kawo ta dakin sa da daren Allahn nan har ya gaya
mata bakar magana?
Sunkuyar da kai tayi tana hura hanci da wasa da yatsun ta, sannan ta juya ta tofar da
kwayoyin maganin da ke bakin ta, Mukhtar ya bi abinda ta tofar da kallo amma bai san mene
ba, ta ce ai da gani na ka san nima takura ni a ka yi na zo, ka san da bazan zo ba, don bani da
bukatar komai a wurin ka ya ce sai ki juya ji koma, shege baya bukatar komai a wurin ki shima. Ta daga idanun ta cike da hawaye ta ce a rayuwa ta ban taba bada hakuri ga kowa ba, ban
taba yin magana nayi nadamar ta ba, amma wannan na yi, na maida wannan kalamin ciki na,
na kora su da ruwa nayi flushing din su tun daren dana furta su.
Ina baka hakuri a kan su, don nima na san basu dace ba, sharrin zuciya ne da fushi, amma
idan ka cigaba da maimaita min su da rike ni da su a ran ka, hakika ka cutar da ni Mukhtar!.
Mukhtar sai ya juya ya shige ciki ba tare da ya iya ce mata komai ba, don (hes cool and
shocked) da sunan sa data ambata yau, ya kuma san da gaske take bata taba baiwa kowa
hakuri ba sai yau. Tabbas UWA daban ce, kuma uwa ta yi a rayuwar diya mace. Wadda ta rasa
UWA ayi mata jajen rashin da bazata mayar ba, har abada!!!
(Allah ka yi wa iyayen mu gafara ba don sun mutu ba, wadanda suka rasa nasu Allah ka kai
rahma da haske da kamshi kabarin su- Takori).
Ba don Mammah ta yi rantsuwa sai ta kwana a dakin ba, da daga nan zata juya ta koma, ai
dai ta yi masa sallamar data dace, kuma da ya bata hanya bai ce ta shigo ba, itada kan ta data
gaji da tsayuwa ta shiga dakin a fusace, amma bata rufe kofar ba ta bar ta a bude fayau.
Sai shi ne da ya ga sauro zai cika dakin, ya mike ya rufe ya wuce ya koma ya cigaba da
abinda ta tarar yake yi kafin ta shigo wato booking din jirgin Lagos online, ta cikin system din sa.
Da shigowar ta dakin atmosphere din dakin gabadaya ya canza da wani irin sihirtacccen
kamshi irin na turaren da ake yiwa amaren kasar Saliyo, wanda a makwabtan su wato kasar
Gambia kawai ake samun shi.
Yana tambayar kan sa wane irin fitinannen turare ne haka Amani ta fesa, mai barazanar daga
masa hankali? Ga gashin nan ya sha wani irin setting an kanannnade shi ya zubo a gaban
goshin ta ya zagaya ta bayan kunnen ta, ya kwanta akan wuyan ta, kasancewar laffaya ce a
jikin ta sosai gashin ya fito ya kwanta a kan dogon wuyan ta. Yana aikin amma hankalin sa ya rabu biyu, neman shidewa yake yi. Allah kadai ya san wane
irin turare Jalan ta turarawa yar ta. Domin dai a karshe Mukhtar sai kashe kwamfutar sa yayi ba
tare da ya san takamaimai ya gama booking din ko bai gama ba?.
Sai ga vedio call din Alhaji ya shigo masa ta whtsp dinsa, alamar yana son magana da shi.
Kasa daga wayar yayi ya dai zuba ma kiran ido, sakamakon yadda kasala mai yawa ta rufe shi
kuma baya cikin irin mood din da zai iya magana da Alhaji.
Tana kallon sa ya mika hannu ya kashe wayar bakidaya, ta tsaya taki motsawa daga inda
take tsaye, ta harde dogayen kafafun ta ta kuma nade hannun ta a kirjin ta tana harare-harare,
ita bata zauna ba ita bata rage laffayar jikinta ta kwanta ba.
