Author : Billyn Abdul Category : Adventure Stories
tako Ina take idanuwanta suka ringa ganar Mata duhu suna neman rufewa.
Innalillahi wainnan ilaihrrjiun,
Ke Inayah,
Inayah?
Innalillahi..
Kanta sukayi suna tarota ganin numfashinta na Neman daukewa.
Hankali tashe suka ringa kiran sunanta a rikice suna rasa abinyi Dan kowa bayason Kiran Dr farhat Musamman yanzu da Inayah din tasan abinda ke Shirin faruwa.
Waya umma yaganah ta dauka Kai tsaye takira Dr Abdul tareda sanar dashi suna zuwa asibiti yanzu da Inayah.
Cikin tashin hankalin abinda sukace yace su Kira gashinan zuwa gidan ya dubata.
Lokacinda sukai wayar Yana gida tareda mahaifiyarsa dataqi komawa tayi zamanta a Lagos dama tuntuni MJ Muhammed yafison zamanta a Lagos itace taqi Amma yanzu tunda 'yarta na garin ta zabi Zama anan su Inna kawai ya rage ataho Mata dasu idan Abdul yaje.
Tareda umma Hadizan suka iso gidan saidai Kuma bayan sun iso suka rasa yanda zasu bawa Abdul Daman shiga har dakin umma duba Inayah gashi abbin yau ya Dan samu sauki ya fita sbd tafiya yakeson Yi ma kwanakin.
Haka dai sukai shahada tunda muharraminta ne suka basa Daman shigowa yaje ya duba Inayah din wadda sosai take neman shidewa da attack din data samu.
Dan taimakon dazai Bata yayi tafara Dan dawowa daidai saidai sbd tashin hankalin data sakawa kanta numfashinta yaqi dawowa daidai haka ya fito ya wuce sbd bazai iya ganinta a wannan hakinba Kuma yasan Inayah Bata samun attack saita Shiga wani mummunan shock na tashin hankali
Koma me akai Mata ya tabbata ya danganci Abbi sbd abinda ya shafesa ne kawai yake saka Inayah cikin tashin hankali Amma Babu abinda yake damunta harta saka arai sbd koyaushe shine kadai Mai mahimmanci agunta.
Yana tafiya Dole Dr farhat suka Kira bayan hankalinsu yakuma tashi da hawayen datake Babu kakkautawa cikin yanayi na daukewan numfashin.
Dama yanzu a gidan Kira kawai Dr farhat ke jira Dan haka ana kiranta jiki na rawa ta taho tana nuna damuwa a fili sosai akan meya samu Inayah din Amma Babu wanda ya fada Mata.
Zuwa Dr farhat yasa Inayah Jin wani sabon ciwo a zuciyarta tafara bori batason a dubata abarta ta mutu
Ita mutuwarma takeso ta huta...
Da mamaki suke kokarin tausarta Amma ta tibure ta dinga zuba kuka tana qin Bari ko tabata Dr farhat tayi.
Basu umma yaganah ba ita kanta Dr farhat hankalinta tashi yayi sosai tafara tunanin ko kwakwalwar Inayah tasamu matsalane?
Haj umma da batasan meyake faruwa ihu da tashin hankalin faman da akeyi da Inayah yasata fitowa bedroom dinta cikin fargaba ta iso dakin umma yaganah da aketa zuba tashin hankalin tana cewa"
Innalillahi,
Lafiya?
Meyake faruwa da ita?
Iska ne akanta?
Dama tanada iska ne kome?
Kasa magana anty Hafsat tayi sai umma yaganah ce tace"
Batada iskan komai
Kawai ciwo take takuma qi Bari a dubata sai rigima takeyi....
Mamaki sabone ya Kama Haj umma
Yanzu akan ciwo da batason a dubata take zuba wannan tashin hankalin?
Dr farhat da abin yafara Bata tsoro ganin sosai Inayah ke kuka tana daga musu hankali tace"
Kodai zaa Kira AA ne sai awuce da ita asibiti can zaa iya fin karfinta a dubata sbd tana kokawa da numfashinta dakeson daukewa Amma taqi barin na taimaka Mata.
