Kurkukun Kaddara Final StepComplete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   37 / 107

108K to 111K   out of 319.4K words

La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu munazzalim, wa'inna hu min sulaiman wa innasu bismillah....

duk tabi ta rude ta rikice duk wata addu'a data zo mata arai cikin hanzari take ambaton ta.

Har murza idanunta tayi don taga ko gizau ya ke yi mata amma koda ta gama goge idanun still babu abunda ya canza.

Cikin rawar murya ya furta"babu abun da zaki 6oye min Anila, Naji komai da kika faɗa a cikin wayarki, inaso ki faɗa min wani video ne na ana kuka gani? A ina kuka gansa? Naji kuma kin ambaci kin kosa su gama bincike su zo su kama ni su wanene? Me kuma nayiwa Ana da naji kina fada mata"? Ya jefa mata tambayoyin a jere..

zazzare idanu tayi tare da haɗiyar yawu ba tare data iya furta kalma ba, jin ta share shi yasa shi daka mata tsawar data razanar da ita a ruɗe ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Uncle wayar da kaji inayi ba dakai nakeyi ba, firar wani drama muke yi watakil kunnuwanka ne suka jiyo maka badaidai ba..."

bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"Karya kikeyi Anila, ko dai ki fada min gaskiya ko kuma inyi maki abun da baki ta6a zata ba..."

afusace ta juyo ta fuskance shi idanunta suka shiga cikin nashi, duk da shakkarshi da takeji hakan bai hana ta furta"ai ba tsoronka nake ji ba, maganar girma ta kare Uncle, mutuncinka ya zube kasa wanwar, wayar da ka ji inayi dagaske ne, nasan komai Uncle, kar nake kallonka, Allah ya tonu asirinka, Naga komai da idanuna balle kace zaka karyata magana ta, wallahi kasan Inda Ana take kawai ka fadamin Ina ka 6oye ta Idan ba haka ba hmmm"

babu alamun ya fahimci inda zancenta Ya dosa sai ma ruɗu daya mamaye zuciyarshi cike da tashin hankali Yace"wannan wani irin zancen banza ne Anila? Kina hauka ne? Meya haɗina da Ana? Kin bani ajiyarta ne da zaki tuhume ni akan 6atanta, anya kina a cikin hayyacin ki kuwa, Ko kin fara shaye shaye ne"?

"Ɗan Iya ba shaye shaye nayi ba, Ina Cikin hayyacina, Idan ma akwai wanda ya fara shaye shayen to kaine mutumin banza, mai fuska biyu..."waro idanu waje yayi cikin rudu ya ke kallon ta.

Dakyar yayi karfin halin furta"Har ni zakiyiwa kazafi Anila? Saboda tsabar rashin kunya da ta6ara ki kalli tsabar idanuna ki gaggayamin magana batare da jin shakkata ba? Wani video ne kike ikirari akai"? ta fahimci yafi damuwa dayasan videon menene suke magana akai.


Harara ta watsa mashi kafin tace"videon komai daka aikatawa Ana, kawai ka fada min Ina Ana take? Tana araye ne ko ka kashe ta"?

aruɗe ya daura hannu saman kan shi ya shafo Sanƙon kanshi tare da jan gemun shi yana faman zare idanunshi kamar na kwarton mazuru.

tsantsar al'ajabi ne akan fuskar shi, tayaya akai har Anila ta samu videon abun da yake aikatawa ana? Tayaya? Anya ba burga ta ke yi masa ba? A sanin shi babu cctv a gidansa.


"Ashe tun bayan da muka dawo gidan nan kake lalata da ana aduk lokacin da takeyin jinin Al'ada, kana amfani da sihirinka ka gusar mata da hankalin ta, sa'ilin da ta gane Allah ya fahimtar da ita komai tace zata tona maka asiri shine ka fara neman hanyar da zaka kawar da ita gudun kada ta jaza maka matsala"

bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Uncle ɗan Iya ya daka mata wadda tayi silar faduwar gaban ta.

