Kurkukun Kaddara Final StepComplete Hausa Novel

Author :  Boss Bature Category :  Complete Novels

Chapter   54 / 107

159K to 162K   out of 319.4K words

Sijnil ƙadar, babu inda aka rubuta jinin Elder ne kaɗai zai iya gadonsa, don haka maganarka babu ƙamshin gaskiya a cikin ta."


"Jan le6e baka karanta da kyau ba, kai da baka jin inyamuranci?"


Ya faɗa yana dubansa.


"Na fahimci masu haɗamar kujerar Elder suna da yawa, sai dai babu wanda zai mallake ta, dole sai jininsa, ku yarda ko karku yarda, wannan maganar dana faɗa tana a cikin littafin tarik sijnil Qadri..." Cike da ruɗu suke kallon shi ....

"Babu ƙamshin gaskiya a maganarka, Elder bashi da wani dangi nasa, idan ma kana nufin ya'yansa to kuwa ba zasu kar6i karagar tsafi ba, saboda sun ƙyamaci abun a zuciyar su, dole sai ɗaya daga cikin mu zai gaje shi.." Jan ƙeya ne ya faɗa..



Gaba ɗaya sautin maganganun su ya cika ɗakin da suke kowa yana tofa albarkacin bakinsa duk dai akan kujerar Elder Obinna.


Musa ransa ya 6aci zuciyarsa ta zo wuya, gani yake rainin wayau ne yasa suka zo don su dakatar da shi, gashi suna ta 6ata mashi lokaci..~_____💞______💗_____💘_____🌹______💋_____💫_____🫀___~



*~THE FINAL ATTACK 2~*




Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin kaninfari 1k Tsimin dabino 1k Gumba 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 4k
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 maganin Infection 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k https://wa.link/l1gcz8 kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki.


*~THE FINAL ATTACK~*



Cikin fusatacciyar murya ya ce, "Na fahimci idan na bi ku ta lalama ba za ku bari in samu abun da nake so ba, na rantse dole In hau karagar Obinna! kota halin ƙaƙa, babu ruwana da ni bare ne, ko ban cancanta ba! Ni ba amincewar ku nake nema ba! In kuwa kuka yi yunkurin dakatar da ni zan yi maku abun da baku ta6a tsammani ba, hmmmmm."


Ya faɗa yana mai yi masu kashedi.


"Ka shiga taitayinka Musa, karka cika zaƙewa, hawa karagar Obinna saida amincewar mu, don haka bamu amince maka ba, saboda baka cancanta ba, kuma ba jininsa bane kai, don haka ka yi gaggawar ba mu zuciyar yarinyar mu tafi da ita..."


Elder din da ya ɗauko maganar bai kai ga direta ba Musa ya tari numfashin shi da cewa, "In har ni bazan gaji Elder ba, to kuwa babu wanda zai gaje shi a cikinku, idan kuma kuna da ja, mu kara da juna wanda ya yi nasara shi ne zai gaje shi..."


Ya faɗa yana sakin shu'umar dariya.


Kallon kallo suka shiga jefawa junan su, yadda ya yi maganar a gadarance da izza yasa suka fahimci da akwai shirin da ya yi masu ta bayan fage.


Takun tafiyar da su ka ji ne ya ja hankulansu ga kallon mai shigowa.


Dr Mark ne ya shigo hannunshi ruƙe da kwalba fara mai ɗauke da zuciyar mutun a ciki duk jini a jikin ta.


kamar baiga sauran Elders din ba, ya nufi ubangidansa yana sakar masa murmushin nasara


"Sir, na yi nasarar cire zuciyarta, batare da na samu wata matsala ba."


Washe baki Musa ya yi kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna, farin ciki ya cika shi.


Miƙa ma Mark hannu ya yi yana kokarin kar6ar kwalbar, Jan Le6e ya buge hannun shi da sandar shi, ya kai hannu Zai kar6i kwalbar, Dr mark ya janye ta.


"Ka yi kuskure Jan le6e, ba a shiga hurumina..."


wani azababen naushi ya kai ma Jan le6e a mummuƙensa.


