Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
mutum yana shirya mutum da tuni Hamida ta gyara min halin Amani, to abotar
tasu ba irin wadda ake kira ta abokin barawo- barawo bace.
Sun dade suna tattaunawa, Mukhtar ya gayawa Alhaji dole sai sun kwana a Lagos kafin
washegari da asubah su bi jirgin Freetown. Alhaji yace ta dai yarda zata je din ko? Mukhtar ya
nisa, kafin a hankali ya ce Alhaji maganar yarda ta je ko rashin yardar ta duk basu taso ba, abu
ne dana sani ba abinda take so kuma take buri a yanzu sama da ganin Innar tata, don haka
zata bi ni ne ko bata so, donmai binciken nata dan damfara ne kawai, alkawari ne na yi mata
kuma dole in cika shi, zan damkata gun mahaifiyar ta in yaso in ta ga dama don Allah kada ta
biyo ni mu dawo.
Ni ba a matse nake ba!.
Kunya ta kama Alhaji, sai ya hau Mukhtar da fada, na tambaye ka wannan? Kullum ana
gaya maka ka koyi lallashin mace kana kara fandarewa Mukhy, ina gaya maka wannan ne
(based on experience), da a ce na lallashi Jalan, na bi ta a hankali, na yi hakuri da ita da
shirmen ta na rashin so na, ban kuma yi zuciya ba na saketa a asibiti wai don tana ikirarin bata
so na, da na jure da har yanzu muna tare bamu rabu ba. Da Allah kadai ya san yawan yayan
mu tare.
Yau ga shi na tsufa da soyayya a kasan rai na ina ta nadama, don duk matar dana aura na
rantse maka a bayan Jalan take, kuma na kasa son ko dayan su irin son da nake ma Jalan.
Matar fari ka tattalata Mukhy, domin bazaka samu kamar ta ba, daban Allah yake bamu su.
Abinda ya dade bai yi ba shi ya yi yanzun wato murmushi, yace a ran sa wato Alhaji bai sha
da dadi ba a hannun soyayya shi yasa yake ji masa tsoro. Shi kam ai mata a kasar su sai
wadanda ya zaba in ya so, mata kamar hurul eeni ma, wadanda suka fi Amani komai. Ita Amani
ta ladan noma ce, kyautar ubangidan sa da ba zai iya cewa baya so ba, ta ja zaren ta yadda
take so in ta gama jan nata lokaci zai zo da shima zai ja nasa watarana.
Haka ya kwana da sake-saken abin a ran sa. Na irin yadda zai aro kalmar hakurin nan da
kowa yake jaddada masa ya rataya a wuyan sa a kan Amani. Tunda ta zama dolen da ba zai
iya kaskantawa ba. Da asubah ya ga sakon ta a wayar sa, da sunan da yayi saving no. dinta da
shi watau AUF (AMANI Usman Faskari) mai nuna ta amince zata bi shi Saliyo. A gajarce ga
abinda Amani ta ce da mijin ta Mukhtar, ba tareda ta kara komai a kai ba.
Yes, Im going!.
Ya dan sakawa sakon nata ido yana nazarin sa, wato bazata ko ce masa yaya ya kwana ba,
balle ya gajiyar hanya, wai miji a kewa magana haka gatsau cikin gadara, shi ina ya san mace
na ma miji magana a haka? A inda ya taso sujjada ce kadai mace bata ma mijin ta saboda
respect, soyayya, kulawa da kankan da kai. Mukhtar ya dan kyabe baki a fili yace.
Kada ma Allah ya sa ki je!.
Yayi alwallah ya fita zuwa masallacin gidan wanda Baban Hamida ya gina like da gidan sa.
Hamida da Amani kwanan zaune suka yi Hamida na gaya mata sai ta yi a hankali da Mukhtar
Diffa, domin maza irin sa wuyar shaani ne da su, in ba ta yi wasa ba ita zata dawo tana cin
kwakwa a hannun sa, tace Mukhtar dinnan mutum ne har mutum, wanda ya gama sanin ciwon
kan sa, ya san daraja da mutuncin kan sa bana jin zai dauki halayen ki Amani, babu alamun
wasa a tare dashi ko sakin fuskar da mace zata raina masa hankali irin yadda kike yi.
Imagine ko sannu da zuwa babu, ko gaisuwa balle ya hanya, abinci wannan kin ki dauka ki
kai masa haba Amani! Miji duk lalacewar sa sunan sa miji balle irin naki Amani wanda kyautar
Allah ne a gareki kuma zabin mahaifin ki.
