AMANI 2 COMPLETE BOOK BY TAKORI.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   8 / 13

21K to 24K   out of 38K words

Allah ba ya motsi, wallahi ba da niyya na fada
ba, ba ni na kashe shi ba, ko da bana masa so na soyayya, ba zan kashe shi ba, ban ma san
yadda ake kashe mutum ba.
Kafin ta rufe bakin ta Abdussalam ya kai kofar dakin.
Ya ciccibo Mukhtar daga gadon ya kwantar a tsakar dakin, sannan ya rike tsintsiyar hannun
sa ya tabbatar jijiyar tana motsawa. Kallo daya ya yi masa ya gane halin da yake ciki wato; sihiri
mai karfi ke fita daga jikin sa.
Ya ce da Amani ta shiga dakin da ta ga ya fito ta duba bayan kofar dakin zata ga kwarya ta
dauko masa, zata ganta da ruwan ganyen magarya a ciki, da gudu ta je ta kawo, ya karanta
wasu kebantattun surori da taawizai na karya sihiri ya tofa a ciki, sannan ya ce ta taimaka masa
ya cirewa Mukhtar riga. In ka ga bare-bare a gurin Amani wanda hannnun ta ke yi yayin cirewa Mukhy riga kamar
tsohuwa yar shekara casain, tana kici-kicin cirewa Mukhy riga, tana kauda kai cikin jin kunya da
faduwar gaba, kamar ta ce kasar ta tsage ta shige, kafin ta kalli kirjin sa mai cike da lallausar
gargasa, baka wuluk, irin ta gashin kan sa, haka ta cire rigar ta jefar, ta koma can gefen su ta
rufe ido tana ta tuba, na tuba ya Ubangiji na tuba! Astagfirullah kuwa a jejjere haka ta hau jero
ta ta kai sau hamsin, don ita gabadaya ta baiwa kan ta laifin ta ne, muggan maganganun ta ne
suka jefa Mukhtar a wannan halin na mutu kwakwai, rai kwakwai.
Abdussalam ya shafe duka jikin sa da ruwan maganin nan, har fuskar sa da gashin kan sa,

ya bar shi daga shi sai short nicker da ke jikin sa, sannan ya maida shi gadon ya ja bargon ya
rufe shi da shi, yana kallon yadda Mukhtar ya bude ido a hankali ya kuma mayar ya rufe, alamar
barci mai nauyi yayi gaba da shi. Fatar bakin sa dake motsawa da ace zaka fahimta, ka kuma
san abida ke zuciyar sa, zaka gane sunan garin su yake ambata watau. DIFFA......DIFFA.......DIFFA!,
(With extreme nostalgia).
Daga baya bakin ma ya daina motsin kiran Diffan, ya yi shiru, ya mike sosai a cikin bargon
don barcin sa yayi nisa.

Faytoory ya maida duban sa ga takurarriya mai barin jiki, Amani, yace kada ki tashe shi sai
ya tashi don kan sa, hakika akwai sammu a jikin sa wanda nake da tabbacin yanzu, ya fita.
Amani ta dago a zabure, tana tambayar Faytoory menene sammu? Ya ce sihiri iyakar tsorata
Amani ta tsorata, don ta san ba ka da mai yi maka wannan sai makiyi, to shi kuwa Mukhtar da
ko aboki bai da shi a Katsina bayan Alhaji, wa zai yi masa sihirin? Ta damu kwarai da jin
wannan zance, don tana ganin rashin farfadowar sa da safe a kan lokaci zai janyo mata tsaiko
ko wani jinkirin na isa ga Kenema. Ba lafiyar sa ce ta dameta ba.
Allah cikin ikon sa ma da Asubah da kan sa ya tashi ya shiga toilet ya yi alwallah, sai da ya
fito ya lura da ita a dai dai kafar gadon tana gyangyadi, da alama a haka ta kwana a zaune. Ya
shiga mamaki yana son tuno abubuwan da suka faru daren jiya ganin barci take amma tana
hawaye, amma kadan yake iya tunawa. Yasa kafa ya shure ta ya ce dallah malama ki tashi ki sallah.
Amani ta bude ido a firgice, ta dube shi tana kulubi, tana kunkunin cewa in gama jinyar ka, in
kwana a zaune saboda kai, amma ka ce min Dalla Malama, wannan rashin godiya har ina!
Amma kadan da aikin dan adam, ka yi masa rana ya yi maka dare. Ka yi da yar halak, cikin
Usmanu da Jalan!. Dan murmushi Mukhtar ya yi, ya daga hannu zai tada sallah sai ya fasa ya ce in jira ki ki yi
alwalar muyi jami tare? Ko har yanzu kina kan bakan ki na bazaki bi limancin shege ba?

