Author : Billyn Abdul Category : Adventure Stories
daskare tana narkewa da tausayin kanta dana jaririyar Dan haka batada zabi daya wuce ta tunkari gidansu salisu ko ummansa Zata karbesu tunda jikartace su taimaketa ta zauna gurinsu ta Rena Ayshatouh idan ko shekara tayi saita barta takoma gidansu idanma sbd itane su Yaya Umar suka koreta daga gida.
'yar qaramar jakar kayanta ta bude tafara duba kudin datake dasu.,
Dari uku da ashirin tagani take jikinta yakuma mutuwa saidai halinda zuciyarta take ciki Batajin akwai abinda zai fisa daci.,
Miqewa tayi ta qarasa bakin titi Anata kallonta sbd Jin yanda jaririya ke kuka sosai a jikinta Dan haka Bata tsaya juran napep ba ta tsayarda Mai mashin ta hau suka tafi.
Gabanta tsananta faduwa da shiga qunci yakeyi sbd hajiyar salisu ma batasan yaya zata karbesuba...
Mai mashin na ajiyeta kofar gidan ta Ciro dari da hamsin ta miqa Masa ta juya ta shige qaramar kofar gidan tana sake qamqame yarta jikinta.
Tun kafin ta qaraso ciki Yara suka fara Isa gurin hajiyar suka sanar Mata Hadiza tazo.
Dan shiru hajiyar tayi kafin ta kalli yaran ta korasu waje ta dawo da hankalinta kansu balaraba dake gidan ta sallamesu suka wuce inda zasu ta kofar baya batareda sun tsaya Gaisawa da Hadizan ba Dan dama a sama sama suke da ita tun salisu nada Rai bare yanzu da basuda alaqa da ita.
Da wata irin dasasshiyar sallama ta shigo hankali sbd muryarta ko fita batayi.
Da mamaki hajiya ta kalleta idanuwanta na sauka kan jaririyar dake hannun Hadizan.
Idanuwan Hadizan zuwa fuskarta ta kalla dakyau take tagane jegone tareda Hadizan Dan haka ta tattaro hankalinta da mamaki a bayyane kan fuskarta tace"
Hadiza¿
Kece nake gani?
Lafiya da Rana tsaka haka?
Ba zaman karban gaisuwar Aishatu akeba.
Kasa magana Hadiza tayi sbd jirin dake dibanta Dan haka a sukwane ta qaraso ta durqusa gaban hajiyar tareda sunkuyar dakai idanuwanta na sake rinewa.
Sake Shiga firgici hajiya tayi tana qin nuna taga jariri atareda hadizanba tasake cewa"
Hadiza nace lfy kuwa?
Kiyi mgana kikai shiru kina bani tsoro...
Dagowa Hadizan tayi tana kallon hajiyar sbd tasan bazatace bataga abinda ke hannuntaba
Idanma Bata ganiba bazatace batajin kukan da Ayshatouh ke tsalawaba.
Sunkuyar dakai tayi tareda bude jaririyar dakyau agaban hajiyar muryarta na a disashe da tsananin damuwa da qunci Mai daci tace"
Hajiya haihuwa nayi su Yaya Umar sukace nabar gida,
Bansan Inda zaniba sbd ko Abokai banda shine nataho Nan....
Dauke wuta hajiyar tayi daga zaune tana kallon Hadizan Baki sake ko fuskar jaririyar taqi kalla.
Qofa tafara kalla ta leqa tsakar gida taga ba kowa tadawo da sauri ta kalli Hadizan cikin tsananin mamaki, firgici da takaici Kai tsaye tace"
Me Zan Miki anan hadiza?
Haihuwafa kikace kinyi?
Haihuwa ba aure fa?
Wace qaddarace wannan takaiki ga wannan mummunan sakamakon? Shine Kuma Zaki zomun Nan?
Ko kunyar 'danki dake gidan Nan bakijiba kika kwaso jiki da jaririn shege kizomun anan?
To Kinga Hadiza tun kafin Raina ya baci Kuma tum kafin wani yaji tashi ki fice,
Mune mukafi kowa hauka a duniya ne dazamu Baki gurin zaman renon barna......