Me zai hana ki kwantar da hankalin ki ku yi zaman ku lafiya ki yi tunanin hanyoyin mallake
abin ki?
Amani ta girgiza kai cikin takaicin Hamidah, tace wai sau nawa zan gaya miki bazan taba son
mutumin nan ba? Ko da shine Hurul eenin maza bakidaya? Ni na kirawo shi da zan masa ya
gajiyar hanya? Ke da kika kirawo shi ba kin masa ba ina ce ya wadatar? Yaron Baban nawa
zan je ina ma ya gajiyar hanya? Na ce miki na shirya zaman aure da shi ne da kike min wani
fatan hanyoyin mallakar sa?
Ta yaya mutum yana aiki a karkashin iko na kuma a aura min shi? Ba don komai Daddy ya yi
haka ba sai don ya bashi lasisin cigaba da wulakanta ni, tunda tun kan in zama karkashin sa ma
yana yi min duk wani launi na wulakanci da kaskaci ga fadin rai kamar firauna.
Na fahimci ko me zan gaya miki hujjata ta rashin kaunar Smart Ass, Bad Egg din nan ba zaki
bani goyon baya ba Habeebty, saboda kema ya asirce ki.
Hamida abun na Amani ya daina bata haushi yanzu don ta koma bata tausayi, tana hango
mata in ta bari tayi asarar Mukhtar bazata samu makwafinsa ba, wajen sanin darajar iyayen ta,
ba wai bazata samu miji ba tunda itama banda halayen ta bata da makusa, ta yarda duk abinda
take fada bilhakki take fadar sa daga kasan zuciyar ta da gaske bata son nasa, ta sha wahala
wajen lallashin Amani kan ta yi masa text tace zata je Saliyo din.
Don Amani cewa tayi ba zata masa wani text ba dan rainin wayo kawai. Sai da Hamida tace
zata je a daren ta gayawa Hajiya Muna cewa ko abinci data ce ta kai masa bata kai ba. Ta ce
kuma wallahi in Hajiya ta ji haka a daren nan zata tasa keyar ki dakin sa, in ya so ki je ki masa
dibar albarkar a kunnen sa.
Sannan ne fa ta typer masa Yes, Im going din. Don ta san Hamidah zata aikata. Ita kuma
bata san meyasa ba duk tsiyar tata da tijarar tata tun da Kawu yace an daura auren su ta ji
kalmar ta yi mata girma a rai, aure fa! Ba karamin alaqa ne aka kulla tsakanin su ta har abada
ba, ji take bazata iya kara hada ido da shi ba balle kuma zuwa inda yake shi kadai ba tare da
kowa a tare da su ba.
Yadda Mukhtar ya kwana sake-sake a kan Amani da halayen ta, da yadda zai jure ma zama
da ita matsayin matar sa uwar yayan sa haka itama Amani ta kwana nata sake-saken, sai dai
nata sabanin nasa ne domin kuwa kwana ta yi tana saka hanyar da zata bi ta kubutar da kan ta
daga auren sa. A haka garin Allah ya waye musu Tun asubah tayi wanka sakamakon wani irin doki da ke cin ran ta na son haduwa da
mahaifiyar ta. Ta zuba doguwar riga mai fadi na wani tattausan cotton lace ruwan goro da aka
yiwa dinki babban riga Senegalese, ta kawo wani dan mayafi cantitly kamar abin tatar koko ta
yafa a kafadar ta exactly yadda ta ke shigar ta a can baya. Amma yau bata shafa lip stick ba ko
powder bata shafa ba. Man shafawar ta kawai ta shafa wato Elizabeth Arden Lotion. Sai ta hau
hada kayan ta a trolley dinta.
Sai lokacin Hamidah ta farka ta gan ta ta saka jaka a gaba cikin tunani, ba komai take
tunanin ba kuma sai yadda zata yi tafiya mai nisa irin haka tare da Mukhtar Diffa. Farin
Baabzinen nan da ya zo rayuwar ta rana daya ya rikita duniyar ta. Ya canzata ya hautsina ta,
ina ta taba kawowa kan ta aure nan kusa, ban da kutsowar Mukhtar Diffa cikin rayuwar su mai
tsafta ita da mahaifin ta???
Amani ta ji hawaye sun kawo wa idon ta cafka, aure na nufin karewar kuruciyar ta kenan fa.
