Author : Jamsy Category : Complete Novels
jin anyi aure ba tare da anga juna ba."
Ajiyar zuciya ya saki, wanda bugun da ya sanya zuciyarta har sai da ta kauda wayar a kunninta ta rintse ido.
"Kin shirya ganina?"
"Eh, kuma na yi maka alƙawarin aurenka ko da ace kai musaƙi ne."
"Shikenan, zan yi tunani in har ya kamata na bayyana miki kaina zan bayyana."
Yana faɗin hakan ya kashe wayarsa cikin tsananin tashin hankali. Safa da marwa ya fara yi a ɗakin, saboda yana jin ko aure ya yi ba zai iya daina jin muryarta da take kwantar masa da hankali ba. To amma kuma ta ya ya zai bayyana kansa kamar yadda ta buƙata? Shin inta gan shi wane hali za ta shiga, wanda ya san lamarin da ƙarshe ba xai yi daɗi ba, saboda yadda ta riga ta mutu a kansa.
"Zuciyarsa ta ba shi shawarar ya tura wani da bata taɓa sani ba, amma sai dai kuma ta gargaɗe sa da aikata hakan, saboda in har ta ɗauka shi ne mahaukacin masoyi ta kamu da son wancan, sai ya ce an yi ba ayi ba.
A ransa ya ji ba zai iya bayyana kansa ba, domin a wannan lokacin yake son ya ɗauko rigimar da zata wargaza farincikin zuriyarsu ba, don haka a kwai sauran lokaci.
Wayarsa ce ta yi ƙara alamun an turo masa da tsaƙo. Da sauri ya ƙarasa gurin wayar don ya duba tsaƙon
"Yayana, na gaya masa cewar ya bayyana kansa gareni ranar bikinka, kuma na yi masa barazanar rabuwa da shi matuƙar ya kasa yin hakan, amma bai ce mini komai ba, sai ma ya kashe waya. Na san zai kira ni kuma ya amince, saboda na san yana sona.
Wayarsa ya ije cikin damuwa ganin abin da ta rubuta.
"Anya Hilah za ta yafe mini matuƙar ta san ni nake wasa da hankalinta?" Ya yi ma kansa tambayar cikin damuwa. Ga mamakinsa sai ya ji hawaye na bin ƙuncinsa. Kansa ya dafe da ke matuƙar yi masa barazana.
Ta bangaren amarya gyara kawai ake yi babu kama hannun yaro. Tun a ranar da aka sanya bikin ta kama shan kayan mata ba tare da ta bi ƙa'idansu ba, saboda so take bayan biki, ya raina kansa. Wannan ji da kai da sham ƙanshi da yake mata ya gane kuransa.
Wajnah na cikin jadawalin mata da ba su tausayawa namiji a bangaren soyayya da aure, domin a tsarin rayuwarta. Ta auri namiji da zai zamo bawanta wanda za ta rinƙa juyashi yadda take so. Wato ta samu miji janitalau, wanda ta ci alƙawarin ko da ba ta samu ba, sai ta maida shi hakan ta hanyar shaye-shayen maganin mata.
A burinta ta so auren namiji wanda yake masifar sonta, don ta yi amfani da soyayyarsa ta juya shi yadda take so, amma cikin rashin sa'a sai Allah ya jarrabce ta da son Huwais, wanda shi ko a cikin family ta san basa shiri, saboda yadda take nuna wayewa da yawa.
A rayuwarsa ya tsani mace wacce feminism ɗinta ya yi yawa. Tun kafin ta fara nuna tana son shi, ya gane ita mace ce wacce take ganin mata sun samu daraja ne ta hanyar buƙatar da namiji yake da shi a garesu, wanda hakan ya sa take ganin kamar namiji bawa yake a garesu, kuma suna da damar da za su juya su yadda suke so.
Tun lokacin ya ɗaura mata karan tsana sam baya shiga sabgarta. Yana ganin ta a mara hankali da ƙarancin ilmin addini, domin duk wani gata da daraja mace Allah ya bawa mace, saboda ita ma halitta ce wcce ya halitta don su bauta masa.
Zaune take a cikin falon ƙawarta mai suna Fahima, da waya a hannunta tana zaɓan kayan mata da Hajiya zamzam; wacce take saida kayan mata a online ta tura mata.
Bayan ta zaɓi kayan da yawa wanda zaɓen yawanci Fahima ce ta taya ta, kasancewar ita matar aure ce har da yarinya ɗaya.
