Author : Sumayya Abdulkadir Category : Taskar Novels
AMANI
2
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com
THE AMINA-BRIDE
A
can cikin gida Amani ce sunkuye tana jan ruwa a rijiya domin tayi wanka, sai ta ji muryar
Kawun ta Malam Idrisu daga zaure yana fadin a shigo da goron da alewa a kai dakin Talatu ta
raba ta baiwa kowa. Sannan ya shiga kwalawa matar sa Baba Talatu kira yana cewa kina ina ne
Talatu? An daura auren UWA da wannan yaron (Mukhtar) yanzun nan, turo min ita, ga nan
sadakin ta in bata a hannun ta.
Talatu ta fito daga dakin ta tana daura kallabi ta dubi inda Amani ke tsaye a gindin rijiya
wadda a lokacin ta dakata da jan ruwan kadan, tana sauraron me Kawun ta Baba Idi ke cewa,
Talatu ta ce ai gata nan a tsaye, tana jin ka.
Kawu Idrisu yace au to! Banza kika yi da ni kenan Uwa? To bar jan ruwan ki same ni a daki in
baki sadakin ki Amani ta cigaba da jan ruwan ta wani malolon bakin ciki ya zo ya tsaya a
makogaron ta, ya ki wucewa ya tokare numfashin ta, ta ma kasa fahimtar me Kawun ta ke nufi
data same shi a daki. Kawai sai gani suka yi ta saki gugan a cikin rijiyar ji kake cundum! Ta
wuce dakin da aka sauke ta.
Kayan ta ta hau tattarawa tana dannawa a jakar da tazo da ita. Baba Idi na can yana jiran
zuwan ta ya bata sadakin ta, ta sulale ta fice daga gidan ba tare da kowa ya ankara da fitar ta
ba. don Talatu ta koma daki tana shiri don fita ta gayawa yan uwa da abokan arzikin su daurin
auren da aka yi yau dinnan da gayyatar su wunin biki a gobe. Daddy da Mukhtar suna dakin da aka sauki Daddy din, suna tattauanawa bayan daurin aure,
kan Mukhtar a sunkuye yana jin yadda Hon. Usman ke masa magana cikin tsananin raunin
murya, wadda babu komai a cikin ta sai kauna da tausayin diyar sa Amani, wadda a yau ya
danka amanar ta a hannun mijin aure mafi soyuwa a zuciyar sa. A daidai lokacin Amani ta fice daga gidan ba tare da sun sani ba, dan acaba ta tare ta ce ya
kai ta tasha. Tunda take a rayuwar ta bata taba hawa acaba ba sai yau. Da ya fizgi babur din
saura kadan ta wuntsilo kasa, ta kama rigar dan acaban nan ta damke tana salati, nan tsamin
hammatar dan Acaba ya kusa sumar da ita. A haka ya fizge ta zuwa tasha yana fadin Hajiya
sakar ni don Allah kada kisa duk mu kifa, in baki iya hawa ba ki taka sayyadar ki mana?
A can dakin Baba Idi, Hon. Usman ya cigaba da cewa Mukhtar wanda a yanzu ya tashi daga
yaron sa ya koma surukin sa.
Mukhtar bana neman komai daga gare ka sai tausayi da kyautatawa ga Amani, bata san
kowacce irin wahalar rayuwa ba kada ka bar ta ta sha wahala, amma na yarda duk inda zaka
shiga a duniya ka tafi tare da ita, ka tausaya mata, ka kasance mai hakuri da halayen ta, na san
zaka iya shi yasa na baka, da na san bazaka iya da ita ba ko kusa ba zan fara tunnanin hada ku
aure ba.
Na lamunce maka kuyi amfani da duk abinda ta mallaka tare, ka taimaka mata ta cigaba da
juya dukiyar ta ko bayan rai na.
Sannan Baban ku Idi yayi magana a kan cewa yana son muje ga dangin ka mu kai musu
matar ka idan iyayen ka basa raye. Yace hankalin sa ba zai taba kwanciya ba in ba ya ga asali
da tushen ka ba, ka yi hakuri da abinda ya ce dinnan, ba rashin kauna bace gaskiyar aure
kenan, ta fanni na bani da matsala da wannan, ka sani ko ba ka da kowa a duniya na riga na
amince ka zama suruki a gare ni.