Auren na nufin ita da Mukhy daga yanzu sun zama abu guda! Ya ilahy! Ina zata kai wannan
kayan bakin cikin da Daddy ya kunsa mata? Ai abu daya zata yi kawai ta huce shine ta yi hakuri
ta jure ta gan ta gaban Innar ta, daga nan kuwa saidai a yi wani labarin ba dai nata da Mukhtar
ba. Abun nufi, yanzu kam ta ajiye duk wasu makaman yakin ta don ta samu ya dangana ta da
Innar ta, daga nan kuwa ko sama da kasa zata taru a kan ta ba zata dawo ba, tunda Daddy ya
daina son ta.
Hamida ta tashi zaune ta gan ta ta hada kai da guiwa tana rafzar kuka har da sheshsheka,
kewar Baban ta take tun kafin ta bar shi, amma ta zabi ta bar shin, tunda shima ya zabi Mukhtar
tsintacce a kan ta.
A ran Hamida cewa ta yi Sahibah! Dadi ne yayi mata yawa". A fili kuma sai ta tambayeta shin
kin yi sallah ne da kika ci wanka da asubahin fari? Sai a lokacin ta tuna bata yi sallar ba. Ta
mike ta shiga bayi don yin alwallah.
Wajen karfe takwas nasafe Haj Muna tasa aka kaima Mukhtar karin kumallo, sannan ta shigo
dakin nasu hannun ta rike da katuwar leda, ta gan su tsaf da su duk sun shirya don Hamidah
tana so ta raka su har airport, Haj Muna ta zauna a bakin gadon Hamidah da suke zaune
kowacce hankalin ta na kan wayar ta, don hira ta ki dadi tsakanin su, tun sanda Hamidah tace
ta yi kwalliya ta gyara idon ta da ya kode Amani ta fusata kwarai. Ta ce kada ta saka mata ido,
ita ina ruwan ta da wani Mukhtar da zata yi kwalliya domin sa? Sai Hamidah ma ran ta ya sosu,
ta ce Sahibah! Kiyi duk abinda kike so in sha Allah ba zan kara yi miki nasiha ba.
Shikenan duk suka zama kurame a dakin kowacce ta ki kara kula yar uwar ta har zuwa
shigowar Haj. Muna. Ta zaune gefen Amani sannan ta shiga fiddo kayayyakin dake cikin ledar
data shigo da ita, tana yi ma Amani bayanin yadda zata ke shan magungunan da ke ciki, Haj.
Muna tace,
ya ta Amani, sai an gwada akan san na kwarai, ni na gaya miki da kudin ki zaki zo neman
kari, kin gan su tafiyayyu ne tun daga Nijar na yo odar su don amfanin kai na. Wannan Uwa ce
kawai zata iya baki su, yanzu nake so ki sha kowanne a gaba na sannan ki daure sauran ki
wuce da su. Amani tayi sakatoto! Tana kallon Hajiyar da kayan hannun ta, kafin ta ce innocently Hajiya
maganin menene? Ni ai lafiya ta kalau, Sahibah ce take bata min rai, shine kika ganni kamar
mara lafiya Hajiya ta ce na sani Amani lafiyar ki kalau, bahaushe kuma ya ce "in kana da kyau
ka kara da wanka". Dalili na anan shine. Na hango miki wani irin miji mai babban alamari irin wadanda ke
wahalar da matayen su a dalilin tarin baiwarwakin da Allah yayi musu.
Mijin ki ga dukkan alamu babban mutum ne, mai tarin ilhama, ban ga ta inda zaki samu kan
sa ba sai ta wannan hanyar kadai, don baki da wayo da kissa da su kisisina irin na yaya mata
sai dolanci. To cigaba da dolancin ki, amma ki kama shi ta nan ta nuna can kasan Amani.
Hamida bata san sanda dariya ta kubuce mata ba don ta lura Amani kallon Haj. Muna kawai
take tana cewa toh! amma kwata-kwata bata san inda zantukan Hajiyar suka dosa ba, ta dai
karba ta aje ta kuma yi godiya. Amma ta ce ba zata iya cin komai a ciki ba yanzu sabida tana jin
yunwa. Hajiyata sa aka kawo musu abinci suka karya amma Hajiyar na fita ta tattara magungunan ta
mayar a ledar su. Ta cewa Hamidah "in kin gama dariyar muguntar taki sai ki je ki gaya masa na
shirya. Hamida ta ce ga yar aiken ki ko? To da mecece? Hamida sai ta dauki wayar Amani ta
danna ma Mukhtar kira ta na cewa ki ji tsoron Allah Amani, mijin naki ne Dirty Human Being?
Smart Ass, Bad Egg. Ai ko karen gidan ku bakya kira da wadannan sunan ba balle mutum dan
adam.
