Author : Jamsy Category : Complete Novels
warned you! Na gargaɗe ka several times, amma ka ƙi saurare. Don haka yanzu kai za ka ji da lamarin ai dama duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan duka. "
"Bari na yi wanka na shirya na je, amma duk abin da ya faru ka yi kuka da kanka." Ya ƙarashe maganar tare da shigewa bayi.
Najib ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, domin ya ƙosa a kammala bikin ya huta da kiran Wajnah.
Bayan ya fito ya shirya cikin shadda mai kyau. Kayan sun amshi jikinsa sai ƙyalli yake yi..
Wayarsa da ke kan dressing mirrow ya ɗauka. Numbarta ya kira tare da kanka wayar a kunnensa.
"Yayana, kuma angon Anty Wajnah." Ta furta da dariyarta ƙasa-ƙasa wanda ya san ta yi ne don ya ɗauka babu abin da le damunta.
"Kina ina?" Ya yi mata tambayar yana sanya handsfree a wayar ya ije ta kan gado yana ɗaura agogo.
"Ina harabar gida ni da su Umnah da Yaya Naufal za mu tafi."
"Ki jira ni yanzu zan fito mu tafi a motata."
Jin abin da ya ce ya sanya ta zare ido da sauri.
"Ka rufa mini asiri! Ango kake yau. Kamata ya yi ka je ka ɗauki Anty Wajnah ba ni ba."
"Na damu da halin da kike ciki ne kina buƙatar na..."
"Am ok Yaya, karka damu ka je ka ɗauko ta, kuma in har Ummu ta ji a motarka na tafi za ta yi..."
"Kin..."
"Please Ya Huwais, I insist!" Ta furta cikin muryar shagwaɓa.
"Kashe wayar ya yi da jan tsuka mai ƙarfi.
"Ƙanwarka ta fi ka hankali da sanin abin da ya kamata, ko da yake kai kasan kana cikin haukar soyayya shi ya sa." Najib ya ce tare da ɗaukar wayarsa ya yi masa tsaye aka don ya miƙe su tafi.
Bisa dole ya miƙe suka tafi. A motar Najib ne suka tafi.
Tsananin ɓacin rai ya ninku kan kyakykywar fuskarsa.
"Na gaya maka ba zan je a ɗauko ta da ni ba, amma shi ne za ka kawo ni gidansu?"
"Don Allah karka kunyata yarinyar nan a gaban ƙawayenta." Najib ya ce ba tare da ya amsa tambayarsa ba.
Ƙara tsuke fuskarsa ya yi yana danne-danne a wayarsa, ganin ta fito ita da ƙawayenta.
"Amarya ba kya laifi." Cewar Najib bayan ya fito ya buɗe mata bayan mota.
Murmushin yaƙe ta yi, yayin da burinta ta yi tozali da angonta wanda tun da aka fara hidimar bikin ba ta ga ƙewarshi ba.
Wani wawan ajiyar zuciya ta saki, lokacin da ta hango shi a hakimce yana danna wayarsa tamkar basarake.
"Ni ban san wane irin mutum bane angon nan, sai rowarshi ake magana. Bari dai na ganshi sai na gane ko kina ɓoye shi ne don kar ayi miki ƙwace."
Ƙawarta Hindatu ta furta tare da duƙawa cikin motar.
Da sauri ta ɗago kanta, don ya firgitata musamman yadda ya haɗe girar sama da ƙasa babu fara'a.
"Wai wannan miji na ki ai dole ki yi rowarshi.Kyawu kamar shi ya yi kansa." Ta ce tana mamakin inda ta samo shi duk da ita ma Wajnah ba baya ba, domin har ta fishi hasken fata. Sai dai na shi zallar kalar fatar ce, ita kuma tana haɗawa da shafe-shafe.
A hankali ta shiga cikin motar, tamkar ba ta son ta shiga. Kallonsa ta ƙara yi tana jin kamar ta ji ta a ƙirjin shi yadda ya yi kyau.