Rawa hannuwan Hadiza suka fara hankalinta yasake mummunan tashi tana kallon hajiya da idanuwanta jajir tace"
Dan Allah hajiya ki yarda Dani ki fahimceni
Kima kaini a dubani idan ana dubawa wallahi tallahi banyi kowace irin barnaba nasamu cikin Nan,
Wallahi cikin salisu ne......
Wata irin mummunan zabura hajiyar tayi tana kallon Hadiza a gigice sbd mamaki da baqin cikin zancenta Dan ta Gama raina Mata hankali kokuwa dai mahaukaciya ta dauketa?
Amma dai Bari ta tabbatar...kallonta tayi a Rikice tace wane salisun Hadiza?
Muryarta Bata fita sosai sbd shaqewar maqoshi tace"
Salisu baban Abdul....
Kasa magana hajiyar tayi ta rufe idonta daya fara sauyawa sbd tsananin bacin Rai da masifar Rainin da Hadiza tazo dashi Dan haka Bata buqatan ma Jin komai ta nuna Mata hanya tace"
Fice Hadiza kibar gabana Dan Allah.
Dagowa Hadiza tayi ta kalli hajiyar sai alokacin hawaye suka ciko jajayen idanuwanta suka fara gangarowa.
Magana takeson yi Amma zuciyarta tayi nauyi bazata iyaba sai wani irin quntataccen kuka Mai ciwo daya zuwar Mata.
Ganin ba tashi zataiba kada wani yashigo yagantama kokuma yaji haukar datake fada yasa hajiyar Kama hannayenta ta miqar tsaye tareda janta takaita har waje ta Kuma gargadeta akan sake zuwa da wata jaririyar gidan da sunan salisu abakinta.
Kuka sosai Hadiza keyi tanajin wani irin azababben ciwo a zuciyarta,
Jin takeyi kaman zuciyarta zata mutu,
Ganin mutanen dake wucewa sunfara Mata kallon mahaukaciya yasata Jan jiki tabar kofar gidan.
Tafiya kawai takeyi sbd Batasan Inda zataba,
Jin jaririyar tayi baccin wuya itama yasata tsayawa ta goyata taci gaba da tafiya.
Tafiya Mai nisa tayi wadda batamasan tayiba har Saida yamma tayi sosai ta nema bakin wani gidan abinci ta zauna tareda sauke jaririyarta ta saka cikin hijabinta tafara Bata nono.
Kasa Shan nono 'yar tayi sbd tuni ciwon zazzabin wahala ya rufeta sbd ba qaramar Rana sukashaba.
Fara jijjigata tayi tana sake cusa Mata nonon Amma Bata amsaba Dan haka ta maidata ta goya.
Shagon dake gefen gidan abincin ta qarasa ta siyo ruwan roba na sauran canjinta dasuka rage Takoma Inda ta baro ta zauna tasake saukoda 'yar ta bude ruwan ta ringa zubawa a murfin robar tana Bata.
Ruwan ma batasha saidai wasu sun shiga cikinta kadan...
Kuka jaririyar keyi sosai Wanda ya qarasa gigita Hadiza..
Batasan ya zataiba sbd kanta zazzabi da ciwone Mai qarfi a jikinta.
Gabanta radadi yake Mata sbd qarin haihuwa da rashin ruwan zafin gasa gurin ga doguwar tafiya cikin azabar Rana Dan haka itama take a gigice.
Kukan 'yar yasa Dole tabar gurin ganin hankalin jama'a yafara yawa kanta.
Cikin wasu mabarata dake gaba kadan bakin wasu super market taje ta zauna tana sake fama da Yar dake kuka har lokacin.
Nanma bata tsiraba sbd anfara Mata kallon zargi da 'yar
Silalewa tayi tabar gurin kafin ayi Mata dukan Satan 'ya takama hanya taci gaba da tafiya gashi duhun dare yafara Dan har anfito sallar magriba.
Tafiya Mai Dan tsayi takuma Yi taji bazata iyaba sbd radadi da azabar da tsakiyar cinyiyinta ke Mata,
Azabar datakeji tafi Mata naqudar haihuwar datayi sbd gurin ya goge sosai sbd tafiya Dan haka tasamu wasu shaguna da Yan gudun hijira suke ta zauna daga can gefe itama.