"Kin ga wannan sha ka ga aikin wallahi ki ɗauka yana da kyau, domin Hajiya Zamzam in har kika ga ta kawo kayan mata na gargajiya yana da kyau, saboda kayanta kin san duk na bature take siyarwa. Kuma da bikina na sha irinsa, shi ne na gaya miki Baban Amrah ya bani kyautar hajji, saboda duk lokacin da na sha ni kaina da ƙyar nake iya riƙe kaina."
Dariya ta kwashe da shi suka tafa. Aikuwa ya zama dalo na siye shi. Don so na ke Ya Huwais ya raina kansa. Ni fa so na ke ko kara na ije ya kasa tsallakawa, domin ya san in bai yi mini abin da na ke so ba, ba zan faranta masa rai ba."
"Eh, gaskiya. Ke ai magani sosai ya kamata ki siya saboda wannan miskilin da za ki aura. Kin ga in ba tsaye kika yi masa ba, wallahi wulaƙanci za ki sha sosai. Musamman da ba ya sonki."
Ƙuta ta yi cikin ɓacin rai." Ki barshi zai raina kansa sosai. Ba ni yake cika yake sharewa ba, saboda kawai na ce ina son shi. Wallahi sai na maida shi namijin ta ce babu boka babu malam. Don kawai Ummu ƴar'uwar mom ce, amma da ko ita sai na shiga tsakaninsu babu boka babu malam."
Dariya ta saki." Ai gara ki je da shirin ki maza yanzu babu tausayi a tsakaninmu da su, saboda kina musu sakwa-sakwa sai wulaƙanci da rashin mutunci. Sam bana son na kasance daga cikin irin matan da suke hide my identity a sirrin ƴa mace groups, kin ga kuwa dole na dage na kashe kuɗina na gyara jikina, don na siyawa kaina daraja da mutunci."
Dariya suka kwashe dashi suka tafa, ban da Habiba ta take kallonsu cikin mamaki tana murmushi.
"Ke dai sha'anin rijalu sai su. Ƙiri-ƙiri sun mayar da mata mahaukata sun sanya musu depression."
"Ai wallahi su suka so. Ke ni fa duk macen da ta zauna namiji na wulaƙanta ta ta ji za ta iya ne, don haka in har kuɗi na aiki zan siya maganin mata na gyara jikina, wanda kafin na ba shi haɗin kai sai ya yi kuka."
"Lallai ba ki da imani wallahi."
Habiba ta kalle su da suke ta magana ba ta sanya baki sai a lokaci ta yi murmushi ta ce," A tunaninku shan kayan matan shi zai gyara rayuwar auren ku? Ba zan fasa gaya muku ba a matsayina na ƙawarku aminiya. Wallahi ku guji shaye-shayen kayan nan da kuke yi, saboda ba ku san da me aka haɗa su ba musamman da bature, domin zai iya kai ku tashar dana sani. Kuna cusawa kanku abin da ba ku da tabbaci a kansa, don kawai ku juya mazajenku. To daga ranar da kuka daina shan kayan matan, ko kuma ya daina muku aiki shi kenan kun rasa damarku? Ni a ganina wannan kuskure ne, domin in har za ku riƙe biyayya da haƙuri za ku juya mazajenku yadda kuke so."
"Hmmm!Ta fara ni wallahi ban san dalilin da ya sanya kika na ce za ki zo yau ba." Wajnah ta ce tana aika wa Habiba da mugun kallo.
"Ki barta ta ci gaba bakinta ne ai. Gajiya da maganar ne ba ta yi ba, kuma kema in ban da abinki har akwai abin da za ta faɗa ya dame ki. Ita da take yi wa mijinta biyayya ai kin ga sakamakon da yake mata. Ƙiri-ƙiri ya muzanta ki a gabanmu, amma kike wannan maganar. Habiba ki zauna ustazanci ya kashe ki, kar ki nuna wayewa kina abu kamar ba graduate mai digiri da masters ba."
"Sai ilmina ya sa na kar na yi wa mijina biyayya? Faɗa ya yi mini kan na yi dare ban dawo ba, kuma in har da bai yi mini faɗa ba, sai na yi tunanin baya sona, saboda duk namiji mai hankali da kishin matarsa ba zai ƙi yi mata faɗa ba a lokacin da muka dawo."
"Eh, ai kin san ni mijina baya kishina, baya ƙaunata shi ya sa bai ce mini komai ba. Ki yi ta zama yana kashe rayuwarki kina fakewa da sunan biyayya."
"Ki ƙyaleta Fahima ta yi ta yi dama ta saba. Cewar Wajnah da take harararta.
"Ni har mamakin yadda muka kasa daina ƙawance dake na ke yi, domin Hausawa sun ce sai hali ɗaya ya zo ake ƙawance, amma sam ke ba ki wayewa kina abu kamar ba cikakkiyar wayyaya ba."
