Ranar Wanka Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 23

18K to 21K   out of 66.9K words

fa ce babu komai. Muna damuwa da yanayinta ko abinci kirki ba ta ci, domin breakfast sai ta kai har 11 ba ta yi ba."


Sosai ya ji babu daɗi yayin da zuciyarsa take gasgata masa ya tabbata azzalumi mai son zuciyarsa.


"Ku yi haƙuri in sha Allahu, za ta daina I will talk to her. I think distressed na karatun exam ne."

"You have to, kuma bana tunanin haka domin exam baya bata tsoro saboda kafin lokacin ma ta gama karatun shi, ina ga dai kamar yadda Ya Naufal ya faɗa haka ne." Cewar Abidin

Binsu da kallo ya yi har suka fice daga ɗakin.

Daga ɗakin na sa kai tsaye gurinta suka nufa, tana kwace da waya a hannuta tana kallon tsaƙon da ya yi mata kafin ya daina mata magana.


Kuka take sosai tana jin matuƙar kewarsa da ƙaunarsa na mamaye zuciyarta.

"Anty Hilah kuka? Ummu ne ta dake ki?" Amnaah ta furta wanda ya sa suka yi saurin hawa gadon suna tallafo ta.

Share hawayenta ta yi tana girgiza musu kai sai kuma ta tsinci kanta da ƙara sakin kukan wanda dukansu suka rungumeta suna taya ta.

Bayan fitarsu ya miƙe tsawonsa a kan gadon yana dana-sanin biyewa zuciyarsa, na ba shi shawarar ya fara mata magana, domin ga shi yanzu ya afka kogin nadama.


Miƙewa ya yi ya ɗauko wayar duk da gargaɗin da zuciyarsa take masa amma ba shi da zaɓin da ya wuce ya yi mata maganar.

Tun da suka shigo suka gama kukan, sai ba su fita ba suna ta hira da ƙoƙarin ɗauke mata damuwa.

Kiran sallar magariba ce ta fitar da su wanda Huwais ya ja su a Masallacin gidan su.

Ko da suka dawo ɗakinta suka koma, ba su bar ta ba har sai da Ummu ta kora kowa ya je ya kwanta.

Bayan sun fita ta yi shirin kwanciya, ta janyo wayarta tare da jero addu'in da ta saba zubawa kan ya kirata.


Buɗe datar da fara shigowar tsaƙon sai na sa ya shi go kamar haka:


"Barka da Juma'a kyakyawa mai farar aniya. Ina mai baki haƙuri bisa ƙin kiran da na yi, wanda na yi ne don ki fahimci soyayyar gaskiya kike mini ko ta ƙarya."

Babu jan aji kamar ba ita mai daraja da kima ba. Ta tura masa stiskers na kuka sau ba adadi. Sai kuma ta ƙara da rubuta


"Eh na faɗa soyayarka saboda iya kalamanka da adinin ka , don Allah kar ka ƙara guje mini."


Tun daga wannan lokacin suka manne da juna a waya. Hilah da ba ma'abociyar waya ba, amma a yanzu datarta a kunne take barin shi, saboda dakon jiran tsaƙon mahaukacin masoyi.

Wani lokacin sai dai ta danna waya tana murmushi. Gabakiɗaya ya sanya ta canza ɗabi'unta. Don Allah ya yi ta da kwanya da ta samu matsala a karatunta da haddarta.

Tsananin mamaki wani lokacin take yi, tare da ganin wautarta na faɗawa son mutumin da ba ta taɓa ko jin muryarsa ba. Ballantana haɗuwa na zahiri, amma tana jin a ranta ta kamu da ƙaunarsa damu-dumu.

A da duk maganar da suka yi sai ta gaya wa masa, amma da ta ga yana mata faɗa ta daina biye masa haka, sai ta daina sanar masa da komi, wanda hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai.

Ganin ƙaramar magana na nema zama babba sai ya yi tunanin dainawa, saboda ranar yasha mamakin kukan da ta sanya masa, tare da yi masa magiyar ya tura mata hotonsa ko ya kirata ta ji muryarsa.

Da sauri ya kashe gabakiɗaya tare da jifa da wayar yana gumi.

Safa da marwa ya shiga yi a cikin ɗakinsa. Lokaci guda ya birkice saboda ya yarda cewar ta kamu da sonshi.

"In har ta buƙaci mu haɗu ya zan yi?" Ya yi ma kansa tambayar cikin tsananin tashin hankali tare da kaiwa bango naushi har sai da ya ji zafi a hannunsa.

Saboda tsananin zafin da yake ji rage kayan jikinshi ya yi. Ya rage da ga shi sai singileti da gajeren wando.

