Author : Jamsy Category : Complete Novels
ɗakinsa.
Takaicin abin da ya yi mata ya sanya ta fara hawaye. Ganin kamar haƙarta ba xa ta cimma ruwa ba, bayan cika baki da kuranta wa ƙawayenta yadda daren zai kasance fa ta yi.
Tana tsaye sororo tamkar gunki, ya murɗa ƙofarsa ya shiga tare da bugata da ƙarfi.
Da sauri ta juya don ta shirya kanta ta shiga cikin ɗakin, domin ta rantse ba za ta bar wannan rana ta wuce a tutan ma"aho ba.
Ɗaki ta shiga ta faɗa kan gado tare da sakin kuka. Sai kuma ta miƙe ta tuɓe kayanta ta shige bayi. Wanka ta sheƙa wanda ta ɓata lokacinta tana dirzar jikinta da mayuka masu ƙamshi da kyau.
Bayan ta gama wankan, ta zauna zaman shafa. Inda ta ɓata lokacinta gurin ƙyalƙyale jikinta da mayuka da turare masu ƙamshi da daɗin shaƙa.
Wata doguwar rigar bacci ta sa mai kyau fari. Rigar har ƙasa take, amma kuma ta na bayyana surar mutum.
Ƙara ɗauko turaren da Hajiya Zamzam ta ba ta yi tare da ƙara shafe ko ina na jikinta. Sannan ta sanya a rigar baccin.
Wayarta ta ɗauka ta duba kanta a madubi sannan ta rufe ƙofar.
A lokacin da ta murɗa ɗakin yana kwance a kan gadonsa, hannunsa riƙe da wayarsa. Bayan ya yi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa kayan bacci. Riga ya sanya da ƙaramin gajeren wando.
Kyawawan dogayen cinyoyinsa masu ɗauke da zararan gashi ya kwantar a saman filo, sannan ya kwantar da kansa a ɗayan filon. Kallon hotonta yake yi, yayin da hawaye suke zuba a ƙuncinsa.
Hannunsa ya kai ya shafa fuskarta, tare da sanya yatsarsa a saman idanunta, yana shafa idanunta da suke ɗaukar hankalinsa ƙwarai.
Ya faɗa cikin kogin tunaninta, ba tare da ya san Wajnah na tsaye tana ƙarewa halitarsa kallo ba.
Wajnah kuwa ji ta yi kamar xa ta sume. Haƙiƙa Allah ya yi mata tagomashi da samun miji mai kyawu kuma ɗan gayu, musamman da ta kalli yatsun ƙafarsa sai ta ji kamar ta duƙa ta lashe.
"Huwais," Ta ce tare da ƙara matsowa kusa da shi.
Da sauri ya miƙe tare da kifa wayarsa domin ya ɗauka ta ga abin da yake kallo.
"Ke! Uban me ya kawo ki cikin ɗakina?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai yana zare mata idanu.
Wal ta yi da idanunta tare da yi mata fari."Ni da ɗakin mijina sai na tambayi izinin shigowa? Karka manta da kai da duk gidan nan mallakina nane."
Tsaki ya yi, tare da da ɗaukar wayarsa ya fita a cikin galary sannan ya ije wayar.
Ganin tana matsowa tana son haɗa jikinsa da nata, ya sanya shi matsawa tare da ƙara daka mata tsawa. Yana ganin zallar rashin kunyarta na shigo masa a haka.
Ransa ya ƙara ɓaci sosai, ganin rashin kunyarta da tarbiya, domin ya tabbata da Hilah ce mai kunya ba za ta taɓa bayyana surarta ba.
"Ya Huwais, don Allah ka bari mu more rayuwar aurenmu. Wallahi na yi maka alƙawarin yin maka biyayya da zama tamkar baiwa a gareka. Ina sonka duk abin da kake son xan yi maka Yayana."
"Ba za ki taɓa samun zuciyata ba, domin na gaya miki tun farko baki cikin jadawalin matan da nake so. Sam ba ki yi mini ba, amm kika na ce sai kin aure ni. Ga gidan nan sai ki zauna a ƙarƙashin aurena, amma ni da jikina ba xa ki taɓa mallakarsu ba."
Duƙawa ta yi jin abin da ya ce. Jawaye ta fara tare da kai hannu za ta kama ƙafarsa wanda ya janye da sauri ya yana harararta.
