Chapter 28 Reading Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel HN Novels

Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 69

81K to 84K   out of 206.1K words

Ahmad kallon Amreesh kawai yake he could feel the drop in temperature


********ZAKEE MANSION


Wani irin katafaren gida ne gari guda mai ɗauke da golden gate side by side securiy ne, buɗe gates ɗin sukayi lokacin da motar su Amreesh ta ƙaraso, suna Faman faɗin '' welcome young masters '' driving Dr Ahmad yake eyes looking ahead Amreesh a gefen sa ya jinginar da kansa, shima dai bai san abinda zasu tarar ba amma yasan koma menene bazai ƙare da kyau ba. Bayan yayi parking ya fito ya buɗe ma Amreesh ƙofa shima ya fito, tare suka jera suka shiga katafaren MANSION ɗin Wanda kusan komai na ciki green and white ne, according to the residents,green represents nature kuma su suna son yanayi dan haka agidan ma akwai itatuwa of varieties of fruits. Gawani chandelier dake hanging high up, Babu single room down stairs sai dai upstairs kuma parts ne ba ɗakuna ba,parlorn ya haɗu sosai duk wani abun more rayuwa akwai a wurin ga daddaɗan ƙamshin dake tashi. Tun lokacin da su Amreesh suka shigo servants ɗin dake kai kawo suka tsaya suna ta Faman kwasan gaisuwa bowing slightly kan su ƙasa, bayan tafiyar su Amreesh daga wurin suka ɗago kawunan su suna ƙusƙus tsakanin su.
Wata corner su Dr Ahmad suka bi da ya sada su da main parlorn da ake family meeting.

Wani kata faren parlor ne wannan ya fi wancan girma haɗuwa da tsari. Gabaki ɗaya ahalin Zakee tun daga Manyan su zuwa ƙana nan su babu wanda baya wurin.

Old man Zakee zaune saman wata kujerar royalty it was made out of pure gold shima kansa kayan dake jikin sa represents royalty duk da ko su ba jinin sarauta bane, shi ba fari ba shi ba baƙi ba tsaka tsaki ne, fuskar sa mai cike da kamala da Dattaku ga kwarjini da haiba da Allah yayi masa, gefen sa Uncle T ne sai cika yake yana batsewa fuskar sa a mutukar murtuke Uncle Naseer shima gefen sa sai karkaɗa ƙafa yake kamar wata mace shima dai fuskar sa ba annuri, sai Uncle Ismael da yake nan kamar ba abinda ya dame sa sai kuma papa baban Amreesh da yayi ta gumi.
Ɗayan gefen kuma matan uncles ɗinsa ne zaune, Hajiya Saude matar Uncle T, Hajiya zakiyya matar Uncle Naseer Hajiya Turai matar Uncle Ismael sai Hajiya maleeka matar papa, kowace da abinda ke yawo aranta musamman Hajiya Turai da zakiyya da suka kasa ɓoye wa, they had alot to gain idan abinda ake zargin Amreesh gaskiya ne to ma ai gaskiya ne tunda gashi abu ya karaɗe ko ina and it's affecting their business.

Daga ƙasa kuma yan mata da samarin gidan ne, Kabir, yaƙub, Malik,Azeezah,maraƙisiyya, da Ummu yayan hajiya Turai ,sai saudat, Usman, haneef Umar,sadeeq yayan Hajiya Saude sai kuma mariya Ja'afar,Adam , yaseer, khaleel,Aymana da sultana yayan Hajiya zakiyya sai
Abdul Malik da Abdul Rahman yayan Hajiya Maleeka.