Idon ta ya firfito waje, ta dauka ya manta sakamakon jiya ya fita daga hayyacin sa, ta dauka
zancen ya wuce, ashe babu abinda ya goge daga cikin kan sa, ko da ya kwana ba cikin
hayyacin nasa ba.
Wannan karon ba musu ta dauro awallar ta fito ta bi shi jamin, don ta tsorata da furucin sa,
wanda yanzu cikin kwanciyar hankali yayi shi babu bacin rai ko kankani a tare da shi, sai da ya
fara da rakaatainil fajr, sannan suka bada faralin asubahi tare, ya nuna mata yadda ake zaman
tahiya na sosai ba irin yadda take yi ba shakwar-kwar a kan kafar ta ba, ya kuma ce ta yi masa
tahiyar ta a fili ya ji. Nan ne Amani ta zumbura baki ta ce ai ban ga shaidar zaman ka Alaramma
ba tukunna, na dai ga shaidar karatun ka a kan kasuwanci, wadda kuma a kan sa na san ka.
Ka bar ni da sallah ta in bar ka da halin ka kai ma tunda dai ba kabarin mu daya ba.
Mukhtar ya kasa cewa komai, don Amani ta zarce da tunanin sa a rashin hankali.
Gashi kan sa yana dan sara masa kadan-kadan, ba ya son yawan magana, sai ya jingina da
bango yana jan carbin sa, yana cewa.
Ya Allah ka taya ni, da abinda ka san bazan iya ba a kan yarinyar nan, Allah ka shirya ta,
idan mai shiryuwa ce, idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ka yi min musanye da mace tagari mafi

alkhairi a kan ta.
Ka shaida ya Ubangiji ban kasance butulu ba, mai manta alkhairi, shi yasa na ke hakuri da
halayen ta. Ka horemin duk wani naui na hakuri da fin karfin zuciya, daga cikin wanda ka baiwa
Annabawan Ka tsarkaka.
Wai sai taji adduar tasa bata yi mata dadi ba, (idan ba mai shiryuwa ba ce Allah ya musanya
masa da mafi alkhairin ta). Me Mukhtar yake nufi da wannn muguwar adduar a gare ta?
Yana nufin Allah ya bashi wata macen data fi ki alkhairi, wadda bazata dinga cutar da shi
daga kalaman bakin ta marassa dadi ba.
Zuciyar ta tayi gaggawar bata amsa.

To ta Allah ba taka ba, in ma mutuwa kake roka min don ka auri wata, saboda kana jin nauyin
Alhaji in ina raye!.

Zai shige toilet domin yin wanka ya dan dakata jin abinda take fada, ashe kin san da auren?
Ai na dauka ko sadakina baki karba ba Baba Idi kika barwa, Baba Idi na aura? Ta fuske kamar
ba da ita yake ba, ya gyada ya shiga wankan sa.
Kafin karfe shiddan da Abdussalam ya deba musu sun kintsa suna jiran sa, ji take kamar tayi
tsuntsuwa ta bar su, don ta ga kamar su duka yanga suke mata. Ko da Faytoori ya zo ma sai da
ya bashi magani cike da kokon duma ya sha sosai, ya bashi kullin wasu a leda ya ce ya jika
kullum ya sha ya kuma yi wanka. Da Mukhtar ya nemi baasi sai kawai ya ce masa na fahimci baka da lafiya ne, wannan kuma
ba komai bane tsari ne da dafai irin nawa na baka.
A motar Abdussalam suka wuce zuwa filin jirgin kasa, a nan ya bar motar tasa suka hau jirgin
kasa mai shiga har cikin Kenema Province.
Zuciyar Amani sai tsalle take a cikin kirjin ta tana kissima ko wacce irin tarba Mamanta Jalan
zata yi mata? Ko zata yarda cewa itama yar ta ce da ta haifa tunda an ce ta samu wasu yayan
bayan ita???
**** **** ****