Idanunsa sun kaɗa jawur kamar garwashin wuta, Uban goshin nan nashi sai naso yakeyi ya hada gumi kamar ba A.c adakin..

a hankali Ya cire glass din dake akan idanunsa Ya jefar da shi ƙasa, tare da sanya tafin hannunsa ya shafo ƙeyarsa har izuwa rantalin sa, gaba daya kansa ya ruɗe Anila ta rikita ƙwaƙwalwarsa..


Dakyar ya shanye mamakin shi ya furta"Anila zaki tabka babban kuskure na zargina batare da kina da ƙwaƙƙwarar hujja ba, Ni fa Uncle dinki ne kinsan wanene ni kinsan halina bansan wani shaidani bane Ya yi maki hudubar da har kika gasgata maganar shi ba, Ni bazan iya aikata rashin imanin nan ba, Ƙazafi ne kawai ake nema ay min..." bai ƙare maganar ba Anila tayi wata irin dariyar takaici


"Bayan kasancewarka Matsafi, Fasiƙi kai ɗin babban makaryaci ne...." ta faɗa cikin fusatacciyar murya tare da nuna masa kofar dakin da yatsan ta.

"ka fuce min daga ɗakina, Bana son ganin ka.."

"Ba zan fita ba Anila, ki zauna muyi magana ta fahimta, kada ki manta ni Uncle dinki ne, duk inda za'aje adawo, dole ki amsa min amsoshin tambayoyin da nayi maki! Wani video ne Ana tayi? A ina kika same shi, ke kika dauke shi da kanki ko kuwa itace ta bar abunda ta dauki videon, sannan bayan ke su wanene suka ka kalli videon.." bai kare maganar ba, ta zare mashi idanunta da suka kaɗa jawur cike da tsanar shi ta furta"bazan faɗa ba, Ka jira ka gani, wallahi dole ka girbi abunda ka shuka, har kana wani fadin kai uncle dina ne, to ai ko ubanane ya aikata abunda kayi wlh saina damƙa shi ga hukuma ta hukunta shi, balle kai karen kaɗa miya, karere a danginsu Abie, ai nasan komai, baku da wata alaƙa ta jini, tsintarka su kayi, wallahi jinin abie ɗina bazai ta6a aikata fasikanci da ka aikata ba..."

maganar Anila ta fusata shi, har baisan sa'adda Ya cije gefen tafin hannunsa ba.

"Cikin lalama ka fita kabar dakin nan, Idan ba haka ba zanyi maka ihun da kowa na gidan nan zai ji, Kuma idan suka tambayeni meke faruwa zan fada musu abun da ka aikata ne..."

harara ya watsa mata, ya juya ransa a 6ace Ya nufi kofar fita daga ɗakin, har ya daga kafa zai fuce sai kuma ya fasa ya tsaya cak, kwakwalwarsa na tariyo masa abun daya faru.

cike da takaici Ya daki jikin ƙofar, evil heart dinsa ta motsa ji yayi bazai iya ƙyale ta ba, tun da har tasan sirrinsa kuma ga dukkan alamu ta kai shi ƙara gurin hukuma, kwara kawai ya aikata abun daya dace.

Anila dake a tsaye tana kallon sa, wani irin faduwar gaba taji, ganin ya datse ƙofar dakinta, murya na rawa ta furta"me.. me.. me zakayi min..? Ba zaka fita ka bar min ɗakina ba? Wallahi zan yi maka ihu.. "

"kada ka kuskura ka tabani, bani kadai na kalli videon ba, zan iya rufa maka asiri amma idan ka cutar dani asirinka zai tonu kowa ya sani..."

jikinta na karkarwa ta soma laluban makamin da zata kwaɗe shi da shi.

juyowa yayi yana huci kamar mayunwacin zaki ya durfafe ta, har wani gurnani ya ke fitarwa kamar mazuru.