Abdul Malik ɗan Uncle T,Abdul Rahman ɗan Uncle Naseer,Umar, Sadeeq da maleek ya'yan Uncle Ismael, su suke taya iyayen su juya family business dukan su sa'an su Amreesh ne
Ga wani irin competition dake tsanin su babu Maison yaga dan uwansa ya wucesa kuma iyayen su basu kwaɓe su ba, amma cikin su Babu wanda ke ƙoƙarin cutar da wani dan hanashi samun cigaba. ra'ayin su baya taɓa zama ɗaya,abu ɗaya da ra'ayin su yazo ɗaya akansa shine tsanar su ga Amreesh Amma wannan ba su kaɗai ba kusan kowa agidan hakane banda granpa da papa, duk dashi papa duk sanda Amreesh yake nesa dashi zai ji yana matuƙar kewa da begen dan nasa amma daga sun zo face to face sai yaji kuma babu wanda yaƙi jinin haɗuwa dashi sama da Amreesh. Sai kuma yan matan gidan dake mutuwar son Amreesh da ko kallo basu ishe sa ba.
Tun tuni suka ƙagu da ya zo su ganshi ko zuciyoyin su zasu samu Salamah duk da wasu daga cikin su, Dr Ahmad shine Abin harin su. Sun kuma san gidan kowane daga cikin su amma they don't dare to go.

Ga baki ɗaya palorn yayi shiru kowa ta ciki na ciki, granpa da kanshi yaga nawar su Amreesh su zo yayi kewar su musamman Amreesh

Turo ƙofar dr Ahmad yayi bakin sa ɗauke da sallama Amreesh biye dashi a baya duka aka yo masu chaa da ido.
Har suka samu wuri suka zauna Ahmad ya gaida uncles ɗin nasa duk da ba wani amsawar kirki suka yi ba. Shi ko Amreesh tunda ya zauna ya maida idanun sa ya lumshe yayi shiru kamar babu sa a wurin da ido suka bishi wani abu na tokare masu maƙoshi amma babu wanda yayi magana.... after a while granpa ya fara magana '' Muhammad mai zakace game da abinda ke ta yawo a kafafen sada zumunta?" Kafin Amreesh ya bada amsa Uncle T a fusace yace '' Yanzu Alhaji duk bayan abubuwan da ka gani you're still asking the ɗan iska? Tunda ya zo nan ya zauna tsabar iskancin da taɓarɓarewa waya gaida?"
Uncle Naseer ya karɓe da faɗin '' bar fitsararren ɗan iska bamu zai nuna ma ya girma ba? Da har zai zo ya zauna inda muke bai iya gaida mu ba! Ya je yana lalata yaran mutane ai dole idanun sa su buɗe'' Uncle Ismael dai bai ce komai ba haka ma old man Zakee duk da kalaman da suke faɗa akan Amreesh na sukar ranshi papa kuma ya yi ƙasa da kanshi, yana mai jin baƙin cikin abinda yan uwan nasa ke faɗa akan ɗan shi,he so badly wants to defend Amreesh yana so ya faɗa musu cewa ɗanshi bazai taɓa aikata abu makamancin haka ba amma ina! Words failed him. Yan matan kuma kowa ce sai cika suke suna batsewa suma basu jin daɗin yanda ake magana akan Amreesh infact they don't blame him sai ma yarinyar da aka kama su tare, a cewar su,she must have seduced him.
Yan samarin ma kowa ya cika da haushin Amreesh for the fact that saboda wannan scandal ɗin, masu hannun jari a Zakee and sons company da yawa sun cire hannun jarin su aside from that dama sun tsane sa.

Hajiya zakiyya tace '' dama Ni nasan tunda aka ce yana da wannan cutar ƙaryan nasan ba gaskiya bane, ji dai yanzu it has been confirmed bin mata yake awaje '' Hajiya Turai tace '' dama pa? Abu jinin masu jajayen kunnuwa you can't expect any less '' Hajiya Saude ta taɓe baki tare da faɗin '' yanxu Ni ba wannan ba ma,baƙin painting daya shafa ma sauran yaran gida pa? Nan pa sai da aka tambaye sa idan aure yake so amma ya murje ido yace shi babu wacca zai aura acewarsa cutar bazata bari yayi mu'amala da wata ya mace ba amma ji yanzu?'' kowa sai tofa gubar bakin sa yake matan su da mazan su banda papa, uncle Ismael da old man Zakee da yayi shiru Yana kallon kowa, idan Ahmad yayi ƙoƙarin kare Amreesh su ƙundumo zagi su jefa masa shida Amreesh, accusing him if being an accomplices.
Duk maganganun da suke babu wacca tashi ga kunnen Amreesh,tuni ya ɗauki abinda zasu faɗa as back ground noise and unnecessary hakan yasa he blocked it, Babu amfani a wurin sa, aside from that lokaci ya basu idan har lokacin ya cika zai tashi yayi tafiyar sa ne,Dr Ahmad ya kalli Amreesh cike da tausaya wa da kuma ƙauna ga ɗan uwan nasa,and he was more determined to defend him
'' shegiyar yarinya itama da tarbiyya bata ishe ta ba,ko mai ya haɗa ta da wannan fitsararren? Oho!" Inji Uncle Naseer
" To waya sani ma ko yara nawa yayi hakan dasu? Yazo ya ɓata wa mutane suna,dama muna da maƙiya da abu kaɗan suke jira suyi ta ya maɗiɗi da mu yanzu kuma sun samu'' Uncle Ismael da yake shiru tuntuni ya faɗa cike da tsana ga Amreesh, su kuma sauran yan mazan sai Allah wadai suke da Amreesh basu da ikon magana tunda Manyan su na magana if not they had alot to say.