Mukhtar da kyar ya iya mikewa ya rage fitilar dakin mai haske ya bar shudiya mai
rangwamen haske, wadda a turance ake kira dim light daga nan ya lallaba ya haye gadon sa ya
ja bargo har kan sa ya kudundune, ya bar ta a nan tsaye don ya fahimci neman rigima take yi
da shi. Amani ta yi kwafa, miskilancin sa ya kara fusata ta, sai ta karasa gadon ta dauki filo daya ta
jefa a kasa, ta warware laffayar ta ninka ta biyu sannan ta rufu da ita, ta kwanta akan kafet mai
laushi tana cewa a ranta me zai kaita hawa gadon nan ko da ya kula ta? Balle yayi wannan
shakulatin bangaron da ita? Ai ko gadon zinare ne ta bar masa. To amma ta kasa barci bayan ta kwanta din, jin numfashin Mukhtar ya sauya kasancewar
dakin yayi tsit, babu komai sai bugun numfashin su da sururun iya kwandishan, yadda
numfashin sa ke sauka da sauri da sauri a kunnen ta, tamkar zazzabi da masassara irin wanda
ya same shi a Freetown ya ci karfin sa. Tana jin sanda ya dauko filon sa ya dawo kasa shima, zazzabi sosai da sanyi yake ji, dumin
jikin mace kawai yake bukata a wannan lokacin, ya fahimci cigaba da kwanciyar sa shi kadai a
gadon daidai yake da ya haka rami ya kashe kan sa... akan matar da addini ya riga ya bashi
damar komai yake so a kan ta. Akan me zai yi ta cutar da kan sa har haka? Shi ya san matsayin sa na namiji kuma matashi mai jini a jika, sannan jinin Issouffou
Masaoudou, yayi matukar hakurin da ba kowanne namiji kamar sa ne zai iya ba a kan mace. Ya
san yana da hanyar da zai samu kan Amani ko da bada yardar ta ba, amma kasaitar sa bazata
bari ba, yana ji a ran sa yafi karfin ya yi forcing mace ta kwanta da shi (by force). A yanzun da
tura ta kai bango, kuma Jalan ta warware ego din sa, ta hanyar wannan kamshi na jikin Amani
da su kadai matan Saliyo suka san sirrin da ke cikin sa, a yanayin da yake ciki yanzu, sai ya
manta ko waye shi, da wannan pride din nasa, sabida ba shi ke sarrafa jikin sa a yanzu ba.
Hakanan ya tabbata suka kwana a haka Allah ma sai ya tambaye shi dalilin cutar da gangar
jikin sa, alhalin jikin sa ma da kowacce gaba ta jikin sa na da hakki mai girma a kan sa, bai
kamata yayi ta biyewa Amani yana cutar kan sa ba, yarinyar da kullum sai ta saka shi a tashin
hankali da wankan janabar babu gaira babu dalili. Yaya akayi yaya akayi Amani bata sani ba don ta soma samun barci, sai kawai taji Mukhtar
ya bi ya kwanta a gadon bayan ta, yana sakin ajiyar zuciya. Domin a yau dauriya da jarumtakar
sa sun idasa karewa. Koko in ce, Mama Jalan ta karar da su da sirrin ta.
Hannayen sa ya saka ya riko hannun Amani dasu, cikin siga ta nuna bukatuwar miji zuwa ga
matar sa, matar ma wadda yake tsananin so, ya ratsa yatsun sa sosai cikin nata, sannan ya
damke su da karfi, kwanciyar sa a gadon bayan ta da yanayin rikon da yayi wa hannun ta a
bazata, ya tsorata ta, domin bata zata ba ko da wasa, a tunanin ta Mukhtar ba zai taba iya hada
jiki da ita ba, don yadda bata son sa ta tabbata haka shima baya son ta, kuma wannan alamari
ta san cewa baya faruwa sai da soyayyah, daga haka ta ji Mukhtar ya janye laffayar jikin ta data
rufu da ita, da zafin nama ya janye laffayar, ya saura Amani da tiny rigar robar jikin ta, Mukhtar
ya ga body structure din Amani ta cikin hasken dim light wanda hakika Allah ya yi wa Amani
halitta wadda ta kasance daya cikin dubu, a cikin na mata dubu kafin a samu irin na matan
Saliyo sai an tona, bai taba zaton haka Allah ya kera Amani ba, wanda hakan ya karasa susuta
komai nasa, ya birkita dan mutanen Diffa. Kafin ayi haka Amani ta ji Mukhy ya rungumeta ta
baya sosai, da wata irin tight hug (runguma tsatstsaura), ya manne ta a jikin sa yana sauke
numfashi mai matukar wahalar fita daga huhun sa.
Tana iya jin yadda jikin sa ke shaking, jijiyoyin jikin sa ke vibrating, yana kara shigewa sosai
cikin jikin ta da kadan kadan har ya shige jikin ta bakidaya, wanda hakan ya gama tsorata ta, ta
soma