Da kakkausar murya yace"kinjama kanki bala'e da masifa Anila, tun da har kika shiga gona ta, bazan ƙyale ki ba, zanyi maki abun na ke yi wa Ana sannan In kashe ki, In kuma binne gawarki a cikin ɗakin nan! Su kuma wadanda kika turawa videon suka gani zan gano su ne daya bayan daya in kashe su..."

hankalinta idan yai dubu to ya tashi, duk tabi ta rude ta razana, sai faman girgiza kanta takeyi kamar yar kadangaruwa, sai zagaye dakin sukeyi taki bari ya damke ta, gaban mirror ta nufa takai hanninta da ke kerma ta rarumi kwalaben turarurrukanta ta dinga jifar shi da su ko gizau baiyi ba,..

"Kada ka matso kusa dani, kada ka ta6ani Uncle, zakayi danasani...."

ta faɗa tana zare mashi idanun ta cikin tsoro

har ta kware baki da niyar ta fasa ihu don mutanan gidan suji, sai dai kash bata kaiga yin hakan ba, ɗan iya yayi kukan kura Ya damƙi keyarta da hannu ɗaya, yakai ɗayan hannun saman bakinta ya toshe shi, Ƙyanƙyami da ƙyamar shi ne ya kama ta, Idanunta suka kaɗa jawur, tadinga kokarin kwace kanta daga rukan da yayi mata ta kasa, tafin hannunsa daya toshe bakinta da shi ta dinga cizo hadi da yakushin shi da akaifunta, amma yaki ya sake ta, tana jiyo knocking daga wajen dakin kamar tayi hauka saboda ta kasa iya furta kalma..


Luxury-incense By Sapnah Borno.
Ta kawo muku turarukan wutan su Na maiduguri dana chad, turarukanta masu masifar dadi da kama waje harma da daukar hankali, indai kikayi kabbasa da turaren ta har wajen da kika zauna indai kika tashi sai kin bar kamshin ki, sannan Tana saida mayukan gashi irin nasu na shuwa Arab masu tasirin gaske, wajen gyaran Amare kuwa babu magana dan tazo muku da Chadian and Sudanese dilka Wanda zaki gyara jikinki da kanki, oga ya kasa ganeki, haka zalika akwai wata humrar ta mai suna hana bacci da kuma sirrin shuwa Abun ba magana, yar uwata ki jarraba turaren yar mutan borno nasan zata zame miki best turaren wuta plug. Tanada turarukan da zaki turara gida, toilet, bedsheets, curtains, kabbasa and hair incense ku jarraba kada ku bari ayi babu ku.
Wardrobe balls
Kabbasa spray
Chadian khumra
Hawee
Halud
Gabgab
Sandal sukkariya
Kajinguru
Dilka soap
Ready to use dilka
Karkar oil
Turaren tsuguno
Habil
Dorut
Dorot after period
Brown khumra
Dufr khumra
Body milk
Sudanese kuleccam
Chadian dufr kuleccam
Musk khumrah.

Maganin matan mu sunada inganci Wanda muke kawo su daga sudan, sannan munada maganin karin girman nono, Wanda basuda effects, ga masu bukatar maganin Matsi ko maganin mata Masu aiki garanti munada su, sannan muna zuwa gyaran jikin amarya a duk garin da take

Our Chadian aphrodisiacs are.
Beejay fire
Sata jagab honey
Wetness and sweetness combo
Daka
Great A sabaya
Breast engagement powder
Ciccibi
Gumbar madara
Gumbar dabino
Bita Zaizai

08093772168


*Welcome, Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan number din 08103884440*~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___✍️~



Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4k
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki.