Rai a 6ace Jan ƙeya ya 6ace ya dira a gaban Mark ya damki kwalbar zai ƙwace, Musa ya shaƙe wuyan shi ya wujijjiga shi tare da ture shi gefe ɗaya.



Jan gemu ya yi kukan kuka ya dira a gaban Dr. Mark, har ya miƙa hannu da niyar ya kar6e kwalbar, Musa ya sa ƙafarsa ya taɗiye shi, gaba ɗaya sun fito da maitarsu a fili, hankalinsu ya tashi haiƙam kowa burinsa ya kar6e kwalbar zuciyar.



(Ina ma a ce zuciyata ce suke rububi akanta, ai dana basu sun bani kuɗi😂 just for fun)


"Baku so zaman lafiya ba, wallahi babu wanda ya isa ya ta6a kwalbar nan batare da na ɗauke masa kai ba..."


Ƙawanya suka yi ma su gaba ɗayan su suna huci kamar mayunwatan zakuna!



Da ganin haka sai Musa ya yi ma Mark alama da hannunsa, shu'umin murmushi Dr Mark ya saki tare da yin fito mai sautin gaske, a ruɗe suke kallon Evil Giants din da ke ratso bango suna shigowa ciki, wasu ta sama suke durowa wasu ma bayyana suke yi a tsakar ɗakin.



"Nasan za ku yi mamakin tayaya akai Giants suka koma suna bin umarnina..." Ya faɗa a gadarance.




"Su kan su sun miƙa wuya saboda sun ga cancantata da in zama ubangidansu, nafi ku jarumta da komai tun da har na kawo ƙaddara da bugun zuciyar kurkuku..." Kwata kwata basu ji tsoro ba, kuma basu karaya ba, duk da sun sha jinin jikinsu saboda masu iya magana na cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi.



"Ku farmake su, bana so kubar ɗaya daga Cikin su a raye!"


"Ma ci amana! Dama burinka ka ga bayan mu butulu, ka jira ka gani idan muka gama da su zamu dawo kanka ne." A cewar Jan Gashi.


Bushewa ya yi da dariya cike da izza ya ce, "Wanda ya ke goyon bayana ya zo mu tafi." Yana faɗa ya juya cike da izza ya yi ma Mark alamar ya biyo bayan shi


"Ku gafarce ni, bazan iya ci gaba da zama tare da ku ba, bazan iya ja da Evil Giants ba, bayan haka nima asirina ya tonu, ina buƙatar wanda zai ƙara mini karfin sihirina don in kare kaina."

Jan ido ne ya faɗa tare da juyawa da sauri ya bi bayan Jan wuya suka tafi.

Jan le6e ma ya ce, "Kada in yi biyun babu, jami'ai nema na suke yi ruwa ajallo, don haka zan bi bayan Jan Wuya, ba don ina goyan bayansa ba, sai don ina so inyi amfani da damar da nake da ita kafin in salwantar da rayuwarsa..."


yana ƙarashe maganar shi bai jira amsar su ba ya juya ya bar gurin.


"Matsoratan banza! Sun bani kunya, ba zamu raga musu ba, dole mu kashe su, sannan mu kuma ƙwace zuciyar yarinyar."

Jan dasashi ne ya faɗa, gaba ɗaya ransu ya gama 6aci, zuciyar su sai tafarfasa ta ke yi da baƙin ciki.



Girman kai ba zai bari su bi bayan shi ba, saboda sun tsani izzar shi batun yau ba ya saba shiga hancinsu da ƙudundune..



Kewaye su Giants suka yi kowan nan su ya ɗaura ɗamarar yaƙi, nan ta ke faɗa ya kaure a tsakanin su da Evil Giants, wata irin ƙura ta buɗe falon, haɗuwa suka yi su shidda suka haɗa ƙarfin sihirin su cikin sa'a suka kashe Evil Giants din dukansu. Sai haki suke yi saboda wuyar da suka sha.