Wani irin wawan ajiyar zuciya ta furta ganinsa domin Allah ya jarabce ta da ƙaunarsa.
Najib ya rufe motar yana faɗin,"Ku shiga ga motoci nan birjik sai mun haɗu a gurin dinner."
"No, bamu buƙatar mota saboda ina da tawa." Cewar Hindatu tana wani yauƙi.
Shiga cikin motar ya yi jin abin da ta ce.
Ya kunna motar ya fara tafiya a hankali.
Wajnah shiru tana sanya ran zai yi mata magana, musamman turaren da ta yi amfani dashi na sace zuciyar miji, amma sai ta ga ko arziki kallo ba ta samu ba, yayin da hankalinsa ke kan waya.
"Habibina," Ta furta can ƙasa-ƙasa da wata irin murya kuma cikin salo da ƙissa, amma yadda kasan da gunki ta yi.
Cikin tsoro ta sanya hannu za ta kama hannunsa.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 17
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Cikin tsoro ta sanya hannu za ta kama hannunsa.
Tamkar za ta ɗora masa wuta, ya janye hannun tare da watsa mata mugun kallo, wanda ya sanya ta yi saurin ɗauke hannunta zuciyarta a jagule.
A haka suke tafiyar, babu wanda ya ƙara magana sai Najib da ya ga shirun ya yi yawa, ya kunna waƙar Umar M Sharrif ya sanya sauti.
Huwais rintse idonsa ya yi cikin wani yanayi. Yana jin yadda kiɗan da waƙar suke sanya shi cikin shauki mai wuyar fassarawa. Surarta yake ayyanowa yana fatan ina ma a ce da ita ce a cikin motar nan.
Ƙamshin turaren Wajnah da ya ƙara sanya masa ciwon kai, da ƙarar sautin waƙar suka ƙara birkita tunaninsa.
"Please Najib, ka kashe waƙar nan tana sanya ni ciwon kai."
"Na rage dai saboda na san kanka ya ɗau hayaniyar mutane. Karka manta yau ranar farinciki ne a gareka."
"Sosai Najib! Allah kaɗai ya san farincikin da na ke yi na samun sa a matsayin miji, domin na san na yi dace." Wajnah ta furta tana masa mayataccen kallo wanda ko kallonta bai yi ba, ballantana ya san abin da take yi.
A lokacin da suka ƙaraso gurin, Wajnah ta yi tunanin zai kama hannunta ko don ya cireta kunyar ƙawayenta da suke damunta da tambayar angon, amma sai ta ga saɓanin haka. Ya nufi ciki yana takun isa tamkar an aiko masa da mala'ikan mutuwa.
Da ido Najib ya rinƙa masa nuni da ya kama hannunta, amma sai ya basar ya nufi hanyar shiga. ganin haka ya sanya ta ƙarasa da sauri gurinsa za ta kama hannunsa.
Da sauri ya janye hannu tare da ƙarawa da sauri. Ranta ya ɓace har ƙwallah suka taru a gefen idanunta. Da sauri ta yi ma za ta mayar da hawayen ta bi shi suka jera.
Suna isa gurin ya ɗauki tafi ina ihu yayin da aka saki waƙar Umar M Sharrif.
Hilah yana shigowa duk yanayin da take ciki sai da ta ji wani irin farinciki ya kamata. Wayarta da ke hannunta tana ta turawa mahaukacin masoyi kalamai ta ije kan teburin.
Murmushi ta sakar masa, tana kallonsa har lokacin da suka shigo ciki xa su zauna.
Ganinta Huwais ya ji wani irin tsau a ransa. Duk da babu wani kwalliya a fuskarta, kuma in har ka yi mata kallon ƙurullah za ka fahimci tana ɗauke da damuwa, amma ta yi kyau kamar a sace ta a gudu.
Wani tsadadden murmushi ya sakin mata daidai lokacin da suka zauna.
"Anty Hilah, Ya Huwais ya yi kyau sosai. Ki bani wayarki na yi masa vedio recording." Amnah ta faɗi tana miƙa mata hannu.
