Author : Boss Bature Category : Complete Novels
min ɗan uwana, shi kaɗai ne dangina da ya rage mini a duniya, na roƙe ka Ya Mubarak.."
A hankali hawayen da suka taru cikin idanunta suka soma dira kan kuncin ta.
A tsanake ya ke bin ta da kallo, kwata kwata babu alamun zai furta kalma saida ta ƙarashe maganartata, ya matso ya zauna kan kujerar dake a agaban gadon nata.
"Baki bani amsa ta ba! Ya jikinki kin tashi lafiya?"
Cikin shessheka ta ce, "Ban tashi lafiya ba, jikina babu sauƙi, in har ba ƙyale Praveen ku ka yi ba, ban ji daɗin yadda kuka buge shi ba, ban yi zaton haka daga gare ku ba."
"Ina so nasan taƙaitaccen tarihin rayuwarki da ɗan uwanki Praveen."
"Idan na fada maka za ku yafe mana?" ta yi narainare da idanunta.
murmushi ya yi batare da ya furta mata kalma ba.
"Ni ɗiyar uncle dinsa ce, Mun taso a gidan marayu, bamu da asali bamu da dangi, a bakin Praveen na ji labarin abun da ya faru da danginmu, saboda ni a lokacin yarinya ce ban mallaki hankalina ba, sanadin zuwa biki danginmu suka yi hatsarin jirgin ƙasa gobara ta kama, mutane da yawa suka rasa rayukansu, a lokacin Praveen shi ya goya ni a bayansa ya daka tsalle ya duro daga cikin jirgin, muka faɗi ƙasa duk mu ka ji munanan raunuka har muka fita hayyacin mu, ƴan sanda ne suka kai mu asibiti, bayan da muka samu lafiya, sun tambayi Praveen meya faru? Bayan daya fada masu, sun tausaya mana sun kuma jinjinama Praveen da ya iya ku6utar da mu daga cikin jirgin ƙasan.
Bayan da muka samu lafiya suka mika mu gidan marayu. A rayuwana bani da gatan da ya wuce Praveen, shine uwata shine ubana, shine dangina, kuma shine komai nawa, bamu samun kulawa a gidan marayun, ba abinci mai kyau, ba sutura mai kyau, Idan gwammanati ko masu kuɗi suka kawo mana tallafi, bamu sani, masu kula da gidan marayun ne suke cinyewa sai su bamu kaɗan wanda ba zai ishe mu ba, Praveen shi yake fita ya yi aikin ƙarfi don ya sama mana abincin da zamu ci, da suturar da zamu sanya, idan bani da lafiya Pravin shi yake nemo kudin da zai kaini asibiti.."
Sir Mubarak dake sauraronta zuciyarsa ta karaya tun kan ya ji ƙarashen labarin su.
"Kwatsam muna zaman mu lafiya a gidan marayun, sai ga wani attajiri ya zo zai yi adopting, tun da ya ɗaura idanun shi akaina ya kwallafa rai ya ce ni yake so a bashi, masu kula damu su ka shawarce shi ya dauke mu mu biyu ni da ɗan uwana ya nuna kin amincewarsa.
A lokacin Praveen baya kusa ya fita neman kudi.
Haka suka bashi ni, na dinga kuka ina kiran sunan dan uwana Praveen.
Basu saurare ni ba, suka nuna min fin ƙarfi gurin ɗaukana ina turjewa suka tura ni cikin motar mutumin.
A dai dai lokacin da motar zata tafi sai ga Praveen ya dawo, ta window glass din motar mutumin na hango sa, na dinga kwala masa kira cikin sa'a ya hango ni, hankalinsa ya tashi ya bi bayan motar mu a guje.
Tafiya muka yi mai tsayi, Praveen bai daina bin motar ba.
Har muka ƙaraso gidan mutumin, ya fito daga mota ya ɗauke ni ya shiga dani ciki, na yi zaton ya yi adopting ɗina ne don ya raine ni tare da iyalinsa, ashe mutumin banza ne, ya dauke ni ne don biyan buƙatar kansa, a lokacin da yake kokarin keta min haddi, Praveen ya ritsa da shi, da ya ke yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, cikin fushi ya dauki kwalbar giyar da mutumin ya sha ya aje akan table, ya kwaɗa masa a saman kansa tare da caccaka masa a cikinsa har saida ya kashe shi.