Ruwan robar data siyawa yarta itama taciro daqyar ta iya karban kadan ta shimfida zaninta agurin ta kwanta tana fidda numfashi daqyar jikinta na rawar sanyi.
Babu Wanda ya lura da ita sbd suma kowa ta kansa yakeyi Bata wani ba dan kowa agurin abin tausayine.
Yarta na dungule cikin jikinta itama tayi bacci.
Hadiza Batasan inda kanta yakeba sbd kusan suma tayi saida sanyin asuba da kukan yarta ya dawo da ita
Ta bude idanuwanta daqyar tana Neman tashi Amma takasa.
Daga kwancen ta sake rungume jaririyarta ta Ciro nono tasaka Mata a Baki.
Ana Gama sallar asuba duka mabarata da Yan gudun hijira dake gurin suka fara watsewa sbd baa barin Zama gurin da daddare kawai suke zuwa su kwanta da gari ya waye kowa yatafi gurin bara.
Daqyar ta iya daddafawa ta tashi tabar gurin
Tafiya kadan tayi tasamu guri ta zauna sbd bazata iyaba.
Anan gurin ta Rana ta fito ta sameta
Mutanen dake wucewa suka fara Bata sadaka sbd sun dauka Bata takeyi
Dayake tana buqatan taimakon ana bata haka ta ringa karba har Allah yasa ta hada 400 ta tashi daqyar ta siya ruwan zafi gurin me shayi ta Sha na hamsin ta siya wasu na hamsin din ta wankewa 'yarta jiki ta gogeta ta maida Mata kayanta da daudarsu da komai.
Har yamma tana garari a hanya Dan haka tasake komawa gidansu salisu
Hajiyarsa Bata tausayawa mataba tayi Mata korar wulaqanci harda munanan kalamai akan 'yarta Dan haka ta sake komawa Inda ta kwana jiya anan ta Kuma kwanciya.
Washe gari ma haka ta sake zuwa gidansu salisu a karon karshe hajiyarsa tayi Mata mummunan gargadin sake zuwa tareda tabbatar Mata da har abada bazasu karbi shegiyar data haifaba amatsayin 'yar salisu.
Ranar tayi kukan data jima batasamu tayiba sbd maganganun hajiyar dakuma ciwo Mai tsanani daya sakota gaba da 'yarta.
A ranar ko bacci Bata samu tayiba a zaune ta kwana tana kallon yarta wadda da alama sanyi ne yayi mummunan shigarta tana numfashi daqyar.
Gabaki daya duniyar tayi mata zafi,
Qunci da nauyi takeji a zuciyarta Mai tsananin gaske..
Washe gari da safe data samu qarfin jikinta ta tallaba takai jaririyarta wani qaramin asibiti datagani a hanya.
Karon farko ana dubata akace Mata 'yar batada lfy sosai,
Zuciyarta Bata bugawa yanda yakamata hakama sanyi na Neman shigarta.
Gado aka Bata Amma sbd batada ko kudi suka korota ta fito tana bin hanya Ahankali idanuwanta na tsiyayar hawaye.
Yau Bata samu gurin kwanciyaba sbd yan hijirar dasuka qara yawa Dan haka Nesa dasu sosai tasamu ta kwanta.
Hankalinta a tashe yake da Inda ta kwanta din sbd itace a nesa qarshe sosai
Wasu irin sauro da cinnaku suka ringa cizonta tanaji Amma Bata ko iya motsawa sbd zuciyarta data Gama mutuwa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya👇
07040727902
MTN card👇
09134848107[11/3, 7:34 PM] +234 808 746 2576: *_39_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Koda garin ya waye daga ita har 'yarta gabaki daya jikinsu kurajen cizan sauro sun bayyana ajikinsu ita hardana cinnaku dasukai Mata kaman Mai wani ciwon take fuskarta ta kumbura.
Tashi tayi ta nufi Inda suke gyara jikinsu ta gyara ta fito ta miqa hanya goye da 'yar tata.
Kwananta hudu agurin aka rarraba musu kudin sadaka a gurin akan kowa yabar gurin
tana karban nata ta tattara tsumman kayanta ta nufi asibiti takai 'yarta data fara nisa.
