Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ɗin nan dake back yard for a whole week '' zaro idanu sukayi suna kallon juna, akwai nisa daga tap zuwa drum ɗin and it's huge
Kathy tace '' Sir please don't.....'' yace '' your punishment is multiplied '' a gasp escaped their lips suka kalli Kathy with accusing eyes
Tayi ƙasa da kanta. Mr kanya yace '' zan rufe idanuna idan na buɗe su nagan ku anan, You will serve for a month straight '' yana gama faɗar hakan ya rufe idanunsa da sauri suka fara gudu, every part of them itch....
Bayan ya buɗe idanun sa mr kanya yabi bayan su da kallo, apart of him believing what they said..... But no evidence
***********************
Koda Samha ta koma ɗakin su it was 7 30 Ashe hanyar da ta bi nada nisa, Ra'esah da fateemah suna kallon ta sukace daga ina rule breaker? Dariya sukayi su dukan su kafin Samha tace '' wani aiki ne ya tsayar dani amma yanzu an gama '' tana gama faɗar hakan ya shige toilet
Na'ema dake kwance saman gadon ta,tabi Samha da wani tsinannen kallo she really hates the girl, Ina ma zata samu ko da one opportunity ne..... Bada daɗe wa ba Samha ta fito, alwala tayi yazo tayi sallah tana nan zaune har aka kira sallar isha'i suka yi Sallah banda Na'ema. Bayan Samha ta tambayi meyasa bata yi Sallah ba tace '' mind ur business '' Jan bakin ta Samha tayi shiru
Fateemah ganin tense atmosphere ɗin hostel ɗin tace '' muje cafeteria'' miƙewa sukayi da hijabban da suka yi Sallah suka nufi cafeteria
Suna tafe suna wasa not minding dare ne, sanyi har ya sauko ga taurarin da suka ƙawata sama, the view was amazing
Ra'esah ta nuna wani tauraro mai haske tace ''Samha kinga wancan tauraron?" Samha da Ra'esah suka kalli inda take nunawa suka ce su basu ga komai ba saida ta ta nuna musu sannan suka ce sun gani,
Ra'esah ta dafe ƙirji tare da sauke ajiyar zuciya ta ce '' thank God ''
Dariya suka sa su duka kafin tace
'' ako da yaushe ina ganin kine kamar tauraron da yake haskawa yake kuma haskaka wanda ke tare dashi Samha,i never liked anyone the way I like you " Ra'esah ta ƙare maganar tana riƙe hannun Samha,itama Fateemah tace
'' Yes samha,you're a shield that protect us from the storm, , U give us courage Sam, Muna matuƙar ƙaunar ki"
Jawo su Samha tayi, and engulfed the three of them in a hug cike da ƙaunar juna kafin Samha tace '' nima ina ƙaunar ku sosai, I can't stand if something were to happen to you''
Sun daɗe a haka kafin suka rabu,
Fateemah tace '' aga wa zai riga kaiwa'' aiko suka kwasa da gudu suna rige rige.
Banko ƙofar cafeteria ɗin sukayi dukan su, suka zube ƙasa suna dariya, kowa ya zuba musu ido giving them weird looks especially saboda hijaban su,no one wears that...
Su dai su Samha ba abinda ya dame su, miƙewa sukayi Ra'esah tace '' na riga'' ''wai ma na riga'' haka sukai ta gardama har suka samu wuri suka zauna, Samha taje counter ta karɓo musu abinci.
Kowa ya maida hankali yana cin abinci some are busy chatting
Samha ta karɓo abincin kenan ta kawo daidai wurin table ɗin wasu, ɗaya daga cikin yaran dake zaune a table ɗin ta saita ma Samha ƙafa ji kake' gwain gwain,tim!!" Duk abinda Samha ta karɓo ya kife ita ma Samha ta faɗi
Wurin ya ɗauki shiru,all eyes on Samha da kuma yarinyar da ta taɗe ta, sai wani ciccin magani take
Da sauri su Fateemah suka zo suka miƙar da Samha suna kakkaɓe ta
'' kin ji ciwo?" Fateemah ta tambaya idanun ta na cikowa da hawaye, Ra'esah looked worried, girgiza kanta samha tayi sannan Samha ta kalli yarinyar
Calmly tace '' baki ga kin ture Ni ba?" Yarinyar ta miƙe ta hayayya ƙo ma Samha da faɗa tana zagin ta sannan tace'' wallahi dan kinga kina ma mutane su ƙyale ki Ni in kin min cimaki uba zanyi'' sakaka Samha tayi tana kallon yarin yar, suma su Ra'esah sun yi mamakin jin yanda yarinyar ta wani bi tana zagin Samha ta zubda habaici...