Hankalinshi ya tashi da ganin abun da ya aikata, cikin sauri ya goya ni a bayanshi, inata kuka ya gudu da ni, da kuɗin hannunsa ya yi amfani muka koma Delhi da zama, gudun kada asirin mu ya tonu a gane mu muka kashe shi.
Bamu da kowa a Delhi, babu wurin kwana, sai dai mu ra6a a wani gidan abinci, anan muke kwana, idan gari ya waye masu kuɗi suka zo cin abinci, Praveen ya kan goge masu motocinsu su biya shi kudi, da waɗannan kuɗin ya ke yin amfani gurin biya mana buƙatunmu, wani lokacin har bara yake yi amma ni bai ta6a bari na fita nema mana kudi ba, shi ya ke fafatuka ni sai dai in ga ya siyo abinci mai rai da lafiya da suturar sanyawa, daga baya madam mai restaurant din ta ɗauke shi aiki, har ta bamu ɗakin da zamu dinga kwana a ciki."
lokacin da ta ƙarasa masa labarin sai ta fashe da kuka.
Sir Mubarak ya tausayama rayuwar su, musamman ita, saboda ya fahimci batasan komai da Praveen ya aikata ba.
"Me kika sani game da auran shi da Saratu?"
"Mun fara soyayya ni da shi tun yana da shekara ashirin, ni kuma ina da shekara goma sha biyu, soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu, amma saboda bamu da halin da zamu yi aure yasa muka jinkirta, to a lokacin da ya ƙara girma ya kai shekara ashirin da biyar, yana da abokai da manyan mutanan da yake yi ma aiki suna biyan shi kuɗi, akwai lokacin da ya zo min da maganar zasu tafi neman kudi shida abokansa, na saka rigima akan kar ya tafi ya bar ni, ya dinga lallashina, har ya samu na amince ya kai ni gurin madam me restaurant, ya bata kudi masu yawa ya ce ta kula masa da ni. Tun bayan da Praveen ya tafi ban ƙara jin ɗuriyar shi ba, kullum sai na yi kukan rashin shi, bana jin dadin rayuwata, da shi nake kwana da shi nake tashi, kullum cikin sa ran ganin shi na ke yi, madam din dake kula da ni ita ke lallashina idan na fara kukan rashin shi. Unexpected wata rana sai gashi ya kira madam a waya ya ce a bani mu yi magana, na yi murna da jin muryarshi ya lallashe ni ya ce in ƙara haƙuri zai dawo mini da abun mamaki, har ya ce zai dinga turo min kudi in sayi duk abunda nake so, tun daga ranar da ya kira kullum sai ya kira ni a wayarta mun gaisa, inta tambayar shi yaushe zai dawo na gaji da jiran shi, still hakurin ya ke bani Lokaci ɗaya rayuwata ta sauya tun da Praveen ya fara tura ma madam kudi, ta sanyani a makaranta, ta siya min surutu masu kyau, komai da zan buƙata siya min take yi, na dinga jin dadi Praveen ya yi kudi zamu daina shan wahala. Wallahi Yaya Mubarak ni bansan Praveen ya yi aure ba, bai fada min ba, ban ma san baya a ƙasar India ba, tsawon lokaci bai waiwayi Delhi ba.
Ranar da ya dawo na yi murnar da bazata misaltuba, nayi mamakin sauyawar shi, yayi min kyaun da bai ta6a yi mini ba, ya zama ɗan gayu mai arziƙi, madam kanta tasha mamakin arzikinsa, har biyayya take masa sau da ƙafa saboda kudinshi.
Koda na tambayesa tayaya akai ya samu arziƙi? Nan ya fara bani hakuri na ce masa meyasa zai bani hakuri kawai ya bani amsar tambayana.
