Author : Boss Bature Category : Complete Novels
Bai da imani bai da tausayi, mugu ne..."
ta ɗan dakata tana share ƙwallarta, fuskarta akan Camera..
*"_watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda ya ce ba zai kyale ni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kun ga ni kaɗai ce a gidan, yanzun nan na ga shigowar shi shiyasa na gudo ɗaki don in samu damar yi maku video. Don Allah don son ku da manzon Allah saw a duk lokacin da kuka kalli videon nan ku yi gaggawar kaishi ƙara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku 6ata lokaci, saboda shi ɗin mutum ne mai haɗarin gaske, ya sha yi min barazana akan in har na kuskura na faɗa ma wani abun da ya ke mini wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na faɗamawa shi yasa na kasa sanar da ku..."_*
Bata ƙarashe maganar ba ta yi saurin katsewa, bugun zuciyarta ya tsananta jin takun tafiyarsa gab da ɗakinta.
Cikin sauri ta janyo pillow ta zuge zip ɗinsa ta fasa soson ciki ta tura wayar a ciki ta maida ta rufe, juyowar da zata yi keda wuya kwatsam ya banko ƙofar dakin ya shigo.
Cikin rawar murya ta furta, "La'ila ha illa anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin!"
*Daga Alƙalamin Boss Bature💗🔥*
ƙyalƙyacewa ya yi da tantiriyar dariyarsa ta shaiɗanu tare da ɗaura kwartayen idanunsa akan fuskarta ya shiga washe jajayen haƙoransa...
"Dama saida raina ya bani zaka dawo don ka cutar da ni! Wai kai wani irin shaiɗanin mutunne? Mara imani da tausayi? Meyasa ba zaka rabu da ni ba?
"Saboda kinsan sirrina! Ba zan ƙyale ki ba, ke barazana ce a gare ni..." Bai ƙare maganar ba ta katse shi cikin fargaba ta ce, "In har baka fara bibiyar rayuwata ba, tayaya ni zan san sirrinka? Meyasa kake aikata fasiƙanci da ni? Laifin me na yi maka? Kawai don ka azabtar da ni? Wallahi ƙwara na mutu da in ci gaba da haɗa jikina da naka! Kasa na tsani kaina, saboda ƙazantar da kake goga min!..."
Cikin shesshekar kuka take yin maganar idanunta a cikin na shi, "Ba zan ƙara bari ka kusance ni ba, ko dai ka fita daga rayuwana ko kuma in tona maka asiri uban kowa yasan me kake aikatawa..."
Ko gizau bai yi ba, sai ma wani shu'umin murmushi da yake saki, "Tun da har kin san komai, kuma kina barazanar zaki fallasa sirrina, ba zan ƙyale ki ba Ana, dama na faɗa maki dama nake jira da zan salwantar da rayuwarki kuma na samu...!"
Gaba ɗaya ta ruɗe da jin maganarsa, gumin tashin hankaline ya fara tsattsafowa ta ko'ina a jikinta, kafin ka ce me tuni tsigar jikinta ta fara tashi haiƙam, la66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!
Ja da baya ta soma yi tana neman hanyar da zata ku6uta daga gare shi, duk inda ta yi sai ya taro ta, gaba ɗaya suka hargitsa ɗakin nata, ta dinga ɗaukar abubuwa tana jifar shi da su, ba yadda bata yi ba don ta ku6uta amma ta kasa saboda ya toshe duk wata hanya da zata iya guduwa, a ƙarshe ya damƙi wuyanta ya maka da bango ya matse ta, idanunta suka firfito waje, numfashinta ya soma kokawar ɗaukewa, ta dinga fitar da nishi tana harba ƙafafunta..
Cikin shakakkar murya ta furta, "A.. Al... Allah bab ba zai ta6a barin ka ba, Allah sa...ssai ya saka min cutarwar da kayi min, idan kana tunanin kashe ni shine mafita ka jira ka gani, ni zanyi silar tonuwar asirinka, kaima zaka mutu ne... "
Akan idanunta ya girgiza jikinshi ya riƙiɗa ya sauya suffar shi ya zama dodo, tsantsar tsoro da tashin hankali mara misaltuwa suka ziyarci zuciyarta, duk da tashin hankalin da take a ciki bakomai take tunanowa ba face ƴan uwanta da Aunty Anila sune damuwarta, babban baƙin cikinta zata mutu batare da ta fallasa asirin shi ba. Bata da mafita da ya wuce Allah, yana kallonta da idanunsa da babu ɗigon imani a cikin su, A haka da ya shaƙeta jikin bangon kokarin keta mata haddi yake yi.