" Ni dai gaskiya na la'anci wannan yari...''

'' Uncle T'' Amreesh ya faɗa with a cold voice eyes expressionless yana kallon Uncle Taheer,duk wannan abin da suke faɗa bai yi niyyar tanka masu ba dama kuma suma hakan suka tsammata, Amma jin suna zagin matar sa yasa shi buɗe bakin sa, kowa dake wurin kallon Amreesh yake cike da mamaki banda Ahmad
'' be respectful when you talk about her '' yayi maganar idanun sa baƙi ƙirin, sai da gaban uncles ɗinsa ya buga basu kaɗai Bama,harda matan su that were making mouth
Uncle Ismael yace '' oh rashin kunya zaka mana akan wata banza karuwa Muhammad?'' kowa sai girgiza kai suke in disbelief.... Amreesh ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya tuni temperaturen wurin yayi dropping kowa ya fara zufa, duk da Amreesh nasu ne they Really are afraid of his ruthlessness ba yaran kaɗai ba harda iyayen su, zufa suka fara duk da sanyin Ac'n wurin. Tuni idanun Amreesh suka koma multicolored this Time around saboda emotions ɗinsa were in disarray bazaka taɓa sanin abinda ke yawo cikin sa ba.

Bayan yagama binsu da kallo with a dangerously calm voice yace '' dukan ku anan U have no rights to question what I do! I'm an adult not some teenager'' they were all stunned ga wani shegen kallo da yake binsu dashi, to them he looked nothing less than the devil suka cigaba da kallon sa cike da tsana

Uncle T yace '' ai maganar gaskiya akayi yarinyar karuwa ce ba komai ba does it hurt you?" Amreesh yace '' U don't disrespect her, she's my wife! Bakuma zan lamunci cin mutuncin matata ba daga koma wane ne'' yana gama faɗar haka ya tashi ya fita.

Comment nd share pls
















WAYE SHI?(Behind the mask) By Autumn 17
Chapter thirty: Bring her home




Bayan fitar su Amreesh wurin yayi shiru kamar anyi ruwa an ɗauke sai kallon kallo ake kowa na al'ajabin maganar Amreesh,Aure? Yaushe yayi auren
Yan matan kuwa their faces turned pale ita Wadda aka kama sun ce ya aura ko wa? Fuskar Hajiya Maleeka matar papa was unreadable dama tunda kowa ke magana bata tofa yawu ba. Papa kuma har yanzu kansa na ƙasa har yanzu ya kasa ɗagowa

Tsaki Uncle T yayi tare da faɗin '' Aikin banza mu za'a raina ma da wayau? Wai yayi aure! To kai Yousuf da kake uban ja'irin ya faɗa maka zai yi aure?'' kowa ya kai duban sa ga Uncle T kafin su dawo da kallon su ga papa da yaƙi cewa komai abun duniya yabi ya ishe sa. Uncle Naseer yace '' ai yaron bai ganin kowa da Gashin ido dan haka ko uban nasa bai sani ba!" Uncle Naseer ya ƙarashe maganar cike da ƙunar rai. Kowa ransa ƙuna yake especially su Hajiya masu buri,yan matan ko zuciyoyin su kamar zasu yi bindiga
Miƙewa Old man Zakee yayi ahankali ya nufi hanyar fita, Uncle Ismael yace '' Alhaji bazaka ce komai ba game da y...'' ɗaga masa hannu old man Zakee yayi
Calmly yace '' mai zance? Ku dukan ku bakunyi magana ba? Ai yin maganar tawa bashi da amfani kun isa ai'' yana gama faɗar haka ya fice wurin ya kacame da hayaniya and the blame was shifted to papa duk da kuwa ya girme su su duka