Over all mutanen cafeteria suma sunyi mamaki ,abinda ya fi basu mamaki the fact that Samha batace komai ba, dan sun san ba'a mata ta ƙyale.sai murmuring ake, a tunanin su ko Samha ta tsorata ne saboda yarinyar da ta taɗetan tana da tsawo ga ƙiba,in fact Samha ta bata suna 'giant number 2' dama tasan yarinyar
Ra'esah da fateemah suka ja Samha suka bar wurin ita kuma yarinyar ta ɗauka tsoron ta suke sai cigaba da tujara take.
Wani Abincin Fateemah ta karɓar musu, suka zauna suna ci suna hira kamar babu abinda ya faru, itako yarinyar har lokacin taƙi yin shiru ƙawayen ta sai zuga ta suke
Soon sai ga dark flames sun shigo, sanye suke da wasu orange ɗin riguna da jeans dukan su, wurin yayi shiru kamar ba kowa wurin. Kusa da table ɗin su samha suka tafi suka zauna, Ra'esah da fateemah became tensed banda Samha.
Bayan sun shigo sai gasu Lucy da zeenah su bakwai suma sun shigo, the atmosphere in the cafeteria became even more tensed
Saboda yanda suke kallon Samha kamar zasu cinye ta ɗanya, itako yi tayi kamar bata San da ko ɗaya daga cikin groups ɗin a wurin ba.
Table ɗin dark flames su zeenah suka zauna so their were eleven of them in total
'' hi guys '' matan suka gaida mazan,da wani jin kai su kuma suka amsa abinci aka kawo masu,suna ci suna hira tsakanin su time to time suna kallon table ɗin su Samha Hauwa a fakaice tace '' the fight is not over '' Samha tasan da ita suke,she smirked she likes it, she doesn't want the fight to be over not yet
Fateemah da Ra'esah tuni suka yi shiru suka cigaba da cin abincin su duk a takure kamar sauran ɗalibai
Samha tace'' naga nawar in koma gida wallahi '' Ra'esah tace '' ai an kusa fara jarabawa '' Fateemah tace '' za mu yi kewar ki Sam ''
Samha tace '' xamuyi exchanging ɗin address, ya Ahmad zai kawoni mu gaisa '' da gangan Samha ta kira Ahmad dan taba zee haushi and she succeeded
Maganganun su,suka ci-gaba da yi while dark flames low key low key suke studying ɗin Ra'esah da fateemah, suma yaran suna da kyau
Lashe bakin su sukayi exchanging knowing glances,idan Samha taƙi samuwa there are other alternatives....
WAYE SHI?(Behind the mask)By Autumn 17
Chapter twenty two: the fall out
The next day bayan an tashi break, Ra'esah ne da su Samha suka shigo cafeteria, unlike the usual atmosphere inda ko ina yake shiru, yau ko ina sai surutu ake, mutane suna duba wayoyinsu suna stealing glances on Zeenah and her co's
Dark flames na zaune a seats ɗin su, ga wasu mata kusan su huɗu zaune a cinyoyinsu doing all sorts of things cikin mutane ba kunya ba tsoron rabbi, su zeenah da Lucy on the same seat, fuskokinsu sun yi baƙi ƙirin, it turned out photos ɗinnan da Samha ta ɗaura a school blog anonymously have gone viral, mutane sai mocking ɗin su suke
SAMHA na shigowa all eyes turned to her, ana ƙus ƙus,duk da babu wanda yasan waya ɗaura hotunan,they were ninety nine percent sure Samha ce.