To amma nima inada na gaba da ni wanda shine waliyi a gare ta, kamar yadda na zama
waliyin ka, dole a yi masa uzurin da yake so na dangana ta da iyayen ka.
Mukhtar ya yi shiru, kansa na kasa, sai kara dukar da kan nasa kasa yake yi yana jin faruwar
komai kamar a mafarki. Wai Amani ta zama matar sa ta sunnah daga yau. Wannan alamari
sounds unbelievable! Amma baa mamaki da ikon Allah. Zuwa yanzu ba zai ce ga gurbin da ya
ajiye Amani a zuciyar sa ba, da wannan sabon matsayin nata na mata a gare shi. Illa iyaka ya
san zuciyar sa bata kin auren.
Amma kuma maganar da Alhaji ke yi yanzu a bar dubawa ce, Alhaji yayi kokari matuka da ya
bashi auren yar sa ba tare da ya san kowa nasa ba, ba kuma tare da ya san wani abu akan sa
ba (asali, tushe da nasaba). Sai ya shiga tambayar kan sa ko shi a karan kan sa ya shirya
komawa gida din? Idan bai shirya ba sai yaushe? Mutuwa bata sallama, duk da cewa har yanzu
zuciyar sa bata huce ba, bata shirya komawa ga iyayen sa ba, amma hakika yana son ganin
Ummami. Ko da ba don mahaifin sa ba zai koma saboda ita, ta kasance mace mai rauni
karkashin ikon mahaifin sa wasu abubuwan da yawa da yake zarginta da su ya kamata ya yi
mata uzuri a kan su, cewa ba ta da karfi a kan rayuwar sa sai abinda mijin ta da kuma aladar su
ta wanzar a kan ta, wato tana bin norms, culture and tradition ne na daular su. Me yasa tuntuni
bai yi wa Ummami wannan uzurin ba?
Da Daddy ya ga Mukhtar ya yi zurfi a tunani, sai yace Mukhy, in fa baka son komawa ni ba
zan takura maka ba, amma ya kamata kayi tunanin cewa yanzu yaya zaka tara wadanda dole
wataran zasu bukaci sani ko ganin dangin su, na fahimci akwai abunda kake boye mini, ko ince
yake damun ka da baka so in sani, amma ina ganin mun wuce wannan stage din yanzu, mun
zama daya fa Mukhy, feel free with me ka gaya min damuwar ka da abinda ya rabo ka da gida
don Allah.
Mukhtar ya muskuta sannan yayi ajiyar zuciya, a hankali ya soma baiwa Alhaji amsa duk da
cewa bai shirya bashi amsar ba.
Alhaji ka yi hakuri ka bar maganar zuwa Diffa zuwa nan gaba kadan, ka bani dama in fara
cikawa Amani alkawarin dana daukar mata first, na kai ta ga mahaifiyar ta bisa amincewar ka.
Nayi maka alkawarin bayan wannan in muka dawo zan dauke ku duka har Baba Idrisu da
Baba Sahura mu tafi Diffa ku ga asali na mu kuma gabatar da Amani ga mahaifa na.
Im very sorry Alhaji, da na boye maka cewa iyaye na suna nan a raye, koda yake da baki na
ban taba furta maka cewa basa raye ba, kai ne kake tsammanin hakan.
Hon. Usman ya shiga Hamdala yana fadin masha Allah, to shikenan Mukhtar, take your
time. Na amince ka dauki Amani ku tafi Sierra Leone daga nan ku nemi mahaifiyar ta.
Zan baka adireshin gidan iyayen mahaifiyar ta a rubuce. Sai kayi muku booking jirgi gobe in
Allah ya kai mu sai ku wuce, na so in yi muku biki na alfarma kafin tarewa amma yanzu ina
ganin ku fara isa ga mahaifiyar ta ko hankalin ta ya kwanta, in yaso ayi komai tare da dangin ta
na Uwa dana uba zai fi sa ta farin ciki har ta karbi auren da sauki, ka san halin mutuniyar taka
har yanzu ba wai ta amince bane, nayi gaban kai na ne na abinda addini ya ce in yi, wato a
matsayin ta na budurwa in zaba mata miji nagari, ba tare da na bi raayin ta ba.
To amma na amince sai in ba Da na Mukhtar bane mijin Amani, in shi ne kuwa bani da haufin
nan bada jimawa ba zai sarrafa min Amani zuwa yadda nake burin ku zauna tare cikin kauna da
soyayya mai yawa.