A nan yake faɗa min, ya yi mini ƙaryar sun je neman kudi shi da abokansa, gaskiyar magana ba haka bane, tafiyar da ya yi batare da abokansa ya yi ta ba, Allah ne ya haɗa shi da wani mutun mai arziƙi ɗan kasar Nigeria ya zo ganin ƴarsa ne dake karatun Medicine anan Delhi, shi kuma ya ta6a taimakon yarinyarsa har ta ji dadi ta nuna tana son su ƙulla abota, lokacin da baban yarinyar ya zo kawo mata ziyara saita haɗa shi da mahaifinta don su gaisa, bayan da suka gana da mahaifinta ya tambayesa su wanene danginsa? Yana karatu? Ko ya fara aiki? Sai ya faɗa masa baida kowa, har ya bashi labarinmu, mutumin ya tausaya masa ya ce zai taimakesa da aikin yi, da shi da ƴar uwarshi amma sai in har ya amince zai auri ƴarsa da ke son shi.
Ya ce mini saboda baya son ya rasa damar da ya samu, kuma yana son rayuwar mu ta inganta, shiyasa ya amince ya bi mutumin da ƴarsa Nigeria, a can aka ɗaura musu aure.
A lokacin da ya bani labarin na ji kishi mara misaltuwa, zuciyata ta karaya amma da ya lallasheni ya faɗamin baya sonta, ya aure ta ne saboda mu samu dangin da zamu jingina da su, mu kuma samu arzikin da zamu wadata kanmu, na ce na amince amma bana so ya yaudare ta, saboda na ji ya ce baya son ta ya aureta, kuma ya taimaki rayuwata da tashi, kada ya nemi kudi ta haramtacciyar hanya, kada ya aikata laifin da zai jefa rayuwarmu cikin wahala, komai zai yi a rayuwa kada ya zalunci wani, nasihar da nake yawan yi masa kenan.
To daga baya ne ya zo zai tafi da ni Nigeria, a lokacin mun yi aure har ma na haifi yarona Naufal da baifi shekaru goma sha ɗaya ba a lokacin, ita kuma matar tasa ta Nigeria tana da ƴa'ya uku a lokacin, duk da ban ta6a ganinsu ba amma ina ganin hotunan su da videos dinsu a wayar shi duk idan ya zo. Ina son ƴa'yanshi sosai saboda ina yi masu kallon yan uwana kuma danginmu....
"Lokacin da Praveen ya zo da ni Nigeria, bai fara kaimu estate ɗinku ba, sai ya kaimu wani gida ya ce in fara zama a ciki, satin mu ɗaya a gidan Naufal ya yi rashin lafiyar da ta yi silar mutuwarshi, a lokacin har mun kai shi asibiti amma ya riga da ya mutu, na yi kuka kamar raina zai fita, har yau bazan manta raɗaɗin da na ji ba, na rasa Naufal.." Ta faɗa tana share hawayen ta.
Sir Mubarak ya ce, "Bamu san komai game da yaron ki ba, bayan da ya rasu su wanene su ka yi jana'izar sa?"
Cikin shesshekar kuka ta ce, "Bayan da muka je asibitin suka tabbatar mana da mutuwar sa, na dinga kuka kamar raina zai fita, docs da nurses suka dinga lallashina a lokacin ma bana jin harshen hausa ban san me suke cewa ba, sai idan Praveen ya fassara min da indiyanci nake fahimtar me suke faɗi, a ƙarshe na fita hayyacina na yanke jiki na faɗi a sume, ban ƙara sanin meke faruwa ba, lokacin dana farfaɗo na ganni a gadon asibiti kwance ga Praveen a gefe, cikin ruɗu na tambayesa da gaske Naufal ya mutu ko mafarki na yi? Ya ce min inyi hakuri ba mafarki bane, da gaske Naufal ya rasu, yau sati ɗaya kenan bana a hayyacina, harma sunyi jana'izarsa, sun ƙone gawarsa a crematorium kamar yadda muke wa mamaci a al'adarmu ta hindu, bazan iya misalta maka halin da na shiga ba a lokacin.
Bayan rasuwar Naufal da wata ɗaya, ya ce zai kawo ni gurin dangin matarsa, amma yana so ya gargaɗe ni kar in kuskura in faɗa ma wani akwai aure a tsakanin mu, idan ba haka ba, zai rasa auran shi, kuma zasu kai ƙarar mu kotu.."