Hankali tashe umma yaganah ta dauko wayarta ta saka Kiran MAJEED sbd ganin numfashinta yafara sama sama.
A natse ya dauki wayar tareda sallama a hankali.
Cikin kokarin daidaita muryarta ta Dan boye tashin hankalin ta sanar dashi Inayar batada lafiya sosai Kuma takasa Bari Dr farhat ta dubata numfashinta na......
Bata qarasaba taji dib alamar ya kashe ne kokuma network ne batasaniba.
Kokarin sake saka kiransa tayi taji Amma Sam Bai dagaba cikin sabon tashin hankali tace"
Inaga network nada matsalar muje da ita asibitin kawai.
Ko asibitin ma win yarda tayi atafi sbd ganin Dr farhat kawai tsananta toshe numfashinta yakeyi
Gashi zuwa lokacin ta matuqar galabaita Dan haka cikin fada sosai umma yaganah take tirsasata tashi.
Koda umman ke fada batama San me take cewaba sbd idanuwanta dake kokarin rufewa...saiga Abbin ya shigo Kai tsaye zuwa dakin umma yaganah din.
Da sauri duka suka juya suna kallonsa baka gane komai a fuskarsa Amma dukkaninsu suna iya hasaso tsananin damuwar dake ransa na ganinta hakan.
Yana shigowa Kai tsaye gurin ya nufa anty Hafsat na Kira sunanta kada ta rufe idonta.
Tana ganinsa ta maida idanuwanta akansa tana Jan numfashi cikin zafi..
Hannuwansa biyu yasa ya tallafota Kai tsaye daga kan kujera zuwa jikinsa Yana Kiran sunanta cikin yanayi na kulawa sosai da damuwar meya sameta.
Daqyar taja numfashi tana tsiyayar hawaye ta bude Baki ahankali tace"
Abbi aure zakayi????
Bata fuska yayi cikeda mamakin yanda taji zancen take ransa yayi mummunan baci Amma dayake bakowa ke gane yanayinsa ba duk Basu ganeba.
Ruwan da umma yaganah ke miqowa ya karba ya Kai Mata abaki cikin sanyi yace"
Relax and breath,
Just breath,
Yawwa deep breath,
Sake Jan numfashin...
Yanda yace tayi takeyi ahankali numfashin nata na daidaituwa ahankali ahankali.
Sam taqi dagowa ta kalli kowa dakin sbd haushi da zafin kowa takeji hardasu umma yagananta.
Ganin tadan dawo hayyacinta yasashi juyowa ya kalli Dr farhat dake kallon ikon Allah Dan tasan Inayah itace mafi so da kauna a rayuwar Abbinta Kuma tasan sangarta da shagwaban Inayahn Amma Batasan yaushe tafara boriba haka kokuwa Dan Bata taba rigima bane gabanta?
Qatuwar budurwa na irin wannan tashin hankalin Amma mahaifinta ko damuwa yayi Mata ko 'yar tsawa baiyiba saima kokarin dawo da ita daidai yakeyi cikin sanyi da nutsuwa tareda boye tashin hankalinsa na ganinta hakan.
Haj umma dake tsaye sake da Baki cikin mamakin dayafi na kullum ya Dan kalla Yana danne yanayinsa kafin ya kuma maida kallonsa kan Dr farhat Kai tsaye yace"
Dr zaki iya tafiya I can handle this,
Thank you.
Juyawa tayi ta kalli Inayah cikin kulawa ta nufeta zatai Mata magana
Inayah tayi saurin fara kokarin miqewa tana kokarin janyewa anty Hafsat ta dafeta tana kokarin tausarta kafin takuma borewa.
Ganin hakan yasa Dr farhat dakatawa tana kallon MAJEED Daya dauke Kai ba annuri ko daya a fuskarsa da duka abinda kowa yayi agidan.
Murmushin yaqe tasaki tareda yimusu sallama ta yiwa Inayah fatan samun sauki ta wuce.
