Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
ina ya dace ta je ba, in ta shiga duniya saboda bakin cikin Mukhtar
ita tayi asara domin kuwa sunan ta ne zai koma karuwa hakan kuma ba zai hana Mukhy
rayuwar sa cikin sukuni da sakewa tare da mahaifin ta ba, kamar yadda yake yi tana nan,
watakila ma har Daddy ya nema masa wata yar mutuncin ya aura masa, ita su manta da ita da
rayuwar ta gabadaya, su shafe babin ta, wannan itace babbar nasarar da Mukhtar zai yi a kan
ta da zata dauwama tana haunting din ta, ta dauwama cikin cizon yatsa ba tare da ta iya
ramawa ba.
Don haka ta yanke shawarar tafiya Bauchi gun Hamidah. Kafin ta samu damar da zata wuce
Sierra Leone daga Bauchin, ko a kafa ko a kan fiffiken ta, zata nemo Innar ta. Duk da ta san
Hamida bazata taba bin bayan ta ba, cewa zata yi a nemi zabin Allah a yi wa iyaye biyayya. Ta
tabbata wadannan sune kalaman Hamidah da basa taba canzawa daga haka. Tuni ta haddace
su har bata son kari.
Zata iya yi wa Daddy kowacce irin biyayya amma banda ta auren kaskanci irin wannan da ya
yi mata, babu kaskacin daya wuce mata wannan a duniya, duk mazan duniya a ce ta rasa miji
na kece raini kamar yadda take macen kece raini sai Mukhy, wato yaron sa da tafi tsana a
duniya a bisa dalilai da hujjojin ta wadanda take ganin sun isa hana ta karbar wannan auren ko
me Daddy zai yi mata a kan sa kuwa.
Sai da tafiya ta mika sosai, suka yi wa shiyyar garin Katsina fintinkau sannan ta gaji da
kukan, ta fiddo hankaci ta share fuskar ta, ta fyace hancin ta sannan ta dauko wayar ta data
kashe ta kunna.
Kamar jira wayar take a kunna ta, sai ga kiran Hamida Balewa ya shigo. Ta yi ajiyar zuciya, ta
sani Hamidah is always there for her whenever she needs her, duk da basu da raayi guda a kan
komai, amma a kalla tana sauraron ta attentively tana taya ta damuwa da damuwar ta, in abin
kuka ya sameta suna kokawa tare, in na bakin ciki ne ma suna yi tare, kuma tana bata shelter a
gidan su a duk sanda ta bukata, da shawarwari masu inganci duk da ba duka take dauka ba,
kafin ta daga wayar muryar ta duk ta dusashe don kuka.
Hamidah tace Sahibah kina ina? Gani a gidan ku, maigadin ku na fadin baku nan duka gidan
kun yi tafiya, yanzu ina zan same ki?
Da dusashshiyar muryar ta data ci kuka ta koshi ta ce, Hamdy, mun yi sabani toh, ina hanyar
Bauchi yanzu haka nima, wajen ki na nufa, don bani da wajen zuwa.
Ta fashe da kuka. Hamidah na jin haka ta fahimci komai, ko dai an daura, ko ana gab da
daurawa shine ta gudo.
Alright Sahibah, ki isa Bauchi lafiya, zan yi waya da Mama yanzu a gyara miki daki na don
watakila ki rigani isa, zan sa direba ya juyo da ni Bauchi nima yanzu duk da na gaji, amma ba
zan kwana a koina ba tunda ba kya nan gara in juyo, tafiyar dare ce dai na san ta same mu.
Suka aje wayar a tare. Sannan Hamida ta kira Mahaifiyar ta Hajiya Muna ta gaya mata batun
zuwan Amani, amma bata gaya mata ko a kan menene ba, mutum ce mai kiyaye sirrin wanda
ya amince mata kwarai da gaske, ta roki Maman ta Haj. Muna kan ta lallashi Amani ta ci abinci
tayi wanka ta kwanta ta huta kan ta iso. Ta kuma ce, don Allah Mama a nemi Panadol a bata ta sha kafin ta kwanta.
Sai dare suka shiga Bauchi, suna ta waya da Hamida, ita tasa direban Baban ta ya zo tasha
ya dauki Amani zuwa gidan su dake unguwar Fati Muazu. Har dakin Hamidah mai aiki ta shiga
da kayan Amani bisa umarin Hajiyar Hamidah. Sannan aka kaita falon Haj. Muna.