_Kar mu tsaya 6ata lokaci, nasan i yanzu sun kusa isa Temple of Evils, don kai ma dodon tsafi zuciyar, mu hanzarta bin bayan su mu kashe su, kafin Musa ya aiwatar da mugun nufinsa"_


Suna ƙoƙarin ɗaga kafafunsu don su bi bayansu, Kwatsam! babu zato ba tsammani suka tsinkayi muryar mutun a cikin kunnuwansu,


"You're under arrest!" Tsantsar ruɗani ne ya hana su juya baya su fuskanci wanda ya yi maganar.



Sunyi matuƙar razana da jin baƙuwar murya, nan take suka fahimci hari aka kawo masu!



"Tayaya hakan zai yiwu? Wayasan da zuwan mu? Ko dai Musa ne ya yi mana cinne?" Tambayoyin da suka cika zuciyoyin su kenan.


"Wanene kai?"? Jan Gemu ne ya tambaya.



"Director General Of Isod." Ya bashi amsa kaitsaye.


Zazzare idanu suka yi a matuƙar ruɗe suka juyo suna kallon shi, yana a tsaye sanye da kakinsa ya goya hannayensa akan broad chest dinsa.


Basu gama razana ba saida suka ga Isod Soldiers da U.s armies suna shigowa falon hannayen su ruƙe da bindigu ƙirar dragon breath.


"Tayaya hakan zai yiwu? Mafarki ne ko gaske? Waya faɗa maku inda mu ke? Kuma Tayaya akai kuka iya shigowa kurkukun nan?"



"Ba zuwa muka yi don muyi fira da ku ba, ku miƙa wuya cikin lalama mu tafi, Idan kuma kuka yi yunƙurin guduwa, jikinku ne zai gaya maku!"



Commender James ne ya fada yana mai yi masu kashedi da kakkausar murya.



"Kar wanda ya kuskura ya matso kusa da mu, idan ba haka ba, zamu salwantar da rayukan ku, baku isa ku kama mu ba, makaminku bazai yi tasiri akan mu ba. An gaya maku ja da mu abu ne mai sauki!" Jan Dasashi ne ya fada cikin fushi da 6acin rai.


Jan Gashi ya ce, "Musa ne ya yi mana cinne, maci amana, ya yaudare mu, ya zama dole mu 6ace ......"



A lokaci ɗaya suka buga sandunansu ƙasa da niyyar su 6ace, sai dai me, babu abun da ya sauya suna nan a inda suke, a ruɗe suka kalli sandunan nasu, cikin zafin nama suka ƙara buga su da ƙarfi, still basu bace ba, firgici da karayar zuciya ce ta same su, sam sun gaza yarda da abun da ke shirin faruwa da su, cikin ɗimuwa suka ci gaba da bubbuga sandunansu ƙasa kamar mahaukata duk sun bi sun ruɗe.


Sojojin dake a kewaye da su sun yi tsaye suna kallon su, kamar masu kallon wasan ƙwaiƙwayo.


"Idan kun gama buga wasan naku, muna jiran ku." A cewar Chief Owais.

Ba su yi aune ba, kwatsam! Wani baƙin hayaki ya soma kurɗaɗowa ta cikin ƙofofin hancinsu akan idanun su, wata irin razana suka yi ganin Evils din jikinsu suna fita wanda hakan na nufin sihirin su ya bar jikin su yanzu saura ƙarfin da Allah Ya halicce su da shi, Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana! Rikicewa suka yi, sun rasa gane wanene ya yi masu wannan aika aikar?