A ransa ya yi ninyar daina kiranta gabakiɗaya a yau, amma kuma ya san da kamar wuya,gurguwa da auren nesa. Don yadda soyayyarta ta yi masa kamun kazar kuku, ba ya tunanin akwai a bin da zai iya dakatar da shi soyayyarta.

"Ta ya ya zan bayyana kaina a gareta, shin in har ta san nine mai zai faru? Na san babu aure a tsakaninmu, amma to ya zan yi da soyayyarta da yake ƙara ninkuwa a cikin zuciyata? Kuma wane mataki iyayena za su ɗauka?"

Irin tarin tambayoyin da suka cunkushe ƙwaƙwalwarsa kenan, wanda ke aiki bisa rashin ƙa'ida. Sai dai, kuma a ra sanya ya ɗauki ninyar duk wuya duk rintsi ko ana ha maza ha mata! Ba zai taɓa barin ta kuɓuce masa ba. Ko da Ummu za ta yi gunduwa-gunduwa da naman jikinsa ne. Kuma duk wani ɗa namiji da zai yi gigin kula ta shi e ajalinsa.

Ga mamakinsa sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka. Yayin da zuciyarsa ke harbawa tamkar za ta fito waje. Ya san cewa kukan nan zai ta yi har ƙarshen rayuwarsa matuƙar bai mallaketa.

Hilah kuwa ganin ya sauka ta shiga cikin matsananin tashin hankali har sai da ta ji zafafen hawaye sun gangaro mata.

Da sauri ta fara tura masa da tsaƙo, amma ganin ya sauka gabakiɗaya ya sanya ta fasa tare da riƙe wayar tana ji kamar ta kwaɗa wayar da ƙasa.

Jikinta a sanyaye tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki, ta fara gwada kiran numbar duk da ta san cewa ba ɗauka zai yi ba.

Ganin wayar ta ƙi shiga, ya sanya ta kashe wayar tare da jifa da ita kan kujera. Hannu ta sanya ta tallabe kanta da take jin yana sara mata tamkar zai rabu gida biyu.

"Ina jin son mahaukacin masoyi shi zai xamo ajalina." Ta furta cikin tsananin damuwa tare da kwaranyowar zafafen hawaye daga kwarmin idanunta.


Zubbur ta miƙe tare da leƙawa falo ta duba ko Ummu na nan. Ganin babu kowa sai tangamemen tibin bangon da ke barazanar mamaye bangon falon, ya sanya ta ruga da sauri ta nufi sashinsa.

Da sauri ta fara ƙwanƙwasawa a hankali tamkar wata mara gaskiya. Knoking ɗaya ya gane wacce take buga ƙofar.

Hannu ya sanya tare da share hawayen da suke zubo masa ya miƙe. Har zai buɗe ƙofar sai ya kasa ganin kansa a madubi da ya yi. Idanunsa sun nuna alamun ya yi kuka.

"Yaya ka buɗe ni ce." Ta yi maganar tamkar wata mai raɗa.

"Ki je zan shigo."Iya abin da ya furta kenan tare da komawa cikin ɗakinsa.


Mamakin kalar muryar da ya yi magana ya kamata, har ta fara tunanin ko ya fara shaye-shaye ne.

Juyawa ta yi cikin takaici ta koma ɗakinta ta kwanta. Filo ta ɗauko tare da rungume shi a ƙirjinta tana ganin wauta da wawancin da ta yi har ta fara son shi.

Washegari da safe bayan ta haɗa break ta karya ta wuce school.

Suna zaune sun gama lectured suna jiran lokaci ya yi, don za su yi sha ɗaya zuwa ƙarfe ɗaya.

Ta kalleta wacce ta ke riƙe da drink na exotic tana sha.

"Lafiya Hilah?" Ta yi mata tambayar tare da dafata ganin yadda ta shiga kogin tunani.

Firgigit ta yi kamar wata mai bacci ta yi tana kallonta. Sai kuma hawaye shar! Suka fara zuba a ƙuncinta.


"Ya zan yi? Son mahaukacin masoyi yana neman ya yi ajalina."

Zaro idanunta ta yi cikin mamaki jin abin da ta faɗa.

Miƙewa ta yi cikin damuwa tare da kallonta sai kuma ta zauna ta kama hannunta.

"Kamar na san mai zai je ya dawo Hilah! Wannan dalilin ya sanya na ƙi aminta da shawarar ya da baki."


"Ki fahimce ni sam bai yi da wata manufa ba, domin ya yi ne don mu gano wane n..."


"To yanzu wa gari ya waya? Kuma mai hakan ya jawo? Kin faɗa son mutumin da ba ki sam wane ne ba. Musaki ne ko mummuna duk ba ki sani ba."

"Ko ya ya yake ina son shi. Ji nake kamar zuciyata za ta kasa daurewa, akan shi zan yi fito na fito da iyayena su nemo mini mahaukacin masoyi."


