Chapter 12 Reading Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel HN Novels

Waye Shi Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 69

33K to 36K   out of 206.1K words

didn't know what to do. Sai kuma ya miƙe ya tafi upstairs, minutes later ya fito hannun sa riƙe da wayar sa da kuma mukullin motar sa.
''Lets go'' ya faɗa yana riƙo hannun ta gently, miƙewa tayi batare da tambaya ba ta bisa, buɗe mata gaban motar yayi tashiga sannan shima ya shiga driver seat yasa seat belt ɗin sa, sannan ya juyo ya kalle ta,she was still crying baice komai ba ya matso kusa da ita har suna jin ƙamshin juna, ƙwalalo ido tayi ta riƙe numfashin ta,tuni hawayen ta sun gudu,sai motsa bakin ta take wanting to say something amma ta kasa, she looked uncomfortable, shi kuma da gangan yayi hakan, tafiyar tsutsa ya fara Mata from her lap towards her waist and upwards yana kallon reaction ɗinta sai wulga ido take here and there ta takure jikin ta wuri guda, ''wh..what Are You doing?" Ta faɗa a tsorace,yanda tawani waro masa idanun ta ba ƙaramin Abu hakan yayi masa ba,matso da fuskar sa yayi gab da tata slightly brushing his lips on hers,wani irin yar taji,matse ƙafafun ta tayi, ta runtse idanun ta da ƙarfi, ganin hakan the corners if his lips twitched ,kara bakin sa yayi saitin kunnen ta yace cikin raɗa'' Your mind is dirty MAHEE,I was only fastening the seat belt '' yana gama faɗar haka ya koma ya zauna, kamar bashi yayi ba, sannan ya tada motar suka ɗau hanya. Buɗe idanun ta tayi amma ta kasa kallon sa,she felt embarrassed Amma ai laifin sa,Who fastens seat belt in such a way? Tsuke fuskar ta tayi, tana turo baki tana ƙunƙuni ƙasa ƙasa, after a while sun kawo buɗe ƙofar yayi ya fito sannan ya buɗe side ɗin da take ,he offered her his hand ƙin karɓa tayi, ba tareda ya jira ta ba ya duƙa ya ɗauke ta chak ya rufe motar ''ni dai ka aje ni'' bai saurare ta ba saida suka iso tsakiyar wurin. Ashe wurin nan ne daya taɓa zama lokacin da ya dawo daga office ɗin Dr Ahmad, sosai wurin yayi mata kyau. '' Masha Allah, i love it'' ta faɗa tana tsalle cike da murna, juyo wa tayi ta ganshi ya samu wuri ya zauna on one of the seats, wurin was looking sophisticated fiye da ranar da yazo, tsalle ta fara tana kamo duk wani ganyen da yayi mata kyau,daga ɗan nesa kaɗan ta hango wani lambu, sakin ganyayyakin da ta tsinka tayi ta ruga da gudu ta shiga lambun wasu furanni masu bala'in kyau, bakin ta yakasa rufuwa, she loved nature

Duk abinda take Amreesh kallon ta yake shima yana jin wani iri a zuciyar sa.he didnt dislike it, and he's not fighting it

Yana cikin wannan tunanin sai gata ta rugo, ɗago idanun sa da suka koma golden yayi ya tsare ta dasu, murmushi take, her dimples visible,

Ɗan ranƙwafowa tayi '' Mr Man kallon fa?" Ta faɗa tana lakace hancinsa,lumshe idanun sa yayi tare da sake buɗe su, ji tayi tsikar jikin ta na tashi, matsa wa tayi ƙoƙarin yi, ƙafarsa ya sa ya taɗo ta,sai gata zaune a cinyarsa, miƙewa zatayi ya riƙe ƙugunta, ɗan zaro ido tayi tace '' yi haƙuri wasa nake''
'' toh ai ni
da gaske nake MAHEE'' ya ƙarashe maganar da wani irin salo, runtse idanun ta tayi tana jin wani irin, riƙe haɓarta yayi tilting his head ya haɗe bakin su. Ƙanƙamesa tayi, she felt so weak, kamar... Jaye bakin sa yayi yana rungomota jikin sa suna faman sauke numfashi tare.