Kwantar dasu akai tareda sakasawa 'yar oxygen Wanda ya cinye kudin nata batareda ansamu na siyan sauran maganiba.
Daqyar takai safe cikin tashin hankali Mai tsanani da qaqa nikayi sbd jikin 'yar jaririyarta daya sake gabaki daya.
Rashin Imani da rashin tausayin asibitin haka suka sallameta sbd rashin magani da rashin kudin siyansa ta rungumo 'yarta ta fito tana hada hanya.
Yau kam komai yasake yimata tsananin da takejin mutuwa take buqata Ido rufe.
Uwarta da ubanta da salisu takeson bi Ido rufe sbd ta huta da qunci da baqin cikin duniyar datake ciki.
Kuka aranar tayisa har idanuwanta basa gani sosai sbd kumbura.
Tahau titi rungume da 'yarta wadda take tsoron dubawa ko ta mutu ko tanada sauran Rai.
Mutuwa take Kira take Kuma fata sbd Babu Inda takejin sassauci a wannan rayuwar.
Wani azababben ciwon gaba take fama dashi da ciwo ciki Mai tsanani,
Ta bangare daya qwaqwalwarta tafara kasa daukan tashin hankalin da masifar datake ciki Dan haka wunin ranar attempting kashe kanta kawai takeyi Amma tsananin qaunar datakewa yarta Yana hanata idan ta kalleta.
Tamkar mahaukaciya tafara komawa sbd taba qwaqwalwarta da abin yafara Musamman mummunan infection din daya shigeta sosai sbd rashin kulawa da gurinda ta Haihu.
Tun tana iya controlling kanta akan yanayinta dayake son juyar da qwaqwalwarta haryazo tafara tsoraran yanayinda jaririyarta da itama kusan Rai ne kawai ya rage Mata Zata shiga idan wani Abu ya sameta.
wani masallaci takai 'yar ta ajiye Zata gudu tabarta ko zaa samu Wanda zai tallafeta Amma saita kasa barinta agurin tadauketa tana hawaye tana jujjuyar dakai tabi hanya tana surautai ita kadai.
Batasan ya akaiba sai gata kwatsam takai kanta hanyar Tasha tana tafiya.
Kaduna ne?
Ina zuwa ne?
Kano ne?
Katsina ne?
A kunnuwanta kalmomin ke sauka suna sake yamutsa qwaqwalwarta...
Jikinta rawa yakeyi sosai kanta na sake juyawa sosai.
Ahankali sama sama takejin cikin nutsuwa wani yayi magana a bayanta.
Assalam alaikum,
Malama Zan wuce ko
Zaki Dan matsa.
Waiwayowa tayi da sauri a firgice tareda kallon Mai maganar.
Saurayine matashi Wanda zatai qani dashi bamai tazaraba sosai.
Sanye yake cikin qananun Kaya Riga ash da wandon jeans black.
Cikin sauri Dan tashar masu mota ya qaraso Yana daka Mata tsawa da cewa"
Dalla matsa ki wuce daga Nan
Kinzo kintare hanya
Idan bara zakiyi ki matsa can.
Yallabai Kace gombe Abuja ne ko?
Kallonsa matashin yayi kafin ya kalli Hadiza data Matsa gefe ta rabe rungume da abinda yake sakaran 'da ne sbd yanda ta rungume zanin cikeda so da shauqi.
Hannu ya saka aljihunsa ya Ciro Dubu daya ya miqa Mata cikeda kulawa batareda yace komaiba.
Hannu ta miqa a hankali ta karba tareda kafesa da Ido tana zuba godiya Kuma takasa tafiya.
Cikin qaguwa ya kalli masu lodin motar yace"
Saura mutum nawane motar tacika hanyar kunsanfa bawani kyaune da itaba.
Yallabai Saura mutum uku motar tacika.
Muje zan biya kudin sauran gurin.
Angama ranka yallabai.
Hadiza dake rakube tanajin haka sai kawai tasamu kanta da biyo bayansa tafara kokarin Shiga motar sbd Jin zaa biya koba komai gwara tashiga duniyar tunda hakane qaddararta.
Kokarin hanata shiga motar direba yafara yana cewa"
Ke tsaya, tsaya
Ina zaki?