Tashi yayi ya fita walking slowly zuciyar sa ƙuntace yaga ɗansa and yet he couldn't even pull him in a warm hug,kowa sai zagin ɗansa yake yana tsine'' masa yet he couldn't defend him! Shin wai shi wane irin ubane? Mai yasa yake sakaci da ya'yan sa gashin yanzu babu ɗayan su dayake tare dashi. Tura ƙofar ɗakin sa da ya gaji da haɗuwa yayi ya shiga closing the door wutar ɗakin kashe hasken ranar da ta kusa faɗuwa ne kawai ya haskaka ɗakin, kusa da window papa ya tsaya yana dafe saitin zuciyar sa idanunsa sun ciko da ƙwalla in a whisper yace '' ya Allah '' ya zauna ya dafe kansa yana faɗi ciki ciki '' If hazel was alive,maybe...may be then...da yanzu family na would have been complete....me yasa Muhammad mai yasa?" Ya yi maganar baƙin ciki shimfiɗe a fuskar sa, he wanted to cry, yana so yayi ihu ko zai ji sauƙi but would that solve it?...

Bayan fitar papa kowa ya fara fita one by one magana ɗauke a bakin su kowa baƙin cikin sa daban amma tabbas suna cikin baƙin ciki.

Amreesh ya fito daga meeting hall ɗin yana tafiya cikin natsuwa fuskar sa idan ka kalla ba zaka taɓa sanin abinda ke yawo cikin sa dan babu wata alamar tashin hankali tattare dashi however,ga wanda yasan Amreesh idan ya kallesa zai ga his face is much more colder than usual, idan Amreesh ya saki fuska sai dai idan yana tare da matarsa ne kawai. His heart felt empty at the moment

Shigar sa mota yayi dai Dai da shigowar saƙo a wayar sa jawo wayar yayi bayan ya zauna a passenger seat ya duba saƙon

“𝐴𝑛𝑜𝑛𝑦𝑚𝑜𝑢𝑠”

_𝐶𝑜𝑛𝑔𝑟𝑎𝑡𝑢𝑙𝑎𝑡𝑖𝑜𝑛𝑠 𝑓𝑜𝑟 𝑢𝑟 𝑎𝑤𝑎𝑟𝑑 𝑒𝑛𝑒𝑚𝑦, 𝑖𝑛𝑎 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑢 𝑙𝑖𝑘𝑒𝑑 𝑚𝑦 𝑐𝑜𝑛𝑔𝑟𝑎𝑡𝑢𝑙𝑎𝑡𝑖𝑜𝑛𝑠 𝑔𝑖𝑓𝑡 𝑢ℎ𝑛,_

𝑌𝑜𝑢𝑟𝑠 𝑠𝑖𝑛𝑐𝑒𝑟𝑒𝑙𝑦 𝑎𝑛𝑜𝑛𝑦𝑚𝑜𝑢𝑠.

Bayan Amreesh ya gama karanta saƙon he realized that scandal ɗin dake yawo ashe wannan ne musabbabi dama ya zargi hakan....cije lips ɗinsa Amreesh yayi eyes icy cold. Dr Ahmad ne ya shigo motar ya zauna driver seat ya ɗan kalli Amreesh tada motar yayi suka fita daga family house ɗin, wayar sa Amreesh ya jawo yayi dialing ɗin Secretary Ayman bayan ya ɗaga curtly yace '' arange meeting with TBC news'' yana gama faɗar hakan ya katse kiran notifications sai popping suke News, business partners and social media.....
Har Amreesh zai mayar da wayar cikin aljihu kiran old man Zakee ya shigo Kamar kar ya ɗaga sai kuma dai ya ɗaga without saying anything from the other end old man Zakee zaune saman gadon sa with a calm voice yace '' Youg Zakee '' Amreesh yayi shiru bai amsa ba oldman Zakee ya ƙara faɗin '' Zakee my friend'' still Amreesh bai amsa ba,Dr Ahmad ya saci kallon shi slowly yace '' Zakee pls'' lumshe idanun sa Amreesh yayi from the other end har old man Zakee ya sadaƙar Amreesh ba zai yi magana ba yaji yace '' Old man '' kyakkyawan murmushi old man Zakee yayi tare da dafe saitin zuciyar sa jin Muryar Amreesh dramatically old man yace'' Wai harnaji sauƙi na ɗauka nima ta shafe ni'' Amreesh ya sassauta Muryar sa yace '' uhm'' kawai, Dr Ahmad yake glancing towards him once in a while yana ɗan murmushi jin yanda Amreesh da kakan nasu ke hira kamar wasu abokai duk da old man Zakee ke maganar all the times Amreesh kawai bai fi ya amsa da uhm,a'a ba.