"Don Allah mijina, ka soni mu zauna lafiya. Ka dubi tsarina da surata babu wacce mace da za ta tsere ni."
"Akwai ta ita ce wacce take zaɓin raina kuma na ke sonta. Ko da ace ba ta kaiki sura ba, amma ta fi ki komai a gurina." Ya faɗa tare da toshe hancinsa saboda ƙamshin turarenta dake hawa masa kai.
Ganin ya toshe hancin ya ƙara baƙanta ranta matuƙa. Ita da take tunanim ƙamshin zai karkato da hankalinsa, sai ga shi yana nuna baya son ƙamshin.
"Wallahi baka isa ba, matuƙar ina cikin gidan nan babu wata ƴar iskar da xa ta shigo gidan nan, in ba so kake mu yi mutuwar kasko dukanninmu ba."
"Karki ƙara zaginta domin a kanta xan yi mummunar saɓa miki."
"Ka kashe ni in ka so, ai xanfi jin daɗi ranar aurenmu ka yi mini shegen duka, kan babu abin da ya shiga tsakaninmu."
Hannu ya ɗaga, sai kuma ya fasa don ya san za ta iya gaya wa a gida.
"Dama na san ba ki da kunya, amma wallahi ba xan ɗauki rashin kunya ba."
"Matuƙar za ka rinƙa kiran wata banza a gidan nan, ni kuma abin da ya fi banxa zan kirata da shi."
"So kike na canza miki halitta." Ya ce tare da komawa ya kwanta.
"Ya Huwais, don Allah ka tausaya mini ka karɓe ni a matsayin mata." Ta ce cikin rawar murya jin mararta ya ƙara murɗawa.
Tsaki ya yi mata tare da komawa ya kwanta.
Ganin haka ya ta bin bayansa ta kwanata tare da rungumeshi ta bayansa.
Wani irin wawan ajiyar zuciya ta saki jin yadda gabakiɗaya tsigar jikinta ya tashi.
Da sauri ya miƙe yana mata mugun kallo da mamakin zallar rashin kunyarta.
"Tashi ki fita ko na saɓa miki."
Abin da ya faɗa, ya sanya ta ɗago idanunta, da ƙyar da suka rine suka canza kala.
"Don Allah ka taimaka mini ina cikin wani hali."
Hannunta ya kama, ya janyota har ƙofar ɗakin ya watsar da ita, tare da mai da ƙofarsa ya rufe.
Kallonta kawai ya yi, ya fahimci halin da take ciki. Sai dai inhar jikinsa zai mallaka mata ba zai taɓa ba, domin komai na sa mallakin Hilah ce.
Komawa ya yi ya kwanta, yana mamakin yadda ta nuna zalamarta da shan kayan matan da ta yi wanda ya san su suke ɗawainiya da ita.
Takaici da baƙinciki suka cika mata rai. Duba ga maza masu kyau da suka nuna suna son aurenta, amma ta nace sai shi. Ga shi ta aure shi yana wulaƙanta ta.
Ƙara ta saki jin mararta ya murɗa sai kuma ta fara ciwo.
Da kyar ta miƙe tana faɗin,"Na shiga uku! Ya Huwais, don Allah ka taimaka mini xan mutu cikina, marata."
"Ya Huwais," Ta kira sunan a gigice jin yadda mararta ta ƙara murɗawa.
Huwais kuwa yadda ya ji muryarta ya rikice sam bai damu ba. Kwanciyarsa ya yi tare da kunna karatun qur'ani, ta yadda xai daina jin buga ƙofa da sunansa da take kira.
Wayarsa ya jawo ya kunna data ya hau online.
Zuciyarsa ke kwaɗaita masa, ya tura mata da tsaƙo, amma wani bangare na zuciyarsa na yi masa gargaɗi.
Sauka ya yi dafa kan gado tare da buɗe labulen windon ɗakin. Tsakar gidan yake kallo, wanda hasken wutan lantarki ya haskaka farfajiyar gidan tankar rana.
"Anya zan iya daina waya da ke? Kai ina ba zan iya ba, domin ta hakanne kawai na ke samun natsuwa a cikin raina." Ya tambayi kansa tare da furta hakan cikin ransa.
"Hilah, ina sonki." Ya ce yana kallon fuskarta a wayarsa, sai kuma ya sanya bakinsa kan nata, ya yi mata kis yana murmushi.