KENEMA PROVINCE, SIERRA LEONE

G
idan da suka nufa matsakaicin gida ne da bai cika girma ba, akwai karamin gate wanda mota
zata iya shiga har cikin sa.
Taxi din data dauko su daga fili jirgin kasa zuwa gidan ta ajiye su a kofar karamin gate din.
Suka karasa, Faytoory ya danna kararrawa yana gaya musu nan ne gidan da Jalan ke rayuwa,
tun bayan rasuwar mijin ta uban yaranta, ta ci gadon wannan kyakkyawan karamin gidan ita da
yayan ta. Fajur, baki ji ana danna kararrawa bane?
In ji Yayan ta Safwan wanda kan sa ke kan allon kwamfutar bisa cinya (laptop).
Rubutu nake yi, bana son tashi. Ta bashi amsa cikin hausar su da ba sosai take fita ba,
amma a junan su suna yawan yin ta, saboda yaren su na Krio da ya mamayi harshen su wanda
shine Lingua Franca na kasar, musamman a lardin su na Kenema.

Hajiya Jalan data fito daga kitchen sai kawai ta karasa ta bude kofar da kan ta. Don ta san
halin Fajur da kiwa. Tunda tace hakan bazata tashi a kan lokaci ba. Don ta san kiwa irin ta
Fajur, zata bar baki ne su yi ta tsayuwa sai ta mula don kan ta zata tashi ta bude.

Fara, doguwa kuma siririyar yarinyar da ke tsaye a wurin ta bi da kallo, doguwa sambaleliya
mai kira da tsayin matan Saliyo, (a perfect replica of herself) idan ba idon ta ne ke mata gizo irin
wanda ya saba yi mata ba, exactly kamar yadda take a tsaye dirarriya shekaru ashirin da daya
a baya. Tana son tuno inda ta san ta amma ta kasa. Sai dai feeling of familiarity da wani
maternal sensation dake kara mamayar ta.
Kamar ta san ta a wani wajen! Kamar ta dade da sani da sabawa da yarinyar da ke tsayen
haka ta ji a ran ta. Amma iyaka tunanin ta bata iya ta tuno a ina ta san ta din ba.
Amani ta jingina da kofa tana kallon Maman ta da bata bukatar a yi mata karin bayani, Jalan
ce, Jalan din Daddy Usman, wadda ta hana shi iya rayuwa da kowacce mace sabida wannan
kyawu nata da haiba da ba duk mata Allah ya yi wa ba, gata nan da kuruciyar ta har yau (at the
age of fourty), wasu hawayen farin ciki suka soma tsera a kan fararen kundukukin ta. A hankali
bakin ta dake rawa ya motsa cikin furta haruffan.
Ma.....Ma... Mama na!.

Jalan, wadda ta zama kamar an soma rewinding casette a cikin kan ta, ta soma zaro idanun
ta sosai, kafin ta mika mata hannu ita kuma ta tafi da gudu ta shige. Suka rungume juna kamar
bazasu saki ba suka saki kuka a tare mai sauti. Mukhtar da Faytoory sai suka koma daga gefe
cikin tausayawa, Mukhtar ya ji hawaye na son tsatstsafo masa domin sai ya ji wannan rungumar
inama shi Ummami ta yi wa, ya tuno tasa Ummamin, yau shekaru kusan goma sha biyar kenan
rabon sa da ita.
Yana ji Faytoory na cewa Amani ta cika ta haka a yayin da shikuma yake tsane hawayen sa
da bayan hannun sa. Mama Jalan cikin jin kunya ta janye jikin ta daga na Amani, tace musu
barka da zuwa ku shigo daga ciki.
Safwan da Fajur, suka mike suna kallon su da bakunta a idanun su, har falon ta ta yi ma
Mukhtar da Faytoory iznin shiga, jikin ta har bari yake, sam ta manta babu mayafi a jikin ta
domin jini ya gama bayyana kan sa, ya gaya mata yar ta ce ta Alhaji Usman Faskari ta biyo ta.
Dama ta riga ta sani ko ba dade ko bajima zata zo gare ta, in har tana raye. Shi yasa bata taba damun kanta a kan ta ba, tunda dama babu shakuwa ta shayarwa a
tsakanin su. Amma lokaci lokaci ta kan tuna cute fuskar jaririyar mai tsananin kama da ita,
wadda bata dauko munin mahaifin ta ba ko a farce, ta kuma tambayi kan ta sau tari ko ta rayu?