"Innalillahi! Hilah, kin san abin da kike faɗi kuwa? Bijirewa iyayenki za ki yi kan wani banza wanda ba ki san waye shi..."


"Kar ki ƙara zagin mini masoyi domin zan iya ɗaukar mummunar mataki a kanki duk da alaƙar dake tsakaninmu."

Tsananin mamaki ya kamata matuƙa gamin ta ɗaga hannu xa ta mareta.

Saukar da hannun ta yi daidai lokacin da ta riƙe kumatunta tana faɗin,"Marina za ki yi?"

"Zan iya miki abin da ya fi haka. Wataƙila ba ki san yadda nake son shi bane. Gab nake da na yi fito na fito da kowa."

"Hmmmm!' Ta furta cikin tsananin mamaki tare da jan ajiyar zuciya mai ƙarfi.

"In har za ki iya ɓatawa da kowa sai na ce kin ɗauko wa kanki dala babu gammo. Sanin kanki wace ce Ummu da kuma irin zafin da take da shi. Tana gani ba za ta yarda ki ƙi auren Hamad ba, saboda wani da ba ta san shi, kuma bayan hakan ba ki yi wa Hamad adalci ba, domin masoyi ne shi na haƙiƙa."


"Allah ya sanya duniya da sama zan ɗauka. Sannan duk abin da zai faru a shirye nake."


Lamarin sai ya yi matuƙar ba ta mamaki da ɗaure mata kai. Ta san wace ce Hilah, domin tana da haƙuri da matuƙar biyayya ga iyayenta. Za ta iya cewa wannan shi ne karo na farko da saɓani ya shiga tsakaninsu.

Da sauri ta sha gabanta ganin ta miƙe zata wuce."Haba sahibata! Kar mu yi haka dake. Na fahimci yadda kike son shi."

Jin abin da ta ce ya sanya ta jata suka koma suka zauna suna fuskantar juna.

"Yauwa dama na san za ki fahimce ni. Soyayyaarsa ce ta sanya na yi miki haka, don ina jin duk wanda ya nemi ya raba ni da shi zan iya jan layi a tsakaninmu."

"Na yarda tun da ga zahiri kin nuna."Ta furta cikin mamaki tare da jinjina soyayya.

"Yanzu mene ne abin yi? Na kasa tunain komai. Kawai ji na ke yi sonsa zai kashe ni."

"Mu yi addu'a, amma ki duba lamarin don Allah. Musammam yadda Hamad zai ji. Kin ga Abu ya hana shi kula ki sai dai ya kira bai fi sau ɗaya a sati a. Cewar sai kin gama karatu, kuma haka ya ji ya amince. Tsawon shekaru nawa yana jiran.."


"Don Allah! Mu bar maganar nan, matuƙar ba shawarar yadda zai sanya ya bayyana kansa gareni ba."


"Addu'a ita ce kawai zan ba ki shawarar ki ci gaba da yi."

Da ta dawo makaranta kai tsaye sashinsa ta nufa domin ta san Ummu ba ta nan. Tun safe ta tafi ta'aziyar rasuwar da aka yi a family su.


Yana zaune da remote a hannunsa yana kallo. Mamakin ƙofarsa da ta gani a buɗe ta yi. Da ta shiga falon tsayawa ta yi tare da ƙura masa ido cikin mamaki.


Ƙurawa junansu idanu suka yi, yayin da take kallonsa cikin tsananin soyayya irin ta 'yan'uwanta, shi kuma kallon so yake mata. Wani irin abu yake fisgarshi daga cikin idanunta yana aika masa da maganaɗisu a cikin ƙwanyarsa.

A hankali ta tako ta ƙaraso zuwa kan kujerar da yake har suna gogon juna

"Ya faɗa min zan ce za ka je na ganka ka sha ado haka?"

Dariya ya yi jin abin da tace tare da sanya hannu sa ya karɓi wayarta da take ƙoƙarin ɗaukarsa hoto.

"Na yi miki kyau ne?"


"Sosai kuwa! Ka ganka ne? Tamkar wata a cikin taurari."


Murmushi ya yi sosai har kumatunsa suka lotsa wanda ya ƙara masa kyau.

"Zan ce zani ba ki ba na buɗe ƙofata ba. Najib ya sanar dani yana hanya zai raka ni zance."


Sosai ta bayyana farincikinta wanda ya ba shi haushi ganin ba ta kishinsa.

"Wow! Wace mai sa'ar ce Yaya? Ko da yake bai kamata na yi maka wannan tambayar ba, tun da na san akwai wacce ta tsaya ta kashe kuma ta tsare tsawon shekaru."


Kafin ta kai aya ta ga yanayinsa ya canza wanda ya sanya gabanta ya faɗi.

"To ba zan ce za ni ba. Najib xan raka mahaifin Samahatu ya ce ya zo." Ya yi mata maganar cikin ɗaure fuska.