Wane gari Zaki?
Abuja" ta furta Kai tsaye muryarta na 'dan rawa.
Ina kudinki na mota?
Waiwayowa tayi ta kalli gefenda matashin yake zaune cikin nutsuwa Yana duba wayar hannunsa.
Ganin tana kallonsa ya fahimci batada kudin motar Dan haka yacewa drivern tahau gurin mutum daya cikin kudin mutum biyu daya biya.
Kasa kallonsa tayi bare tasake Masa godia saima sauke kanta datayi qasa tana sake rungume jaririyarta.
Hanya aka dauka aka fara tafiya Mai nisa kowa yayi tsit a motar Yana aikin gabansa masu bacci Kuma nayi.
Ahankali ahankali idanuwan Hadiza suke cikowa da hawaye tanajin wani irin masifaffen ciwon Kai da zabar ciwon ciki.
'yarta take ji,
Ita take tausayi ba kantaba,
Jin kanta na neman juyewa yasa tafara jin kaman tace a tsaya ta sauka.
Yanayin yanda take sake qanqame babynta yasashi Dan dagowa ya kalleta dakyau yaga tarin tashin hankalin dayake ciki kafin ya maida kallonsa kan babyn cikeda kulawa yace"
Ki Dan sassauta riqon
Kina matse babyn sosai Inaga.
Da sauri kaman qaramar yarinya tayi saurin sassauta riqon tareda bube jaririyar gabaki daya Dan Tasha iska.
Wani irin mamaki da firgici ne ya kamasa ganin babyn wadda alamun rashin lafiya sosai da yin nisa ya bayyana atareda da ita,
Gabaki daya babyn yunwa tagama kamata tako ina.
Dauke kansa yayi daga kallon jaririyar sbd zuciyarsa bazata iya jurewa kallontaba.
Tafiya suka cigaba dayi mai nisa da gudu..
Guri biyu aka tsaya siyan abinci Kuma ya siya Mata yabata sbd lurada akwai yunwa tareda ita.
Duk abinda ya siya Mata ya bata bataciba suna jikinta dunqule sbd bazata iya ciba ita kadai tasan tsananin halin azabar datake ciki.
Daga Nan Basu sake tsayawaba a hanya suka cigaba da zuba gudu a hanya.
Qarfe Tara da mintuna arbain da takwas suka isa birnin tarayya.
Kowa fitowa yayi daga motar yana haramar daukan kayansa ya wuce.
Daga shi sai jakarsa dake rataye a kafadarsa ya fito Yana sake saka Kiran Wanda aka aiko daukansa daga gida.
Ahankali Hadiza ta tako gefensa ta kallesa qafafuwanta na 'dan yin rawa.
Tsalle zuciyarta keyi ga abinda zuciyar tata ke ingizata ga aikatawa.
Jin takeyi zuciyarta ta kwanta data barmasa 'yarta ta gudu sbd yanada tausayi da Jin qai Dan kuwa ita batada tabbacin zatakai labari ayanda takejin azaba da radadi cikin jikinta.
Bazataso wani Abu ya sametaba 'yarta ta gararanta...
Jin mutum kusa dashi yashi juyowa da Dan sauri sbd ya Dan firgita.
Kallonta yakeyi da mamaki sosai batareda yace Mata komaiba.
Ganin kallon dayake Mata yasata kallon 'yarta cikin kokarin daidaita kanta tace"
Nagode sosai Allah yasaka maka da Alkhairi.
Amin" kawai ya iya furtawa Kai tsaye Yana cigaba da wayarsa.
Yana aje wayar drivern ya tura aljihun jeans dinsa drivern gidansu yace Saura kadan ya iso.
Jakarsa ya juyo zai dauka daga qasa gefensa idanuwansa suka sauka kan zani kan jakar tasa.
Da sauri ya waiwaya Babu kowa gefensa da bayansa.
Sake jujjuyawa yayi Yana Raba idon matar data bar Masa zanin.
Jakar ya riqe zai dauka ya watsar da zanin agurin sai zuciyarsa ta kasa Dan haka yakai hannu kawai zai janye zanin yaji alamun Abu aciki
Batareda ya taba tunanin ganin komaiba bare 'dan mutum ya bude zanin aikuwa yayi Ido biyu da babyn.
