Author : Boss Bature Category : Complete Novels
bai faru da ni ba, sai wannan ne zai sa in fita hayyacina har in kasa gane wanda ya aikata mini? Wannan azzalumin shine ya sadaukar da ni a kurkukun, kuma shine ya yi ma mahaifiyata asiri a ranar da ta haife ni ta tafi ta bar ni tsawon shekaru ba a san in da take ba saboda tasan wani sirrin shi da ya danganci kurkukun ƙaddara, shine kuma ya yi ma Uncle ɗina Shureim tare da makwabciyar su asiri saboda ta ce bata son shi Uncle ɗina take so sannan kuma yana jin haushin mahaifinta Sheikh Imam. Shi Elder ne! Duk abun da aka zayyana yana aikatawa wallahi..." Kuka ne ya ƙwace mata ta duƙar da kanta, duk da yadda ta yi maganar da tsawa har tana nuna Alhaji Musan da hannu ya sa6a ma dokar kotun amma alƙalin ya kasa dakatar da ita, gaba ɗaya kotun ta karaɗe da hayaniyar mutane, ƙarfin halinta ya matuƙar burge mutane, kuma ta ba mutane tausayi, hatta alƙalin ma ta bashi tausayi, umarnin a mayar da ita wurin zamanta alƙalin ya bada, kusan a tare Benazir da Owais da Shureim harda kakanninta da ƴan uwanta prisoners duk suka miƙe don su tarbe ta, kotu fa ta harmutse da hayaniya, har saida alƙalin ya bubbuga gavel ɗinsa tare da ambaton, "Order, order!" Sannan kotun ta daidaita, daga haka alƙalin ya sanar da kotu zata tafi hutu na ɗan wani lokacin kafin a dawo a ci gaba da sauraran shari'ar.
Bayan wa'adin da alƙalin ya ɗauka ya ƙare aka dawo zaman ci gaba da sauraran shari'ar. A lokacin lauyan masu ƙara ya buƙaci Benazir, Batool, Shuraim, Ummi da kuma Sheikh Imam duk suka fito ya yi masu tambayoyi, duk suka amsa mashi saidai ba komai da ya faru da su suka faɗi ba sun bar wasu abubuwan matsayin sirri, haka shima lauyan dake kare Alhaji Musa ya yi masu tambayoyin ba kamar Batool ya fi yi mata tambayoyi game da komawar su kurkuku, a lokacin har saida alƙali ya buƙaci a gabatar masa Dr Mark, Chief Owais ne ya yi ma kotu bayanin cewa ya gudu amman suna akan binciko shi za su samo shi su kawo shi kotu shima da sauran likitocin dake da sa hannu a case ɗin.
Ƙarshe dai sai da aka ƙure lauyan alhaji Musa saboda tarin hujjojin da aka gabatar a gaban kotu waɗanda ke nuna yana aikata duk laifukan kuma yana cikin elders, tun kan a dawo kan Pravin ya tabbatar ma kotu yana cikin elders don yasan shima za a samu hujjojin da zasu tabbatar da shi ba kamar da ya ga harda vedio recording ɗin alhaji Musa na cikin Cell ɗin hukumar Isod aka kunna ma alƙalin in da wasu maganganun da ya yi suka tabbatar da laifukan da ake tuhumar shi, ya san shima sun yi maganganun da Owais shiyasa ya saduda, amma ya ce ma alƙalin wllh Baba Obie ne ya yaudare shi ya saka shi cikin su ba da son ran shi ba.
Bayan sauraran tarin hujjojin lauya mai ƙara, alƙali ya tambayi lauyoyi masu kare waɗanda ake tuhuma kan ko suna da sauran abun da za su ce,
Gaba ɗaya wutar su ta ɗauke, saboda basu da wani ƙwarin gwiwa ko hujjar da zasu iya kare su, gashi akwai masu son su nemawa dattijon arziƙi sassauci saboda da yawansu mutanan da suke mutunci da shi ne, da ƙyar wani bayerabe daga cikin su ya yi ƙarfin halin miƙewa ya ce,
"Your Honor, while we acknowledge the severity of the crimes committed, we urge the court to consider the defendants ages, health, and social status. We request leniency in sentencing."
(Ya mai girma mai shari'a, yayin da muka amince da girman laifuffukan da suka aikata, muna roƙon kotu da ta yi la'akari da shekarun waɗanda ake tuhuma, da lafiyar su, da kuma matsayin su na zamantakewa. Muna neman a sassauta hukunci) Ya faɗa tare da komawa ya zauna.