Hajiya Muna ba tun yau ta san Amani ba, da irin amintakar da ke tsakanin ta da Hamidah tun
suna sakadire a Ulul Albaab Science Secondary School Katsina suke tare, ta dubi kyakkyawar
fuskar Amani ta ga duk ta yi zuru-zuru idon ta ya kode don kuka tayi wujiga wujiga da wahalar
zaman motar haya don bata saba ba, nan take ta gane ba zuwan arziki Amani ta yi ba wannan
karon kamar yadda ta saba, don duk zuwan da take yi Bauchi a jirgi take zuwa har wani lokacin
da rakiyar yar aikin ta Rakiya wadda ke daukar mata jaka.
Yau kuma ta gan ta helter-skelter daga ita sai jakar kayan ta babu alamun tun wayewar garin
yau ta yi wanka. Amma tunda basu gaya mata me ya faru da ita ba da yasa ta irin wannan
balaguron wahalar sai itama bata tambaya ba, tace a ran ta in ta yi wari zata ji ne.
Ta sa aka shiryo abinci mai rai da motsi ta saka ta a gaba da lallashi da ban baki irin na uwa
har sai da ta yarda ta ci kadan, amma jin abincin nan Amani ke yi tamkar dussa sabida yadda
zuciyar ta ke cunkushe da bacin ran Daddy da abinda yayi mata. Ba don mahaifi mahaifi bane
kotu zata yi karar su su biyun alkali ya bi mata hakkin ta. Amma me? Ta sani duk tsiya tana jin Daddy a ran ta, tana son Baban ta wani irin so, ba zata
so ya tsaya a mumbarin shariah da yar sa ta cikin sa ba ko da kuwa ace ta samu tabin hankali
ne.
Amma Mukhtar kam will pay for that, btunda ya amince aka yi mata auren dole da shi bazata
taba yarda ta zama matar sa ba, bai isa ba bai kai wannan matsayin ba, bari Hamidah ta zo su
nemi mafita, tana tunanin tafiya Saliyo a cikin satin nan kawai in ta je kuma ta tafi kenan, ko a
gidan talbijin da radio ne zata nemo Maman ta mai suna Jalan, tunda Daddy ya ce suna kama
sak, kuma sanda ta haife ta kamar girman ta take in ji Daddy. In ya so sai ta yi amfani da hoton
kanta da kanta ta nemi Maman nata da shi (a wautar ta). Duk da dai ko hoton ta bai taba nuna
mata ba. Amma dai zata je Saliyo kota halin kaka, ko da zata bi lungu-lungu layi-layi ne tana
tambayar mai suna Jalan mai kama da ita. Abu daya kenan da zata iya fadi a kan Maman nata
watau sunan ta.
Haka tayi ta tunani irin na soki burutsu da rashin madafa. Ta yi wanka a dakin Hamida ta yi
sallolin da ke kan ta. Tana cikin sallah tana kallon kiran Mukhtar na shigowa wayar ta da sunan
da tayi saving lambar sa da shi. Ya kira sau biyu bata daga ba sai bai kara ba. Don shi mutum
ne mara jure wulakanci.
Can kuma sai ga na Daddy. A lokacin ta idar da sallah. Amma daga Mukhtar din har Daddy
din sai ta rufe ido taki amsawa, babu wanda ta amsawa don a ganin ta basu da abinda zasu
gaya mata ta yafe wannan laifin da Daddy yayi mata.
Ta bar su suka yi ta kira har suka gaji suka saurara mata.
Daddy ya mata dogon text wanda a ciki yayi ta lallashin ta abun tausayi, yana tambayar inda
ta shiga? Yace tana so hawan jinin sa ya tashi ko? Tana so rabin jikin da yake motsawa shima
ya karasa mutuwa saboda damuwar rashin ta ko? Amma ko karantawa Tafisu bata yi ba ta
share shi (deleting) don ta san data karanta zata samu rauni a zuciyar ta ta fasa aiwatar da
kudurin ta.
Sai ta kira Hamidah ta gaya mata ta sauka lafiya da irin tarbar da Mama tayi mata, tace I
really appreciate Mamas welcome, sai naji kamar Mama na ce, kin ji dadin ki Hamdy, mother is
everything, yanzu wa ya isa ya yi miki auren dole Mama na raye? Auren ma da bawan gidan ku.
sai kuka. Hamida ta yi maza ta ce akul Sahibah! Ki gyara kalaman ki, ta ina ya zama bawan gidan ku?
Don kawai yana ma Daddy aiki yana biyan sa albashi? Kin san bauta kuwa? Kin san tun a wane
karni aka daina bauta sai ta Ubangiji?
