Inaaya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Adventure Stories

Chapter   29 / 43

84K to 87K   out of 128.5K words

sbd a bazata yaji zancen.

Ahankali ya daga hannuwansa Yakai kan hannuwanta Yana kokarin janyeta kenan saiga Haj umma da umma yaganah kusan atare sun shigo palon kaman aike....

Da sauri Haj umma ta dakata tana kallon ikon Allah lokaci daya tana dauke idonta Kuma.

Umma yaganah kuwa juyawa tayi abinta batareda ta tsayaba tana jinjina sangantar Inayah sbd tasan itace me wannan aikin ba Abbin ba.

Ganin Haj umma yasa duk yaji yana sake shiga wani yanayi na sanyin jiki ya janye Inayah din zaiyi magana ta sake komawa ta maqalesa tana cewa"

Abbi Dan Allah kabarni da aurena zanyi biyayya akan da....

Salati haj umma ta sake tana maido da kallonta kan Inayah dataqi Kota kan idonta tabi.

Ba Shiri Haj umma ta kamo hannunta tana janyota gefenta tace"

Yaushe zakiyi nutsuwa nikam 'yar nan?
Yanzu uban naki kike damuqa haka gaban mutane kina maganar aure.

Tashi cikin turawa haukane akace Miki?

Maza wuce daki kisan abinda kikeyi
Mace da kunya da kamun Kai aka santa.

Haj umma idan na Kama kaina to Abbi zai iya auren wata yabarni da wannan auren..

Daga Haj umma har abbin kasa magana sukai sbd zancenta ya mugun Basu mamaki
Ya dago ya zuba Mata indanuwansa dasuka sake kashe Mata jiki tanajin kaman zuciyarta Zata fashe akan kishin hada sunansa da wata takuma rabarsa.

Haj umma kuwa sake sallamawa Inayah tayi sai takasa cewa komai ta qwalawa umma yagana Kira.

Umma yaganah najin Kiran tasan zaa Rina Indai akan MAJEED ne Inayah Bataji hakama Haj umma da alama itama tanada aiki tunda tana cikin uwaye masu kishin yayansu.

Umma yaganah na fitowa Abbin na wucewa batareda ya tsayaba Dan baisan mezai iya tsayawa saurara ba kuma.

Yaganah meyasa Inayah bakinta baya tauna zance ne?
Kunga illar rashin kwabarta
Gashinan sai zantuka takeyi marasa kan gado.

Cikin nutsuwa da umma yaganah tace"

Ya aka iya sai hakuri da addua Haj
Inayah din ce akwai kuruciya sosai atareda ita.

Fada Haj umma tafara Yi umma yaganah na Bata hakuri aka dai kashe maganar taja Inayah zuwa daki.

Bataiwa Inayah fadaba sbd itama zuwa yanzu tafara ganin rashin kyautawar Haj umma saidai Kuma bazata nuna hakan gaban Inayah ba sbd kada taci da ganin rashin kyautawar Haj umma din.

Batace komaiba Dan batada abin cewar Dan haka ta juya ta fice Takoma aikin datakeyi kitchen.

AA MAJEED na Isa bedroom dinsa zaunawa yayi kan sofa ahankali tareda Dan rintse Ido Yana dafe goshinsa sbd Dan juyawar da kansa keyi.

motsawan da zaiyi Qamshin black opium ya Shiga hancinsa daga kayansa na Inayah Dan haka ya miqe ahankali ya zare ya janyo towel maroon ya daura a qugunsa ya nufi toilet Yana Dan sake dafe goshinsa.

Wanka yayo yafito ya shirya cikin Kelvin Klein sweatset yana qamshi Mai sanyi ya fito ya nufi masallaci sallar magriba.

Tunda tadawo daki haka kawai takasa samun nutsuwa da sukuni tayita hawayenta tagama ta tashi itama tayi alwawala tayi sallar magrib tana idarwa ta dauki wayar Neesah daketa faman kiranta.

Sun jima suna waya tana Bata hakuri da qarfafa Mata gwiwa akan aurenta kafin suka kashe.