"Arrest them!" Chief ne ya faɗa, da sandunan hannayensu suka soma kokarin kaima sojoji bugu, aikuwa suka rufe su da bugu saida suka raunata kowace ga6a ta jikinsu, suka yi masu bugun mutuwa, suka wanke jikinsu da jini, daga wanda ya rasa hakoransa sai wanda ya rasa idonsa ɗaya, duk saida suka rarrabasu da kayan jikinsu ya rage daga su sai gajerun wanduna, jikin nasu ma babu kyan gani duk gashi cunkushe wasu ƙazamai da su, gaba ɗayan su farar fata ne, basu ta6a muzanta da shiga tashin hankali ba irin na yau, kafin sojoji su tafi da su, ɗaya daga cikin su ya fakaici idanunsu ya yi saurin zare bindiga daga ƙugun soja batare da sojan ya ankara ba, ya harbe maƙoshin shi nan take ya faɗi a mace, ɗaya kuma Zuciyarsa ce ta buga da bakin ciki nan take ya faɗi shima a mace, sun ƙwammace su kashe kansu akan a tafi da su saboda sunsan ba zasu yi masu da kyau ba, a tunaninsu mutuwa ce mafita a gare su, basu san cewa sun ƙara jefa kansu cikin musiba bane don har ƙwara su ji kunyar duniya.



Sojojin basu ji dadin wadanda suka mutu ba, saboda ba su son su mutu batare da sun fallasa ma duniya abun da suka aikata ba, sun fi so su ji kunyar duniya, su kuma gir6i abun da suka shuka.

Ukun da suka rage basu a cikin hayyacin su shiyasa basu iya ta6uka komai ba, dama da igiyoyinsu suka zo, aikuwa suka ɗaɗɗaure su kamar dabbobi, shidda daga cikin sojojin suka fuce da su daga kurkukun ta ainihin babbar ƙofar fita daga kurkukun ƙaddara wadda a ƙalla tayi shekaru sama da ashirin batare da an buɗe ta ba sai yau da dubunsu ta cika! Ko tayaya akai hakan ya faru? Nima na ruɗe amma bari dai mubi alƙalamin Boss !


Shin Ina Jan Wuya ne 😳?




Ransa fari fat, ya ƙaƙa6e kwalbar zuciyar a ƙirjin shi, shine a gaba gaba, Dr Mark yana a gefen shi, Jan ido da Jan le6e suna a biye da bayansu kamar bindi, sai zumbula uban sauri suke yi don su ƙarasa ga temple of evils.


Inda mazaunin dodon tsafin su ya ke, tsabar yadda suke sauri kamar zasu tashi sama..



Lokacin da suka kusa ƙarasawa daga inda suke suna iya hango Temple of Evils da ke a kewaye da wasu samudawan Evil Giants, dogaye ne masu fadin kirji, tun da uwata ta haife ni ban ta6a ganin mutane masu irin ƙwanjin su ba, kallon su kaɗai zai iya sa gaban mutun ya fadi, ga mutum mai tsoro har suma zai iya yi idan ya gansu saboda firgitarwar da ke gare su, zai yi wuya in mutane ne ba zallar evils ba, hatta sautin takunsu kamar na dawakan yaƙi, gaba ɗayansu a sanye suke da jajayen dogayen riguna masu huluna, baka iya ganin komai nasu daidai da idanuwansu sai dai su su ganka, wadannan Evils din daban suke ko a gidan Kurkukun Ƙaddara, sune masu tsaron temple dinsu wato mazaunin dodon tsafin su. Suna da ƙarfin iko, basu san wani abu wai shi tausayi ko imani ba, saboda babu wannan a cikin zuciyar su, kuma suna da sharuɗɗansu, kafin ka tunkare su ka tabbatar babu tsarki a tare da kai! Ba'a ambaton sunan Allah gurinsu ko wani abu da ya shafi addini! Suna da girman kai da izza, basu magana sai dai suyi kwatance da hannayensu, suna dariya amma basu kuka, ba su ɗaukar raini, kuma ba a yi masu ƙarya, uwa uba ba su son maci amana, ba su yarda da kowa in ba Elder Obinna ba da aminin sa Jan Harshe, su kaɗai ne suke basu umarni su bi batare da an samu matsala ba, amma bayansu babu wani mahalukin da ya isa ya kawo masu wargi batare da sun azabtar da shi ba. Kuma idan zaka shekara kana zarya a gidan kurkukun ƙaddara ba zaka ta6a ganinsu suna sintiri ba, basu wuce iyakarsu, aikin su a temple yake nan kaɗai zaka iya ganin su, bakowa ke iya ganin mazaunin dodon tsafi ba sai mai sihiri a jikin shi, ko lokacin da sojoji suka kawo farmaki sun shiga ko'ina amma idanunsu basu gane masu mazaunin dodo ba, idan masu karatu ba zasu manta ba, Unaisah tamu tagargajiya ta ta6a yi masu leƙen asiri har suka yi mata wankan jini, itama a lokacin Allah ne ya nufa zata ga temple din da idanunta sai dai bata ga ainihin mazaunin dodon ba, da kuwa ta gama gani a duniya.