"Ni dai ba zan fasa daina gaya muku haskiya ba. Don haka shawara ya rage ma mai shiga rijiya. In kun ga dama ku daina shaye-shayen kayan mata. In kuma ƙun ƙi ina jiye muku ranar da za ku yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada don za ku tsinci Talatarku a Laraba."
"Ke ce dai za ki tsinci Talatarki a Laraba, saboda yadda kike nuna kina tsoron Abban Iklas, watarana sai ya sanya ki kuka, don sai dai ki ji a shanun tashi ya yi auresa."
"Wannan tsakaninsa da Allah ne. Ƙin gaya mini shi ne kawai laifin, amma ni ba zan iya hana shi abin da Ubangiji ya ba shi dama ba."
"Allahu Akbar! Sannu mai sani. Allah ya sa da gaske kike kar kizo mana kina kuka. Ni da kika ganni mijina da kishiya sai dai na ƙiyama da ba ni da ikon hanawa, amma bai isa ya ce zai yi aure ba."
"Lailai ko kina da aiki in har mazan zamanin nan ne."
"A'a Habiba, kar ki yi mata baki. Ko ni da Ya Huwais baya sona ba zan taɓa bari ya yi mini kishiya ba, saboda ko ƙanwarsa da yake ji da ita wallahi ina shiga sai na raba shi da ita. Ballantana wata kishiya can."
"To Allah ya ba ku sa'a. Ni tafiya zan yi kar habibi ya dawo don zan yi masa tuwon shinkafa."
"Hmmmh! Kina wahalar da kanki ga masu aiki, amma ki je aiki ki dawo ki yi girki." Cewar Fahima.
"Ai ni kuma in dai abinci ne bani da matsala, saboda ni a shegen kishina ko abincin Ummu ya ci ba nawa ba, za a samu matsala."
"Ni dai ba zan iya girki ba, haka kawai da girkin zanji ko da rainon yarsa da ɗaukar ɗawainiyarsa?"
"Duka ai bautar Allah kike yi." Habiba ta ba su amsa tana riƙe da ɗan makullinta.
"Bar ni na ji da ɗaya haka kawai na ɗaura wa kaina wahala. Yawancin full house wife duk a ƙanjame suke, saboda ba sa samun lokacin da za su huta ga ɗawainiyar gida ga miji da yara."
"Allah dai ya bamu lada kawai." Cewar Habiba don ta guddura da maganar.
Wayarta ta yi ƙara, wanda ta kalla ganin numbar mijinta ne, ya sa ta ruga da gudu zuwa gurin motarta tana ɗaga musu hannu.
Bayan fitarta suka dawo cikin falon suka zauna.
"Ni fa Habiba mamaki take ba ni, yadda ta yi sakaci mijinta na ba ta lokaci in xa ta fita, domin duk yadda nake son Ya Huwais ba zan aminta da wannan dokar ba."
"Ita ta ga za ta iya, ai sai ta yi." Fahima ta ce tare da zaunawa a gefenta suka ci gaba da zaɓen kayan matan.
Huwais ransa a ɓace yake, tun lokacin da Abu ya tursasa shi zance zuwa gurinta. A ransa yana jin bai san abin da zai ce mata ba, domin shi ko kallon kirki baya tunanin zai iya mata.
Tsaki ya ja tare da ɗauko wayarsa da ke maƙale a soket yana caji. Numbar Najib ya kira wanda ringing ɗaya ya ɗauka da sallama.
"Abu ya tursasa ni zuwa gurin Wajnah, please gobe da yamma zaka raka ni." Ya na faɗin haka, ya kashe wayar don baya son ya ce masa komai.
Da ƙyar Abu ya shawo hankalin Ummu, har ta bar maganar don ta yi ninyar hukunta Hilah, amma maganganun da ya gaya mata, ya sanya ko a fuska ba ta canza mata ba.
A mota suna tafiya shi da Najib babu wanda ke magana. Najib ne yake tuƙi da motarsa, shi kuma hankalinsa na kan wayarsa da yake chatting da Hilah.
Duk da cewar da ɓacin rai a fuskarsa, amma duk tsaƙon da ya tura mata ta turo mishi da reply sai ya murmusa.
"Ya kamata ka sanar mata da zuwan mu fa." Najib da ya waiwayo ya kallesa yana faɗin haka.
Ganin bai tanka masa ba, wanda hakan ya tabbatar masa sai bai ji shi ba.
Hannunsa ya kai ya fisge wayarsa tare da duba abin da yake yi.
"Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 14
"Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya."
