AMANI 2 COMPLETE BOOK BY TAKORI.pdf

Author :  Sumayya Abdulkadir Category :  Taskar Novels

Chapter   13 / 13

36K to 38K   out of 38K words

purple din jambakin
Elizabeth Arden lipstick kalar material lace din dake jikin ta kyakkyawar mahangurba. Sai Allah
ya ceci Amani daga can nesa da ita kafar bene ta tsaya.
Ta dauko mayafin wanda dashi da babu duk daya dai ta dawo. Baba Idrisu yayi sallama ya
dawo dakin don ya dan zaga toilet ne. Alhaji ya nuna mata gefen Mukhy ya ce nan ne wajen
zaman ta family meeting zasu yi.
Kallon da Mamma Jalan ke mata ne yasa ta yarda ta zauna a gefen Mukhy din, ba tareda ta
yi musu ba. Jalan ji tayi kamar ta fashe da kuka a kan irin taunar cingam din da take yi a gaban
kowa. Ta na Allah-Allah a tashi meeting din ta ci uban ta. A Saliyo ta dan samu saiti, wato yanzu
an dawo gaban Alhaji da ke daure mata gindi shine zata koma halin ta? Ita kuwa Amani tana
sane duk abinda take yi don ta kular da Mukhy ne, wato ta rama cin mutuncin da yayi mata, ta
san baya son ta da cin uwar kwalliya irin haka. Balle daurin gaban goshi. Har taunar cingam din
ma baya so ya taba ce mata ba tarbiyya bane.
Alhaji bai san tana yi ba. Haka Mukhy bai bata hankalin sa ba balle ta kular da shi din data ke
so, ya ce Mukhtar yau ina son in san tarihin ka, abinda ya fiddo ka daga gida, da kuma abinda
yasa baka so ka koma kusan shekaru tara kenan. Lokaci yayi da zaka je gida tunda ka fara aje
iyali. Ba fata ake ba, amma akwai mutuwa akwai kuma ciwo. Ba damuwa muka yi mu san cewa
kana da asali ko baka da shi ba, amma lallai zamu kai Amani ga iyaye da yan uwan ka don su
san da zaman ta, tunda auren sunna ne muka kulla, wanda muke fatan a samu zurria a mai
albarka a cikin sa.