Ina kara cewa ka yi hakuri da Amani, hakuri ba dan kadan ba, har ka aro wani ka kara a kan
wanda kake da shi, mai hakuri shi ya kan dafa dutse har ya sha romon sa.
Ina mata kwadayin samun tarbiyya wadda ta dace daga gareka.
Daga nan Alhaji ya ce ya gyara masa shimfida yana so zai kwanta ya huta, ya jaddada masa
cewa ya yi booking masu jirgin tafiya Saliyo tun a daren yau, ya kuma shiga cikin gidan ya
gayawa Amani yanzu idan ya fita cewa ta shirya gobe zai cika mata burin ta. shi kuma Mukhy
zai cika mata alkawarin ta. Bayan ya bar dakin da Alhajin yake dakin da aka sauke shi ya nufa wato dakin Kamilu, sai ya
tsaya daga zaure ya kira Isyaka da ke wucewa ya ce in ka shiga ciki ka turo min Amani, kace
sakon Alhaji zan bata. Kunya ta sa ya kasa shiga gidan kamar yadda Alhaji ya umarce shi.
Yaro Isyaka ya je cikin gidan ya duba har dakin Laure ya duba da na Baba Talatu amma bai
gan ta ba, ya tambayi Laure ko tana ina? Tace nima tun dazu ban ganta ba. naje makaranta
yanzu na dawo. Ya koma ya gayawa Mukhtar bata nan. Mukhtar ya ce ya koma ya tambayo
Baba Talatu, ko ta gaya mata zata wani wuri, Talatu ta ce rabo na da ita tun da na gan ta a
gindin rijiya bayan daurin aure, kafin in fita zuwa makwabta, Kawun ta ya yi mata kiran duniyar
nan ta karbi sadakin ta amma yarinyar nan tayi funfurus ta yi banza da shi bata je ba har ya gaji
ya fita masallaci.
Mukhtar bai san sanda ya baro zauren ya tako ya shigo gidan ba, har da shi aka caje gidan
kaf babu Amani babu ko tsinken ta.
Daga baya kwakwalwar sa ta gaya masa babu shakka Amani ta samu labarin daurin auren
su ne daga bakin Baba Idi, ta kuma yanke hukuncin gudu. Da dai ta bi umarnin mahaifin ta a
kan sa.
Zuciyar sa tayi bakikkirin, ran sa yayi mummunan baci da Amani, yana mamakin kafiya da
taurin kan ta, wai shi mace ke gudu! Macen ma wadda in ba don darajar mahaifin ta ba ko kallo
bata ishe shi ba, bai ji ya damu da inda ta tafi ba don ya san dai ba zata yi nisa ba, tunda bata
da adireshin Maman nata, yana ji a jikin sa Balogun Sunday yaudarar ta kawai yayi, yafi
damuwa da halin da Alhaji zai shiga in aka gaya masa cewa ta gudu!
Ya dade tsaye cikin kunan rai, ya tambayi kan sa ko meye aibun sa haka da Amani ke masa
irin wannan kiyayyar, bayan na kasancewar sa yaron Baban ta kamar yadda take yawan
ikirari???
**** **** ****
“THE RUNAWAY BRIDE”
A
mani Faskari, jingine jikin tagar motar haya ta Sharon mai tafiya garin Bauchi, ta yi kuka tayi
kuka a cikin mota har ta godewa Allah. Da wuya wani abu ya sanya Amani kuka, mace ce mai
dakakkiyar zuciya kuma jajirtacciya mai jin cewa ko me namiji zai iya itama zata iya, amma yau
da ta tabbatar da igiyar auren Mukhtar ta hau kan ta, daga bakin da ba zai mata karya ba, igiyar
kuma ba ta kowa ba ta Mukhtar Diffa, babu shakka an shammace ta, domin bata taba kawowa
haka da wurwuri Daddy zai yi wanan danyen hukuncin ba, ta dauka ko zai yin sai ya nemo
dangin Mukhtar tukunna wanda kafin nan ita ta yi kokari ta gudu gun Innar ta.
A wannan lokacin she cannot control her tears domin ji tayi tagama faduwa kasa warwas!
Babu class dinnan, ta kare mata, kuma yanzu bata fi sauran mata ba tunda ta kare a yaron
Baban ta.