💔~______________________________~🌹💘🔥💋~


"Aunty Anila, lafiya kika kulle room door din ki? pls ki buɗe min, baby junaid yana son ganin ki gayanan abayana na goya shi sai faman turbune min fuska ya ke yi...." daga wajen dakin Zahra tayi maganar batasan halin da Anileerh ta ke a ciki ba


Muryar junaid ta jiyo yana fadin"mommy ki buɗe mana kofa, mu shigo..."

idanunta sun kaɗa jawur hawayen da suka cika su a hankali suke zarya kan kuncin ta, Uncle dan iya dake kallanta wata yar iskar dariya ya saki kasa kasa, Cikin muryar raɗa ya furta"ina ta ya ki bakin ciki Anila, daga rana irin ta yau ba zaki ƙara jin ko da muryar su ba, zaki rasa kowa naki za kuma ki rasa kanki saboda shegen bin ƙwaƙƙwafin ki da kafiyarki..."

iza ƙeyarta yayi, tana turjewa yasa karfi gurin ingizata suka shiga toilet, Ya datse ƙofar, ba tare daya saki bakinta daya toshe ba, Yajata har izuwa gaban bathtube faucet Ya kunna tafasasshen ruwan zafi Ya fara kwararowa da gudun gaske Tiririnsa Ya cika toilet din.. hankalinta ya ƙara tashi ta zazzare idanunta kamar ƙwayar zasu faɗo kasa, Hular data rufe kanta tuni ta jima da barin kan nata.

lokacin da bathtube din Ya cika da ruwan zafin, ya ƙara da sihiri gurin tafasa shi, sannan ya kamo wutsiyar Sumar kanta Ya zura a cikinsa nan take gashin Ya kone akan idanun ta..

wata irin razana tayi ta dinga ƙoƙari ƙwace kanta daga gare shi, tana ta gunjun kuka ta rasa ina zata tsoma ranta, tsoro da fargaba ya kamata.


"Zaki fada min Inda kika samu video din ko kuwa kin za6i in zabka ki a cikin ruwan nan kamar yadda ake zabka kaza..."

ya faɗa tare da buɗe mata baki don tayi magana..."ko da kinyi ihu ba zasu ji ki ba.." Haki ta dinga yi dakyar ta iya furta"koda na fada maka, ba za ka fasa kashe ni ba, ba zaka yi min wayou ba, mutum mugu irinka ba ya yafe wa wanda yasan sirrinsa..."

bata kare maganar ba, Ya damƙi kanta ta tsiya ya tura sa gab da ruwan zafi, Hucin da ta shaka ne Ya haifar mata da karancin numfashi, ta fashe da kuka saboda azabar da taji, wata irin azababbiyar mura ce ta farat ɗaya ta kamata hancin ta yadinga sakin wata irin tsinkakkiyar majina mara kauri.

Cikin shesshekar murya ta furta"zan.. Zan faɗa! Zan faɗa maka! Kada ka kashe ni dan Allah..."

saida ya bari ta galabaita ta fara fita hayyacin ta, kana ya ɗago da kanta, ya kura mata kwartayen idanun nan nasa marasa kyan gani, abunka ga farar fata fuskarta tayi jawur kamar ka ta6a jini ya ɗigo.


"Ina sauraronki..." kasa magana tayi sai haki take yi.

Tsawa ya daka mata"zaki fada ko kuwa"? Cikin disasshiyar murya ta furta"ka riga ka makaro Uncle, kona fada maka ba abun da zaka iyayi saboda na riga dana turawa Jami'an isod videon A yanzu haka sun fara bincike akanka..."


dafe kanshi yayi da hannu ɗaya tsantsar tashin hankali da fargaba ne a cikin idanun shi, cikin shi ya duri ruwa..

bai gama shiga tashin hankali ba, Unexpected jiniyar motocin da ke shigowa gidan ta karaɗe kunnuwan kowannansu..


Su Uncle dan iya ido Ya raina fata, Jikinshi ya hau kerma kamar mazari..