Zafafan hawaye ne suka zubo mata tana kallon Amani, wadda har zuwa lokacin kukan farin
ciki take yi ta hada kai da bango.
Mukhtar ya dubi Jalan sosai da tsoro da mamaki domin yatsan ta na karshe mai cindo da ya
dauki hankalin sa a duka hannyen ta, da wasu attributes na ta da yawa, musamman data juya
baya tana tafiya takun ta a kan duga dugai irin na Ummami, duk da kai tsaye bazaa ce tana
kama da Ummami a fuska ba, amma a wulge suna kama din, musamman idanun ta da dirin
jikinta mai kauri ba irin na Amani dan shalaf ba, ga kuma cindon nan guda biyu dake hannun
Ummami a nata hannuwan duka biyu hagu da dama itama.

He was shocked! Truely shocked! Amma wace hujja gare shi na cewa Jalan jinin Ummami
ce? Shi kan sa bai san komai akan Ummami ba, ko kasar data fito bai sani ba, babu wannan
shakuwar a tsakanin su tun yana yaro, da zata yi hira da shi balle ta gaya masa wani abu
makamancin wannan. Ya dai san Ummami ba yar Nijar bace, ba kuma haihuwar Diffa ba, wato bakuwar haure ce
da aka auro tun ana cinikin auro matan Saliyo ga masu mulkin kasar Nijar, amma bata taba yi
masa matashiya a kan kasar data fito ba ko zancen wani nata, yo ina ma ya gan ta ya zauna da
ita? Sabida har ya bar gida ba shi da wannan alfarmar irin ta shakuwar Da da mahaifi da ita.
Nan da nan wannan boyayyar suffar tasa ta bacin rai da rashin walwala mai bayyana lokaci
lokaci a tare da shi ta zo ta lullube yanayin sa na annuri da yake ciki a yanzu, wato fuskar nan
tasa ta bacin rai da hadewar fuska wadda da ita ya fi kamantuwa a koda yaushe.
Faytoory kan sa sai da yayi noticing canzawar fuskar Mukhtar, a lokaci guda yayi jazur ya
hade kamar hadari, duk wata walwala da ke kan fuskar sa a baya ta bace. A ran sa cewa ya ke
Dubi dai yadda uwa ta rungume yar ta a bainar jamaa tana kuma zaune da yayan ta biyu a falo
guda, daya tana homework daya na aiki a computer, ita kuma tana dafa musu abinci amma shi?
Umh! Ummami bai taba samun zama irin wannan da ita ba tunda ta haife shi, sai ka ce ba
haihuwar sa ta yi ba, ko kuma tana dana sanin haifar tasa.
Kada ki so ki ga yadda fuska da idanun sa suka koma a wannan lokacin.
Kafin ka ce meye wannan Jalan ta cika gaban su da kayan abinci da abin sha na alfarma,
fadi ta ke ku ci ku sha, na tabbata kun sha tafiya, na tabbata daga Nigeria kuke. Ko daga
Freetown zuwa Kenema sai mutum ya jigata a jirgin kasa.
Tana zama a kujera domin su gaisa Amani ta kara komawa jikin ta sai da ta san yadda tayi ta
kwanta a jikin ta, kunya ta kama Jalan, ita kuwa Fajur ta kasa hakuri, ta matso tana tambayar
Maman nasu Mamma wacece wannan mai kama da ke haka? Ke! Daga mun Mamma na
Safwan yace Yayar mu ce ta Nigeria ko? Sai kuka ya kwacewa Jalan. Amani ta mika musu
hannu ta jawo Fajur da Safwan jikin ta.
Jalan ta hada su su duka ta rungume a jikin ta tana cewa alhamdulillah! Jiki na ya dade yana
bani kina raye dama, ko ba dade ko baji ma kuma na san zaki zo gare mu muddin da gaske na
haife ki a duniya.
Mukhtar ya zamo kasa ya na bata hakuri cewa ta daina kuka, ga yar ta nan Alhaji ya ce a
kawo mata. Yana rokon gafarar ta, kuma yana so in babu damuwa zai kira Alhaji a vedio call su
yi magana da ita.
Ta ce babu komai amma ba yanzu ba sai ta gama ganawa da diyar ta.
Faytoory ya yi musu sallama cewa zai wuce gidan sa, ya ce ko Mukhtar ya bi shi gidan sa ko
hotel mafi kusa zai kai shi? Sai Mamma Jalan ta ce shi din Mukhtar waye a wurin Alhaji Usman
Faskari?
Mukhtar ya sunkuyar da kai kasa sosai ya kasa amsawa, sai Abdussalam ne ya gaya mata
cewa mijin Amani ne. Angon ta. Alhaji ya gaya masa ya daura musu aure ko tarewa basu kai ga
yi ba, tasa fitina sai an kawo

8 / 13