Ita dai bata ce komai ba amma ta sa a ranta zata canza sunan koda ba da wani sunan mai
maana ba, amma dai zata canza wannan din, ganin yadda Hamidah ke Magana a kai kamar
zata yi kuka. Hakan yasa ta tabbatar bata son sunan ga Mukhtar. Ko yaya ne tana ragawa
Hamidah saboda duk tijararta ta san Hamida Balewa mai kaunar ta ce. Mukhtar na cikin sanya links din hannun rigar da ya sanya ta ash colour getzner ya ga AUF
na kiran sa, dauke kai yayi kamar kada ya daga don ya san arziki ba zai sa Amani kiran sa ba.
Abu daya yasa shi amsawa ganin lokacin tafiyar su filin jirgi yayi. Don haka ya amsa, amma ba
tare da ya ce uffan ba. Sai ya ji Hamidah ce, ta ce sun gama shiryawa kuma direba yana bakin
entrance na masaukin sa da mota bakar land cruiser zasu raka su har filin jirgi.
Mukhtar sai ya samu kan sa da cewa Hamidah madallah da karamcin ki. Madallah da kawa
irin ki. Allah ya baki miji na gari kema.
Ki yi min godiya wajen Hajiya mun gode sosai, da zumunci, Alhaji ya ce a yi muku godiya".
Zuciyar Hamidah ta cika da jin dadin wadannan kalamai na Mukhtar, sai ta ji wani karfin
guiwa ya shige ta na son kara taimakawa aminiyar ta ta zauna da wannan mutum da babu
wada ya taba shiga ran ta kamar sa. Hakika Mukhtar Diffa, yana da charisma ta farin jini a duk
inda ya shiga, ba ga manya ba ba ga yara ba. Duk wanda wata kankanuwar muamala ta hada
shi da shi sai ya so shi, ya kuma bar shi da begen son cigaba da alaqa da shi idan ya bar
wajen.
Har dakin Hajiya Muna Hamida ta raka Amani ta yi mata sallama daga nan suka wuce
maadanar motocin gidan. Tana janye da jakar Amani.
Tuni Mukhtar direban ya bude masa mota ya shiga gidan gaba ya zauna yana jiran fitowar
su, yana yi yana duba agogon fatar dake daure damtsen hannun sa samfurin RADO. Da suka
karaso ta cikin farin glasses din da ke idon sa wanda ya makala shi saman dogon karan hancin
sa ya hango Amani tana tahowa, da gantalallen mayafin da ta yafa, tafiyar nan tata kamar ta
macen Dawisu bai canza ba, duk da cewa zuciyar ta da kamannin ta sun canza zuwa na bacin
rai zallah. A hakan kuma sai tayi wani irin kyau ba dan kadan ba. amma mayafin da ta yafa
wanda saman kirjin ta kawai ya lullube ya bakanta masa rai. Haka ya shanye abin a ran sa
albarkacin direba da Hamidah. Suka shiga baya su biyun ita da Hamidah direba ya saka jakar
kayan ta a boot kusa da jakar Mukhtar, sannan ya shiga mazaunin sa ya ja motar suka fita daga
gidan su Hamidah.
Sai da suka hau kwalta sosai Hamidah ta gaida Mukhtar, kamar ba zai amsa ba sai kuma ya
amsa din, har ya ce mata "yaya fama da bakuwa?" Sai ta yi murmushi ta ce ai na saba da
wannan bakuwar tawa mai rigima, mai giggiwa. Ta mudubin motar Amani da Mukhtar suka hada
ido unexpectedly ta sakar masa harara, bai yi kasa a guiwa ba wajen maida mata da wadda tafi
tata zafi. Ya kuma maida kan sa bisa titi.
Hamida tace don Allah Mr. Mukhtar da kun sauka ku kira ni in tabbbatar kun sauka lafiya. Ya
ce "in sha Allah". Duk Amani na jin su, amma ko kallon su bata kara yi ba. Sai haushin Hamidah
da ya kara cika ta.
Sun tarar jirgin da zasu hau zuwa Lagos har ya kusa gama lodi, don haka a gurguje suka yi
sallama da Hamidah ta bashi jakar Amani a hannun sa, ya hada da tashi yana turawa Amani na
bin shi a baya, yana cewa a ran sa yau shi Mukhtar ne da dakon kaya, Alhaji ya ce yayi komai
don ya lallaba ta, amma kuwa dakon kaya ai is frustrating, musamman ga namiji kamar sa, to
amma ita yanzu din iyalin sa ce. Annabi SAW kuma yayi umarni da a tausayawa mata, dattijai
da kananan yara, a agaza musu. But duk da