Anila dake ta sakin numfashi sama sama ga raɗaɗi tana ji amma ahaka take sakin murmushi"bakaga komai ba Uncle, nasan za ka yi mamaki, lokacin da ka juya baya kana kokarin kulle kofar dakina, a tsakanin wannan lokacinne na dauki wayata nayi hanzarin tura ma su sakon su kawo min agaji.."

bata kare maganar ba, sakamakon shaƙar da yayiwa wuyanta, ranshi yayi makura agurin baci, kumatunsa har kerma su ke yi.

kasa furta magana yayi saboda 6acin rai da zullumin kada su riske shi, da karfi Ya wurgar da ita tayi gadan gadan zata fada cikin kwamin wankan kafin ya 6ace daga cikin toilet ɗin bat babu shi babu burbushin shi...😳

_(Shin menene dalilin da ya kawo Uncle ɗan Iya ɗakin Ana? Bakomai bane face yazo ya sanar da ita game da aikin daya sama mata don ta shirya ta tafi interview, sai kuma Ya risketa tana waya harya tsaya yana sauraron firar su)_


Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un...." mami ce ta fada yayin da take fitowa daga kitchen, da gudu ummi ta biyo bayanta, koda idanun ta su ka yi arba da abun da mami ke wa sallallami nan ta ke ta ɗaura hannayenta biyu asaman kanta tana ambaton la'haula walaquwata illa billah sojoji agidan nan? Bayin Allah kodai 6atan hanya ku ka yi ne"?

Hankalinta atashe ta ƙarashe maganar tana kallon Isod agents din da ke shigowa Falon, sanye cikin kakin su, hannayen su ruƙe da bindigogi..

Watsowa zahra tayi da gudu bayanta agoye da junaid ta nufo falon Jin jiniyar motoci tun kan ta ƙaraso idanun ta suka yi mata tozali da isod soldiers ja da baya ta soma yi a tsananin tsorace ta zazzare idanunta, numfashinta kamar zai ɗauke saboda tashin hankali da ta shiga.

Mahboob dake a cikin toilet Yana wanka, ko da jin jiniyar motoci a cikin gidansu, aguje ya fito daga toilet din jikin shi duk kumfar da bai kaiga ɗauraye wa ba, Ya dafe guntun towel din daya daurawa qugunsa, jikinsa na 6ari ya nufi window din dakinsa ya zuge ta tare da leƙe kansa, dafe kirjin sa yayi da tafin hannunsa cikin rawar murya ya furta"Allahumma Ajirni Fi Musibati wa akhluf Li Khairan Minha....". 😳

Komawa Cikin Toilet din yayi ya ɗaurayo jikinsa da ruwa, Jikinsa na bari Ya dawo dakin Ya ɗauko Jallabiya Cikin closet dinsa ya zura a jikin shi.

Da ɗan gudunsa Ya fito daga dakin

"Wayyo Allah Mommy, Ni sauke ni in tafi gurin mommy, bana shon ganin su.."

baby junaid ne ya fashe da kuka yana ta duma ma zahra dundu abayanta don ta sauke shi sai dai hankalin nata gaba daya ba akan shi ya ke ba..


Mami kamar zata saka kuka tace Dan Allah ku fada mana meya kawo ku gidan nan? Ni nama rasa ganewa yan sanda ne ko yan fanshi ne"

ba su iya ganin fuskokin su saboda mask din da suka saka.

Wani mai budaddiyar Murya ne daga Cikin su yace"Ina mai gidan?


Kallon juna su ka yi, murya na rawa Mahboob daya karaso Yace"su biyu ne, Abie da Uncle din mu wa kuke nema a ciki"

ummi tace"mun shiga Uku, ganin mutanan nan ba alkhairi bane, Ni dai Allah yasa ba wani bane ya tsokano mana su ba"


"Ɗan iya muke nema! idan yana a cikin gidan ku yi mana sallama da shi"


"Mahboob ka shiga ɗakin shi ka duba" har mahboob Ya juya zai tafi muryar Anila ta katse su"Baya agidan Ya 6ace akan idanuna"

gaba daya suka juya suna kallon ta, fuskarta tayi jawur saboda hucin ruwan zafin daya dake ta ga hawayen da suka cike idanunta, tunkan ta karaso Junaid ya sauko daga bayan zahra Ya nufe ta yana kuka, daukar shi tayi tare da rungume shi a

37 / 107