Ita ko samha as usual she confidently stepped in walking side by side with her sisters as they chat happily
Ra'esah CE a matuƙar ba zata suka haɗa ido da Emmanuel ya wani kashe mata ido yana shafa lips ɗinsa and biting it at the same time, wani irin faɗuwa gaban ta yayi
Na'ema ko tunda suka shigo kallo guda tayi musu ta ɗauke kai,cike da baƙin cikin kusancin su.
Wani table kusa da table ɗin su zeenah wata yar yarinya duma duma cike da ɗaga murya tace
'' Ashe ma duk wannan ɗage ɗagen,da jiji da kan na banza ne tunda har ba'a da ƙarfi,aikin banza....''
Tana faɗar wannan maganan mutane suka ɗauka akayi musu chaa,the silent mockeries became loud wani irin kunya ne ya rufe su
Suka fara mayar da martani ga waɗ ke zagin su Amma to No vail
Hakan ya zafafe su, Lucy ta miƙe cike da zafin zuciya ta jawo Samha ta fara duka, Samha was stunned
Sauran ma suka taso suna taya ta,ganin za'ayi wa Samha taron danandagi yasa su Ra'esah shiga don su taya ƙawar su.
The girls were busy beating each other black and blue, sun yi buɗun buɗun saboda sai da suka kai ƙasa suna faɗa. Sai banke tables suke suna jan gashin juna suna yagawa juna uniforms
Mutanen cafeteria were cheering them on, Na'ema abun ya ƙara bata haushi ganin duk tsawon lokacin da suka kwashe tare da su Ra'esah they never made any attempt to help her when in trouble... Amma Samha da basu daɗe da sani ba? They are ready to sacrifice their lives for her. Wani irin tsanan Samha taji ya shige ta,Yes! She hates the girl kuma idan da zata samu dama she will ruin her.
Suko mutane sai shewa suke ganin skirt buɗe a banza, the guys were hitting the table the cafeteria became absolutely chaotic
Sai naushi suke exchanging, Samha was having the best time of her life, acikin wurin Babu wanda yayi ƙoƙarin raba faɗan, Na'ema ji take ina ma ace za'a lakaɗawa Samha da su Ra'esah the beating of their lives
Suko dark flames tuni suka ture yan matan nan da suke zaune saman cinyoyinsu suna kallon faɗan suna lasar baki, Emmanuel yace'' we have to make our move on those girls soon,I can't wait to have a taste'' da sauri Chibuke yace '' ai nima na ga nawa, amma yaushe?"
Da wani irin shegen murmushi Andrew yace '' be patient, when the time comes ba su biyu kaɗai ba har da waccan hot headed girl ɗin itama hannu zata shigo''
Yana gama faɗar hakan suka wani taɓe kamar wasu mata
Mutane sun shagala da kallon faɗa,wasu na faɗin '' kuci gaba'' wasu na faɗin '' what a smoky punch '' all sorts of comments suka ji ance
'' what's going on here?" Da sauri mutane suka yi shiru waɗanda ke tsaye saman table da waɗanda ke tsaye na zama saman seat ɗin su
Masu faɗa suka wani yi saurin disengaging with Samha giving Ameerah wani irin wawan mari ji kake' tas!
Mutane suka wani rufe baki tare da waro ido suna faɗin ''e woo'' ''the slap enter ooo''
'' chai Da slap fit reset pesin brain''
'' sorry no cry ye''
Ameerah jin abinda mutane ke faɗa ta fara kokuwar ita ala dole sai ta rama, Mr kanya da yake kallon komai ya wani daka mata tsawa
Tsit wurin ya ƙara yi, su Samha sai huci suke mutane kuwa kowa ta ciki na ciki
Mr kanya yace '' Luciana Park, Katherine Brown, Amarachi iheukwu, Zeenah Aminu, Hauwa'u Bello,Ameerah Usman, Maryam kabir Fateemah Muhammad, Ra'esah Nasir '' daka tawa yayi yana kallon Samha, ya lashe leben ƙasa, yana kallon Samha he had been waiting for the moment he will punish her, da ƙatuwar murya yace '' **MS*RULE* *BREAKER,follow me!" Yana gama faɗar hakan ya juya ya fita, Mutane nata shewa,the girls looked kamar an tsamo su daga rame, gashin samha,Lucy, Katherine, Ra'esah da fateemah looked like birds nest.
