AMANI 2 COMPLETE BOOK BY TAKORI.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   5 / 13

12K to 15K   out of 38K words

haka yaji abin weird a gare shi.
Seat din shi a cikin jirgin kusa da nata ne, tana daga jikin taga a takure yana gefen ta. Amani
tana ji ana a daura belt jirgi zai tashi amma taki daurawa. Ba don tana da burin ganin Innar ta
ba, kafin Allah ya dau ran ta da ta roki Allah jirgin ya fado duk su mace da dai ta zauna da shi
har abada a matsayin mijin ta uban yayan ta. Jirgin Max Air ya daga da su, Mukhtar sai ya saka hannu a bayan kwibin ta yana fastening
mata belt din, ko babu komai diyar Alhaji ce shi kuma servant din Alhaji ne, don haka ba faduwa
bane don ya hidimta mata a dalilin Alhaji Usman Faskari ne, jirgin bai dire su a ko'ina ba cikin
dan kankanin lokaci sa a birnin Ikko. Da suka sauka shi ya dauko kayan su again suka fito daga terminal, mai taxi ya zo gaban su
yana tambayar ina zasu je? Mukhtar sai yace masa any nearest good hotel. Amani bata ji ba,
don a lokacin tana waya ne da Hamidah tana gaya mata gasu a Ikko, amma bata ga an ce a
tsaya a shiga jirgin Freetown ba, Hamida ta fashe da dariya ta ce to kika sani ko jirgin yamma
ne ko na dare? Ta ce,
bar zancen wasa Hamidah, kina gani fa ya tsayar da taxi, gidan wa zamu je?" Hamidah ta
kasa tsayar da dariyar ta ta ce "ki fidda ni a lamarin ki, tunda babu arziki a ciki, naga alama baki
san Annabi ya faku ba, ina laifinsa ya baro komai nasa da ayyukan sa da Alhajin sa, don ya
dangana ki da Maman ki?" Amani ta ce "to ni na saka shi? Ban ce a bar ni a ga iyawa ta ba?
ban ce a bar ni zan kai kaina ba? Kuma in jirgin yamma ne zamu shiga ba waiting lounge zamu

je mu zauna ba?
Hamidah ta ce.
"Ki tambaye shi mana da kan ki ina zaku je din? Me yasa zaa yi transit? Ni Hamida ina nan
Bauchi ina na san me kuke ciki ke da mijin ki a birnin Ikko?
Dole ta kyale Hamidah don daga karshe ma ta kashe wayar ta daga gama fadin hakan
hakan, bata so Mukhtar ya san da ita Amani take waya kada ya dauka ko da saka hannun ta a
rashin mutuncin da Amani ke yi masa, fatan ta Allah yasa wannan tafiya ta zama silar shiryawar
su da kuma sanadin alkhairori a cikin auren su. Already mai taxi ya saka kayan su a bayan
motar, ya budewa Mukhtar gidan baya ya shiga.
Hajiyar tsayawa tayi kikam tana jiran karin bayani na inda zaa je daga gare sa. Amma bata
ga alamar Mukhy na da niyyar yi mata bayanin komai ba, sai ma wata muguwar harara da
Mukhtar din ya sakar mata, wadda ita kan ta ma amsa ce na cewa ba bayanin da zata samu
daga bakin sa. Zata yi magana ya ce a fusace, idan kika sake kika tambaye ni ina zamu je? Zan ce miki sayar da kan ki zan yi a Ikko
malama. Don kan naki zai yi tsada, kamar yadda kike yarinya mai tsada, na tabbata zai isheni in
ja jarin da zan yi kudi, in tashi daga matsayin yaron Baban ki, ko kya daina raina ni.
Sakatoto ta yi da baki tana kallon sa. Kafin ta yi aune taji ya fizgi hannun ta ya saka ta a
bayan motar ya rufe. Shi kuma direba bai bata lokaci ba ya ja motar.
Hotel din dake manne da Lagos International Airport ya kaisu wa to Legend Hotel. Mukhtar
ya sallame shi da kudin da suka zarta abinda ya bukata, Amani ta zauna na tsayin lokaci a cikin
motar, ta kasa fitowa daga motar nan, kai ko kwakkwaran motsi ta kasa, ta rasa inda zata saka
kan ta ta ji dadi a wannan lokacin. Sai wani irin kokawa take da numfashin ta saboda bakin ciki.
Saboda (this will be the first day) da zata kebe da namiji, kuma mai amsa sunan mijin ta a
muhalli guda, sannan wai a ce ba kowa bane mijin face MOUKHTAR DIFFA. Wani kwayan
mutum guda daya da duk duniya babu wanda ta ke wa kallon bai isa ba, kallon abnormal
human being, kuma matsala ga farin cikin ta irin sa. Ta tsani halayyar sa, girman kan sa da
charismatic personality din sa, ta raina shi kamar yadda ta raina Karen kofar gidan su, tana
ganin sa a ba komai ba, face yaron gidan su, mai hidimtawa Alhajin ta don samun na abinci,
wanda karfi da yaji ya kwace mata mahaifi, ya shiga tsakanin soyayyar dake tsakanin ta da
mahaifin ta, soyayya mai asali da tushe wadda Alhaji ke yi mata.
Zuwan Mukhtar cikin rayuwar su ya canza wannan. Ya sauya rayuwar gidan su gabadaya,
ya sauya mata mahaifi da dabiun sa. A dalilin shi mutum ne mai charismatic personality da duk
inda yaje sai an so shi. Ta fahimci kamar ita kadai ke kin Mukhy a duniyar subhana, kuma
kamar shi din ya zame mata dole a yanzu, aure ba wasa bane duk da bata da ilmin sa, abinda
ta sani akan aure shine mijin da igiyoyin auren ta ke hannun sa, sai yadda ya ga damar yi da
rayuwar ta da gangar jikin ta har wani lokacin, da zuciyar ta. Ya Rabbal Alamin. Wane irin balaI
ne ya tunkaro ta haka?
Saukar ta daga motar nan na nufin yau zata kwana daki daya da Mukhtar Diffa! Matsayin miji
da mata na Sunnah. Wannan wace irin bakar rana ce da bata san kaddarar da ta yi mata
sanadin ta ba? Ai ko Mukhtar bai sayar da kan nata ba kamar yadda ya ce cikin gatse, ta
tabbata sai ta gwammace bata san wani mai suna Mukhtar ba, daga irin halayen sa da ta
fuskanta na son girma da rashin daukar raini, muddin bazata sauke kai ta yi masa irin
girmamawar da yake so, ya kuma taso ya ga ana yi masa ba, ya ga mace (wato mahaifiyar sa)