Shiru ya danyi tareda sake hadiye 'dacin ransa ya juyo ya kalli Inayah dake hawaye sosai har lokacin ta dago ta kallesa take taji wani sabon 'daci da qunci na cika ranta matuqar Abbinta zai auri wata mace....
Tasowa tana sakin sabon kuka Zata bar dakin umma yaganah ta riqeta tana cewa"
Zan mareki idan bazaki nutsuba
Ba'ason hauka kinji ko??
Sabon kuka Mai qarfi ta saki tana cewa"
Umma yaganah bazan iya nutsuwaba Ni kubarni natafi banason ganin kowa....
Aurenma banayi na fasa bazan zauna da kowaba da Abbina.....
Sai alokacin Haj umma ta fahimci duk wannan tashin hankalin akan meye,
Takaici ne da mamaki suka tarar Mata wato duk wanna daga hankalin jama'ar gida da borin kaman me tashin iska da asthma duk akan ance MAJEED zaiyi aure ne?
Wannan halin na Inayah na shashanci Yana Bata takaici da damuwa Dan haka cikin siqewa tace"
Yanzu dama duk wannan ihun da tashin hankali dakikeyi kika daga hankalin kowa duk akan majeed zaiyi aure ne?
To so kike gabaki daya ya qare rayuwarsa gurin tattali da renonki shi Kuma bazai Gina tasa rayuwarba?
Da Ina tareda shi tunima dayayi auren Dan bazai zauna saidai yaga 'yaya wasu na tarawaba shine zakizo kina shirmen ihun kuka da......
Cikin kuka Inayah tace"
Ni nace bazan Tara Masa 'yayan bane?
Ai Nima Zan Haifa Masa idan kika barmu...
Fiddo idanuwa Haj umma tayi cikeda mamaki,
Su umma yaganah da Anty Hafsat ma tsit sukai yau ciwon bakin Inayah yayi musu Dadi duk da duk kunya ta kamasu da sauri umma yaganah ta buge Mata bakin sbd karta qarasa.
Shi kansa abbin kasa magana yayi sbd mamakin bakin Inayah Daya Gama wuce tunaninsa hakama da bacin ran zancen dasuka sanar Mata da wani abin yasameta ayau acikinsu babu Mai abin fada masa sun kashe Masa 'ya ko me??
Numfashi ya sauke a boye Yana sake kawar da bacin ransa ya kalli Haj umma dake kallonsa jiran abinda zai fada sbd duk suna iya hango zallar bacin ransa duk da boyewar dayake kuwa.
Daidaita kalamansa yayi cikin nutsuwa yace"
Umma Ina dauka maganar auren Dr farhat bamu gama meyasa zaku dagawa Inayah hankali da zancen bayan bawai Kai karshen maganar akayiba.
Umma yaganah da Anty Hafsat ya kalla suma yace"
Meyasa zaku sanar da ita umma tunda kinsan halinta
Yanzu gashi tana neman illata kanta akan hakan,
Maganar aurena da Dr farhat Kar akuma tadasa a gabanta sbd ba........
Maganarsa tasa Inayah fashewa da sabon kuka tareda juyawa da gudu tabar wajen tana cewa"
Kenan yin auren zaiyi da Dr farhat.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107
[11/9, 11:49 AM] +234 816 828 4180: *_53_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Rintse idanuwansa dasuka Dan sauya yayi tareda juyawa yabar gurin shima Yana kansa na Kuma sarawa dama gashi kwana biyun Yana fama da ciwon kan.
Yana barin gurin umma yaganah Haj umma suka kalla itada anty Hafsat sukaga yanda tayi zuru da mamaki dashiga tunanin agaban kowa MAJEED zaiyi mata magana Mai Kama da fada kaman shine uban nata.
Juyawa tayi jiki a sanyaye ta koma bedroom dinta tanaji wayarta na ringing juwairiyyah na Kira takasa dauka sbd ranta ba Dadi ko kadan bazata iya wani bacin ranba sbd yanzu juwairiyyah Zata sake dorata akan abinda zai quntata ranta.
Anty Hafsat Kuma bayan Inayah tabi zuwa dakinta Dan tausarta Amma rarrashinta duniya tayi Inayah din Taki Dena kuka.