Ya yi min barazana sosai, ya ce duk abun da ya faɗa akaina in amsa da haka ne na amince masa, ranar dana fara tsintar kaina a cikin estate ɗinku bazan misalta farin cikin da na ji ba, duk da wasu basu kar6e ni da hannu bibbiyu ba, waɗanda nake ta zumuɗin gani saida na yi danasanin haɗuwa na da su saboda ƙyarar da suke mini. Hajiya Saratu ta tsane ni, ƴa'ƴanta ma sun tsane ni, basu san ni auntyn su bace, kuma ni kaɗai ce dangin ubansu da ya rage a duniya, amma na yi masu uziri komai da ya faru Praveen ne sila, da tun farko ya faɗa masu matsayina a gurin su ya kuma daraja ni da ba su tsane ni ba, kuma hada ƙarin muna zaune a gidanku shi ya ja min ƙasƙanci a gurinsu. Kuma wlh ya so ya maida ni gidansa amma ni na nuna bana so saboda na saba da ku, ina son ahlinku, na ɗaukeku kamar dangina da na rasa..."
Bata ƙarashe maganar ba, ta ji ya saka hanky kan fuskarta, a hankali yake share mata hawayenta, idanunsu a cikin na juna, duk sai ya ji ba daɗi, ya yi danasanin marin da ya yi mata, kuma da ya san bata da sanya hannu da ba abun da zaisa ya tuhume ta.
"Ya Mubarak, ka taimaka ma rayuwarmu, ku yafe mana, ku bar mu mu ci gaba da zama tare da ku, zamu gyara kuskuren mu"
Murmushin takaici Sir Mubarak ya yi.
"Ki faɗa min meyasa kika bi Praveen kuka gudu? Kinsan laifin da ya aikata..?" Gabanta ne ya faɗi rass!
Cikin rashin nutsuwa ta fayyace masa komai da ya faru.
Girgiza kai ya yi cike da takaicin ƙaryar da Praveen ya yi mata.
"Hmmmm, Praveen ba gaskiya ya faɗa maki ba, ba Hajiya Saratu bace me laifi, batasan da aure a tsakanin ku ba, kuma ba ita bace ta tura maku aljanu ba, hasila ma tsoron hulɗa da mai aljanu take yi balle har ta yi mu'amala da su, bayan haka yanzu haka da nake maki magana, Hajiya Saratu tana a kwance gadon asibiti.."
Cikin ruɗu da tashin hankali ta furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un! Meya faru da ita? Meke damunta? Meyasa praveen ya yi min ƙarya ne? Ni dai Allah Ya sa bashi bane ya yi silar kwanciyarta gadon asibiti ba..!"
Ta faɗa da damuwa akan fuskarta.
"Ya Mubarak ka fadamin meke faruwa? Wani laifi Praveen ya aikata ma ku?
Shiru ya yi yana sauraron muryar Owais dake yi masa magana ta cikin earbuds din dake a maƙale da kunnansa, komai da suke tattaunawa yana sauraron su, Sir Mubarak ne ya kira shi don ya ji komai.
Cikin harshen yarbanci ya ce, "Owais, ina fata ka ji komai?"
On the Other hand Owais ya ce, "Na ji Uncle, Hajjaty bata da laifi, bata san komai da Praveen ya aikata ba.."
"Ta nemi in faɗa mata meke faruwa kana ganin yakamata mu sanar da ita?"
"Uncle, ka fadamin ta yi 6arin ciki, nasan i war haka jikinta babu lafiya, jininta zai iya hawa, a yadda na ji shaƙuwarta da Praveen, idan ta ji abun da ya aikata zata shiga mawuyacin hali ne, amma me zai hana mu bari sai ta ji sauƙi sosai?"
"Owais, ka yi magana mai ma'ana, na gode da shawararka."
Daga haka suka yi sallama ya mayar da dubansa ga hajjaty, dama jiran shi take yi ya gama wayar,
"Pls ka faɗamin wani laifi ya aikata? Dan Allah kada ka ce zaka 6oye min, na fada maka bani da kowa in ba Praveen ba, shine gata na, bana so na rasa shi! kuma me ke damun Hajiya Saratu?"