Bayan wasu mintuna ta zauna facing him, tace '' let's make memories '' ta faɗa tana miƙewa tare da riƙe hannunsa ta jawo sa, suka koma cikin lambun, wayar sa ta karɓa ta fara yi musu hotuna, ta tsinko wani red flower ta maƙala masa a gefen kunne tacigaba da yi musu hotunan kala kala,wani su biyu,wani shi kaɗai, fuskar sa aɗan sake in each of the photos. Sun daɗe awurin kafin suka koma cikin motar.
Driving ɗin su yayi zuwa wani haɗaɗɗen Continental restaurant kusa da teku, the view was magnificent ordering ɗin abinci yayi musu suka ci before they go back home.

Sosai Salmah take cikin farin ciki, zatayi masa godiya, he's phone rang excusing ɗin kansa yayi, ita kuma ta haye upstairs ɗakin samha ya shiga tayi wanka ta canja kaya sannan tayi
Sallar maghrib da isha'i.

Tana nan zaune magan ganun Samha na mata yawo ta miƙe zaram ta miƙe ta nufi wardrobe, she does intend to take their relationship to the next level

Wata riga green color daidai cinya tasa sai bum short the same color,taje gashin ta tayi tasa wani daddaɗan hair oil, sannan ta fesa wasu turaruka masu shegen daɗi ta shafa lip gloss

'' so tempting '' ta faɗa tana ƙyalƙyalar dariya.

Fita tayi daga ɗakin zuwa ɗakin Amreesh,tura ƙofar tayi ta shiga, ɗakin was dimly lit,ga sanyin AC dake tashi da ƙamshin turaren sa,haɗa ido sukayi ta mirror,he was wearing just towel.ƙasa tayi da idon ta

For a second her courage wavered har zata koma sai kuma ta rufe kofar ta ƙarasa ciki hugging ɗinsa from behind. Ajiye kwalbar turaren dake hannun sa yayi ya zagayo da ita gabansa. Wrapping ɗin hannunta tayi around his neck, shim kallon ta yake hannunsa a ƙugunta pulling her close murmushi tayi Sannan tayi ƙasa da idanun ta tace '' Thank you so much REESH, I had so much fun today ''

Ɗaukar ta yayi ya nufi gadon da ita, zuciyar ta sai bugu take kamar zata fito daga ƙirjinta ajiye ta yayi sannan ya yo kanta, he was romancing her passionately ita ma tana biye masa.

They were on cloud nine they wanted each other,sunyi nisa sosai yaji kansa na wani irin Sara masa, dakatawa yayi ya dafe kansa ya faɗa gefen ta, rikicewa tayi tana tambayar sa meya faru

He couldn't even talk sai kansa da yake nuna mata, rungume kansa tayi tana kuka sai kuma ta fara yi masa addu'a kafin kan ya lafa masa
Sheshsheƙar kuka take sosai tana rungume da kansa
Buɗe idanun sa yayi his eyes fell on her
'' Mahee'' ya faɗa da Muryar sa that felt weak ɗagowa tayi suka haɗa ido, da sauri ta yi cupping ɗin fuskar sa tana tambaya idan lafiyar da lau
jinjina kansa yayi '' ki dena kuka kinji?'' ya faɗa yana share mata hawaye jinjina kanta tayi Sannan ta miƙe ta nufi closet ɗin sa ta ɗauko masa blue colored pajamas ta tayasa sawa, ta maida towel ɗin toilet sannan ta zo ta kwanta. Kusa dashi,jawo ta yayi ya rungume ta and slept like that....