Har bayan magriba suna fama da Inayah din Haj umma dake dakinta tana Dan jiyo yawon umma yaganah da Anty Hafsat gurin rarrashin Inayah din sama sama
tayi banza dasu sbd gabaki daya ganin takeyi su suka Gama lalata Inayah din da bakinta baya tauna magana sam Sam.
Ana gap da ishai haka anty Hafsat ta hakura ta tafi gida tabar umma itama tayi nata rarrashin ta hakura ta zubawa sarautar Allah Ido.
Abincin dare ma kusan daga ita sai Haj umma ne sukaci Inayah taqi fitowa shima MAJEED din baizoba Koda Haj umma takirasa shayi kawai yace akai Masa.
Zubbi ce takai ta ajiye Masa a palonsa ta fito ta dauki da Inayah ma da umma tace ahada Mata takai mata Amma ko motsawa Inayah batayiba tana kwance.
Duk dubara da rarrashin umma yaganah Inayah kin Shan ko tea tayi Dan haka jiki a mace umman ta barta taje ta kwanta.
Zafi da ciwo zuciyarta ke Mata sosai bayan hawaye Babu abinda takeyi sbd bazata taba iya kwatanta Abbinta da wata macen ba,
Wannan zafin datakeji har abbin ma takejin zafinsa akan lamarin.
Kwana tayi da ciwo a Rai da damuwa me tsanani Dan haka Koda garin ya waye da wani zazzafan zazzabi ta tashi Mai qarfi.
Zubbi da umma yaganah ne akanta hankali tashe umma na rage Mata zafin gashinta da farin qaramin towel
Zubbi kuwa chocolate custard me zafi ta hado Mata da farin soyayyan qwai Mara komai aciki.
Kasa Shan komai tayi Saida umma yaganah ta nuna Mata rauninta na itama Zata iya kuka idan Inayahn bataciba kafin Tasha custard din aikuwa ko Gama Sha bataitaba amai ya taso Mata da sauri zubbi ta kamata takaita toilet ta ringa Aman cikin wahala sbd rashin qarfin jiki.
Bayan tagama ruwan zafi zubbi ta hada Mata tayi wanka ta fito umma ta dauko Mata wata qaramar Riga Mara tsayi Mai taushi ta saka Takoma ta kwanta jikinta na tsananta zafi.
Wanke toilet zubbi tayi ta gyare dakin tsaf ta kashe Mata AC ta kunna humidifier bayan tazuba wasu turaruka cika masu dadi suka fice daga dakin har umma.
Umma na barin dakin tana Isa nata ta dauki wayarta ta saka Kiran MAJEED.
Ta jima tana ringin kafin ya daga murya ahankali yace"
Barka da yau umma.
Barka MAJEED,
Yau baka fitoba Allah yasa lfy dai ko?
A natse Yana danne yanayinsa yace"
Lafiya kalau alhmdllh,
Yaya Inayah?
Tana Nan tana Rigimar ko?
Numfashi ta sauke a sanyaye tace"
Tanata rigima tun jiyan gashi yanzu ciwo yashigo ciki sbd zazzabi Mai qarfi takeyi custard ma datakeso Tasha tayi amansa,
Bansaniba ko Dr farhat din zaa Kira tazo ta dubata Amma Kuma wata sabuwar rigamat zatayi tana ganin Dr farhat din.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda cewa"
Ganinan zuwa zanfara dubata kafin Akira likitan.
Kashe wayar umma tayi tareda ajiyewa gefe tana Zama kan kujera tana cewa"
Allah yasa ta tsaya taji maganarka.
Kwance take tanajin zazzabin sosai bacci na Dan daukanta Yana sakinta duk da hakan tunanin Abbinta da aurensa na maqale cikin ranta.
Turo kofar dakin yayi Kai tsaye tareda shigowa a natse sbd shima ciwon Kaine atare dashi.
Fararen Fendi wears ne ajikinsa
yau Qamshin nasa ma ahankali yake tashi daga jikinsa sbd Bai wani saka turareba Qamshin na jikinsane daya dade da Kama Turaren Mai sunyin Dadi.