Bayan nazarin da Alƙali ya yi, ya ɗan numfasa na wani lokaci, kafin ya ɗago ya dubi ilahirin mutanen dake a kotun.
Cikin kakkausar murya ya furta.
"I have reviewed the evidences presented in this case, and I find the defendants guilty on all counts, The crimes committed are among the most heinous and reprehensible imaginable..." Karanto hukuncin da kundin tsarin dokokin ƙasa ya tanada ga dukkan laifukan ya yi kafin ya dunƙule hukuncin da kotu ta yanke masu ya ce,"The court hereby, sentences each of the defendants to, Life Imprisonment without the possibility of parole (ɗaurin rai da rai batare da sakin layi ba) a cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa."
Sallallamin da jikokin Obie ke yi ne ya cika kotun, ba ka jin sautin komai sai na, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.!
Gaban Elders ya shiga faɗuwa cikin firgici da kiɗima suke ƙara zazzare jajayen idanunsu, ganin yadda reshe ya juye da mujiya, abun da suke yi ma wasu yau sune za a yi mawa, kurkukun ƙarƙashin ƙasa da alƙali ya faɗa wani kurman kurkuku ne saboda tsaronsa da uƙubarsa ya sa mutane suke yi masa laƙabi da kurkukun azaba, saboda mawuyacin abu ne mutun ya zarce watanni batare da zafin jail ɗin ya lahanta fatar sa ba, ƙuntatarsa kamar ƙabari, baka ganin kowa babu haske cikin duhu, ɗan hasken da za'a iya samu na wasu hudoji ne guda uku da ke a saman jail ɗin, dai dai da wanda zai kawo maka abinci ba zaka gansa ba, ta wata ƙaramar ƙofa da ke a jikin ƙofar jail ɗin su ke zuro maka kwanan abinci, kai kanka ba zaka san an kawo maka abinci ba, in har ba ka jiyo motsin buɗe ƙaramar ƙofar ba, daga kai sai halin ka a cikin jail ɗin nan, ba shige ba fuce, da yawa waɗanda ake kaiwa cikin kurkukun miyagun ƴan ta'adda ne masu haɗarin gaske, kamar Elders ɗin dai.
Alƙali bai dakata ba ya ɗaura da cewa, "Dukiyar su da suka mallaka ta haramtacciyar hanya, Kotu ta mallakawa waɗanda abin ya shafa.." Ya faɗa yana kallon bangaren da fursinonin Kurkukun Ƙaddara suke a zazzaune kan kujeru sun yi shiru sun nabba'a, fuskokinsu ɗauke da murmushin farin ciki, kamar su zuba ruwa ƙasa su sha, sun ji daɗin hukuncin da aka yankewa Elders, ransu fari tass, ba don Dg ya gargaɗe su akan su nutsu ba in an shiga zaman shari'ar, da ba abun da zai hana su fasa ihun murna.
"Ƙadarorinsu da suka mallaka ba bisa ƙa'ida ba, za a yi gwanjon su, abun da aka samu gwamnati zata yiwa ƙasa amfani da su..."
Alƙali Salahudeen bai dakata ba, ya ci gaba da cewa, "Bayan haka kotu ta soke duk wata daraja da muƙami na su, bugu da ƙari, kotu ta bayar da umarnin a saka sunayen su a cikin rajistar masu aikata laifuka ta ƙasa!"
Alƙali Salahudeen yana kai ƙarshen maganar shi, ya damƙi gavel ɗin gefensa mai kama da metal hammer ya buga da ƙarfi saman table ɗin gabansa,
(shari'a ta ƙare) Zauren kotu ya harmutse da hayaniyar al'umma, masu kuka suna yi, masu murna suna yi, masu 6acin rai suna yi, kowa da abun da ya dame sa.
Prison Officers tare da Soldiers ne suka tasa ƙeyar Elders suka fito da su harabar kotun, mutane daddabe da su, ƴan Jarida sai neman tattaunawa suke yi da iyalansu sun ƙi basu haɗin kai saboda tashin hankalin da suke a ciki.