Tana a cikin mawuyacin halin nan kwatsam idanunta suka hango mata Baby Junaid dake kokarin buɗe ƙofar dakin ta, ya zuro hannunsa ta ciki.
Wani irin faɗuwar gaba ta ji, kamar ta fasa ihu, saboda tsoron kar Ɗan Iya ya gansa don tasan muddin ya gansa sai ya kashe shi.
Da ƙarfi ta dinga yin kuka tana fasa ƙara, duk don ta hana shi jiyo sautin muryar Junaid dake kiran sunanta.
Junaid da ya ji kukanta, ya fago da idanunsa kaitsaye suka sauka akan bayan ɗan iya, a firgice ya razana tare da kware bakinsa ya fasa gigitacciyar ƙara ya bi ya ruɗe tsigar jikinsa ta shiga tashi ganin dodo.
Wani iko na Allah kwata kwata dan iya bai jiyo shi ba, kuma ya bashi baya, kuma harda ihun da Ana ke saki ya hana ya jiyo kukan Junaid.
Girgiza kanta ta dinga yi, da hannu ta dinga yi masa alamar ya gudu ya gudu.
Nan take ɗan iya ya ji aransa akwai mai kallonsa, yana kokarin juyawa,
Junaid da ya gama razana cikin ikon Allah tsoro yasa ya juya a guje ya nufi ɗakin mommynsa, yana gudu towel dinsa na ƙwancewa, har tuntu6e ya yi ya faɗi ya miƙe da ƙyar yana kuka ya shige ɗakin su.
Yana shiga ya fara neman gurin da zai 6oye kansa.
Jikinsa na kerma ya buɗe wardrobe, ya taka gidan farko ya ruƙe na biyu da hannayensa ya haye sama ya kutsa cikin kaya ya 6oye, adai dai lokaci ɗan iya ya saki Ana ta yanke jiki ta fadi ƙasa bata mutu ba sai dai ta fita hayyacin ta.
Ya juya cikin sauri ya fito daga dakin ya soma neman wanda ya shigo gidan ya dudduba ko'ina bai ga kowa ba, har ɗakin Anila ya shiga a lokacin Baby Junaid ya daɗe da sumewa, bai ji wani sauti ko alama da zai bayyana masa akwai mutun ba.
Hankalinsa ne ya kwanta da ya tabbatar babu kowa kuma ya tuna basu dawo ba, ya baro su acan gidan Abdallah babu wanda yasan ma ya dawo gida.
Lokacin da ya koma ɗakin ya taras da Ana, sungumarta ya yi a saman kafaɗarshi ya 6ace daga inda yake ya dira a ɗakin sirrinsa, ya ajiyeta anan bayan da ya kafeta da sihiri ta yadda bazata iya ta6uka komai ba in ba da izininsa ba, ko magana ba zata iya yi ba, balle ta motsa jikin ta, kwata kwata bata a hayyacin ta. Ashe tsawon lokacin da suke ta neman Ana tana a ɗakin sirrinsa, shi kaɗai ya san inda ya 6oyeta, ba ci ba sha, bata iya komai, ta zama mutun mutumi, babu rabon Ana ta rayu, ya riga da ya gama da ita.
Daga baya ne da ya tabbatar ta mutu sai ya haƙa rami ya binneta a ciki, sati ɗaya kafin zuwan Isod Agents, shiyasa lokacin da suka haƙa ramin suka taras da gawarta bata yi komai ba saboda bata daɗe da mutuwa ba da kuma ikon Ubangiji.. 🥹
RIJF (ANAH)
(Kunji komai da ya faru a tsakanin Ɗan iya da Ana)
~__________________________________🔥🌹~
"Cau cau, gafara dai, namiji Uban maza, The mastermind behind the conspiracy da girman kujerarka Uban munafukan duniya, sarkin mugaye, an buga da kai an barka Jan wuya Alhaji Musa. Ƙaramin su babbansu, ko ku ce big boss, duk nine. Mai izza, mai arziƙi, mai jiji da kai, shugaban azzaluman duniya, wanda mutuwa ke tsoronsa, dodon dodonni, wanda ya fi ƙarfin kowa saboda sihirin sa..."