An yagama Zeenah gaban riga,skirt ɗin Maryam sai zamewa yake, kowa dai da nasa.
Sai hararar su suke suna zage zage, ita dai Samha ta juyo wurin su Ra'esah tana tambayar su if they are okay murmushi Fateemah da Ra'esah suka yi sannan Fateemah tace''we Are okay,'' Ra'esah ta ƙara da faɗin '' it was fun'' ta ƙarashe maganar tana licking ɗin lower lip ɗin ta kamar wadda taci wani abin zaƙi
Dariya samha tayi tace '' wato kuma kun zama kamar Ni Ko?"
Fateemah tace '' Zama da maɗaukin kanwa...''
''shike kawo farin Kai ...'' Ra'esah da Samha suka ƙarasa mata suna dariya,jin dariyar su yasa mr kanya juyowa ya basu wani hard look,tsit suka yi Katherine tace '' waɗan can shegun yaran suma sai mun koya musu hankali ''
Amarachi tace '' ai dole amma yanzu ba wannan ba,naga da mutumin nan yana ɗaukar direction ɗin kitchen.... yane?"
Saida Kathy tayi maganar before the others notice suka fara ƙunƙuni suna zaro idoMr kanya baima San suna yi ba. Bayan tafiya mai nisa suka kawo kitchen ɗin Mr kanya yayi musu alamar su jira shi sannan ya shiga kitchen ɗin su Zeenah su kam sun rantse baza suyi aiki a kitchen ba,dama punishment ɗin su na 2wks is still pending
Ra'esah tayi ƙasa da murya tace '' daga gani mutumin nan kitchen zai kaimu'' Samha tace '' toh meye matsalar?"
Fateemah tace '' hmm! Baki san in an Kai mutum kitchen,sai ya ƙwammaci....'' maganar ta ta yanke lokacin da Mr kanya ya fito yace su Ra'esah su shiga daga ciki,
Sannan yayi masu Zeenah alamar su bishi, dariyar mugun ta su Zeenah suke suna ma su Samha gwalo
Ƙarasawa ciki su Samha sukayi,wasu chef ne kusan su biyar ga baki ɗaya fuskokinsu ba alamar rahama dukan su tiƙa tiƙa da ƙaton ciki,ƙowa cikin su sanye Da Kayan girki
Su Fateemah sai zaro ido suke.
Without talking ɗaya daga cikin chef ɗin yanuna ma su wani zinc cike da tulin wanke wanke,wasu a ƙasa wasu a sama wasu a cikin wurin,duk da su uku ne it will take time kafin su gama aside from that ko sun gama they will need paracetamol
Cikin sanyi jiki suka isa wurin,sai da suka fara ɗibar ruwan da suke buƙata dan wanke wanken sannan Samha tazo ta tsaya,she was to wash the plates, Ra'esah ta ɗauraye Fateemah ta kife, tun da chefs ɗin suka nuna masu aikin su sannan suka ci-gaba da girke girken su....
Samha ta tsira ma kwano nin ido for a while 'baza mu wanke waɗannan kwanon ba' ta ayyana
Ra'esah ta taɓa Samha urging her to start washing the dishes, ganin taƙi yasa Fateemah matsar da ita ta fara wanke wa, Ra'esah na ɗauraya samha ko taƙi yin komai they didn't bother suka ci-gaba da wanke wa, Samha ta saci kallon chefs ɗin sannan ta kalli su Fateemah kafin ta maida kanta zuwa ga kwano nin, an evil smirk crept on her face
Ganin tasa hannu yasa Ra'esah faɗin '' kin ma kanki da baki....'' her words were cut short lokacin da Samha ta saki plate ɗin ya faɗi ƙasa ya tarwatse
Sakin baki fatee da Eysah suka yi suna kallon Samha at the same time duka chef ɗin suka juyo suna kallon su disapprovingly
Samha tayi murmushin rashin gaskiya tace '' sorry hannu na ne ya goce '' chefs ɗin basu ce komai ba suka ci gaba da aikin su.