Kenan sunan TAFISU ya bar ta yanzu, bai dace da ita ba yanzu, duk sauran mata sun fi ta
aji, ajin ta ya fadi! Tunda a karshe duk gatan nata da ego din ta da Daddy ke fadi ta kare a bada
sadakar auren ta ga mijin da zata kira yaron gidan su, mara asali mara nasaba da ko tushen sa
baa sani ba. Tana da tabbacin Daddy sadakar ta ya baiwa Mukhy, tana da tabbacin sadakin ta ma Daddy
ne ya biya, don Mukhy ta tabbata ba zai taba cewa yana son ta ba ko da yana son ta din, balle
zata iya rantsuwa ta ci laya kan cewa yadda bata kaunar sa haka shima baya kaunar ta, ko
magana da yake mata a kan dole ne bisa tirsasawar Daddy da ko kallo bazata ishe shi ba a dai
wannan girman kan nasa da rashin son raini, kamar yadda itama koda kuskure bata taba jin
son sa a ranta ba sai jin zafin sa, na kwace mata soyayyar mahaifin ta da yayi, tana bakin cikin
wannan abu, tana kishin Mukhy for that, tana jin haushin wannan matsayi da yake da shi a gun
Alhaji mai girman da ya kamo nata ko tace ya zarta nata yanzu a wurin mahaifin ta Hon.
Usman.
Babban abunda ke sa ta kara tsanar Mukhy shi ne rashin walwalar sa, kamewar sa mai
hanawa ka tunkare shi da maganar da ka yi niyya, ko ta shirya ci masa mutunci ko rama rashin
mutuncin da yake mata kallo daya zai yi mata ta ji bazata iya ba, a takaice yanayin rayuwar sa
mai matukar aji da yanayin halittar sa na rashin daukar wargi ko raini yana ci mata tuwo a
kwarya, yana hanawa ta taka shi a duk sanda ta so.
A wurin ta wadannan halaye ne da bata so a Da namiji, domin zasu hana ta jan zaren ta
yadda take so a gun mijin auren ta.
Allah da ya halicce ta yayi ta mutum ce mai tsananin izzah da fadin rai, wato mai tsananin
son a bata girma, mai son mulkar mutane a karkashin ta, ta yadda in sun ganta har suyi ta
bare-baren jiki don cika umarnin ta, a duniyar ta mutum ce ita mai son kowa ya zauna a kasan
ta, tana juyawa tana mulki yadda take so, tana kuma taka duk wanda ya shiga hancinta. Tun
tasowar ta a haka ta taso da wannan mummunar dabia, tunda a kan ta Daddyn ta ya raine ta,
cewa ta fi kowa gata, ta fi kowa iko, wato ta riga ta taso a matsayin mutum mai juya mutane a
karkashin ta da basu order su bi, sai ta ke fatan hakan ya dore har a gidan auren ta, har kuma
karshen rayuwar ta wato shima mijin duk da ta aura ya ya zama tana juya shi kamar hakan.
Amma auren Mukhtar ta tabbata babu shakka sai dai ita ta koma kasan sa, a irin halaye da
dabiun sa da ta dade da sani, wanda wannan wani abu ne da bazata taba yarda da shi ba.
Daddy ya gama kaskanta ta, don haka ta yanke shawarar barin su shi da Mukhtar din nasa,
ta bar musu gidan ta bar musu garin, in ya so Daddy yayi zuciya ya haifawa Mukhtar din sa
wata yar a gobe ya aura masa. Tunda ya asirce shi har yana fadin bai iya surukuntaka da kowa
sai shi. Ita wallahi sau dubu gara mata Alhaji Sadi akan Mukhy, ko babu komai zata juya shi yadda
take so, musamman data fahimci yadda ya gama macewa a son ta, zai yi wuya tasa kara ya
tsallake duk yawan shekarun nan nasa. Sannan zai yi ta tarairayar ta ne irin na tsohon da ya
dau yarinya, amma Mukhtar??? Wani kukan ya kara kwace ma Amani, ta kifa kai a kan tafukan ta tana ta yi ba kakkautawa.
Wato duk wasu plans din ta na gidan aure Daddy ya rusa mata su, ta hanyar aura mata
wanda ya fita izza. Mujin da yake da tabbacin bazata iya mulka ba.
Iyaka tunanin ta bata ga