A wata ƙatuwar Prison Van za a shiga da su, wasu har sun fara shiga, Musa yana ta gurnani yana tirjewa kamar 6auna, bai aune ba, ya tsinkayi muryar hajiya Sarah a kunnansa. "Ba na ta6a faɗa maka ba? In har akwai mai cutar wani tsakanin ni da kai Allah zai yi masa sakayya..." A firgice ya waigo yana fitar da hucin 6acin rai.
Tana a tsaye ta sanya baƙar abaya da niƙab.
A hankali ta zame niƙab ɗinta, ta watsa mashi kallon ƙasƙanci. "Hakkin Unaizah ne ke bibiyarka, la'ananne... "
Ta faɗa tare da tofa mashi kakin majina saman fuskar shi, ya yi wata zabura kamar zai cafkota sojoji suka rurruƙe shi, tare da ingiza shi cikin motar kamar dabba sai waiwayonta yake yi cikin ƙunci da baƙin ciki.
Yana tsaka da waiwayon ta, ya hango hajiya Layla a bayanta bakinta washe kamar wadda ta tsinci haƙori, ɗaga mashi hannu ta yi, "Allah ya raka taki gona Musa, Allah ya ƙara nauyin ƙasa, sai mun haɗu a filin hisabi na lahira.."
Ta ƙyalƙyace da dariya, wani irin baƙin ciki ne ya ziyarce shi kamar ya haɗiyi zuciya.
"Ina maka fatan sauka ƙabari lafiya, kar ka wani damu zan ci gaba da kula da mommyna.."
A ɗimauce ya kai idonsa ga Omar, yana tsaye bayan Chief Owais, wlh kwata kwata bai lura da su ba a kotun saboda bai ɗaga idonsa ya dubi kowa ba ashe duk sun hallara.
Unexpected ya tsinkayi muryar Sheikh Imam Malik a cikin kunnansa. "Musa ina tayaka murnar kar6ar sakamakon zunubin ka na duniya.. "
Cikin 6acin rai ya wurga idanunsa gurin da Imam Malik ya ke, gabansa ne ya faɗi ganin Ummi da Shureim sun saka Imam Malik tsakiya, daga gefen su Batool da Unaisah ne tare da Benazir, sai faman washe baki suke yi.
Ya Ilahi! Kamar ya fasa ihu yake ji saboda baƙin cikin da ya turnuƙe zuciyarsa, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi magana Isod soldiers suka turmuƙa kan shege bayan motar, suna juyo kururuwar baƙin cikin da ya ke saki.
Daidai Lokacin da Isod soldiers suka fito da baba Obie suna ƙoƙarin shigar da shi bayan motar, ƴa'ƴansa da jikokinsa suka kewaye shi, suna ta kuka kamar ran su zai fita.
Ya dinga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, cikin karyewar zuciya, kallon bankwana yake musu, saboda ya san ba zai sake ganinsu ba, wannan tafiyar bata dawowa bace ta mutuwa ce.
Babu Saratu a cikinsu, a gida suka kulle ta a ɗaki, Momma ma bata halarci kotun ba, da wasu daga cikin jokokinsa.
Da raunannun idanunsa ya dubi ƴa'ƴansa cikin sanyin murya ya ce, "Ku yafe min, yawancin yaran da nake sadaukarwa na ku ne, wataƙil idan kuka yafe mini in samu salama a cikin Zuciyata"
A tare suka haɗa baki gurin furta, "Zamu yafe maka, amma ka fara amsa buƙatar mu, ka musulunta baba, muma shi kaɗai ne fatan mu, ko mun samu mu dinga saka ka a addu'ar mu."
Girgiza kanshi ya yi zafafan hawaye na sintiri kan fuskarshi ya ce, "Kuma kun sani, tuba na ba zai kar6u ba a wurin Allah, ban tuba ba saida asirina ya tonu? Bayan na sani na take sani?"
Roƙonsa suka dinga yi suna masa magiya kamar zasu haɗiyi zuciya, Sheikh imam Malik ya sanya baki ya ce ya taimaka ya amsa buƙatar ƴa'yansa shine abu na ƙarshe da zai yi musu a duniya, da ya san halin da ya jefa su da bai musa akan buƙatarsu ba, har yanzu suna son shi, kuma musuluncin da zai kar6a kan shi zai yi mawa, shi ba zai ce kar ya musulunta ba, babu wanda ke shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa, in Allah ya so shi da rahama sai ya ga ya samu sassauci.."