na yi wa mijin ta (mahaifin sa) a gidan su ba, wani zubin tamkar ta yi masa sujjada, to kuwa zata
sha wahalar sa.
Ya riga ya san babu wannan tarbiyyar a tare da ita, to daga yau zata fara daukan ta bisa dole,
in ba haka ba bai da wani courage na kai ta gaban iyayen sa a matsayin matar sa uwar da ya
zabawa yayan sa.
Tunanin ta ya gama bata cewa Mukhtar ya tsayar da su a Lagos ne don ya samu damar da
ya dade yana neman samu a kan ta, wato damar da zai wulakantata son ran sa, a inda bata da
mai ceton ta sai Allah, shine dalilin da yasa ya shirya musu kwana wuri guda da sunan transit,
bata yi tunanin cewa Mukhtar mijin ta ne da shariah ta halarta zaman nasu waje guda ba a
yanzu.

Har Mukhy ya je ya kama masu daki ya dawo Amani na zaune cikin mota bata ko motsa ba
tana ta tunanin da bai bata mafita ko guda daya ba. Ya dauki kayan su a booth ya kai ya dawo
tana nan yadda ya bar ta; ihu ne kawai bata kurma ba. Damuwar duniya da bacin ran da take
ciki ya gama bayyana kan sa a kan kyakkyawar fuskar ta, wadda yanzu ta hade tayi jazur
idanun ma suka yi jazur abin ki da farar mace.
Mai taxi ya kunna mota ya ce ta fita shi zai wuce, sai ta juya kai ta dubi inda Mukhtar ke
tsaye, ya harde hannuwan sa a kirji yana kallon ta, yana jira ta gama sake-saken wadda zata
fishsheta, kafin ya gaya mata cewa shima bai shirya kwana daki daya da mace ba, don bai taba
ba, kuma bai shiryawa rayuwar sa hakan a nan kusa ba, don bai shirya sallama samartakar sa
ga macen da bata san darajar shi ba.
Da a ce zai iya, da ya gaya mata hakan ko don hankalin ta ya kwanta, cewa daki ciki da falo
ya kama musu; shi ciki ita falon, don ma ta daina kissima abinda take kissimawa wanda shi bai
taba kawowa ran sa ba.
Mai taxi sai ya koma masifa yana fadin ta fitar masa a mota zai tafi, haka dole kanwar na ki,
Amani ta ja dogayen kafafun ta ta fito masa daga mota, rataye da yar farar hand bag din ta mai
matukar kyau samfurin LV (Louis Vuitton), da cokalelen takalmin ta kamar zai huda kasa, sai
Mukhtar ya saki ajiyar zuciya ba tare da ya san ya yi ba. Ya juya, ita kuma ta bi shi a baya, a
haka suka isa har cikin lifter, inda suka shiga ya tashi da su ya sauke su a kofar dakin da ya
shigar da kayan su.
Bata da zabi banda na bin sa ciki, tana tafiya tamkar ba ita ba, sabida yadda tayi cooling. Kan
ta yayi down, bata ko iya dago kan ta. Duk da haka ba wai ta rasa komai bane daga izzar ta da
takamar ta na halitta ba. Wadanda da su Allah Subhana ya halicce ta. Kuma dai an ce hali
zanen dutse ne amma tabbas a wannan lokacin bakin ta kanwa yayi laasar. Sai dai da yake an ce aure yakin mata, ni TAKORI na yarda da wannan zaurancen, domin
kuwa hakika yau naga tasirin sa a tare da jarumar mu mai kasaita da izza wato Amina (Amani)
domin tasirin sa ya kurda cikin jikin ta yana yaqar ta ta koina ba tare da ta sani ba, dalilin da
yasa tayi dan sanyi kenan, a lokacin da Mukhtar ya sanya mukulli ya bude kofar dakin nasu, ya
bata hanya ta fara shiga, sannan ya wuce ciki ta bishi a baya, sai dai a wannan lokacin idan ka
lura da kyau zaka fahimci gab take da fashewa da kuka wanda ta san idan ta yi shi babu mai
taimakon ta!!!
**** **** ****

​Suna shiga dakin Mukhy ya maida kofar ya rufe, sannan ya dau jakar kayan sa ya wuce
ciki batare da ya kara bi ta kan Amani ba. Don yunwa yake ji sosai, in yana jin yunwa kuma (at