Numfasawa ya yi kafin ya ce, "Allah shine gatan bawansa Hajjaty, zan faɗa maki amma ba yanzu ba, ki fara samun lafiya tukunna, sannan karki damu da maganar hajiya Saratu, ta ji saukin jikin ta yanzu."
In a cool voice ta ce, "Shike nan zan jira har zuwa lokacin da zaka fadamin! Amma dan Allah ina Praveen ya ke?"
"Karki damu, Praveen yana a wurin mu, kuma mun sanya doc sun yi masa treatment na rauninsa."
"Zan iya ganin shi?"
"A'a, ba yanzu ba." Gyaɗa kai tayi, "Shikenan..."
"Amma yana inane? Kuma ni a ina nake?"
Bai amsa mata ba sallamar Nurse ta katse su, mikewa ya yi ya nufi nurse din, "Pls, ki ci gaba da bata kulawa, duk abun da take bukata ki yi mata shi, ina so ta samu cikakkar lafiya."
"Okay sir, zan yi iyakar bakin kokarina.." Juyawa ya yi tare da kallon Hajjaty da ke kallon shi.
"Zata kula da ke, ko me kike bukatar ci ko sha ki tambaye ta zata yi maki, idan kika zauna salin alin, Praveen zai kasance cikin ƙoshin lafiya.. "
tana kokarin yi masa magana ya sa kai ya fuce daga ɗakin, kamar ta fasa ihu..
"Pls, baiwar Allah, ki fadamin ina ne nan? Meyasa ya kawo ni? Kuma meke damuna ne?"
"Am sorry ma'am, bai bani izinin in faɗa maki inda kike ba, bansan komai ba, abun danasani ya kira ni ne don in duba lafiyar ki.." Shiru ta yi zuciyarta duk ba dadi.
~_________________________________~
To fa manema labarai sun fara dandazo a layin Obie Estate sun haɗa uban cunkuso, burin su kawai su samu damar ganawa da ahalin Obie don su samu na ɗaukar rahoto, ba dan dakarun sojojin da ke a kewaye da Estate din ba da tuni sun 6urma ciki saboda tsabar zaƙuwa, masu ruwa da tsaki a mulkin ƙasar, sun kasa sun tsare suna jiran jin meke faruwa?
Haka zalika ƴan jami'iyar Jdp da App sun ƙagu da su san meke faruwa, saboda duk sun ji labarin kewaye gidajen ƴan jam'iyarsu da soldiers suka yi, dama cikin yan kwanakin nan mutane sun fara tsegumin rashin jin ɗuriyar baba Obie, basu ji labarin yana a ƙasar ne ko ya yi tafiya ba, haka Alhaji Musa ma sun ji shiru babu duriyar shi, Ɗan-iya da ya fi kowa baki kusan kullum suna samun labaran yan siyasa a bakinshi ta gidajen radio da shafukansa na social media shima sun ji shiru ba labarinsa.
Saboda yadda mutane ke kiran layukan su a waya yasa suka kashe wayoyin su.
Alhamdulillah Hajiya Saratu ta samu lafiya, har an sallame ta, amma momma har yanzu memory ɗinta bai dawo ba.
A main Falo na gidan baban suka haɗu gaba ɗayan su domin tattaunawa game da shawarar ya zasu yi da jama'ar da ke jiran su ji daga bakin su? Kowan nan su yana fargaban asirin mahaifinsu ya tonu, saboda gudun tozartar da zai yi da kuma su kansu, suna zullumin mutuncinsu da zai zube a idon duniya.
Gaba ɗaya sun nuna basu san a fallasa sirrin, saboda basu son asirin shi ya tonu a bainar jama'a, suna jin fargaban abun da zai biyo baya, da kuma halin da uban nasu zai shiga, kuma basu son a gurfanar da shi gaban kotu, sun ƙwammace su bashi poison ya sha ya mutu, saboda basu son ma su ga tashin hankalin da zai fuskanta, ƙwara ya mutu su san babu shi a duniyar, duk da mutuwar ba hutu bace a gare shi, amma su a wurinsu ƙwara