**********************

Lokacin da Samha da Ahmad suka ɗau hanya, the ride was silent at first, from time to time Ahmad yake kallon ta ta madubi,and sai dai yaga itama shi take kallo.
After a while Dr Ahmad ya ce '' duk kewa tace haka my lady?" Ya faɗa yana kallon titi,ɗan langaɓar da kanta samha tayi kamar mai tunani sai can tace '' gaskiya na duba cikin list ɗin waɗan da zanyi kewa, unfortunately ur name didn't...." Shiru tayi tana murmushin gefen baki ganin yanda Dr Ahmad ya wani ɓata fuska. Shiru sukai babu wanda ya sake cewa komai har suka ƙaraso, Samha tayi mamakin ganin girma da tsaruwar makarantar kaman a Turai, the school was so huge. Fitowa Dr Ahmad yayi ya buɗe mata ƙofar ta fito sannan ta jira ya shiga gaba ta bisa baya, amma tsayawa kawai yayi yana kallon ta turo baki tayi hakan yasa ya ɗan sosa ƙeyar sa Sannan yayi pointing hanya yana faɗin ''after You my lady '' sosai take jin daɗin 'my lady' ɗin da yake kiranta dashi.
Tafiya ta fara yana biye da ita. Kafin kuma su jera suna tafiya cikin shiru, a comfortable silence. '' kinsan yanda nake ji acikin zuciya ta my lady?" Dr Ahmad ya faɗa don a ɗan kwai nisa kafin su isa. Satar kallon sa Samha tayi suka haɗa ido da sauri ta ɗauke nata looking ahead, ya cigaba da faɗin'' jina ke kamar inyi kula'' Samha bata San sanda ta tuntsire da dariya ba. Tace '' ƙato da kai zakayi kuka?" Yace '' to Ni ba mutum bane? You understand the pain of being away from your loved ones don't you?" Shiru samha tayi bata ce komai ba '' I'm already missing you Samha, Dan Allah kada ki bari wani ya ƙwace mun wuri a zuciyar ki. Ni kuma zan ta jiran ki har sai kin dawo na aure ki!" Sanya shiru tayi tun lokacin da ya fara magana tana jin zuciyar ta na motsi, abinda take suppressing na ƙoƙarin resurfacing. Zatayi magana taga har sun kawo hakan yasa tayi shiru directly office ɗin principal suka nufa, principal ɗin middle aged man ne, gaisawa sukayi da Dr Ahmad Samha ta gaida shi sannan ya nuna musu wuri su zauna. Bayan sun zauna ne Dr Ahmad ya ce '' gata na kawo ta, she's my wife to be'' Dr Ahmad ya faɗa yana kallon Samha data waro ido jin abinda ya faɗa, ta ƙasan table ta taka ƙafarsa " ouch'' hararar sa tayi. ba da dadewa wa ba aka gama komai yayi directing ɗin su zuwa wani office inda za'a ba Samha everything she needed. Tafiya sukayi office ɗin aka ba Samha class SS 2A da kuma key ɗin hostel ɗin ta da school uniform books and bags and locker keys. Jikin Samha yayi sanyi,yanzu shikenan? She's gone? Saidai lokaci zuwa lokaci zata dinga zuwa gida? Ajiyar zuciya ta sauke. Fita sukayi daga wannan office ɗin,Dr Ahmad ya nufi mota ya ciro akwatin ta kafin su tafi hostel ɗin tare. Samha ta shiga damuwa hakan yasa bata iya ƙarema hostel ɗin kallo ba. Suna kawowa dai dai ƙofar wurin wata mata ta taso ta tarbe su,it was the matron, ba abari baƙi su shiga hakan yasa ta zo ta karɓi akwatin daga hannun Dr Ahmad. Tsaye tayi taƙi Binta sai da Dr Ahmad yayi mata alama da ta bita sannan tace '' toh zaka jira izni?" Jinjina kansa yayi,sai sannan ta bi bayan matron ɗin. Room no 024 shine ɗakin samha, suna kawowa ƙofar daidai an buɗe, wata doguwar yarinya ce baƙa ta buɗe ƙofar saye take da wata half cut da wando crazy. Wani kallo tayi wa Samha ta watsar, Samha was too busy to care, zasu shiga yarinyar tace ''wait WHO are you?" Matron Ce tayima yarinyar bayani don tuni Samha ta shige, wani gado ta gani by the window with a blue bedsheet,da kuma cupboard maƙale da gadon ita ma blue,sai study table the same color can ajiye abubuwan ta, ta karɓi akwatin daga hannun matron tanay mata Godiya kafin ta juya ta fice.