Tukunnama ta ina neman halal da dogaro da kai ya zama bauta? Sahibah, Ubangiji da ya
halicci dan adam ya girmama shi ya karrama shi a kan duka sauran halittu, ki daina kaskanta
dan adam ko waye shi wai don yana ci a karkashin ki, musamman shi Mukhtar a yanzu, ki ringa
sanin irin kalaman da zaki ke furtawa a kan sa yanzu, sabida mijin ki ne, da iyaye suka daura
muku aure na musulunci ke da shi. Ba ruwan malaikun ki (Raqib da Atid) da cewa wai bakya
son sa aka aura miki, dukkan furucin ki da ayyukan ki a kan sa zasu rubuta ne kawai ga lahirar
ki.
In haka ne ina amfanin kalaman batanci da kaskanci ga mijin auren ka ko yaya yake?
Balle Mukhtar bai yi kama da yadda kike kaskanta shi ba, bai yi kama da wulakantaccen
mutum ba. Wai me kika dauki kanki ne Amani?
Inna akramakum indallahi atqaakum!
Yanzu dai ki bar komai a hannu na sai na iso, sai mu shawarta abun yi, ki kwantar da
hankalin ki kin ji Sahibah? Idan ina nan babu mai miki abinda ba kya so in zuba ido, wallahi sai
inda karfi na ya kare wajen taya ki kwatar hakkin ki, amma banda akan mahaifin ki, ko yaushe ki
dinga tuna matsayin Daddy a gare ki, da wahalar da yayi dake da rayuwar ki, da tsayin lokacin
da ya dauka yana faranta miki, ko a cikin iyaye shi na daban ne, ya fi karfin yayi hukunci a kan
rayuwar ki ki tsallake ki zauna lafiya da Ubangijin ki.
Ko nasihar Hamida ta shige ta, to fa bata bar ta ta yi tasiri mai yawa a tare da ita ba, duk da
ta san Hamida gaskiya ta fada. Sai ta hau lullube tasirin kalaman Hamidah da hujjoji na son
zuciya, tare da cewa ko me Daddy yayi mata a rayuwa hakkin sa ne ya yi mata tunda shi ya
haife ta ya kuma raba ta da uwar ta, amma bashi da ikon yi mata auren dole. Ta koma ta jingina
bayan ta a gadon ta kwanta a gadon Hamidah ta rufe idon ta, ta ja duvet ta lullube har saman
kan ta, tana jin duniya na kara kuntata a gare ta in ta tuna igiyoyin auren Mukhy har ukku sun
hau kan ta.
A haka Hamidah ta iso gidan ta tadda ita. Ta dauka barci ta ke yi, bata san ta dai rufe ido
bane kawai tana dandanar azabar zuciya, sai ta aje jakar hannun ta da mayafin ta ta shiga toilet
domin ta rage marar ta, kafin ta fito Mukhtar ya cigaba da kiran layin Amani. Wayar na gefen
kan ta amma ta saka ta a silent don ma kada su cigaba da damun ta shi da Alhaji don haka
bata san ma ana kiran nata ba. Mukhtar kuwa Alhaji ne ya saka shi a gaba da magiya kan yayi ta kiran layin nata ko Allah zai
sa ta dauka, yayi mata albishir din ta dawo gida daga inda ta yi kaura a kaita Sierra Leone har
dakin mahaifiyar ta in har an same ta a raye, in dai zata yi hakuri da mijin da ya zabar mata, ya
ce, Mukhtar ya lallashe ta kawai ta dawo, in yaso ta fadi duk abinda take so ya yi mata, don cikin
hukuncin da ya yi babu canji har abada ko bayan ran sa Mukhtar zai cigaba da rikon igiyar
auren ta.
Shi yadda Alhaji ke shagwaba Amani yana tattashin ta da gudun bacin ran ta abun yana
matukar bashi mamaki da tuajjibi, wai dama akwai irin wadannan iyayen a wannan zamanin da
muke ciki, ko a kasar shi ne kawai babu irin su? Ko a nashi lardin ne kadai babu su?
Hamida taga wayar Amani na haske sai ta lallaba ta leka. Sunan da aka yi saving mai kiran
da shi shi ya tabbatar mata Mukhtar ne da kiran nan ba wani ba.
DIRTY HUMAN BEING!.
Dariya ce mai karfi ta ji tana son kwace mata, ta toshe bakin ta. Ta lallaba ta dauke wayar ta
fice da ita can harabar gidan su ta samu kujerar roba fara tas ta zauna a karkashin bukkar shan
iska ta gidan su, sannan ta amsa wayar Mukhtar da sallama.