Kirari ya ke yi ma Alhaji Musa yayin da ya ke shiga cikin Cell ɗin da ya ke. (😂)
Abun al'ajabi ba ya ƙarewa duniya, ni kaina da nake rubutawa saida na razana da ganin ɗan tahalikin nan, garƙame a cikin Cell, wato ruwa ne ya daki babban Zakara.
Ba ka jin komai sai sautin nishinsa da gurnaninsa kamar wani namun dawa, yana a zaune dirshan a ƙasa kamar mabaraci, ko suturar kirki babu a jikin shi, sai gajeran wando baƙi, ƙafafunsa a ɗaure suke da leg irons.
Dana kallesa sai da gabana ya faɗi ganin yadda halittarsa ta sauya, rabin fuskarsa ya lalace sakamakon Acid din da Unaisah ta watsa masa, fatar gurin ta zagwanye gwanin ban ƙyama, da ido ɗaya yake gani Sakamakon ruwan acid din da ya shiga idonsa ɗaya ya lahanta shi, gaba daya fatarshi ta lalace da raunukan bulalan da Evils suka yi ma shi har yau bai daina jin raɗaɗin azabar su ba, idan suka fara masa zogi ba halin ya sosa saboda da zarar ya sosa sai fatar ta ɗuri ruwa ta fashe ta dinga fitar da gur6ataccen ruwa mai ɗoyi, kafaɗarsa ta hagu da Unaisah ta yanka da zarto ta kumbura suntum har surgery aka yi masa a gurin amma still bai warke ba, ciwon har ya shafi hannunsa na dama ya kumbura suntum ya zamar masa jalli joga.
Gaskiya Unaisah ta lahanta bawan Allahn nan ba kaɗan ba, da zai samu damar da zai ku6uta wallahi ita ce mutun ta farko da zai fara kashewa har lahira, a yanzu haka da yake zaune wutar baƙin ciki ce ke ruruwa a cikin zuciyar shi.
idonsa ya kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin sa, ga wani jan ruwa da ya kwanta a ciki.
Yana jin kirarin da DG ke yi ma shi, ya murtuƙe fuska kamar gwaggon biri saboda muni, ƙyanƙyami da ƙyamarsa ne suka cika Owais ya kasa zama sai dai ya tsaya a tsaye, ya toshe hancinsa da hanky.
"Allah ya yafe maka Musa, tun a duniya kenan ka fara ganin sakamakon zunuban daka aikata, ina ga idan aka binne ka inda dukiyarka ko wani abu da kake taƙama da shi ba zai cece ka ba sai mugun halin ka? Ko da yake ba zuwa na yi don in yi fira mai tsayi da kai ba, nasan yanzu ka gane Allah ɗaya ne! Da juyi ɗaya Allah ya rikito da kai, ya kar6e komai da kake taƙama da shi, ya ɗebe albarkar rayuwarka, ya raba ka da kyawun suffarka! Ya kar6e dukiyarka da ƙarfin sihirinka! Ya raba ka da kowa naka, ya kuma zubar maka da mutuncinka, ya bar maka ranka da baƙar zuciyarka don ka ga ishara da idanunka, kai hatta ƴan jami'iyarka sun soke ka daga member ɗin su, sun ma ce a ƙaddara cewa basu taba saninka ba, saboda kowa gudu yake ya ra6eka ta shafe shi. Matarka tana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, tun lokacin da ta ji abun da ka yiwa jinjirarta daka raba ta da ita, nan take ta yanke jiki ta faɗi, yayanka Alhaji Ubaid ya yafe ka daga zuri'arsu, ya ce a daina ma kiran ka da Musa Wadata, saboda Alhaji Mu'azzam Wadata ba ubanka bane, ya fayyace ma kowa dangantarku, mahaifiyarku ƴar aiki ce a gidan su, halinta sak irin naka, bayan da mai gadin gidansu ya yi mata ciki, ta ƙulla makirci ta ce cikin Alhaji Mu'azzam ne, sai da tasa ya aureta bayan ta yi silar mutuwar mahaifiyar su Alhaji Ubaid, ta asirce Alhaji Mu'azzam, da ta haifo ka, ta ci gaba da mu'amala da mai gadin gidan, harta samu wani cikin ta haifi ƙanwarka, saboda Mu'azzam ya samu matsalar haihuwa, ƴa'ƴanta duk ba nashi bane, ta yi ne don ta ci gadon shi. Abun da na fahimta, shaiɗaniya ce ta haifi shaiɗan, mugun halinka a nono ka tsotse shi..."