Mukhtar ya nutsu sosai yana sauraron ubangidan sa kuma surukin sa a halin yanzu, ya san
gaskiya ya fada, amma sabanin lokutan baya da in yayi masa maganar gida ransa ke baci yau
shi da kansa cikin nostalgia (begen gida) yake domin ya fara gajiya da gorin Amani. Kuma ya
saka a rana sa cikin satin nan in Allah ya yarda zai koma gida ko da Amani bazata yarda ta bi
shi kasar su ba.
Mukhtar ya ce.
Labari na mai tsaho ne Alhaji, and very complicated, tragic story. Wanda nafi so in yi
revealing din shi tare da ku da iyaye na a zaune gabadaya.
Abinda zan iya cewa a yanzu shine iyaye na suna raye (as far as I know), ina kuma da
labarin duk halin da suke ciki ta hanyar wani abokina na kuruciya mai suna Ari.
Na fito daga yankin Diffa. Diffa din wani babban birni ne da ke kudu maso gabashin
jamhuriyyar Nijar. Garin na da iyaka da tarayyar Najeriya daga kudu maso gabashin kasar.
Birnin Diffa ya samu asali tun a lokacin daular Borno (Kanem-Bornu Empire). Wato tun
lokacin 1900. Asalin mutanen da suka yi rayuwa a cikin ta a lokacin Kanurai ne (ko kuma
Barebari). Amma yanzu Diffa ta hada kabilu guda uku; Larabawan Diffa wadanda ake kira (Diffa
Arabs), Buzaye da kuma Tubawa, duka suna cakuduwa suna rayuwa a cikin ta. Diffa tana nesa da kimanin kilomita 1360 daga babban birni Niamey.
Iyayen mahaifi na sune asalin kabilar Diffa Arabs, watau Tubawa ne, yaya ga Sultan
Oumarou Mai Diffa, wadanda tarihi ya nuna kakannin su, su suka kafa daular Diffa Arab.
Mohammed Bazoum kan sa, wato shugaban kasar mu na yanzu dan asalin Diffa ne daga
kabilar mu ta Diffa Arabs. Sai Mukhtar yayi murmushi ya dubi Daddy, Alhaji iya labarin da zan iya baku kenan a kan
inda na fito, maganar iyaye na ko abinda ya fiddo ni daga gida sai mun je gaban Ummami da
mahaifi na Sultan Issoufou Massaoudou, a yanzu dana yi hankali na ga ya dace nayi exposing
ciwon zuciya ta gare su, su san halin dana rayu ciki a kan su, maimakon in yi ta rike shi a kasan
rai na ina fama da shi tun daga kuruciya ta har girma na.
Alhalin su basu san ina da shi a kasan rai na ba. Ko sun sani, ban taba tattauna shi da su ba.
Na dade ina fama da wani dabaibayi mai fizgata ga nesanta da gida, kullum dabaibayin nan
cewa yake dani in kara nesanta kai na da Diffa, ta hakan ne kawai zan samu nutsuwa da
kwanciyar hakali, idan ba haka bazan taba zama cikin nutsuwa ba.
Rana daya tun zuwan mu Saliyo na tashi na nemi wannan dabaibayin a tare da ni na rasa,
na nemi fargabar da ke mamayata idan na tuna Diffa na rasa, na ji komai ya yaye daga cikin
kaina duhun da ke zuciya ta ya koma haske.
Wannan alamari ya faru da ni a wannan tafiyar da muka yi zuwa Saliyo, tun daga lokacin
hankali na ya koma gida da son ganin iyaye na, kuma jin zafin su da ke raina na samu yana
decreasing gradually (raguwa a hankali), a halin yanzu ina iya yi musu uzurin da a baya bana
iya yi musu, ina shaukin ganin su, sannan a shirye nake ga fuskantar abinda a baya nake
tsoron fuskanta a gida, komai tsaurin sa.
Na shirya komawa gida a halin yanzu. Hakika Alhaji yanzu na shirya ko ba don Amani ba zan
koma gida. Lokacin tafiya ta gun Ummami yayi. Ina jin kaina a zan iya fuskantar kowanne irin
kalubale da zai iya tunkaro ni with a very big and brave heart, wadda a baya ban mallaka ba, na
rasa farin ciki tun ina yaro, na kasance cikin kadaicin rayuwa wato solitude mai sakawa dan
adam inferiority complex, a dalilin iyaye na basu yi min abinda nake so ba.