Daga jin sallamar da amon muryar da nutsuwar da ke ciki muryar kai har ma da tarin respect
ya san ba Amani bace. Ga dukkan mamakin sa, sai ya ji wani tsoro da fargabar abinda zaa ce
masa ya samu mai wayar na shigar sa, a hankali ya amsa sallamar Hamidah, sannan duk suka
yi shiru na yan dakikai irin na rashin sabo da juna, Hamidah ce ta karya shirun da cewa. Mr. Mukhtar ne ko?
Ya amsa mata, rather subdued, cikin sautin sa da alamar mamakin inda ta san shi haka farat
daya ta ambaci sunan shi, bai yi tunanin ma Amani ta yi ajiye numba din sa ba balle a ce
tanazancen sa da wani nata a yadda ya san bata son sa dinnan bata kuma son zaman sa a
gidan su, kuma bata so wata alaqa take hada su.
A kasaice yace mata eh, nine. Excuse me pls, Ko zan iya sanin daga ina aka amsa wayar
nan?
Hamidah tace daga garin Bauchi ne. Bauchi?! Mukhtar ya tambaya cikin mamaki, a me ta je,
kuma wa ya kai ta? Ya jerowa Hamidah tambayoyin a jere a sukwane, don kuwa bai ga alamun
ta fidda ko sisi daga account din ta ba, balle ya yi tunanin ta hau jirgi. Hamidah ta gaya masa
gaskiyar komai na yadda suka yi sabani ita da Amanin, ta tafi Katsina wajen ta ita kuma ta taho
wajen ta a Bauchi. Mukhtar har da ajiyar zuciya da ya ji cewa a (Sharon) wato motar kasuwa ta
je Bauchi ita kadai, ya tausaya mata a ran sa, don ya san wani abu ne da bata saba ba, duk a
cikin kiyayyar sa ne ko meye ma ya san zata iya, yace,
pls my sister do me a favour, kada ki gaya mata na kira kuma kin amsa, ki bani address din
gidan naku zan zo in tafi da ita gobe, saboda a bisa umarnin mahaifinta Sierra Leone zamu
wuce daga nan gidan ku kai tsaye in sha Allah, zan canza booking din da nayi mana ya zama
daga Bauchi zamu wuce Lagos, inda zamu hau jirgin Freetown.
Hamidah ji tayi farin ciki ya lullube ta kamar ita ce Amanin, burin kawar ta at last zai cika. Zata
ga Innar ta! Ta san kowacce irin damuwa Amani ta saka kanta a ciki a kan auren ta da Mukhtar
zata zo da sauki muddin zata ga mahaifiyar nan tata data kallafawa rai. In ta ga dama ma tace
bazata dawo ba, hakan zai fiye mata kwanciyar hankali in har Amani tana tare da Maman ta,
fiye da in ita Hamidan ta ki bata goyon bayan bijirewa Daddy ta bar gidan su ta nausa wani
wajen da bazaa gan ta ba, don ta san halin aminiyar ta sarai ba tun yau ba, bata saba in tana
son abu ko ta saka kanta abu a hana ta ta karfi ba, tunda ta taso ya riga ya saba da yi mata
komai take so komai tsaurin sa, shi yasa yanzu Daddyn ke shan wahalar ta da ya zo yana son
tankwara ta ta karfi, bayan tun tasowar ta ba haka ya sabar mata ba.
Sun yi sallama da Mukhy a kan in ya sauka a Bauchi goben zai kira ta, ta bashi lambar wayar
ta, har rokon sa ta yi da kada ya kama hotel in ya iso, tace akwai gidan saukar baki a nan cikin
gidan su, tunda dole sai sun kara kwana a Bauchi kan su wuce Lagos din.
Bayan sun gama wayada Hamidah ya gayawa Alhaji ashe wajen kawar ta ta tafi a Bauchi.
Nan dai hankalin su ya kwanta suka soma shirin komawa Katsina washegari. Baba Idi ya ce
wallahi idon sa idon Amani sai ya zane ta.
Sai da suka tsaya a Funtuwa Sahura ta yi sallama da yayanta ta dauki kayan ta sannan suka
wuce Katsina, har da Kamilu, wanda Mukhtar ya ce ya dinga kula da Alhaji har ya dawo tunda
zai yi tafiya gobe. Duk irin kulawar da yake masa ya nunawa Kamilu, ta ci da sha da shan
magani da tsaftace masa jikin sa, kuma Kamilu yayi alkawarin kwatantawa. Alhaji