Komawa tayi wurin Dr Ahmad tasa mesa jingine da wani oak tree yana ganin ta ya miƙe yana murmushi tace '' ai na ɗauka baxaki dawo ba'' turo baki tayi suka fara tafiya, yanzu ma cikin shiru, the sun was about to set,ga iska maidaɗi ne dauke da sanyi da yake kaɗawa, the trees were swaying Samha felt lonely she wanted to cry. Dr Ahmad shima gabaki ɗaya zuciyar sa ba daɗi ji yake kamar ya ɗauke ta su tafi tare

Tsaya wa yayi yana facing ɗin Samha da taƙi yarda su haɗa ido bayan sun kawo dai dai motar sa. '' ayi karatu kin ƙi? Banda jan magana and most importantly, don't forget me Sam"! Dr Ahmad yayi maganar yana murmushin ƙarfin hali
Hawaye Samha ta fara,cije leɓensa na ƙasa dr Ahmad yay,he didn't like it,matso wa yayi yana goge mata hawayen yana mata alamar ta dena kuka amma...how could she? Tayi kewar kowa amma tafi kewar sa fiye da kowa! Jitayi yayi wrapping ɗin arms ɗin Sa around her in a hug, itama for the first time she hugged him back tana sheshsheƙar kuka... bayan wasu mintuna ya kai bakin sa saitin kunnen ta cikin raɗa yace ''sai wata rana my lady'' daga haka ya juya ya shiga motar yayi reverse ya tafi without looking back he didn't want to see her tears....










WAYE SHI?(Behind the mask) By autumn 17

Chapter fifteen: First day at school
𝑊𝐴𝑌𝐸 𝑆𝐻𝐼?
(𝐵𝑒ℎ𝑖𝑛𝑑 𝑡ℎ𝑒 𝑚𝑎𝑠𝑘) 𝐵𝑦 𝐴𝑢𝑡𝑢𝑚𝑛 17

𝐶ℎ𝑎𝑝𝑡𝑒𝑟 𝐹𝑖𝑓𝑡𝑒𝑒𝑛: 𝐹𝑖𝑟𝑠𝑡 𝑑𝑎𝑦 𝑎𝑡 𝑠𝑐ℎ𝑜𝑜𝑙


Ta daɗe tsaye a wurin har Saida taga rana ta faɗi sanyi ya fara sauko wa kafin ta goge hawayen ta, ta juya walking slowly ta fara tafiya wani irin kaɗaici na fisgar zuciyar ta, har tayi rabi ta kusa kai hostel taji ance '' hey '' kamar bazata juya ba sai kuma ta juyo a wani irin slow motion she instantly recognized the girl, it was Zeenah yarinyar da suka haɗu a restaurant har ta zauna akan cinyar Ahmad. Maida kallon ta Samha tayi zuwa ga abokan ta dake biye da ita they were all together that day, yanzu ma sai wani cika suke suna batsewa.

Itako Zee kallon Samha take, yarinyar kyakkyawa ba makusa wani irin tsanar Samha ya shiga ranta.
Ganin suna ɓata mata lokaci yasa Samha yin gaba ta fara tafiya,da sauri Zee ta wani finciko ta '' ke wace ce banga ma magana ba zaki tafi?" Kallon ta Samha take, she was dumbfounded yanzu ita meye haɗin ta dasu, sauran ƙawayen Zee ko sai zuga ta suke hakan yasa ta tsaya ɗan da Samha sannan cike da gargaɗi tace '' stay away from him'' tana gama faɗar haka ta tura ta sannan ita da tawagar ta sukayi gaba. Bahaka suka so ba, sun so Zee tayi ma Samha duka ko su duka su taru su bata kashi....Zee tafiya take tana ƙara ji aranta dole tayi maganin Samha, tun lokacin da suka sauko daga mota Zee ta gansu suna tafiya tare,da farko ta ɗauka yan uwa ne hakan yasa take binsu abaya ba tare da sun sani ba,anata tunanin idan an gama ma Samha komai they will become friends and with their relationship,tafi samun dama da Ahmad, sai da aka tafi office ɗin principal take jin labari daban
Take zuciyar ta tafara tafasa dan ita da gaske son Ahmad take.
Haka ta cigaba da binsu bayan sun fito daga office ɗin to be sure and she saw them both hugging ji tayi kamar taje ta wawwanka ma Samha mari even right now she wished she could damage her beautiful face!! Fuskar Zee tayi ja saboda fushi, ƙawayen ta na biye da ita suna gaya mata ways to make samha's life miserable