Cikin nutsuwa ya tako har bakin gadon ya tsaya Yana kallonta ahankali cikin nutsuwa ya lumshe fararen idanuwansa Yana budesu akanta cikeda kaunarta Mara sirki da qarfi wadda take gine cikin ransa shiyasa Sam Baya son bacin ranta ko damuwarta Amma tacika rigima yanzu duk akan aurensa dake kanta data dauka ta saka arai.
Bude idanuwanta dasukai nauyi da sauyawa sbd zafin zazzabi Jin mutum akanta tasan Abbin ne sbd qamshinsa daya shiga hancinta.
Maida idanuwanta tayi ta rufe tanajin nauyin kirjinta na qaruwa sai kawai hawaye suka fara gangaro Mata.
Yana ganin hawayen nata yaji jikinsa yaqara sanyi ya zauna ahankali bakin gadon nata tareda Kai hannunsa dakeda sanyin ACn Daya fito ya taba goshin yaji zafinsa sosai
Da kulawa sosai yace"
Da wannan zazzabin naki ajikinki kike sake wani kukan Inayah??
Kinason ciwo ya kwantar dake ne?
Meyasa bazaki Dena kukanba haka?
Juyar da kanta tayi tana sake sakin kuka Mara sauti a wahalce batareda tace Masa komaiba.
Shigowar Haj umma ne tareda Salimat data kawo wasu ruwan da towel Zata rage Mata zafin jikinta da umma yaganah tace zubbi takuma Yi Amma zubin na aikin gyaran Haj umma Dan haka ita takawo.
Haj umma kuwa duba Inayah din tazo yi sbd rashin lafiyarta yasa gidan kaman anyi mutuwa kowa tsit ba walwala tunda princess din gidan ba lafiya.
Salimat na ganin Abbi a dakin ta ajiye ruwan kan bedside drawer ta juya ta fice.
Haj umma ma da 'yar kulawa kadan tace"
Yaya jikin nata?
Allah yabata lafiya
Amma saita sakawa kanta salama
Wannan kukan Babu abinda zai qara Mata sai ciwon.
Amin"MAJEED ya amsa a taqaice Yana sake taba gashin Inayah din daya zafinsa yaji duk ya daga Masa hankali harya Dena Jin nasa ciwon kan.
Cikin kulawa yace"
Ina Ms Salimat take tazo ta rage Mata zafin jikin kafin Dr farhat tazo ta dubata..
Fadan sunan Dr farhat kawai yayi yasata sake tsananta hawayenta saiga umma yaganah ta bude kofa itama ta shigo da tea me zafi a tray tazo ta ajiye.
Umma yaganah ki rage Mata zafin jikin Nan yayi yawa kafin likita tazo ta dubata jikin nata Yana tsananta zafi sosai...
Cikin kuka ta tashi zaune daga kan gadon tana cewa"
Ni banason Dr farhat ta dubani
A Kira Dr Abdul....
Satar kallon Abbi umma yaganah tayi tana matsowa gurin gadon Zata dauki qaramin towel din Fadi tas
Cikin kuka Inayah tasake cewa"
Ni har rage zafin banason tunda ba zafin danakeji a zuciyata zaa rageba,
Wlh abbi idan kayi wani auren zuciyata bugawa zatayi nidai Dan Allah kacewa Haj umma bakason auren Nan bazakayiba
Banason kowa ta Zama matarka saini kadai.....Ni ko rage zafin banason umma tamun Kai zakamun idan bakaiba banason kowa yamun abarni zafin ya kasheni na mutu na huta bazanga ka aura kowaba.....
Wannan karon salati Mai qarfi Haj umma take saki idanuwanta na rarrabuwa tsakanin umma yaganah da MAJEED taga yanayinsu akan wannan tsabaragen rashin kunyar da iskancin na Inayah Amma saitaga kowannensu yayi shiru kusan itama umma yaganah taji kunyar zancen Amma Kuma majeed yafisu shiga mamakin saidai kaman koyaushe baa cika gane reaction dinsa akan Abu.