times) zuciyar sa a kusa take.
Da ta gaji da tsayuwa dole ta nemi kujerar falon ta zauna, tana maida numfashi, so ta ke ta yi
wanka ko ta ji dadi a ran ta da jikin ta, sabida yadda jikin ta ke mata danko danko na gajiyar
tafiya, amma ta daure don tana jin nauyin shiga toilet alhalin yana dakin. A ran ta tana jira ya zo
ya ce ta shiga ciki ita ta hau gadon, kada ta yi ciwon baya in ta kwana akan kujera, in ya so shi
ya kwana a falon, amma gogan nata sai ji ta yi yana kakkabe gadon, da alama kwanciyar sa zai
yi. Ita kuwa ko oho.
Amani ta dauki kayan wankan ta a jakar ta ta shiga toilet ta kulle da key ta ciki, sannan ta yi
wankan ta a hanzarce kuma a darare, don ji take kamar zai bude ta a toilet din, ta samu ta ji
dadin jikin ta, sai ta dauro alwallah ta zo ta bada faralin sallar azahar ta wuce su a hanya.
Mukhtar tunda ya canza kayan jikin sa zuwa na barci yayi sallah sai ya kishingida yana hutawa
a kan sofa-bed na dakin cike da gajiya, ko ci kan ki bai ce mata ba.
Daga bisani yunwar cikin sa ta dame shi, sai ya janyo kan telfon din hotel din ya kira
restaurant din su, ya bada odar abinda yake so ya ci wato pounded-yam and egusi soup, sai ya
tuna Amani bai san favourite food din ta ba tun sanin sa da ita, do haka ya fito ya tadda ita, da
kan telfon din a hannun sa ya fito falon da ya bar ta a zaune, ya samu ta yi wankan ta har ta
shafa mai, tana sallah lokacin, daidai ta sallame sallar ta ta mike kenan tana nade mayafin ta,
ya dube ta ya ce.
Hajjaju may I know what you want to eat? Amani tayi banza da shi kamar ba ta ji shi ba, wai
ita ce Hajjaju, irin ya maida ita tsohuwa din nan, ko me yake nufi da wannan sunan? Ko duk
cikin ire-iren wulakancin sa ne zai dubi yarinya yar kwalisa kamar ta ya ce mata Hajjaju?
Ganin ta yi kicin-kicin da fuska kuma bata amsa shi ba, yayi kasa da murya ya ce ba da
matar dakin nan nake magana bane? Ko Hajjaju bata ji na?
A fusace ta juyo, ta watsa masa manyan idanun ta da ke cike da tsana, raini da fushi mai
yawa, ta ce idan na ji, ka kuma ban ga damar amsawa bane sai me? Sai a ka ce dole sai na
amsa?
To bana cin komai, ko dole ne sai na kula ka? Ina ruwan ka da cin abinci na ko rashin sa?
Hanya ce kawai ta hada mu, zuwa Saliyo, kuma da sannu zata raba mu, so ka tsaya iya
matsayin ka na abokin kan hanyar Saliyo.
Mukhtar ya ce ni kuma na yi rantsuwa sai kin bani amsar me zaki ci, kin yi kadan in yi miki
magana ki mayar min da zancen banza, ni zaki gayawa hanya ce ta hada mu alhalin kina
matsayin matar aure na dana biya sadaki dagumi na ba na wani ne ya biya min ba? Ya soma
takowa zuwa gare ta kafin tayi aune ya saki kan telfon din hannun sa ya yi wuf! Ya kama tsinin
karan hancin ta da bakin rashin kunyar ya murde su tare, sai da Amani ta saki kara don azaba,
tana son kiran ka cece ni Daddy! Amma Mukhy ya murde bakin da hancin ya hana sauti fita sai
da wasu hawayen azaba suka feso mata. Sannan ya sake ta yana fadin this is last warning!
Kika kara yi min rashin kunya wanda ya fi shi zan miki. Kuma duk abinda nasa a ka kawo sai kin
ci wallahi ba zan yi asara ba.
Ya zauna a kujera ya kira kitchen, ya ce su kawo masa tuwon dawa miyar shuwaka. Shi
kuma pounded-yam with egusi soup.
Ba jimawa aka kawo, tana tsaye inda ya murde mata baki tana hawaye dafe da bakin nata