Alhaji na karbi auren da ka bani da hannu bibbiyu, banida bakin da zan godewa kyautatawar
ka gare ni, da rikon da kayi min, na karbi Amani zan tafi da ita cikin ahali na duk da ikirarin ta na
rashin son auren mu, ni na karba na kuma gode. Na kuma yi alkawarin rike ta da amana har
karshen numfashi na. Alhaji sai ya saki hamdalah yana fadin, na gode Mukhtar na gode Allah ya yi maka albarka,
Im the one to thank you for changing my life positively, tunda ka zo gare ni rayuwa ta ta canza,
albarka ta lullube rayuwa ta, dukiya ta ta rubanya ta yi albarka yadda ban taba zato ba, don
haka nine da godiya na kuma yarda duk lalacewar da duniya tayi, har yanzu akwai masu
mutane masu amana akwai kuma mutanen kirki, kai dai kayi wa dan kowa alkhairi ba sai naka
kadai ba. Baka san wanne zaka ci amfanin sa ba. Kuma baka san wanne ne zai ji kan ka ba.
Sai ka shirya mana motocin da ya dace muyi tafiyar a ciki, wadanda basa makalewa a cikin
sahara. Ya ce ai Alhaji a Land-Cruiser din ka kawai zamu tafi, tana da tsaho da fadi, a kalla zata
dauke mu nida kai, Mamma da Baba Idi da Baba Sahura, da ita wannan. Ya nuna Amani da
baki. Amani ta galla masa harara ta murguda baki cikin takaici, wai ita yake cewa ita wannan,
alhalin ya lissafa sunan kowa, wato ita bata kai matsayin da zai fadi sunan ta ba, irin wannan
rashin darajawar da yake mata shi yake sawa take kara tsanar sa, tunda gashi ya kara fadi a
gaban iyayen ta da ita kanta cewa ya gode da sadakar ta da Alhaji ya bashi. Hawaye ya surnano daga idon Amani Faskari, yau ita ce zata koma rayuwa a kauyen Nijar!
Wata alkarya da ko sunan ta bata taba ji ba, wai Diffa. Da sunan aure a inda bata da kowa.
Mafarkin ta na tafiya yin masters a jamiar QUEEN MARY UNIVERSITY OF LONDON ya zama
tarihi! Ya bi ruwa! Ta zama cikin Diffa Arabs, makiyayan daji da bata san ko yaya aladu da
dabiun su yake ba.
Sai gani aka yi Amani tana rafzar kuka, ita ba abun tace bazata ba, ta san ba mai bin bayan
ta, Mukhtar bayan saye Ubanta da mugun sumumu-kasau din sa, Uwar ta ma ya saye yanzu,
sai abinda ya ce. Shi kadai ne mutum a idanun su.
Ta yi magana yanzu Mamma ta kumbura mata baki, tunda kuma a kusa da ita take zaune.
Mukhtar ya fita yasa Tajuddeen ya fido Land Cruiser din Alhaji ya ce a kai ta service a kuma
yi mata full tank, gobe asubanci zasu yi zuwa kasar sa. Kuma shi da kan sa zai tuka motar.

Tajudden tun a lokacin ya soma kewar Mukhy, wani kwayan mutum guda daya wanda ya
zame masa tamkar dan uwa a gidan Alh. Usman Faskari, ba irin alkhairin da baya yi masa. Ya
yi wa Mukhtar fatan alkhairi, yana hawaye, tare da rokon sa ya dinga zuwa suna ganin sa
lokaci-lokaci. Ko albarkacin Amani da zai dinga kawowa ganin gida. Haka yai ta sallama da duk maaikatan gidan. A daren kowa ya hada kayan da zai tafi da su
banda Amani, sai Mamma ce ta zo ta hada mata da kan ta. Kwana ta yi akan kujera tana kuka,
kafin asubah bayan ta ya rike, wuyanta ya kage, kuma a haka suka ce bazasu jira ta ta yi
wanka ba ta yi sallah kawai su kama hanya, don already Mukhy (wanda yau wata irin shiga
yayi, ta asalin ainahin larabawan Diffa), in ba har ka yi masa farin sani ba bazaka gane shi ba,
ya shirya tsaf cikin kayan kasar shi a jikin shi wato traditional attire na Diffa Arabs ya fito a
ainahin kamannin sa na Tubawa ko kuwa larabawan Diffa). Kasancewar duku-duku ne cikin su
babu wanda ya ga irin shigar da Mukhy yayi, musamman da yana cikin mota ne a zaune, ya
tada mota ya bata wuta a waje, su kawai yake jira su fito.

Mamma duk zafin ta sai da tausayin Amani ya kamata ta hada da lallashi, ta kuma yi mata
alkawarin zata kawo mata Fajur daga baya in ta gama makaranta, kuma zata bar Baba Sahura
ta zauna da ita har sai ta saba da mutanen data tarar, kuma zata nemi Yayar ta dake Nijar ta
hada su. Wannan ne ya dan sanyayawa Amani, amma in ta tuna ta bar comfort zone din ta
kenan zuwa wani kololuwar kauyen Nijar bata sanin sanda take sake rushewa da kuka, tana
laantar Mukhtar da kaddarar data yi sanadin zuwan sa gidan su.
**** **** ****

MU BIYO JARUMAR TAMU AMINA-AMANI, UWAR BABA IDI, SANNAN TAFISU YAR
GIDAN BABAN TA… ZUWA YANKIN DIFFA A LITTAFI NA UKU DON GANIN YADDA ZATA
KAYA TSAKANIN TA DA MIJIN TA MUKHY’ DAN KABILAR LARABAWAN DIFFA.

13 / 13