Matsowa umma tayi tana kokarin Mata fada a fakaice sai kawai abbin ya miqa hannu ya karbi towel din tareda cewa"
Ba damuwa Zan Mata.
Cikin ruwan ya saka towel din ya Ciro ya matse ruwan ya Dora Mata a goshi har lokacin hawaye takeyi.
Ahankali yace"
Hawayen ya Isa haka tunda gashi inayi.
Riqe hannunsa dake goshinta tayi ahankali jikinta na sanyi da zuciyarta sbd bazata iya fushi da Abbinba
A hankali tace"
Abbi kayi hkr ka yafemun bazan sakeba.
Neman sakewa jikinsa keyi yayi qarfin halin riqe yanayinsa tareda sakar Mata murmushi cikin tsananin kulawa yace"
Shikenan Dena hawayen.
Kwantawa tayi jikinsa tareda zura hannayenta ta rungumosa daga zaunen dayake tana cewa"
Abbi shima auren karkayi Dan Allah.
Wani mawuyacin yawu Mai daci ya hadiye ta maqoshinsa Yana sake kokawar dedeta kansa.
Umma yaganah juyawa tayi ta fice salin alin batareda dogon motsiba.
Haj umma ma dai ganin Inayah ba mutuncine da itaba yasata juyawa ta fice tana cewa"
Idan kafito MAJEED Ina nemanka.
Daga shi har Inayah din basuji abinda taceba sbd shi kokarin riqe kansa yakeyi da kyakkyawar rungumar da Inayah tayi Masa tareda kwantar da kanta jikinsa yanajin dumin jikinta na Shiga nasa jikin ahankali.
Ahaka sukai shiru Babu me magana Saida suka jima ahakan kafin ta Dan dago ta kalli fuskarsa da shima ya juyo ya kalleta cikeda shagwaba tace"
Abbi Dan Allah ka fasa auran kowa bama Dr farhat kawaiba.
Muryarsa a shaqe cikin nutsuwa yace"
Meyasa Zaki daga hankalinki akan hakan Inayahhh????
Lumshe fararen idanuwanta tayi ta bude Masa itama a hankali tace"
Zuciyata zafi da ciwon hakan takeyi,
Bazan iya hadaka da kowaba Abbi,
Kai mijinane Ni daya,
Bazan iya gani kaje gurin wataba bayan Ni ko zuwa gurina bakayi haryanzu baka daukeni matarkaba.....
Wasu kakkauran yawun yakuma hadiyewa cikeda mamaki da bugun zuciyarsa dake tsananta yakai hannu ahankali ya cire towel din dake kanta Yana kallon tsakiyar idonta dasuke bayyanarda tsananin soyayyar dake dawainiya da zuciyarta....
Matsota yayi jikinsa ahankali fuskarsu ta matsu data juna
Numfashinta Mai dumi ya ringa sauka kan fuskarsa da shiga hancinsa Yana bude kofifin hakurinsa da jarumtarsa ta danne abun dayake ransa da jikinsa....
Rufe Ido kadan yayi ya budesu akanta itama har lokacin shi take kalla zuciyarta na kasa daukan zafin sonsa aranta dayayi Mata yawan gaske.
Jin jikinsa da zafi yasata Dan zame hannunta Daya ta dauko towel din da sanyin ruwa takai wuyansa ta shafa Masa ahankali tana kallon wasu jijiyoyin wuyan nasa dasuka fara fitowa take.
Sake shigewa jikinsa tayi tana ajiye towel din sbd batada karfin jiki karfin haline kawai na ganin Wanda zuciyarta ke bugawa sosai akansa...
Towel din ya dauka ahankali daga jikinsa batareda ya gara debo Masa wasu ruwanba ya Kai fuskarta yafara gogawa Yana gangarawa zuwa wuyanta ahankali Wanda hakan yasata Jin wata mummunar kasala tana sake lafewa jikinsa.
Yana zuwa wuyanta hannnun rigar jikinta Mai santsi ya zame saman kirjinta ya bayyana take suka saki numfashi lokaci daya Yana goge Mata saman kirjin zafi na keta koina ajikinsa