wanda take ji kamar Mukhtar ya tsinke shi daga jikin ta, ya ce zauna mu cinye shi tas tace Allah
ya sauwake in ci abinci da kai, abincin ma tuwon dawa, nayi maka kama da yar talaka ne? Ko
aka ce maka kowa ma faqiri ne irin ka? Maganganun ta sun tsorata Mukhtar don rashin
tarbiyyar magana da ke cikin su ya isa, ya ce sannu yar Qaruna, wato bakin naki har yanzu bai
mutu ba ko? Yana bukatar sabon garambawul ya mike ya doshe ta tayi maza ta haura bayan
kujera kamar wata yar wrestling. Mukhy ya ce mara kunyar karya, ki tsaya mana in ba tsoro ba?
Ki gani in ban yi reshaping bakin ba ta hanyar kara miki girman sa? In the way and manner da
gobe da kudi aka ce ki yi min rashin kunya da gorin arziki wallahi baza ki yi ba ta ce ba tsoron
ka nake ba, bana son ganin ka kusa da ni ne, balle kodaddiyar fatar ka ta gogi tawa, don ban
sani ba wannan farin naka ko ka hada dangi da zabiyu (albinos).
Mukhtar ya hadiye zafin da maganar ta yi masa ya ce Allah ko? Su zabiyu ba mutane bane
kenan? Zaki ga zabiyu ganin idon ki, ranar da kike shayar min da fararen yaya na masu kama
da zabiyu, na lura fata ta ta tsole miki ido, don tafi taki haske, idan ke mayya ce ki ci kan ki, ni
kurwa ta kur! Amani ta soma hawayen bakin cikin kalaman sa ta ce Kada Allah ya nuna min wannan ranar,
ko makamanciyar ta ko a cikin mafarki! Wato ranar da zan haihu da kai.
Aka kwankwasa kofa ya je ya karbo abincin ya dawo.
Ya zauna ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa da dadin rai ya manta da ita a tsaye, Amani na
nan tsaye har zuwa lokacin kamar soja ta ki zama, don ta fara tsorata da irin kalaman sa kamar
ba Mukhtar ba, ya ce ki zauna ki ci tuwon nan ki kuma cinye shi tas, ba zan yarda ki kwana da
yunwa ba saboa hakkin ciyarwa, kin ji ko yar Qaruna? Idan kuma kika ki, wallahi mai raba ni da ke a dakin nan Allah ne kadai,.
Amani bata san sanda ta zauna gaban tuwo tana kuka ba, bakin ta har yanzu bai daina
radadin murdar da ya sha ba, bata so a kuma, ta

5 / 13