Kalamai masu tausasa zuciya Imam Malik ya furta masa, amma baba Obie ya kafe akan bakansa.
Sojoji suna ƙoƙarin su shigar da shi, kwatsam! Muryar Hajiya Saratu ta karaɗe kunnuwan kowa.
"Baba! Baba...!" A ruɗe ya shiga wurga idanunsa yana ƙoƙarin ya hango ta, kamar mahaukaciya, babu kallabi ko takalma a ƙafafunta, twins suna a biye da ita, hannayen kowan nan su ruƙe da mayafinta da takalmanta, ganin halin da take a ciki ne yasa mutane suka dinga darewa suna bata hanya don ta wuce, kowa ya razana da ganin Minister of Health cikin wannan halin.
Hankulan Yayyenta ya tashi, basu san tayaya ta buɗe ƙofar ɗakin da suka kulle ta ba, wallahi da gudu ta nufi baba Obie tana ƙarasowa ta rungume ubanta tana kuka, shima kukan ya 6alle masa, hankulan kowa dake a gurin ya dawo kan su, gwanin ban tausayi, baiwar Allah mace mai rauni, a lokacin ta fidda rai da shi, cikin shesshekar kuka ta ce, "Baba ka yi haƙuri, kulle ni suka yi a cikin ɗaki shiyasa ban zo ba, meyasa zasu hanani ganinka bayan wannan ne gani na ƙarshe tsakanina da ubana. Baba ka yi haƙuri ni dai na yafe maka duniya da lahira, Ubangiji Allah Ya yafe maka, kuma zan dawwama ina yi maka addu'a akan Allah ya yafe maka zunubbanka..."
Kalaman Saratu sun karya zuciyarshi, rungumar da ta yi mashi tasa ya ji sanyi a cikin zuciyarshi.
"Saratu, mahaifin ku ya ƙi kar6ar musulunci..."
Sheikh Imam ne ya faɗa yana daga bayanta.
Baiwar Allah ita sam ta manta baban nasu ba musulmi bane, hada guzurin cazbaha ta kawo mashi wadda zai dinga yin tasbihi da ita a cikin jail.
Maganar Sheikh Imam Malik ce ta tunasar da ita, nan fa ta fara roƙon shi tare da damƙa mashi casbahar a cikin tafin hannunsa ta dunƙule masa yatsunsa don kar ya yada ta.
"Baba na roƙe ka ka musulunta saboda tsoron Allah baba, ba don saboda mu ba, don Allah ka taimaka ma rayuwana..." Tana kuka hada majina, har lokacin bata raba jikin ta daga na shi ba.
Tunkan ta ji amincewar shi ta shiga karanto mashi kalmatusshahada, cikin karyayyar murya ya dinga amsa mata har ƙarshe.
Gaba ɗaya suka haɗa baki gurin furta, "Alhamdulillah, Allahu Akhbar..."
kwata kwata ba su yi zaton zai iya furta Kalmatusshahada ba.
Suna kuka suka ce, "Mun yafe maka baba, duniya da lahira, Ubangiji Allah ya yafe maka."
At lease ya samu sassaucin radadin da yake ji a cikin zuciyar shi ganin ya faranta masu.
Sheikh Imam Malik ya tausaya masu bai san sa'ar da hawaye suka fara zarya kan kuncin shi ba.
"Baba na canza maka suna, daga yanzu Imam zamu dinga kiran ka ba Obinna ba..."
Cikin kuka ta faɗa, murmushi ya yi, idanunsa akan fuskarta a lokacin ta ɗago da kanta.
Ya sumbaci goshin ta, ya miƙa ma Hateem hannu ya matso kusa da shi yana share ƙwallarsa, shima ya sumbaci goshin shi tare da hugging nasa, Sharafudeen ya matsa ya rungume shi, tare da sumbatar goshinshi, da sauri Deen da Lateef suka rungume shi, suma ya sumbaci goshin su, Abdul Razak ya matsa ya sumbace shi, Sir Mubarak ma ya je ya rungume shi sosai.
Owais dake kallon komai shima ya zo ya yi hugging nasa tare da sumbatar goshinsa, ƴan jarida da ke kallon komai sun ma kasa mayar da hankalinsu kan aikinsu, sai aikin share hawaye suke yi, basu ta6a ganin soyayya tsakanin Uba da Ƴa'ya irin wannan ba, kowa al'ajabi ya ke yi, duk irin cutarwar da ya yi masu amma basu daina son shi ba, wannan bakomai bane face Ikon Allah.