Samha ta ɗau mintuna tsaye wurin still trying to process what just happened,sai kuma tayi wani murmushin mugun ta tace a fili '' yara kun taro match, i love this '' ta ƙarashe maganar licking her lower lip.
Barin wurin tayi zuwa hostel ɗin su, koda tashiga room mates ɗin ta duk sun dawo unlike ɗazu da basu nan. Binta suka yi da idanu ita ko directly wurin kayan ta, ta tafi ta cire veil ɗin da tanaɗa tare da ribbon ɗin da tana ɗe gashin ta, sannan ta sa hannu ta warware gashin allowing air to enter. Waro idanun su room mates ɗin ta sukayi ganin yawan gashin ta, magana suke ƙusƙus wata yar siririya cikin su ce ta fara tashi ta tafi wurin samha that was arranging her clothes in the cupboard,ji kawai tayi ana taɓa mata gashi, swiftly ta juyo, fuska ɗaure take kallon yarin yar, murmushin tsoro yarin yar tayi sannan ta miƙo hannunta '' Hi I'm fateemah'' kallon hannun yarinyar samha tayi sannan tace'' dan sunan ki Fateemah sai aka ce ki taɓani?" The other two girls exchanged glances kafin yarinyar nan data buɗe ƙofa ɗazu ta ja tsuki tace '' mutum kamar biri amma sai jan ajin tsiya, damar abun ma mun san gashin kanti ne'' ɗaya yarin yar dake zaune kusa da wadda tayi maganar tace ''haba Na'ema ai ke daga ganin wannan gashin kinsan bana kanti bane'' har zuƙowa Na'ema tayi tace '' ke Ra'esah ki shiga taitayin ki, badai dake nake ba ko to wallahi ki fita daga idanuna in rufe toh'' a tsorace Ra'esah tace ''Allah ya baki haƙuri'' Daga nan taja tayi shiru ita dai Samha sauraren su take but she didn't say anything,ita ko Fateemah taƙi tafiya tayi tsaye tana cigaba da yaba gashin Samha ,jin har yanzu yarinyar na tsaye bayan ta yasa ta sake juyowa da sauri Fateemah tace '' can we be friends '' ''A'a'' samha ta faɗa tana ɗaukar wata doguwar riga loose fitted tashiga toilet ɗin dake ɗakin, ɗan turo baki Fateemah tayi determining Bazaa ta haƙuri ba till they become friends with Samha. Komawa tayi saman gadon ta da yake kusa da ɗayar windown ta zauna, kowa nada gadon sa in a corner, sai rug shimfiɗe a tsakiyar ɗakin, samha ta ɗauki blue, Fateemah nada pink, Ra'esah green sai Na'ema purple. Truly ɗakin ya haɗu. Bayan Samha ta shiga,sake fitowa tayi ta kwashi toiletries ɗin ta,ta jera su a bayen kafin ta shiga wanka. Koda Samha ta fito yanda ta barsu haka ta same su, Ra'esah reading her text book, Fateemah tana nan tana jira ta fito ita kuma Na'ema tana danna wayar ta. Gaban madubin dake manne da wardrobe ɗin ta ta tsaya,ita sai yanzu ma tayi noticing. Kwaso su turarunkan ta da originally ta shirya su a wardrobe tayi ta mai da su saman dressing table ɗin sannan ta zauna ta shafa mai ta fesa turare, zata fara gyara gashin ta sai ga Fateemah tazo da murmushi '' can i help you?" Kafin samha ta amsa har ta ɗau mashaci ta fara shace mata gashin ta gently, Samha ta ji daɗin yanda Fateemah tayi mata hakan yasa ta lumshe idanun ta sai kuma ta tuntsire da dariya cikin ranta tana faɗin da gida ne saidai ita tayi ma salmah haka ganin tana dariya Fateemah tace '' now can we pls be friends? Dan Allah'' the girl was so persistent and she looked cute not bad jinjina kanta Samha tayi sannan tace '' amma idan kika yi offending ɗina, that's it'' da sauri Fateemah ta jin jina kanta cike da farin ciki tayi ma Samha alƙawarin bazata bata haushi ko wani abu ba... Komawa saman gadon ta samha tayi Fateemah ta biyo ta tana bata labarin makarantar

12 / 69