Yayin da suke tunkarar su,


Wani mayaudarin kallo Mark ya ke bin Musa da shi mai wuyar fassaruwa, batare da shi Musan ya lura ba, da alama akwai wata a ƙasa.



Jan ido da Jan le6e dai sai bin su suke yi kamar jela, kowannansu da muguwar manufarsa a rai.


Lokacin da suka ƙaraso gaban ƙofar Temple din, dakatawa suka yi da yin tafiya ganin yadda temple Evils din suka kare kofar shiga.


Cike da gadara Musa ya soma yi masu magana cikin harshen su na matsafa,


"Na cika sharuɗɗan da aka buƙata, na kashe Kaddarar Kurkuku, na kuma cire Zuciyar Kurkuku." Ya faɗa yana nuna masu kwalbar zuciyar cike da alfahari.


Sannan ya ɗaura da cewa, "Don haka ku bani hanya in wuce ciki, yanzu ni ne shugaban ku..."


Ya ƙarasa maganar cikin izza yana cika yana batsewa.


Da hannu, ɗaya daga cikinsu ya yi mashi kashedi mai nuni da gargaɗi.

Ƙyalƙyacewa ya yi da ƴar iskar dariyarsa cike da izza ya ce, "Kada ku ce za ku yi min taurin kai, ni ne uban gidanku a yanzu, dole ku miƙa wuya ku yi mini biyayya sau da ƙafa, idan ba haka ba da zarar na hau karagar Elder zan shafe babinku, ku bani hanya in wuce..." Ya faɗa yana dariya.

A hankali Dr Mark ya soma ja da baya da baya, cikin takun sanɗa ya arta a guje batare da sanin su ba, ya rage saura su uku.



"Ba ku ji abun da ya ce bane? Ku bamu hanya mu wuce, mu ƙarasa aiwatar da abun da ya kawo mu." Jan ido ne ya faɗa a tsawace...

"Anya kuwa ba a yi kuskuren wani abu ba? Meyasa suka ƙi bamu hanya mu wuce? Idan har da gaske sharuɗɗan sun cika kamata ya yi tunkan mu ƙaraso zasu dare su bamu hanya..."


Jan le6e ne ya faɗa zuciyarsa cike da kokwanto.


Cikin sauri ya dubi kwalbar zuciyar da Musa ya rungume a ƙirjinsa.

Nan take gabansa ya faɗi ganin wani abu.

Cike da tashin hankali ya ce, "Musa mun mutu! Ka ja mana bala'e, wannan ba zuciyar yarinyar bace...!" Kai tsaye maganar Jan le6e ta dira a kunnanshi, kusan a tare Jan ido da jan wuya suka dubi zuciyar dake a cikin kwalbar nan take suka ga tayi duhu baƙiƙƙirin sa6anin ɗazu da jini ne a jikin ta, tsantsar ruɗani ne da tashin hankali ya bayyana akan fuskokin su, wallahi an shammace shi, gaba ɗaya ya razana ya bi ya ruɗe ya rasa gane meke shirin faruwa da shi? Wanene ya ci amanarshi ya yaudare shi, tunawa da Mark yasa shi saurin furta sunan shi, "Mark!! Mark..!!!" Gabansa ne ya fadi ganin babu Mark babu alamarsa nan take ya fahimci Mark ne ya ci amanar shi ya bashi zuciyar evil giant a matsayin zuciyar Batool! Bai ta6a

54 / 107