Ganin yadda ransa ya ɓace ya sanya ta ji babu daɗi.

"Am sorry ina ɓata maka rai! Ka yi haƙuri ni fa adalci na ke son ka yi wa Anty Wajnah."Sai kuma ta yi shiru ganin ita kanta soyayya ya sanya za ta yi butulci.


Da sauri ta kama hannu sa da ya yi banza da ita yana canza tasha domin ta gama ba shi haushi.


"Na fahimci yadda kake ji Yaya, domin ni kaina ina cikin halin da kake ciki, wanda in zan auna da yadda nake ji zan iya maka adalci."


"Yauwa 'yar ƙanwata na manta ta faɗa son mahaukacin masoyinta." Ya ce mata cikin murmushi tare da jan hancinta.

"A soyayya ta ne ya hauka ce, amma shi mutum ne mai hankali, musamman yadda iya furta kalamai cikin baiwa da da hikima. Sannan duk ilmina sai da na sara masa gurin amafani da ayar Allah da hadisan manzon Allah."


"Au dama akwai namijin da za ki iya yabo kamar haka? Bayan kin sha gaya mini babu namijin da kika taɓa gani irin.."

"Come on, Yayana. Kai fa na daban ne, kuma ɗan'uwana na jini, shi kuma soyayyace a tsakaninmu. Har yanzu kana nan a matsayinka na musamman ne kai. Special and extraordinary."


"Hmmmmh!" Ya ce mata kawai amma ya ji babu daɗi yabonsa da ta yi."


"Da gaske na ke yi, kuma magana na ke son mu yi." Ta furta mishi tana kallonsa tare da kama hannunsa duka ta riƙe.


"Fita zan yi ki bari sai na dawo, don na san kan mahaukacin masoyinki za ki yi maganar." Ya ce domin har ga Allah kishi yake yi sosai, ganin ba ta san shi bane, amma ta faɗa son wani can.


Ta buɗe baki za ta yi magana sallamar Najib ta katse ta.

"In ka ga wata dole ka ga zarah. Ni dai har yau ban taɓa ganin ƴan'uwa masu tsananin ƙaunar junansu ba." Ya furta tare da ƙarasowa yana tafa hannunsa yana dariya.

Dariya suka yi tare da miƙewa."Barka da zuwa Ya Najib." Ta furta yayin da ta nufi frij ɗin sa ta ɗauko ruwa mai sanyi da drink ta ine, sannan ta nufi kicin don ta ɗauko cup.

Bayan ya amsa sai ya bita da ido kamar yadda ya ga ya raka ta da ido har ta ɓule.


Naunauyar ajiyar zuciya ya saki tare da shafa sumar kansa yana murmushi ya juyo yana kallonsa.

Hira suka fara yi har ta ɗauko kofin ta ɗaurayo ta ije masa.

"Ni bari na tafi, Yayana, sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya dawo da kai cikin aminci." Da larabci ta furta tare da tsayawa tana kallonsa.


"Yauwa, ƴar ƙanwata. Allah ya yi miki albarka." Ya furta cikin jin daɗin addu'ar da ta yi masa.


"Amin." Ta amsa tare da ɗaukar jakarta tana yi wa Najib sallama.

A hanya Najib yake driving babu wanda ya fara magana sai ya waiwayo ya kalle shi ya maida hankalinsa kan hanya.


"Ina mamakin shaƙuwarku da ƙudirinka kan ƙanwarka, wanda na tabbatar da tsoron Allah da kake da shi ne yake rinjayar zuciyarka, amma da tuni ka yi abin da ba'a so."


"Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba."





TUNATARWA
Shin kina daga cikin matan da karatun Novels yake ɗauke musu hankali suke barin sallah ta wuce su? Ko kina daga cikin masu daina karanta Kur'ani ko azkar duk saboda karatun Novels? Don Allah yar'uwata musulma ki daina barin sallolinki na wuce ki saboda karatun litattafai Hausa, saboda ko mu MARUBUTA da muke yin typing da zarar lokacin sallah ya yi muke tashi mu yi sallah. A kiyaye da ibadu musamman sallah saboda ita ce farko da za a fara dubawa a cikin ayyukan mu. Da fatan za ki ji kuma ki hankalta. Fatanmu mu gudu kuma mu tsira tare. Allah ya bamu ikon aikatawa Amin. Taku Jamila lawal Zango.



Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423


*RANAR WANKA...*



NA



JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"



☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 8


BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba."


"To ta ya ya, za ka mallake ta? Kar ka manta ciki ɗaya kuka fito. Na sha gaya maka sheɗan ne kawai ke son wasa da zuciyarka, da yi mata ingixa mai kantun da xai sanya ka aikata abin da duniya za ta la'ance

7 / 23