Ƙara ɗaukar wani plate ɗin Samha tayi Fateemah tace '' dan rabbi ki bi ahan...'' ƙara sakin plate ɗin Samha tayi Ra'esah tace '' mun shiga uku Samha '' chefs ɗin suka ƙara juyowa giving them a hard look Samha tace '' the looks u gave me scared me'' ta faɗa with a nervous smile
The chefs gritted their teeths and continued their works, the girls are a nuisance,haushi suke ji sosai
Sun saba aikin su cikin kwanciyar hankali amma yau gashi... Their thoughts were cut short lokacin da Samha ta sake sakin wani plate ɗin Ra'esah ko tace bazata sake bata wani ba dan haka ta ɗauraye da kanta ta kife,ashe plate Bai zauna ba plate ya faɗo tsuke fuskokinsu chefs ɗin sukayi Fateemah ta ɗau wani plate zata wanke her hand was slippery hakan yasa plate ɗin ya sulɓuce ya faɗi ji kake' taras taras
Chefs ɗin sun gama ƙuluwa,mu ciya suka ɗauka, Fateemah tace '' oh oh looks like trouble,''
Ra'esah tace '' RUN!!!" Dukan su suka ari na kare with the five chefs behind them.
Gudu suke suna dariya, babban chef ɗin yace '' idan na sake ganin mai kama da yarinya sai na ɓaɓɓalla ta." Ya ƙarashe maganar yana huci sauran chefs ɗin ma na taya shi
Bayan sun dawo cikin kitchen ɗin,biyu daga cikin chefs ɗin took over daga inda su Samha suka tsaya bada daɗe wa ba sai ga babban chef ya tura su waje ya rufe ƙofar kitchen ɗin why? they were also breaking plate kamar su Samha
Wurin Cherry blossom su Samha suka zauna suna faman dariya Fateemah tace '' You should have seen the face of that fat man,kamar zai yi kuka''
Dariya suka kwashe dashi Samha tace '' yanzu ba gashi mun tsira ba? Da yanzu muna kitchen Muna kwasar wanke wanke!" Dariya suka yi sosai kafin su ɓuge da wasa, sai yamma liƙis suka bar wurin on their way to the hostel suka haɗu da su zee, kamar wa'yanda aka ba kashi,
Ashe wani ɗaki mai mugun datti Mr kanya ya kaisu sun Sha aiki and they regretted not staying in the kitchen,turus sukayi ganin su Samha kamar ba abinda ya same su, with an evil smile Samha tace '' Kai! Sannun ku fa, da kun tsaya kitchen kamar mu da babu wani aiki da za kuyi amma....'' she let her words linger,su Ra'esah suka kwashe da dariya,the looks on their faces were priceless
Juyawa sukayi suka tafiyar su happily suka bar su zee baki sake
''shegun yara daga gani ba aikin da suka yi''
Zee taja tsuki ta ci-gaba da tafiya cike da jin haushi.
Hostel suka koma by then it was 7, wanka sukayi, sukayi Sallah suka jira har isha'i sannan suka tafi cafeteria,bayan sun dawo wayar Samha tayi ringing without looking at the caller ID ta ɗauka tana dariya kan wani abu da fateemah ta faɗa, Sannan tace '' ke ko?" Tayi maganar tana kara wayar a kunne, Ra'esah ta ƙara da faɗin ''ba wani itako!,kowa yasan Adrian son ki yake,ke ma kuma kina son shi ehe ''
Samha cikin wasa tace '' eh son shi nake and I can't live without him and I ...'' maganar ta yanke lokacin da taji ance ''My lady '' wani irin daskarewa Samha tayi,idanu waje, from the other end Dr Ahmad wani irin ƙunci yake ji a zuciyar sa,shi sai yanzu ma yayi na damar Not finding her a day