Wanka ta tashi tayi sbd batai niyar fita cin abinci ba tana fitowa ta saka Riga da wandon Balenciaga masu kauri tana kokarin hayewa kujera chatting ta tuna gargadin Abbinta na rashin fitowa cin abinci Dan haka ta miqe da wayarta a hannu tareda zira slippers ta fito tana qamshin black opium Mai sanyi.

Tana fitowa ta nufi dakin Haj umma ta Bata hakuri suka fito kusan tare zuwa dining din haj umma na sake nanata Mata ta Dena sakawa ranta banzayen tunani akan MAJEED sbd ubane agunta.

Batace komaiba har suka Isa suna Zama saiga Abbin ya shigo cikin nutsuwarsa da kwarjini sai qamshinsa yakeyi komai nasa a kame da nutsuwa.

Zama yayi Yan gaidasu umma kafin ya kalli Inayah dake kallonsa cikin sanyi da alaman ban hakuri.

Shikenan ya Isa"
kawai yace Mata ahankali cikin kulawa.

Murmushi tasake tana maida kanta ga abincin da aka dafa tuwon shinkafa da miyar ganye masu lafiya da Naman kaza da kifi.

Bata fuska ta danyi sbd Bata cikason tuwoba Dan Haka kadan ta zuba tuwon tanaci da spoon ahankali..

Shima abbin da spoon yakecin tuwon a natse.

Wayar Inayah din ce tayi ringing sunan Dr farhat ya bayyana akai ta saki siririn numfashi tareda daukan wayar a gundure tace"

Dr farhat I will call you muna cin abinci.

Kashe wayar tayi Bata jira amsartaba ta ajiye.

Jin Dr farhat ce yasa Bayan ajiye wayar haj umma Dan kallon MAJEED fuska asake tace"

Dr farhat nada kokari jiya ta hadani da mahaifiyarta mun gaisa sunada karamci sosai....

Shiru kowa yayi harshi abbin.

Jin yanda Haj umma ke yabon Dr farhat yasa Inayah kasa shiru tace"

Haj umma Ni kullum fada kikemun Amma kinata yabon Dr farhat,
Bayan nice jikarki Kuma....

Da idon umma yaganah tai Mata tsawa tana hanata qarasawa.

Murmushi Haj umman tayi tace"

Ke dince su yagana sun sangartaki da yawa kin kasa sanin kin girma,
Bakisan abinda kikesoba da Wanda bakyaso komai fada kike...

Ni yanzu Abbi kawai nakeso bayanshi banason koma....

Qwarewa abbin yayi da abincin dake bakinsa yafara tari ahankali.

Da sauri ta dauki ruwan ta taso ta kawo Masa tana cewa"

Sorry Abbi,sannu...

Matsesa tayi gurin basa ruwan
Turarenta yaringa Shiga hancinsa take ruwan suma suka fara kokarin qwaresa ya ajiye cup din Yana daidaita nutsuwarsa yace"

Thank you.

Kasa magana Haj umma tayi bakinta take ya mutu har aka Gama Babu Wanda yakuma magana acikinsu.
##MAMUH#
#HOTLOVE/ROMANCE




_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107
[11/8, 9:55 AM] Sweet sis: *_51_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Qin wucewa tayi bedroom dinta tabi bayan Abbi Wanda baisan tana bayansa ba Saida yashiga palonsa taji mutum a bayansa Yana juyowa suka hade Saura kadan ta Fadi ya tarota ta dawo jininsa.

Shiru tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa dayake kokarin hanawa karban kowane yanayi.

Cikin nutsuwa ya zareta Yana cewa"

Meyake damunki ne kwanakin Nan Inayah?

Murmushi tasake tana kamo hannunsa bayan ya zauna itama ta zauna gefensa tareda shige Masa sosai tana cewa"

Abbi Ni bansaniba ko nayi lefi yanzu ka daina ji Dani kaman da,.

Ko Dan Haj umma Bata Sona ne?....

Wani kallo ya juyo yayi Mata da idanuwansa dasuka Dan sauya cikin Dan fada yace"

Karki Kuma cewa haka,
Ki Dena hada matsayinki Dana ummana kowa matsayinsa daban...karna sake Jin hakan a bakinki.

Ahankali tace"

Sorry Abbi na dena
Amma Abbi ai zaka barni a matsayin matarka ko?????.....

Rintse idanuwansa yayi da wani irin yanayi na mamaki da fara kosawa da zancen
Yaushe Inayah ta Zama haka akan aurene Bai saniba?
Bude idanuwan yayi tareda juyowa ya zuba Mata su gabaki daya Yana kallon bakinta da yayi maganar zuwa kirjinta dake harbawa da sama sbd fargabar zancenta Mara control daya sake fitowa bakinta ba Shiri.

Farare idanuwanta dake kallonsa cikeda kauna Mai girma ya maida NASA idanuwan Yana kalla....

Hannunsa dake cikin nata takuma kamawa tana kallonsa a sanyaye.

Kasa cewa komai yayi Yana kokawa da tunanika dake yawo akansa Yana kokarin kwantarda kansa.

Ahankali ta furta sunansa cikin wata kasalalliyar murya wadda ta sanya tsigar jikinsa tashi sbd numfashi Mai dumi data furzo a fuskarsa bayan Kiran sunan nasa.

Ganin har lokacin baice komaiba sai idanuwansa Daya dauke ahankali daga kanta Yana maidawa kan tv Dake kunne.

Ahankali cikin seta murya yace"

Haryanzu maganar aure Bata fita bakinkiba Inayah.

Yanda yayi magana da wata shaqaqqiyar murya yasa jikinta mutuwa itama ta kwantar da kanta a kan hannunsa tana cewa"

Abbi Ni naka auren kawai nakeso yanzu ai.

Sake danne numfashinsa yayi Yana basarwa.

Sosai tayita yimasa fira wadda duka yawanci shagwabane ta ringa zuba Masa wadda tagama take neman lalata kamewarsa da wuce tunaninsa akan yanda Inayah din take abubuwan dabaisan a Ina tasaniba.

Tana tafiya dakinta ya miqe ya nufi toilet din bedroom dinsa Kai tsaye ya sakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwansa dasuka sauya Yana sake riqe kansa da kamewa.

Ita Kam tana komawa daki sallar ishai tayi zuciyarta cikeda farin cikin yau tayi fira da Abbinta kaman da
Tayi Shirin bacci ta haye gado tayi kwanciyarta tana jin yanayi Mai qarfi fa girma a zuciyarta gameda Abbinta Wanda takejin yanafin na dah.

Washe gari fes ta shirya cikin haricca long knitted skirt and blouse milk sai vincci loafers ta fito ta wuce aiki Bayan taje ta gaida Haj umma
Umma yaganah Kuma tare sukai breakfast Abbinta Kuma Bai fitoba da alama Bai tashiba.

Agurin aiki yau ma umma Hadiza tazo sunyi fira sosai kafin tadawo gida.

Tun a harabar gidan tasan anty Hafsat tazo sbd taga motar CM daya.

Batai tsammanin samun harda dr farhataba a gidan Dan haka duk fitarta da Anty Hafsat Basu wani samu sinyiba gashi Haj umma ta cika kowa da kulawarta akan Dr farhat wadda itama sosai take nuna Jin dadin hakan Dan tasan tagama samun guri a gun AA MAJEED.

Har dare Basu samu sunyi maganaba yanda ya kamata saidai sama sama anty Hafsat din tasake nanata Mata akan itace Zata gyara aurenta yazama kaman kowanne aure da kanta.

Bayan tafiyar anty Hafsat da Dr farhat rasa abin kamawa tayi saidai ta shiririce gurin waya da Neesah wadda suka qarasa shiriricewa akan firarrakinsu na Yan Mata yanda suka Saba.

Sallar ishai tayi ta fito zuwa dakin umma yaganah sbd sunci abinci already tun dazu taredasu Anty Hafsat.

Tana Shiga dakin zubbi tace"

Abincin Sir yazama ready zaa aje a dining ne kokuma zaa kai Masa dakin Haj umma?
Ko a palonsa zaa Kai?

Kallon Inayah umma yaganah tayi daga zaune tace"

Kije ki Kai Masa palonsa basai an jera a dining ba.

Fitowa tayi tareda zubbi batareda taje dakinta ta sauya kayaba ta dauki qaramin tray din da tea ne akai sai faten dankali dayaSha kayan ciki da curry.

Kai tsaye palonsa ta nufa da tray din tana shakkar kada abbin yayi Mata fadan kayan jikinsa sbd akwai sanyi gashi Riga da wandon baccine ajikinta masu santsi Kuma wandon ba har qasa bane ko bra Babu ajikinta.

Tana shiga palon sanyin AC daya Gama gauraya da turarensa ta shaqa tareda nufan table ta ajiye tray din tana dagowa Yana fitowa daga bedroom dinsa sanyeda pyjamas shima
fuskarsa tayi fresh kaman baya Shiga Rana.

Akan kayan jikinta idanuwansa suka fara sauka ya dauke Kai Yana qarasowa ya zauna.

Zama tayi gabansa tana daukar tea din ta miqa Masa tana cewa"

Abbi barka da da fitowa.

Numfashi yafara saukewa ahankali kafin ya dago ya kalleta tareda sakin taqaitaccen murmushi yace"

Barka Dr Inayah majeed.

Dadi taji sosai ta taso daga gabansa ta dawo gefensa kusa dashi sosai tareda dafa cinyarsa Saura kadan ya qware da tea din dake bakinsa tayi saurin janye hannunta tana kallonsa Dan itama batasan a cinyarsa ta Dora hannunba.

Daqyar ya hadiye Wanda ya kurba a bakinsa tareda juyowa ya kalleta idanuwansa na gangarawa ga bakinta dake motsi tanason yin magana Amma takasa sbd idanuwansa dake Neman rudar da ita.

Qamshinta ya shaqa ahankali tareda Dan rufe Ido ya bude Yana ajiye cup din hannunsa ya juyo gabaki daya Yana kallonta
Magana yakeson yin Amma qamshinta yayi Masa yawanda yake kokawa da nutsuwarsa ya hadiye numfashi ahankali zai bude Baki yace ta tafi tayi saurin Kai hannunta kan bakinsa ta rufe sbd tasan korata zaiyi....

Saukar tafin hannunta Mai taushi akan bakinsa yasashi rufe idanuwansa dasuka sauya ya bude ya watsa Mata idon numfashinta na shiga hancinsa tareda qamshinta Kai tsaye Wanda yasa numfashinsa Dan sauyawa.

Janye hannunta yayi Kai tsaye Yana fuskewa tareda daukan cup dinsa yakai bakinsa Yana kurba a natse yace"

Kije ki saka kayan sanyi ki kwanta akwai sanyi yau.

Zuciyarta dake bugawa da qarfi ta dafa da sauri tareda kallon gurin tana Jin yanda bugun zuciyarta ke qaruwa.

Juyowa yayi ahankali ya kalleta Jin Bata motsaba
Yaga hannunta kan kirjinta dayaketa kaucewa kalla sbd yanayin datake ciki....

Sosai tsatsayyun kirjinta suka nuna basa batareda bra sbd yanda suke motsawa kadan cikin santsin rigarta.

Kaman Mara lafiya ya dauke Ido daga kanta yakasa tambayarta lafiyarta data dafe kirji sai kawai a hankali yace"

Kije ki sauya kafin sanyi ya kamaki.

Bata musaba ta miqe ta nufi kofa ta fice sbd bugawar da kirjinta yakeyi yasata Shiga fargaba da tunanin itakuma.

Tana fitowa Palo suka hadu da Haj umma data fito daga dakin umma yaganah dubota da ciwon kan datace tana Dan ji tun yamma.

Da boyayyan mamaki take kallon Inayah wadda ke tafiya a sanyaye hankalinta baya ma kan Haj umma din Dan Bata lura da itaba.

Kai tsaye dakinta ta wuce tareda fadawa kan gado tana shigewa bargo ta lumshe ido tanajin sabon feeling Mai qarfi akan Abbinta.

Daqyar tayi bacci da daren Dan haka tayi lattin tashi...

Shima Abbi ranar baisamu wani bacci ba Dan haka tunda safe ya shirya ya fice sbd zuciyarsa dake buqatan iskan da Babu Qamshin Turaren 'yarsa ko kansa zai sake.

Da wuri Inayah ta dawo Dan kawai tasamu fira da Abbinta Amma Bai dawo da wuri ba
Qarshema ranar sai dare yadawo Bayan sunyita jiransa itada Haj umma Amma sai kusan 10 yadawo Kuma Kai tsaye yayi musu Saida safe ya shige sbd Yana tareda gajiya.

Haka Inayah taqi tafiya daki saida ta dafa tea takai Masa tareda cake Mara zaqi sosai sbd Sam bayason zaqi ko kadan.

Haj umma na kallo Inayah taje palon nasa Kuma ta dauki mintuna sosai kafin ta fito Wanda itakuma tsayawa tayi yafito daga bedroom Amma tayita jira Bai fitoba Dan haka ta tahowarta ta wuce daki jikinta a sanyaye.

Washe gari haka abbin yakuma fitar safe Bai tsaya breakfast ba Kuma Bai dawoba sai dare yauma.

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun abin na Wasa saigashi Abbi ya rage zaman gida Sam Baya Zama he's always busy Sam yaqi bawa kowannensu time sbd Haj umma tafara tunkararsa da maganar Dr farhat Wanda Inayah Bata saniba batada labari
Umma yaganah ce kawai tasani Kuma taqi barin Inayah taji zancen sbd rigimarta.

Hankalin Inayah tashi yayi fiyeda komai,
Rashin lokacinsu daga Abbinta yasata sukukucewa ta daga hankalinta sbd tsoron ko tayi wani lefin ne tunda itama tasan bataji.

Haj umma ma tashi hankalinta yayi tashiga damuwa tareda Dora lefin akan Inayah tayi masa lefi ne shiyasa yake cikin damuwa Dan kuwa damuwa ta nuna sosai akan fuskarsa.

Jin Abbinta na cikin damuwa yasa hankalinta ninkuwa atashi Dena fita aiki sosai tana Neman hanyar zaunawa da Abbin tabasa hakuri.

A bangare Daya pressure din da Haj umma ke basa akan ya aura Dr farhat yasa ciwon Kai Mai tsanani kamasa qarshe ya Dena fita sbd Yana buqatan kansa ya sake sosai.

Ga Inayah duk yanda taso ta kusantoshi bayaso yanzu sbd matsalar da hakan ke basa
Itakuma ganin hakan saita rikice da damuwa sbd bayason tana zuwa gurinsa sosai.

Dr farhat ce tazo daga gidansu ta dubasa sbd ciwon kan ya tsananta Masa.

Rashin bacci ne da damuwa yake damunsa abinda yafadawa Haj umma.

Hakan kuwa yasa Haj umma yanke shawaran aurawa majeed din Dr farhat Kai tsaye sbd yasamu Mai kulawa dashi,

'danta yana buqatan kulawar mace
Wadda Zata sakasa farin ciki tabasa kwanciyar hankali Kuma bataga hakan atareda Inayah ba wadda bayan shagwaba datake zuba Masa Babu abinda Zata iya Dan haka bazata zuba Ido 'danta ya mutu abanzaba ko jikiki Bata samuba.

Anty juwairiyyah takira tanayiwa wannan bayanin akan harta Kira qanin abbansu MAJEED din zaa saka lokaci a je Neman auren.

Umma yaganah damuwa da nata tashin hankalin tashiga Jin hukuncin Haj umma din Wanda Kuma Babu Mai iya takesa tunda itace uwar MAJEED Bayan shi Babu Mai iya tsallake wannan zartarwar.

Hafsat takira a waya tace tazo tana nemanta sbd Dole sufara shawarar yanda Inayah zataji wannan mugun labarin.

Abinda Bata saniba shine MAJEED din ya amince kokuwa? sbd batai maganar dashiba Kuma shima baizo yamataba.