Cikin raunanniyar murya ya furta, "Allah Ya yi maku Albarka..." Ya mayar da dubansa kan Imam Malik ya ce, "A matsayina na mahaifinsu, na baka amanar su, na mallaka maka ƴa'ƴana, ka maye musu gurbina, ga autana duka na baku amanarta, ita kaɗai ce mace a cikin ku tana da rauni, don Allah Imam ka amshi tayi na ba don mugun halina ba... "
Cikin sanyin murya sheikh Imam yace,
"Na kar6a hannu bibbiyu Imam, zan ruƙe maka amanar su, In sha Allah bazan bari su yi maraicin Uba ba..." Murmushin ƙarshe Baba Obie ya sakar musu, daga haka sojoji suka shigar da shi cikin motar.
Wani irin kuka hajiya Saratu ta fashe da shi, ta zube kan gwiwowinta tana ambaton, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..!"
Cikin sauri yayyenta suka rurruƙeta tare da miƙar da ita tsaye, Hateem ya rungumeta a ƙirjin shi, suka haɗu suna lallashin ta cike da ƙarfin hali.
Suna a wannan halin, suka jiyo kukan Praveen kamar ƙaramin yaro, yana ta sambatu yana ambaton sunan Hajjaty da ƴa'ƴanshi, kusan a tare suka kai duban su kan shi, yayin da Prison Officers suka nufi ɗayar motar kurkukun, sai tirjewa yake yi, idanunsa jawur ya ke duban twins ɗinsa da Saratu da ta ɗago da kanta daga ƙirjin Hateem tana duban shi.
Haushin shi da tsanar shi ne ya cika zuciyar su, babu alamun sun ji tausayin shi.
Zaid ne kaɗai ya ɗan tausaya mashi har ya je gaban shi ya ɗan rungume shi, Sir Mubarak ya nufe shi yana zura hannu cikin trouser pocket ɗinsa ya zaro wasiƙar da Hajjaty ta bayar a bashi, ya zura mashi a cikin aljihun gaban rigar shi sannan ya ce, "Hajjaty ce ta bayar a baka, bata samu damar zuwa ba, tana a kwance gadon asibiti tana jinyar zuciyarta, idan ka samu halin karantawa ko a cikin jail ne ka daure ka karanta..."
Wata irin karayar zuciya mai haɗe da nadama ce ta riske shi, bai ƙara samun damar furta kalma ba, Prison Officers suka tura ƙeyarsa cikin Motar.
Iyalan Ɗan Iya ne kaɗai ba a samu wanda ya halarta ba, sun fi kowa fusata, dama can ba son uban nasu suke yi ba.
A kan idon kowan nan su motocin suka fuce daga arean kotun.
Kafin mutane su watse, Alƙali Salahudeen sai da ya nemi ganawa da ahalin Obinna, musamman ya zauna da su a office ɗinsa bayan ya bayyana musu irin halin da ya shiga na jin abun da Obie ya aikata, ya kuma jajanta musu sannan ya jinjinawa Owais da ƴan team ɗinsa bisa ƙoƙarin su na kamanta adalci da gaskiya.
Kafin barin su kotun, chef na gidan Owais wanda ke kula da ɗakin Natasha ya kira Owais a waya cikin tashin hankali ya faɗa masa cewa ya je kai mata abinci, ya iske ta kwance ƙasa rai hannun Allah, tana yin bleeding ta hanci da baki, yanzu haka sun garzaya da ita Obie Hospital.
Hankalin Owais ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hanzarce ya faɗa ma su Ummi abun da ke faruwa da Natasha, ya ce ma Sajeed da Sajeeda su shiga motarshi, a gaggauce suka shige cikin motocin su, a lokacin Sarah ta ji komai itama ta shiga motar Omar saboda ta ƙudiri aniyar sai ta ɗanɗana mata raɗaɗin da ta ji na abun da ta yi ma ƴarta Unaizah.
Lokacin da suka ƙaraso Asibitin bayan da suka fito daga motocin su cikin sauri suka nufi ciki.
Kaitsaye suka wuce ICU, suna ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin, sai ga Docs din dake dubata sun fito fuskokinsu babu annuri.
Gaba ɗaya suka ruɗe fargaba ta cika su.
Owais ya tambayi Doc din meke damunta? Ya