"Please, bana son wulaƙanci ka bani wayata. Tun da ka ga Allah ya jarabce ni da sonta babu makawa sai na auret.."
"Ta ya ya Huwais? Tun da kake ka taɓa ganin an yi irin wannan auren? Sheɗan ne kawai ke ruɗarka kaɗa maka gangar sheɗan."
"Mu bar maganar kana ɓata mini raina." Ya furta cikin ɗaga murya.
"Zan yi shiru ne don kar ka ɗora laifin a kan Wajnah, da ba ta ji bata gani ba, amma ba zan fasa gaya maka gaskiya ba, a matsayina na amininka, amma ka sani auren ka da Hilah sai dai in ana mutuwa a dawo, sai ku dawo ba a matsayin ƴan'uwa ba."
"In kuma Allah ya ƙaddara sai ka mutu."
"Ta ya ya?"
"Ni ma ban sani ba amma jikina yana ba ni matata ce!"
"Hammh!" Kawai ya ce cikin takaici ya ci gaba da tuƙi ba tare da ya ce masa komai ba.
Da suka isa ƙofar gidan maigadi ya buɗe musu sula shiga.
Wajnah na zaune a cikin ɗakinta mai dillah na dirzanta. Ƙanwarta Batula ta ƙwanƙwasa ƙofar.
"Waye?" Ta yi tambayar cikin ɗaga murya.
"Anty Wajnah, Batula ce. Mommy ta ce in gaya maka Ya Huwais na falon Daddy." Da sauri ta ture hannunta jin abin da ta faɗa.
"Ok, ki ce gani nan zuwa." Ta bata amsa yayin da fuskarta ya cika da farinciki.
"Ana dilkan za ki fita? Ki gaya mishi ya jira ki."
"Mijin nawa zan shanya ya jira ni? Kin san da yadda na samu ya zo?"
"To asarar dilkan za ki yi?" Ta yi mata tambayar a maimakon ta ba ta masa.
"Eh, wankewa zan yi in ya tafi na dawo." Ta ba ta amsa tare da shigewa bayi.
Saboda tsabar murna ɗauraye jikinta kawai ta yi. Cikin ƴan mintina da bai fi goma ba, ta shirya kanta cikin riga da siket masu kyau ta sanya mayafi ta fice zuwa falon.
Da sallama ta shiga, idanunta na kan Huwais, da yake riƙe da waya har yanzu chatting yake yi yana murmushi.
Murmushin da yake yi ya sa ta yi tunanin ko ita yake yi wa.
"My baby, na yi tunanin ba za ka zo ba, sai an kawo maka ni a matsayin mallakinka." Ta furta cikin kissa tare da samun gefensa ta zauna har suna gogan juna.
Ba tare da ya jinkirta ba, ya matsa can ƙarshen kujera bayan ya haɗe rai, ya ɗan tsaki ƙaramin tsuka, wanda ya sanya jikinta ya yi sanyi.
Wataƙila da ta shigo ba ta yi tunanin da wani yake ba, domin ba ta lura da Najib da yake kujera one seater, sai da ya yi gyaran murya.
Kasancewarta wayayyar mace sai ta basar da abin da ya yi mata.
"Laah, ka ce da abokinmu kake tafe?" Ta yi masa tambayar tana kallonsa, sai kuma ta mai da hankalinta kan wayarsa da yake kallo.
Datar ya kashe ba tare da ya tanka mata ba yana kallon gefe.
Najib ne ya ce,"Amarya bakya laifi ko da kin kashe ɗan masu gida." Dariya ta yi tare da jin farinciki na kirarin da ya yi mata, wannan kirarin ya sanya kika shanya mu ko? Ko da yake laifinmu ne da bamu sanar miki ba."
"Ku yi haƙuri ana mini dilka ne sai dai na wanke."
"Mun haƙura dama ba mu yi fushi ba."
Murmushi ta yi jin abin da ya ce tana satar kallonsa da ya ƙara kici-kici da fuska.
"Ina wuni?"
Kamar ya amsa kamar kuma motsi kawai da bakinsa ya yi. Ganin haka ya sanya Najib ya miƙe,"Ni bari na baku guri da fatan za ki kula mini da shi?"
Yaƙe kawai ta yi ganin yadda yake cisgata, amma a zuciyarta ta ji daɗin fitan nasa, musamman da tun da ta shigo ta nemi natsuwarta ta rasa, yayin da kayan matan da take sha suka fara aikinsu.
Ji ta yi kamar ta rungume shi ko ta faɗa jikinsa. Tana mishi wani irin so musamman yanzu da take jin baba so akwai buƙatar ta ji ta a