Tunkan Owais ya ƙarashe maganarshi Musa ya fasa wata irin kururuwar baƙin ciki, har saida gefen bakinsa ya fashe jini ya dinga ɗiɗɗigowa, dama a raunace bakin yake, abun da ya fi tsana a rayuwar sa shine tushen shi, wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyarsa, ya ji zafi da Alhaji Ubaid ya fallasa sirrinsa wlh da zai gansa a gabansa ba abun da zai hana ya binnesa da ran shi.
Yana gurnani cikin fushi ya furta, "Idan ma kana faɗamin ne don in saduda, to ka daina, ba a halicci zuciyata da rauni ba, ba zan ta6a karaya ba, ba abun da zaisa na yi nadamar abun da na aikata!"
Ƙyalƙyacewa da dariya Owais ya yi hakan ya 6ata masa rai..
"Ina mamaki ne mutumin da rabin fuskarsa ya lalace, ba hannu ɗaya, ba ido ɗaya, wai shine ya ke da audacity din da zai iya furta wannan maganar? Me ya rage maka da bazaisa ka yi nadama ba? Bayan ga tsoro nan da tashin hankali kwance cikin idonka...."
wata shu'umar dariya ya saki kamar jaki na haniniya.
"Na ci dubu sai ceto, ba yadda kuka iya da ni, na riga dana ci riba, babu hukuncin da za ku yi min wanda zai kai wanda na yiwa rayukan dana azabtar, raina ɗaya ne tak, da shi na kashe ɗaruruwan rayuka, da shi na azabtar da rayuka, da shi na 6ata zukatan rayuka, wanda har abada ba za a ta6a mantawa da ni ba.."
ya faɗa yana damula mummunan bakinsa.
Owais ya ji zafin maganarshi, ganin kamar babu alamun karaya a tare da shi, a ransa ya furta wannan wani irin shaiɗanin mutunne? Anya mutun ne Musa? Gaba daya Elders sun saduda banda shi, in wani ne yake a halin da yake a ciki wlh ko kalmar alifun bazai iya furtawa ba, amma da ya tuna wanene Musa gurin girman kai da izza sai ya fahimci koda ya karaya ba zai bari ya gane ba ko dan ya baƙanta masa rai.
Hakan yasa shi sakin murmushin gefen fuska.
Kafin ya soma yin magana cikin nutsuwa yana kallon cikin idanunsa.
"Waɗannan rayukan daka azabtar yanzu suna a cikin rahamar Ubangiji, sun barka da tarin hakkinsu akan ka, idan kana farin ciki saboda ka zalunce su to ka daina, kanka ka zalunta Musa! Ai kai musulmi ne, kuma ka san Allah baya yafe hakkin dake atsakanin bayinSa. Me ya ja ma shiga halin da kake a ciki?" Ya faɗa yana nuna sa cike da ƙyanƙyami.
"Hakkin waɗannan rayukan, sune zasu baibaiyeka da fitintinu iri iri har abada, bayan haka bari na yi maka fashin baƙi tun da na fahimci kai dabba ne, jahili, kuma daƙiƙi.."
cikin fushi ya ke jifar Owais da harara da idonsa ɗaya kamar ƙwayarsa zata faɗo ƙasa.
"Yanzu na ƙara yarda cewa zalunci ƙaiƙayi ne da ke komawa kan me shiƙa, abun da baka sani ba, silar tonuwar asirin ka, ƴar ka Zeenatu ta kashe kanta saboda jin wanene Ubanta da kuma zaluncin da ya yi ma ƴar uwarta Unaizah..."
bai ƙare maganar ba Musa ya yi wata irin zabura kamar zai miƙe, ya zaro idonsa waje cikin tashin hankali da baƙin cikin jin abun da kunnuwansa suka jiye ma shi.