Zaro Ido yayi da sauri tareda mayarda zanin ya rufe babyn zuciyarsa na rawa.
Da sauri tafara waigawa koina Yana zazzare idon Neman Hadiza.
Daukan babyn yayi dan Dole ya rungume Yana sake jujjuyawa Neman Hadiza.
Fara tashi hankalinsa yayi dayaga dagaske yakasa ganin uwar babyn.
Kokarin komawa yakeyi gurin motar dasuka iso sai kawai ya hangota tana sauri zatabar tashar tana zazzare idon kada ya ganta.
Da sauri ya bita
tana ganinsa ta sake sauri ba Shiri ta tare Mai mashin ta haye suka bar gurin da sauri.
Tashin hankali da tsananin mamakine da firgici yasashi Neman wani mashin din ya hau Amma tuni Hadiza da me mashin dinta suka bace Masa.
Me wannan matar tayi ne?
Me take nufi?
Da gangan tana sane ta bar Masa babyn ta gudu fa.
Innalillahi wainna ilaihrrjiun..
Meyasa zatayi haka?
Dama mahaukaciyace Basu luraba?
Meyesa Zata gudu tabar Masa baby ?
Ina zai Kai babyn to?
Yawo ya ringa Yi dame mashin hankaki tashe Amma sun kasa ganin hadiza ko Mai Kama da ita.
Dukkanin qwaqwalwarsa tsayawa tayi cak shima
Ya tsaya rungume da baby ajikinsa Yana Jin jiri na Neman zubar dashi,
Ya zaiyi da wannan babyn?
Bazai iya komawa tashaba sbd baisan wazai bawa babynba,
Baimasan wazai fara tunkaraba a tasha da babyn sbd Babu ruwan kowa babuma Kuma Wanda zai karba.
Innalillahi wainna ilayhirrajiun" yafara maimaitawa dukkanin jikinsa na saki.
Mai mashin ya fadawa Inda zai kaishi
Wata qaramar police station yaje da babyn suka qi karba sukace yace babban station kawai.
Wata station din yakuma zuwa sukuma sukaqi karban 'yar suna zargin kodai yarda Yar kawai yakeson Yi.
Wata sabuwar masifar yakuma Shiga lokacinda yagama yawo da babyn Babu wata mafita ko daya.
Yanayin babyn kawai ya tabbatar masa da babyn sosai tayi nisa batada lafiya Dan haka ya tattara a nufi wani private asibiti yakaita su duba.
Suna karbanta take sukai dakin jarirai da ita.
Fada suka fara yimasa sosai ganin yanayin datake ciki.
Duk abubuwan zasuyi Mata sunyi suka sakata a kwalba sbd ma sai allah Kam idan Zata rayu.
Tashin hankali sabo yakuma Shiga lokacinda suka zayyano Masa cututtukan dasuke cin babyn.
Biyan komai yayi kafin ya samu ya wuce gida yabar babyn anan sbd akwai masu kula da babies a dakinsu.
Koda ya Isa gidansu mahaifiyarsa na ganinsa cikin tashin hankalin rashin daukan wayarsa da rashin ganinsa da driver yayi har kusan qarfe daya da rabi na daren yayi.
ABDULMAJEED..Ina ka shiga daga isowarka?
Lafiya kuwa?
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali idanuwansa na qanqancewa da tashin hankali da damuwa yace"
Hajiya umma kaina kaman zai fashe
Zanshiga nayi sallah tukuna.
Cikeda kulawa tace"
Jeka kayi wanka da sallar ka huta da safe mayi magana.
Juyawa yayi Yana hada hanya ya nufi hanyar dakinsa Yana jin kansa na sake tsananta ciwo.
Zubewa yayi qasa tsakiyar dakin Yana dafe kansa,
Daqyar ya tashi ya qarasa isa ya tube kayansa ya shafa toilet.
Wanka yayi ko zai samu kansa ya Dan sake tareda alwala yafito.
Jallabiya da gajeran wando kawai yasake yayi sallah ya miqe a daddafa ya Isa kan gadonsa ya hau ya kwanta tareda rufe fararen idanuwansa dasuka qanqance sbd tashin hankali da damuwa.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN