Kurkukun Kaddara Final StepComplete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   81 / 107

240K to 243K   out of 319.4K words

sun saki baki da hanci, sunata kallonta, surar jikinta tayi matukar jan hankalin su, kamar su kai mata hari sai faman hadiyar yawu su ke yi kamar wasu mayu..


Sautin highheels din kafarta Ya cika kunnuwansu kwas! kwas! kwas!! Saboda hall din yayi tsit ko tari ba kaji kowa ya nabba'a yana kallon Unaisah yayin da take tunkarar Stage still da ɗan gudun ta.


"Sis, Kin manta da hularki! ..."


Muryar Batool ce ta katse mata hanzarin ta, a rude taci burki, sumar kanta tayarfo ta gaban forehead dinta, sai haki takeyi tana zazzare gray eyes dinta dara dara..

Kunya ta hana ta dubi mutanan da ke kallonta, duk ta kame kanta kamar marar gaskiya..

Ƙarasa shigowa ciki Batool tayi jikinta sanye da black abaya, ta saka niqab akan fuskarta, cikin sauri ta nufi Unaisah ta daura mata mortarboard din asaman kanta.


"Thank you sis.." ta faɗa a wahalce kafin ta dubi admins din su adabarbarce tace..


"Ina bada haƙurin makara da nayi.." murmushi kowan nan su yayi su kansu suna alfahari da ita komai nata na burgewa ne.


Dean yace"kinyi laifi Unaisah, bakizo da wuri ba, kin bar mu munata kwala kiran sunanki, makoshinmu duk ya bushe, don haka dole mu hukunta ki"

arude tace"am sorry sir na gane kuskure na bazan ƙara ba ." ta faɗa tana kama kunnanta..


Photographers din dake a gurin har sun fara daukarta hotuna da videos, sautin cameras din su ya cika hall din ƙyat! ƙyat!! hasken camera duk ya kashe mata idanun ta, tunkan abasu iznin su ɗauka, ga dukkan alamu ta tafi da imanin su..

Da hannu vice dean ta nuna mata inda zata tsaya murya na rawa ta furta"thank you ma'am"

ta hau kan stage din daga gaban mic ta tsaya, all eyes on her.

Dean da kanshi Ya mika mata ƙyautarta tare da certificate din ta, cikin girmamawa tayi masa godiya.

Students sunata kiran sunanta, waving ta dinga yi masu tana yin tsadadden murmushin nan nata.

Calmly ta soma yin speech cikin nutsastsiyar muryarta

"Alhamdulillah, thanks be to Allah for showing me this day I've been waiting for I'm incredibly happy I'd like to thank those who supported me, including my parents, my mentor, and my teachers, thank you very much, May God reward you with the best of his blessings"

kowa dake a gurin ya nutsu yana sauraran speech dinta, yanayin yadda take magana cikin harshen turanci ba karamin tafiya tayi da su ba, muryarta kamar ana busa sarewa don dadinta, wasu har lumshe idanunsu su ke yi saboda yadda take ratsa kunnuwansu, gashi tana magana dimples dinta na lotsawa, in ta yi murmushi ko ta yi dariya ba ƙaramin Jan hankalin su ta ke yi ba.

Bayan data kammala jawabin ta.


Commissioner of Education ta nemi ganawa da iyayen ta saboda ta jinjina masu bisa ga kokarinsu na tarbiyantar da yar su.


"Iyayena basu halarta ba.." ta fada tare da sunnar da kanta kasa, kowa ya shiga damuwa da jin abun da ta faɗa, azaton su wani abunne ya faru daya hana su zuwa.


"Meyasa? Ko wani uzirin ne Ya ruƙe su? Amma ya kamata ace sun zo ta ya ki murna" vice ce ta fada.


"hidima ce ta hanasu zuwa.."


bata ƙare maganar ba, Batool ta yi su6ul da baka gurin furta

"hidimar auranta... "

dafe kai tayi da tafin hannunta, tana aikawa Batool harara a fakaice, wato ta kwafsa mata, gaba daya hall din suka sanya shewa da tafi kamar zasu fasa bangon hall din..

Muryoyin students suka cuka kunnuwanta.


"Unaisah wanene zaki aura? Wani me nasaran ne zai mallake ki"?


"Yaushe ne bikin naki?


Gaba daya sun cika ta da tambayoyi kamar yan jarida ta rasa wa zata fara amsamawa.


"Listen pls.." Dean ne ya faɗa nan take kowa yayi shiru.

Dubanta yayi"Unaisah meyasa baki fada mana kin kusa yin aure ba uhym? Wani mai sa'ar ne zaure ki? Meyasa mu ba'a gayyace mu ba"? ya fada da fara'arsa.

ga dukkan alamu kamar sun manta abunda su ke yi, jin maganar auren ta yasa hankali ya koma kanta.

Kunyace ta kamata, ta sanya tafukan hannayenta ta rufe fuskarta, hakan ba karamin dariya ya basu ba, cike da nishadi kowa ke kallonta kamar sun samu tashar bollywood..

"Ke muke sauraro Unaisah.."

zolayarta suka dinga yi..

Dakyar ta samu kwarin gwiwar furta sunan shi.

"Dg Owais... " cike da mamaki kowa ya zare idanu yana kallon ta, suka kama tafa mata..

Manyan Baƙin dake a gurin suka shiga jinjina kan su aransu suka ayyana shine daidai da ita, don mallakar hamshakiyar mace irinta sai babban goro magogin karfe 👑


"I invite you all to my wedding next week, after Friday prayer, at the Sheikh Imam Malik mosque here in Abuja"


("Ina gayyatar ku baki daya daurin aurena a mako mai zuwa, bayan sallar Juma'a, a masallacin Sheikh Imam Malik da ke nan Abuja)

bata kare maganar ba ya katse ta da cewa "There's no invitation card?"


Tana noƙe kai cike da jin kunya tace "Sorry Sir, I forgot to send the invitation to our school WhatsApp group"


Vice dean tace "Okay idan kin koma gida, kada ki manta ki tura mana, don ba zamu bari ayi babu mu ba, duk da bikin na manya ne amma tun da ɗalibar mu za'a aurar toh damu za'ay komai sai munga abun daya turewa buzu nadi"

cikin zolaya ta ƙarashe maganar, dariya suka sanya gaba ɗayan su.


daga bisani aka kikkira sauran graduates din da suka tantanci ya bo aka karramasu


Daga bisani photographers suka cigaba da ɗaukarsu hotuna, sunyi da malaman su, sunyi da bakinsu, sun ku ma yi da yan uwansu dalibai, kowa burinshi ya yi hoto da Unaisah musamman special guests din nan ta tsone masu ido, saukin ta ɗaya sunji wa zata aura, da ba abun da zai hana su addabeta, ita Batool da yake ta rufawa kanta asiri ta sanya abaya da niqab bata ja hankalin kowa ba, da itama sai sunyi rubibinta saboda kyawun surarta.



~________________________________🌹~


Students ne tsaitsaye agaban katafaren Pool din makarantar sun kewaye Graduates.

photographers sunata daukarsu hotuna.

Graduates Suna ta wurga hulunansu saman Iska cike da nishadi.


Kwatsam sukaga Unaisah ta wurgar da gifts dinta Cikin pool ta juya cikin sauri ta nufi parking space, gabansu ne ya fadi ganin abun da tayi kuma kwata kwata bata waiwayo ta dubi kowa ba..


Sajeed ne ya daka suka ya fada cikin ruwan ya dauko gifts din da ta jefar.

Batool da sauran yan uwansu suka bita da gudu suna ƙwala mata kira, Unaisah! Sis! Ukhty!

ko waiwayon su batayi ba, A kan ground floor ta jefar da graduation gown dinta da sauri Batool ta ɗauke mata ita.


Ta kuma jefar da hularta haris Ya dauke ta, gaba daya sun rude sun rasa gane meke damun ta kamar mai ta6in hankali..


"Unaisah ki tsaya pls! Ina zaki je ba'a kammala party ba! Meke damunki ne? Kina cikin hayyacinki kuwa? Baki ga abun da ki ka yi ba"?



Ko sauraron su batayi ba, kuma tana jin su.


"Pls Unaisah ki bi a hankali, kada ki fadi, takalmanki zasu iya kayar dake.."

Babu alamun zata tsaya, bodyguard din da ya kawo su yana atsaye bakin motorsa Yana jiran su, tun lokacin da ta fara zuwa School Chief Owais ya bashi aikin kula da su, don ya runka kai su school ko in zasu fita outing ita da Batool kwata kwata basu hawan Bus.

Yana hango ta yayi saurin buɗe mata cardoor ta shige ciki ta zauna ta kulle kofar, tare da kifa kanta saman laps dinta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya! daga gani akwai wata damuwa da ke cin zuciyarta.."

"Ma'am, what's wrong? Why are you crying?"

Bodyguard din ne ya tambaya yana lekenta ta saman gilashin tagar da ke a bude.

Batare data dago ta dube shi ba, cikin shesshekar kuka tace"am ok, ba abun da ke damuna, ka kaini gida kawai, banaso na kara minti daya a cikin school din nan.."

"Amma yan uwanki suna ta kiran sunanki"?

"Kada ka sauraresu, ka shiga kawai ka kai ni gida.." duk baiji dadin halin da take a ciki ba, lafiyalou ya kawo su baisan meya bata mata rai ba.

Shiga ciki yayi ya zauna a driver's seat, kafin su Batool su karaso tuni motar ta fuce daga gate din makarantar.


akan idanun su, kwata kwata basu ji daɗi ba, ko celebration din ba'a kammala ba ta tafi tabarsu da kayayyakin ta, mutane sai tambayarsu su ke yi Ina Unaisah? sai dai su ka yi karyar anyi mata kiran gaggawane shiyasa ta tafi, gaba daya suka kasa zama makarantar, saboda hankalinsu yaki kwanciya da halin da Unaisah ta shiga farat ɗaya..

A hankali Motar ta kunno kai cikin harabar katafaren Gidan daddynta dake a cikin Imam Estate.

Drivern nayin Parking, ta buɗe motar, cikin sauri ta nufi main falo, tana dira kafarta ciki, kunnuwanta su ka jiyo mata muryoyin su.


"Ni wallahi tun farko banso aka sanya bikin nan sati uku ba, yayi kusa, yanzu gashi abubuwa suna nema su haɗe min"

"Dan Allah ki daina damuwa, meye a ciki toh? mu fa namu gyara amarya ne kawai, Owais ya riga daya yi mata komai"

"Hmmm ba zaku gane ba"


"Da yaushe ne za'a kawo Invitation bags din"?

"Yau ne fa, ɗazu nayi waya da daddynta ya faɗa mun sunyi magana da Owais, wai daga Companyn su zahra za'a kawo kayan"

"Allah ya kawo su lafiya"


"Bari na sake kiran Aneelerh naji Ya jikin nata! Nasan ma ba lallai yau ta samu damar zuwa ba kinsan me laulayin ciki" da zolaya ta yi maganar..

A hankali ta dan saci kallon su da idanunta wadanda suka kaɗa jawur..


Su uku ne zaune kan Sofas, Mommynta da Ummi tare da Aunty Danejo, basu daɗe da dawowa daga kasuwa yin siyayyar kayan abincin biki, a falo suka baje kan rug suna huce gajiyar su.

A hankali ta ɗan zukunna tare da zame takalmanta daga kafafunta, ta ruƙe su a hannayenta don kada suji sautin tafiyarta, Cikin sanɗa ta dinga tafiya har ta samu ta haye upstairs ta nufi bedroom dinta ta shige, jefar da takalman tayi kan floor, Idanunta cike tab da kwalla ta nufi gaban gadonta, ta zukunna tare da janyo drewer chest din jikin gadon, bakomai ne a ciki ba face kyaututtukan da ya ke bata, anan take ajiye su, ramadan boxes, Eid gift boxes, Hajj gifts, umra gifts.

Cikin shekarun nan ya bata gifts sun kai guda ɗari Uku.

Runtse idanunta tayi gam, hawaye suka dinga sintiri kan kuncin ta, ta rasa ya zatayi da zuciyarta? Meyasa bazata daina azabtar da ita akan son abun da bazata taba samu ba?

_Ka hanani bacci, ka hanani sukuni, ka hana wani ya maye gurbinka a cikin zuciyata, ka mutu ban huta ba, ka zamar mun ƙarfen ƙafa, tayaya zanyi aure da jarabar son kasancewa da matacce? Ya ilahi_

Zancen zuci ne takeyi.

Ta rasa gane ya akai hannun agogo ke nema ya koma baya! Meyasa saida auranta ya rage saura kwanaki kaɗan zuciyarta ta ke matsa mata akan son matacce wanda babu shi araye?

Why why why...!!!

da ƙarfi ta furta, tare da rufe drawer din, ta kifa kanta jikin gadon, ta gaza yarda itace zatayi aure ba tare da shi ba! Farin cikinta ragagge ne, duk nasarar data samu batare da shi ba faɗuwace a gareta.


Da tunaninsa take samun kwarin gwiwar gudanar da komai, kuma da tunaninsa take jin dadi.."

duk don ta cire shi a zuciyarta yasa ta rabu da komai na shi da take da shi amma ina kamar tana kara rura wutar sonshi a zuciyarta, bata da hotunanshi amma idanunta sun gaza mantawa da suffarshi, kwakwalwarta ta haddace memories din su, wata irin kasalace ta baibaye ta, dakyar ta lalla6a ta haye kan gadonta, ta janyo pillow tayi hugging dinsa a kirjinta sosai, ta dan lumshe idanunta, eye lashes dinta sun jiƙe sharkaf da hawaye.




_Kyakkyawan murmushin shi, Kallon shi, dariyar shi, tafiyar shi, sumar kan shi, hancin shi, la66ansa, kyawun surarsa gaba daya, komai nashi takeso ta sake gani, tayi mahaukacin kewarshi, tayaya zata iya ganinsa bayan ya mutu? Wallah ji take da ace ana iya dawo da wanda ya mutu araye da ba abun da zai hana ta ki dawowa da shi._


Numfasawa tayi tana mai kara ƙanƙame pillow din data matse a kirjinta, ji take kamar shi ne ta rungume.

Farkon haduwarsu ta fara tariyowa.

At first time datayi tozali da shi duk da tashin hankalin da take a ciki saida ta razana da ganin kyawun shi.

Nutsuwa tayi tana cigaba da tariyo komai daya faru a tsakanin su tun a gidan kurkukun ƙaddara.

Rana ta farko da jikinsu ya fara haduwa dana juna, ita kadai tasan me taji but,taji wani abu mara misaltuwa duk da ba wani hankali gareta sosai a lokacin ba Amma abun yana a ranta...



_"Kai wani irin jaki ne? ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko"?_


_"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."_


Tunawa da waɗannan maganganun da suka ta6a yi ne yasa batasan sa'adda ta ƙyalƙyace da dariya ba...


"My man, inama ace kana araye, da na nuna maka baby Angel dinka ta girma, itama tayi abun nan irin na yar gidan daddy da ka ke muradin ganin ta da su.."


ta faɗa cikin karyayyar murya kafin ta ci gaba da tunano abubuwan da suka faru a tsakanin su.


_the sounds is soothing me, I can't stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_

"Dame zaka biya ni idan na koya maka"?

"I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want"

"does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?"

"yeah"

Murmushi tayi tunawa da wannan firar ta su.

_"My man na soka kamar raina, na so mu rayu a matsayin ma'aurata, dana nuna maka irin masifar son da nake maka, zan zama baiwarka, in dauki dukkan ɗawainiyarka, in mallaka maka kaina kamar bana sona, meyasa ka mutu ka barni? Meyasa burin mu bai cika ba? Har yau ina danasanin tursasa maka da nayi duk da nasan wayou na ko dabarana bai isa ya sauya abun da ya ke rubutacce a cikin littafin kaddarar ka.."_


ita kaɗai take ta sambatunta, in ta fara tunanin shi saita shafe awanni tanayi kamar mara aikin yi... 💔


~__________________________________💫~


Suna tsaka da fira, sallamar Batool ta katse su, a tare suka dago suna kallon ta yayin da take shigowa hannunta ruke da Graduation gown din Unaisah, sajeed da Haris suna abiye da bayan ta, kowannan su Ya ruke kayan Unaisah data jefar, a rude Benazir da Ummi suka mike suna duban su.

"Babe! Ina kuka baro Unaisah din? Wannan ba graduation gown din ta bace"? Ummi ce Ta faɗa tana nuna rigar hannun Batool.


Sajeed ne ya labarta mata abun daya faru, hankalinsu Ya tashi..
Batool Tace"ummina bata dawo gida bane"?

"Bata dawo ba Batool, bamu ganta ba, amma abun da daure kai? Kamar dai mai tabin hankali, babu abunda akai mata kuma?

Ta fada da ruɗu akan fuskarta.

Damuwa ce ƙarara akan fuskar Benazir"Ku fada min gaskiyar abun daya faru! Ko dai ta samu sa6ani da wanine a cikin ku"?


"Wallahi Aunty Benazir babu abun da akayi mata.."

"To ina ta tafi ne"? Ta kuma tambaya.


Ummi tace"tun da ranta a6ace ya ke zai iya yiwuwa ta shigo tagan mu saita lallaba ta wuce ciki, muje mu duba dakin nata.."


Cikin sauri suka nufi bedroom din ta.

"Babyna Kina a ciki"? benazir ne ta fada tana bubbuga ƙofar dakin.

Daga ciki suka jiyo voice din"mommy, am sorry na dawo ban fada maku ba, bana jin dadi ne amma da sauki yanzu. "

"Haba Unaisah, wani irin rashin lafiyane zai sa ki watsar da kayan graduation dinki"? Shiru tayi saboda bata da amsar da zata ba..

"Zoki buɗe min ƙofa tunkafin ranki ya 6ace" saukowa tayi daga kan gadon ta buɗe ƙofar, gaba ɗaya suka bi ta da kallo..

Daga yanayin ta suka fahimci bata da lafiya.

"Me ke damunki"?

"Mommy, zazza6i ne amma na sha magani" shafa wuyanta Benazir tayi jin da zafi yasa ta yarda da maganarta"Allah ya baki lafiya" ameen ta masa, danejo ma tayi mata sannu da jiki..

Ummi tace"Allah ya baki lafiya, ki koma ki kwanta, ki samu kiyi bacci"

Amsawa tayi da toh.

Ummi ta dubi Batool "Babe, ki zauna tare da ita, ki kula mana da ita" amsawa tayi da toh.


sauran su ka yi mata fatan samun lafiya.

Sajeed da Haris suka mikama Batool kayan Unaisah, bayan ta kar6a suka nufi ciki ita da Unaisah



Bayan ta ajiye mata kayan a cikin closet din ta, ta juyo ta dubi Unaisah dake a kwance kan gado.


"Sis, badai har yanzu baki daina wannan tunanin ba"? Ta faɗa da damuwa ta zauna kusa da ita tana kallon fuskarta da tayi jawur saboda kukan da tasha.

"Batool na rasa ya zanyi, kwanakin nan kamar ana sabunta min kaunar shi..." ta fada tana jan majina..

"ke kadai kika san da wannan maganar, pls amana kada ki fada ma kowa amma bana jin zan iya zaman aure, saboda tunaninsa da nakeyi zai iya jaza min matsala..." idanun Batool tuni sun cicciko da kwalla, tausayin yar uwartata ne ya kamata.

"Ba irin addu'ar da banyi ba akan Allah ya cire min son shi amma babu abun daya sauya, Ina azabtuwa Batool" ta fada tare da cusa kanta cikin pillow.

Girgiza kai Batool tayi hawaye har sun fara sauka kan kuncin ta"bani da maganin abunda ke damunki, al'amari ne mai girma Unaisah, nima yafi karfina, zaman aure bazaiyi yiwu da tunanin son kasancewa da wani wanda babu shi araye, amma menene mafita"?

"Babu mafita Batool"

"Baki tunanin idan muka faɗawa su mommy zasu nema mana mafita" a firgice ta dago tare da zare idanunta cikin na Batool

"ukhty kinsan me kike fada kuwa? Wannan ba mafita bace, tayaya ma zan iya fada masu? Abun da kunya kuma ba zasu dauki maganata serious ba, zasu ce bani da hankali ne"

Jinjina kai Batool tayi"kin faɗi gaskiya Ukhty, to ko in fadama daddyna" wani kallo mai kama da harara Unaisah tayi mata, Batool ta kwashe da dariya..

"In haka ne nima inje in faɗawa daddyna mana ..' dariya su ka yi..

"Kinsan wani abu, pls mu cigaba da addu'a, babu abunda ya gagari ubangijinmu, in sha Allah

81 / 107