Inayah na asibiti anty Hafsat tazo cikeda damuwa sbd umman tafara Mata bayani a waya shiyasa batazoba Saida ta tabbarda Inayah na asibiti.

Tagumi suka rafka dukkaninsu biyun cikin dakin umma Bayan umma yaganah tagama yimata bayanin abinda yake faruwa ta Dora da cewa"

Hafsat ki kokarta ki sake nutsar da ita tasan abinda takeyi Dan kuwa kishiya da qananun shekarun Nan nata da sangantar datake basune zasu fiddataba Duk kuwa da tsananin son da MAJEED ke Mata idan ya auri wata macen yasamu nutsuwa a gurinta bazata sake gane komaiba.

Numfashi anty Hafsat ta sauke cikin takaici da damuwar maganar tace"

Umma Inshallah Inayah bazata taba wulaqanta a hannun AA ba saidai Zan dage na sake lurar da ita abinda yake gabanta..Amma dai yanzu inaga kada abari tasan Abbin aure zaiyi kusa.......

Inayah dake bakin kofar shigowa dasuka Bari a bude Zata shigo
A Rikice qafafunta na rawa tace"

Aure Kuma?

##MAMUH#
#HOT/LOVE/ROMANCE
#MAJEED& INAYAH









_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya👇
07040727902

MTN card👇
09134848107[11/9, 11:49 AM] +234 816 828 4180: *_52_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
Da sauri suka kallo kofar lokaci daya atare cikin mamaki da fargaba.

Anty Hafsat ce tayi saurin tasowa tana kokarin riqo hannunta su qaraso ciki tana cewa"

Yaushe kika dawo Inayah?

Bata amsa tambayar ba sbd batama wani gane me Anty Hafsan ta fadaba qafafuwanta na rawa zuciyarta na bugawa da qarfi tace"

Anty Hafsat abbi ne naji kuna maganar zaiyi aure fa?

Kinga Inayah zauna muyi maganar a natse ba abinda kikaji din bane wata maganar muke......

Kasa Zama tayi ta tsaya tana kallon umma yaganah da duk tayi wani iri sbd damuwa wadda take bayyane qarara a kan fuskarta

Take taji wani mugun tashin hankali da 'daci na cika maqoshinta zuwa bakinta da qyar ta tattaro yawu tace"

Anty Hafsat fuskar umma yaganah ta nuna tana cikin damuwa
Karki wani boyemin ku fadamun Gaskia idan aure Abbi zaiyi Ni insani..

Yanayin yanda tayi maganar muryarta a harde da tashin hankali da firgici yasa umma yaganah sauke numfashi tana dagowa ta kelleta dakyau cikin sanyi ta janyo hannunta tana cewa"

Zo ki zauna Kuma ki nutsu hafsat Tai Miki bayanin komai banason hayaniya ko tashin hankali iya maganace kawai tunda ba auren aka Riga anyiba.

Wani nauyi kirjinta ya qara Mai tsanani hartaji numfashinta na Neman toshewa daqyar Anty Hafsat ta zaunar da ita suka kalleta su duka atare cikeda damuwa.

Umma yaganah ce taci gaba da cewa"

Kofa nutsu karki jawowa kanki ciwo nafada Miki bakomai bane Dan yaqara auren tunda dama ai kinsan koba yanzu ba Dole MAJEED zaiyi aure wata Rana tunda ke naki auren bawani daukansa aure kukaiba kinata shirmen sagarta da shagwaba kin kasa tsayawa kisan me kikeyi
Mahaifiyarsa kuma ba tsayawa zatayi tana kallonsa Yana garariba Babu aure ga manyanci na Neman cimmasa.

Anty Hafsat ce ya karbi zancen da cewa"

Ko ahaka dai ba komai bane Inayah
Kishiya kaman Dr farhat ai ba Zaki daga hankalinki ba tunda kinsan halinta tasan naki Kuma kaman yanda umma yaganah tace baa dauraba karki saka damuwa tun yanzu........

Kasa riqe numfashinta dake kokawar toshewa tayi sbd maganganunsu dake fasa zuciyarta

29 / 43