Har ya fara yi mata typing, sai kuma ya kashe wayar duka ya ja bargo ya kwanta.
"Ya kamata na ba ki lokaci."
Wayar kuma ya kunna tare da tura mata tsaƙo.
A lokacin da tsaƙon ya shigo, tana zaune a kan sallaya bayan ta idar da sallah tana kuka.
Sosai take jin zafin yaudarar da ya yi mata, domin ta ɗauka yadda yake kalamansa da natsuwarsa, da kuma kyautar ban girma da yake mata mutum ne mai nagarta. Ashe mayaudari ne.
"Wayyo Allahna! Haƙiƙa ka cutar da zuciyata." Ta furta cikin muryar kuka tana jin zuciyarta kamar za ta yi bindiga ta fito.
Wayarta ta ɗauka tana duba duk chatts ɗin da suka yi. Wasu ta yi dariya wasu kuma ta yi murmushi mai haɗe da kuka.
"Ina sonka, why za ka yaudare no?" Ta rubuta mishi hakan sai kuma ta ƙara da
"Don Allah ka bayyana mini kanka, wallahi na yi maka alƙawarin zan aureka matuƙar kana sona."
Ji fa ta yi da wayar, ganin duk tsaƙonnin da take tura masa babu amsa, domin tun jiya lokacin da suka yi alƙawarin xa su haɗu, ya kashe waya bai ƙara hawa ba.
Tana ije wayar tsaƙo ya shigo, wanda da sauri ta ɗauka a ranta tana addu'ar Allah ya sa shi ne.
Ƙaramin tsaki ta ja, tare da canzawar fuskarta ganin tsaƙon Yayanta ne.
"Ya Huwais, ya ke yi? Shi da ya kamata ya kasance da matarsa." Ta yi ma kanta tambayar hakan.
Tsaƙon ta duba inda ta ga ya rubuta jamar kamar haka;
Ƙanwata, na kasa bacci tunanin halin da kike ciki da kewar gida sun dame ni.
Murmushi ta yi sosai tana mamakin ƙarfin zuciyarsa, domin ta yi tunanin duk borin da yake yi da xarar sun keɓe a tare zai ba da kai bori ya hau, kasancewar babu namiji da zai kasance da Wajnah ba tare da ya kware mata ba.
Yayana, don Allah ka yi bacci. Ina hadda ne kuma ni ma yanzu zan kwanta.Ta rubuta tare da tura masa tsaƙon sai ta kashe wayarta ta kwanta.
A lokacin da tsaƙon ya shigo, hankalinsa ya tashi sosai don bai yi tunanin idanunta biyu ba.
Da sauri ya janyo wayar, ya karanta murmushi ɗauke a fuskarsa. Iska ya ja tare da fesarwa.
Juyawa ya yi ɗaya ɓangaren ya danna numbobinta don ya kira.
"Ba ta yi bacci ba, tana cikin damuwar da na sanya ta. Ki yafe mini Hilah sonki da ƙaunarki suka janyo mini haka.
Ransa ne ya ɓace, matuƙa jin wayarta a kashe. Ya san ta kashe ne don karya kirata.
Ƙaramin tsaki ya ja, tare da jan bargo daidai lokacin da ya ji Wajnah ta ci gaba da buga ƙofa.
Duk yadda ya so ya yi bacci ya kasa.Ji yake gidan kamar ba mallakinsa ba. Miƙewa ya yi ya shiga cikin bayin ya ɗauro alwala tare da shinfiɗa dadduma ya tayar da sallah.
Kamar kullum istikhara kan lamarin ya fara. Tun ranar da ya fara sonta yake istikhara kamar yadda ma'aiki ya umurce mu da mu yi in muna son aikata wani abu.
Istikhara
* Neman zabin Allah, wata sallah ce mai raka'o'ibiyu, wacce yinta sunnah ce mu'akkada (sunnahce mai karfi), wacce manzon Allah ya koyar dasahabbansa ita har tazo garemu kamar yadda al-qur'ani ya iso gare mu, sallace da akeyi yayin neman zabin Allah akan wani al-amari kamar;aure, sayan gida/mota aikin gwabnati da daisauransu, sai dai ita wannan sallar ba'ayin ta a kan abin da ya ke wajibi ko mustahabbi akan ka; kamar neman zabin Allah akan yin azumin ramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitar da zakka, azumin alhamis da litimin da dai sauransu.
* Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan sun ci karo, misali: mutum ne yake son yaje umra karo na biyu a lokaci guda kuma yana so ya je wata kasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allah akan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su.
* Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikin lamarin sa, to ba zai yi nadama ba In sha Allah. Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159].
* Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) a cikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce:
"Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkumta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibatiamrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaanathumma raddini bihi."
"Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari]
* Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannan karantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafan koyarwa don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace
* Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi.
* Wannan Addu'a ta istikhara ana yin tane bayan ka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970].
* Babu wani hadisi daya inganta da yazo dasurorin da ake karantawa, a cikin sallar nemanzabin Allah.
* Haka kuma babu wani hadisi da yazo daga Annabi cewa idan mutum yayi istakhara zaiyimafarki ko zaiga wani mutum yana yi masa bayani al-amarinsa.
* Babu shakka duk wanda ya yi zai samu natsawa cikin abin da Allah madaukakin sarki ya zaba masa.
* Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutane dayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayin nutsuwar zuciya, idan aure ne sai kaji zuciyar kata qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka farasai kaji zuciyar ka tanutsu da sana'ar.
* Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana,ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita ne daga lokaci zuwalokaci har sai ka sami biyan buqata, sannan Ana yin tane ko da lokacin da aka hana yin sallah ne,idan bukatar hakan ta taso, domin ita tana daga cikin "Nawafilul Asbab" - "Nafiloli masu dalili".
* Wannan kenan don gane da abunda ya shafi Sallar neman zabin Allah madau kakin Sarki,Muna fatan Allah ya bamu damar Aiki Abin da muke rubutawa da karantawa.
Still yanzu ma natsuwa fiye da ta, da ya samu wanda ya ƙara ninka masa ƙaunarsa.
Ajiyar zuciya ya saki tare da janyo filo ya kwanta a sallayar.
Wajnah kuwa tun tana buga ƙofa, tana kuka tana kiran sunansa, har ta kasa sakamakon mararta da ya riƙe ya murɗe ko numfashi ta kasa.
Kallonsa kawai xai sanya ta rikice ballantana da ta haɗa jikinsa da nata.
Rintse idanunta ta yi cikin azaba tana kiran sunan Allah. Ta haƙura ne saboda duba agogo da ta yi ƙarfe ɗaya har da kwata. A lokacin ta gane ko kwana ta yi tana buga wa sam ba zai buɗe mata ba.
Jikinta ya yi sanyi matuƙar gaske! Domin bata taɓa tunanin bayan auren ba zai iya ɗauke kansa daga jikinta har ya wulaƙanta ta ta.
"Wace ce wannan da ta sace zuciyar mijina?" Ta yi wa kanta tambayar tare da jifa da filon da ta danne mararta.
Kuka sosai take yi yayin da wani sashe na ɓangaren zuciyarta yana gaya mata Huwais ba zai so ta ba.
Hawaye masu zafi suka ƙara kwaranya a idanunta, daidai lokacin da mararta ta ƙara murɗawa. Gurmususu a ƙasa ta shiga yi, tana kiran sunan Allah har ta samu sauƙi.
A hankali ta miƙe tana jan ƙafa ta shiga cikin ɗakinta. Kan gado ta kwanta tana nishin wahala da ƙyar.
Ta daɗe a haka har zuwa ƙarfe uku. Wayar Wahida kuwa ta kira yafi cikin kwandon masaki.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 20
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Ta daɗe a haka, har zuwa ƙarfe uku. Wayar Wahida kuwa ta kira yafi cikin kwandon masaki.
Tun da take ba ta taɓa kwanar wahala ba, domin yadda ta ga dare haka ta ga rana. Har zuwa kiran sallar farko ba ta rintsa ba
Kiran sallah na biyu ta ɗauki wayarta, tana dafe da mararta ta kira numbar Wahida, tana adduar Allah ya sa ta ɗauka.
Ta cika da farinciki jin wayar na ringing.
"Wash! Fahima ki taimaka mini mutuwa zan yi." Ta furta tana nishin wahala.
"Innalillahi lafiya?Ai sai da na gaya miki kar ko sha maganin nan da yawa, saboda shegen kafiyarki kika kai kanki kika baro. Allah ya sa bai illata ki ba." Ta faɗa tana mata dariyar mugunta.
"Ni