"Ungo ƙaramar wayar ki yi masa saboda ni ma ya yi mini kyau har a tashi zan rinƙa ɗaukarsa hoto. Yayanmu mai kyau ne ko ne, haka matar da ya aura ko?" Ta ƙarashe maganar tare da kama mata kumatu tana murmushi.
"Eh kuma sun yi kyau kema kina da kyau sosai." Dariya ta yi bayan ta miƙa mata wayar ita kuma ta tafi.
Kallonta yake yi kamar zai cinye ta gani yake duk babu wanda ya kaita kyau.
A lokacin da M.C ya fara bayani tare da sanarwa abokin ango zaji ba da tarihin ango. Huwais, ya yi wa Najib nuni da ya zo.
"Please, Hilah na ke son ta bada tarihina, domin babu wanda ya sanni sama da ita." Ya furta wa Najib cikin muryar roƙo.
"Kana ganin hakan babu matsala?"
"Bana tunanin akwai don Allah?"
"Ok, shikenan." Ya ce tare da zuwa gurin M.C ya yi masa bayani.
Bayan ya gana jawabinsa ya gyara muryar sannan ya ce,
"A yanzu za mu kira ƙanwar ango wanda ita ce za ta bayar da tarihin Yayanta."
Kowa ya ji wani iri har da ita kanta Hilah.
Ummu kuwa sam ba ta ji daɗin haka ba, domin ta san duk shirinsa ne. Ɓata ranta ta yi daidai lokacin da Hilah ta kalle ta.
Jikinta a sanyaye ta miƙe, tana kallonsa da yake ɗaga mata hannu don ƙarfafawa.
"Gaskiya Wajnah, sai kin tashi tsaye, saboda yadda na ga mijinki na son ƙanwarsa zai iya sakinki saboda da ita."
"Ba ki san yadda na tsane ta ba, duk da cewar ƴar'uwata ce, amma wallahi ko kallonta bana son yi, domin da zan samu ko rabin son da yake mata da na ji daɗi."
"A to ki dai tashi tsaye dangin miji ba a iya musu, musammman yadda yake ta kallonta yana mata murmushi xai nuna yana sonta sosai."
"Ki barni da shi za ki ga yadda zan juya shi. Mai wuyar na mallaka masa kaina." Ta ce cikin ƙuna tana kallon Hilah da take jin kamar ta shaƙeta.
A hankalinda natsuwa ta fara bada labarinsa, wanda ya tsura mata idanu yana kallonta. Gurin ya yi tsit ba ka jin komai sai zazzaƙar muryarta da yake tashi a cikin speaker.
Zuru ya yi mata da idanu yana jin yadda take maganar cikin harshen turanci. Kallonta yake yi da sha'awa yana mamakin yadda ta san kanshi fiye da shi. A ransa ji yake kamar ya tashi ya rungumeta ko ya sace ta su je can wata duniya daga shi sai ita su yi rayuwarsu.
Bayan ta gama bada tarihin, rayuwarsa gurin ya ɗauki tafi da waƙa ban da Ummu da ta ci magani.
Aminiyar amarya ta ba da tarihin amarya, sannan aka saki waƙa. An ci an sha an kuma na ta cashewa sai fatan ba da zaman lafiya.
Hilah miƙewa ta yi tana rangaji ta fita daga cikin hall ɗin, saboda ƙarar waƙar yana hawa mata kai.
Kallo ya bita da shi har fice daga hall ɗin. Tun daga lokacin ya rasa natsuwarsa sai kallon agogo yake yi yana kallon ƙofa.
Wani guri wanda ba a jiyo sautin ta samu ta zauna.
Gorar ruwan dake hannunta take watsa ma fuskarta.
Zama ta yi tare da buɗe bakinta tana shan ruwan. Bayan ta gama ta ije gorar tana kallon ciyayin da suke luf a gurin, kuma suka ƙara ƙawata gurin.
Rintse idanunta ta yi cikin damuwa har yanzu in ta tuna da yaudarar da mahaukacin masoyi ya yi mata, sai ta ji ƙwallah na zubar mata.
Gefen hannunta ta sanya ta share hawaye tare da sunkuyar da kanta ta cusa a tsakanin cinyoyinta.
"Hilah, har yanzu ba za ki cire damuwa a ranki ba?" Ta ji muryarsa da ta yi matuƙar tsoratata.
Da sauri ta miƙe tare da waigawa don ta ga inda yake, amma sai ta ganshi a gefen ta yana zaune.
"Innalillahi Yaya, yaushe ka fito?"
"Hankalina ya kasa kwanciya bayan kin bar gurin kamar yadda na zargi tunani kika fito ki yi."
"Don Allah ka koma ciki ƙarar kiɗan ne ya sanya kaina ciwo."
Hannu ya sanya ya kama kan yana faɗin," Ayya, sorry bari na yi miki addu'a."
"No ka barshi xan je mota na ɗauko magani a jakata." Ta ce tare da sauke hannunsa da ya ɗora saman kanta.
"Ok, to mu je na raka ki."
"Please, don Allah ka koma" Ta ce cikin wata irin murya kamar za ta yi kuka.
"To sarkin kuka bari na koma kar ki yi kuka." Ya ce da sauri tare da juyawa yana waigenta.
Har ya bule tana kallonsa. Haƙiƙa ta san yana mugun sonta. Kullum godiya take yi da Allah ya ba ta ɗan'uwa mai tsananin ƙaunarta, wanda ta san ko bayan babu ran iyayensu ba zai bari su wulaƙanta ba.
Komawa ta yi ta zauna. Kiran wayarsa ya rinƙa shigowa. Da sauri ta miƙe ganin ya turo mata tsaƙo.
Tana komawa gurinta ta zauna, ya saki ajiyar zuciya hankalinsa na kanta duk motsi ta yi sai ya kalleta.
Kafin a tashi taron ran Wajnah ya ɓaci matuƙar gaske. Tun da suka je gurin ko kallon kirki ba ta samu ba. Ko da aka kira su yi rawa. Ransa a jagule ya miƙe shi ma don kallon da Ummu ta yi masa ne.
Da ma shi rawa ba ɗabi'arsa bane don haka ya yi ƙiƙam kamar soja. Yana ganin yadda Wajnah take rawa kamar za ta karye.
Bayan sun gama rawar, aka buƙaci iyayen ango su zo. Ummu ta yi ƙoƙarin manna musu ruwan kuɗi haka Abu. Daga ƙarshe aka kira ƴan'uwan ango. Tun da Hilah ta shigo hankalinsa ya koma kanta.Kuɗi ya ciro ya rinƙa manna mata.
Ganin kuɗin da yake manna mata, ya sanya ta fice da sauri daga filin rawar. Ran Wajnah ya ƙara ɓaci har ta kasa jurewa tana harararsa.
Bayan an gama dinner suka tattaro suka dawo gida. Daga gurin dinner aka wuto da Wajnah ɗakinta.
Cikin tsananin farinciki take kallon gidan da kyawunsa ya yi matuƙar tafiya da hankalinta. Haƙiƙa tsarinsa da yanayin gidan ya burgeta, kuma iyayenta sun yi bajinta ƙwarai!
Zama ta yi kan one seater tana kallon Wahida da take shayar da ƴarta mama.
"Gaskiya gidanki ya yi kyau sosai! Abin da ya rage miki sai ki kama maigidan da kyau, yadda babu wata ƴar iska da za ta shigo miki gida, domin irin mijinki shi ne mace ke hauka in zai ƙara mata kishiya."
"Lallia ma Wahida, har yanzu kamar kallon ƙaramar yarinya kike mini. Kin san yadda na samu har aka yi auren nan? Sau biyu ana sanya ranarmu ana fasawa. Ai yadda na sha fama kafin na shigo cikin gidansa ku ƴan'uwansa sai na ga dama zai rinƙa kula su, ballantana wata kishiya. Ni Allah ya tsare ai gaba da baya zan tsare don no kishiya in my house."
Dariya suka kwashe da shi tare da tafawa.
"Ai ban ga laifin ki ba Wajnah, don ko ni mijina shi da wata sai dai matan aljannah da ban isa na hana shi ba, amma a duniya babu macen da ta isa na yi sharing mijina da ita, in kuwa ta kuskura ta aurar mini miji sai na nuna mata mijin wata ta aura. Don ba zan yi shukar ƴaƴan itatuwa ba mu ci da wata." Mardiya ta ce.
"Yadda mijin ki yake jarumin namiji, dole sai kin zama jaruma in ba haka ba kina ji kina gani za a yi miki sakiyar da babu ruwa."
"Duk wacce ta kuskura ta shigo mini gida nice ajalinta, don sai na canza mata kammanni ta yadda ko iyayenta suka ganta ba za su gane ta ba ballantana shi."
"Ato ai gara ki kula saboda kula da kaya yafi ban cigiya."
"Shi ya sa maganin da Hajiya Zauzau ta bani ta ce na sha ƙwara ɗaya tall! Kin san Allah? Guda uku na shanye."
"Kan uban nan! Wallahi babu ruwana in kika kashe kanki, kin san ƙarfin maganin mata na bature?" Cewar Wahida tare da zare idanunta.
"Ai in za ka sha giya ka sha ta dubu." Ta furta tana dariya.
"Wallahi babu ruwana kar ki kira ni."
Dariyar ya yi ita ba ta ce komai ba.
Huwais da Najib a gaban Abu suna zaune yana mishi nasiha.
"Ƴar'uwarka ce Wajnah, kuma yau ta koma matsayin matarka. Tana da haƙƙi da dama a kanka, wanda in har ba ka sauke mata ba Ubangiji xai tambaye ka. Kana da sani kuma kai ba yaro bane, kasan haƙƙin da Allah ya rataya maka, don haka kar na ji na ga abin ƙi a rayuwar aurenku. Ka riƙeta tsakani da Allah Ubangiji zai jiɓanci lamarinka, sannan ka sani zaman aure bauta ne na Ubangiji ba zaman jin daɗi ko san rai ba. Duk abin da ka yi mata na cutarwa Allah sai ya tamabaye ka, kamar yadda in har ta saɓa maka ita ma Ubangiji zai hukunta ta. Don haka a matsayina na mahaifinka ina mai jawo hankalinka da ka riƙe amanar Allah sai Allah ya jiɓanci lamuranka."
Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi, har yana jin hawaye na son zubo masa, jin nasihar da Abu ya ke masa.
"Shin ko zuciyata za ta aminta na xauna da ita, bayan bana sonta kuma ban taɓa jin ta burge ni ba?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa.
"Na gama za ka iya tafiya, sai dai in mahaifiyarka na da abin cewa." Ya ƙarashe maganar yana kallonta.
"Ai ka gama cewa komai, sai dai na ƙara masa da cewar ya kula da ita, ya san cewa ita ƴar ƴaƴata ce, wacce muka fito ciki ɗaya, sam ba zan lamunci ya cutar da ita ba, kamar yadda ita ma ba zan barta ta cutar da shi ba. Ya riƙe ta tsakani da Allah don ɗorewar zumuncinmu "
"To ka ji abin da mahaifiyarka ta gaya maka. Ka tashi ka tafi gidanka Allah ya yi maka albarka." Abu ya ce yama kallonsa.
Har ya miƙe, sai kuma ya kasa tafiya ya ɗago idanu suka haɗa ido da Ummu, da tun da ya miƙe take kallonsa.
Jikinsa ya ƙara sanyi da ya tuna nasihan da suka yi masa, wanda ba ya tunanim zuciyarsa xa ta iya amincewa ya aikata hakan. Ji ya yi kamar ya xauna ya gaya musu wacce yake so, amma ya san a matsayin mahaukaci za su ɗauke