"Meyasa na ga tun yanzu ka fara karaya, ai ban kai ka in da na ke son ka je ba, bayan haka rayukan daka ƙullawa makirci cikin kankanin lokaci sun warke daga raɗaɗin da ka ƙunsa musu, Shureim da Ummi suna atare da ƴar su Batool, da zarar mun gama shari'arku, zamu shafa fatihar auren su..."
cikin ƙunci da damuwa ya ƙara murtuke fuskarsa, ji yake kamar ya binne kansa don bakin ciki, zuciyarsa sai tafarfasa take yi..
"Sheikh Imam malik, da ka ƙullata a ranka, ka daɗe kana zaluntarsa don ka ƙunsa masa bakin cikin da zai yi silar mutuwar sa, a yanzu haka yana nan da ransa da lafiyarsa, harma ya je gano matarka Sarah da ke a kwance gadon asibiti, ka duba ka ga fa duk irin cutarwar da ka daɗe kana yi masa bai ji komai ba.."
Wata wutar baƙin ciki ce ta taso mashi ya dinga buga kansa jikin bangon bayansa, jikinsa ya ɗau zafi rau, ya Ilahi, Ya rasa ina zaisa ranshi ya ji dadi? Duk tsawon lokacin da ya ɗauka yana wahalar ƙulla masu makirci don ya baƙanta masu rai kenan yanzu komai ya tashi a banza? Hakan na nufin haƙarsa bata cimma ruwa ba? Kwata kwata Imam bai ji zafin komai ba a ransa? Shifa duk a zaton shi imam malik yana a kwance gadon asibiti rai hannun Allah, ciwon zuciya ya kama shi ashe wai har yana da kuzarin da zai iya taka ƙafar sa!
Chief Owais da ya lura ya haɗa masa sha tara na baƙin ciki wani sanyi ya ji yana ratsa zuciyarsa..
"Ka kwantar da hankalinka mana ai ban ƙarasa maka labarin ba, ƙanwarka Laura..." Zare idanunsa ya yi cikin damuwa.
"Sakamakon razanar da ta yi lokacin da ta ji komai game da kai, ta haɗiyi zuciya ta mutu."
gigicewa ya yi gaba ɗaya ya rikice har baisan sa'adda ya fara cizge akaifunsa ba, duk ya faffasa su, jini ya dinga tsattsafowa.
"Sannan, na ji abun da ya faru da kai, na taya ka baƙin ciki, ashe shatun bulalin jikinka, Evils ne suka zane ka, bayan sun tu6e maka suturarka ka dinga ihu kana kuka, suka shafe maka jikin ka da gishiri suka jefa ka cikin ruwa, na ce dama tsakanin shaiɗan da ɗan uwansa shaiɗanu ana samun sa6ani? Sai kuma na ji wai na hannun damanka Mark ne ya ci amanarka, ya musanya maka zuciyar Batool da ta giant, abin takaici! A ƙarshe burinka bai cika ba, kuma zaka mutu baka cika shi ba...."
Wani nishin baƙin ciki da Alhaji Musa ya saki nan take ya burkuta zawo a cikin wandonsa, wari ya cika cell ɗin.
Chief Owais ya toshe hancinsa da bakinsa da hanky, har sai da ya yi kakarin mai.
Da ƙyar ya iya furta, "Ƙato da kai kana sakin kashin zaune, ko ka yi zaton ni kaɗai nake tare da kai..."
Ya faɗa tare da nuna masa surveillance cameras ɗin dake a kowace kusurwa, "Ba wai iya jami'an isod ke kallon ka ba, duniya ce take kallonka..."
Wata zabura Alhaji Musa ya yi jikinsa ya hau kerma kamar mazari, tashin hankali tsantsa ne akan fuskarsa, kunyar duniya ta kama shi.
6a66akewa da dariya Owais ya yi, "Haba ranka shi daɗe, meyasa tun yanzu zaka razana? Ba zaka bari mu shiga kotu ba.."
Ya faɗa tare da juya masa Screen ɗin Ipad ɗin hannunsa, wai ashe tun zaman shi live video ya ke ɗauka.
Alhaji Musa ji ya yi kamar ya haka ƙasa ya binne kansa saboda wutar bakin cikin dake azabtar da zuciyarsa, Owais ya gama da shi, ya kashe shi da ranshi, ya ruguza duk wani mutuncinsa a idon duniya,