After a while old man Zakee yace '' kawai sai naji kayi aure Muhammad,how is it done like that uhm? Nida naso inyi attending ɗin auren ka in zama cikin abokan ango sai kuma naji cewa har anyi auren babu Ni? Ban ji daɗi ba young Zakee'' Shiru Amreesh yayi bai ce komai ba sanin bazai yi magana ba yasa Ahmad fara ba oldman haƙuri dan dama wayar a speaker take.. oldman Zakee ya sauke ajiyar zuciya sannan yace '' when will you bring her home?" Idanun Amreesh dake lumshe ya buɗe yana kallon screen ɗin shima Dr Ahmad ya kalli Amreesh waiting to hear his reply,sanin da oldman yayi Amreesh na iya ƙi yasa ya fara lallashin sa akan ya kawo matar sa tasan dangin sa suma su santa ba'asan abinda gobe zata haifar ba, Dr Ahmad yace '' zata zo granpa '' wani kallo Amreesh yayi masa shiko yaƙi yarda ya kalli Amreesh ɗin '' yauwa na gode Dr Zakee '' yar dariya Ahmad yayi jin granpa ya kira sa da Dr Zakee


09:00
Tsaye take bakin window jikin ta sanye da wata rigar Bacci baƙa iya guiwa, hannayen ta naɗe a ƙirjin ta kanta jingine da frame ɗin windown, kanta saye da hula baƙa fuskar ta ɗauke da damuwa with a every ticking of time bugun zuciyar ta ƙaruwa yake, she was afraid idan pa dangin Amreesh suka ce Dole sai ya rabu da ita? Idan pa shima yace bazai zauna da ita? Lokacin da ya shigo Bayan sun dawo daga ko ina ma suka tafi he didn't even look at her. Wannan warmness ɗin datake gani a fuskar sa ako da Yaushe idan suna tare babu shi yau why? Itama taga Abinda ke trending a social media Amma ai ba laifin ta bane ko? Hawaye suka ciko idon ta,she felt tired she was depressed hawayen suka fara silalo wa suna jiƙa gaban rigar ta. Turo ƙofar Amreesh yayi ya shigo saye yake da gray pajamas sai ƙamshi yake zuba wa. Yanzu suka gama magana da board of directors it ended in tension wasu na faɗin zasu janye hannun jarin su idan har Amreesh bai fito yayi public speech yayi addressing ɗin issue ɗin scandal ba har directors ɗin sukayi Magana suka gama Amreesh baice komai ba. Abinda suke barazana ne kawai he owns 70 percent of the company 's shares and he made the company without him it will collapse. Tsayuwar sa taji bayan ta juyo wa tayi crashing herself into his arms tana kuka tace'' yanzu kaima zaka juya min baya ne? Abinda Ya faru ba laifi na bane why do I feel like you're also blaming me?" Ƙara rungumota jikin sa yayi haɓar sa akan ta with a deep voice yace '' ba haka bane Mahee,i was trying to settle things bazan taɓa juya maki baya ba.'' Salmah sai kuka take kamar ranta zai fita slowly yace '' I'm sorry '' yana patting ɗin Bayan ta. Sun daɗe a haka kafin ya zauna bakin gado sitting her up on his lap yana share mata hawaye yace '' kwanakin nan You cry too much I'm afraid you will fall sick'' yayi maganar cike da kulawa yana

28 / 69