Ranar Wanka Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 23

39K to 42K   out of 66.9K words

jikinsa.

"Ya Huwais don..."

"Please, ba na zo bane don ki ɓata mini rai. Bisa tursasawar iyayena nazo. Na sha gaya miki bana ƙyaunarki. Sam ba ki a cikin jadawalin matan da na ke so, amma kin na ce dole sai kin aure ni, don haka ki shiryar kurɓar ruwan guban da yafi na maciji dafi a cikin gidana, saboda ba za ki taɓa samun farinciki a cikin gidana ba."

"Eh na ji kuma na amince, matuƙar zan rayu a ƙarƙashin inuwar aurenka, a shirye na ke da ko wane irin zama a cikin gidanka."

"Shikenan, sai ki je gidan ga shi nan ki zauna, amma ni ba za ki taɓa mallakata ba, kuma na gaya miki ina da wacce nake so, nake burin ta zamo uwar ƴaƴana."

"Don Allah Ya Huwais, ka taimaka mini wallahi a shirye na ke na ba ka farinciki, domin ina matuƙar sonka."Ta ce bayan ta duƙa ta kama rigarsa.

Fisge rigar ya yi cikin ɓacin rai," Ba za ki taɓa mallakar zuciyata ba, domin ba ki da matsuguni a cikinta."

Kukanta ya ƙaru jin abin da ya ce. Fara tafiya ya yi. Tsaye ta yi cikin damuwa tana kallonsa. Lokaci guda ta ji ranta ya ƙara ɓaci, wanda har ta gwammace da bai zo ba.

Yana ƙoƙarin fita Najib ya murɗa ƙofar ya shigo. Kallonsa ya yi da ya fice ba tare da ya tanka masa ba, sai kuma ya kalli Wajnah da har yanzu hawaye take sharewa.

Kunya da takaici suka lulluɓe shi, ya kasa ce mata komai sai dai ya juya ya fice.

Wajnah ji ta yi kamar ta kashe kanta. Wani tangaras da aka yi kwalliyar fulawa da shi, ta ƙwada shi da ƙasa tare da fashewa da kuka ta yi sashin Mommy.


"Ya Huwais ba ya ƙaunata mommy."

"Ki daina ɓata hawayenki mai wuyar ki shiga cikin gidan, domin kina da kyau da babu namijin da zai wulaƙnata ki."


Abin da ta faɗa ya ɗan sanyaya zuciyarta, amma har yanzu tana jin tana mata ƙuna. Rintse idanunta ta yi tana kin kamar ta mare shi lokacin da yake gaya mata yana da wacce yake so, wani irin mugun tsanarta ya shiga cikin ranta har take jin za ta iya ajalinta.

"Yanzu abin da ka yi ka kyauta? Don Allah ka tausayawa yarinyar nan, masoyinka ba ya taɓa zama maƙiyinka." Najib ya furta cikin ɓacin rai ya ɓna kallonta.

"Yanzu mu da muka zo yin maganar abin da za mu ba su da biki ga shi nan ka ɓata komai, wallahi kunyar yarinyar na ji ya sanya na kasa magana."

"Duk abin da na yi mata laifinta ne ai ba a aure dole."

Tsaki kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba cikin takaici.

Haƙiƙa Ummu ta shirya wa bikin nan domin kayan lefen da aka haɗa kaya ne na gani na faɗa.

A falo aka baza kayan suna ta gani cikin sha'awa. Hilah ita kanta kayan sun yi mata ƙwarai! Don Ummu ta yi ƙoƙari sosai.


Gidan da Huwais zai zauna gida ne mai tsananin kyau da tsari. Gidan part biyu ya kuma haɗu sosai. Daga sashin Wajnah sai na shi mai ɗauke da ɗaki biyu da dining kamar dai Wajnah.


Abu ya gina masa gidan mai kyau da tsari.

Iyayen Wajnah sun yi matuƙar ƙoƙari, domin hatta sashinsa sai da suka cika da kaya, duk da cewar Abu ya hana domin Huwais zai gyara bangarensa, amma suka buƙaci su sanya masa kayan.Kaya ne na gani na alfarka aka yi.

Kasancewar mahaifin Wajnah shahararren ɗan kasuwa ne, da yake da shoping mall da yawa a garin Abuja. Ya yi bajinta sosai gurin yin mata kayan, musamman da take ita ce ƴa ta farko da zai fara aurarwa.

Mahaifiyarta ma ba a barta a baya ba, saboda ita ma tana business na atamfa less sa sauran kayan amfanin mata.

Haƙiƙa gidan ya tsaru matuƙar gaske.

Ya rage saura sati ɗaya biki hankalinsa ya tashi matuƙar gaske! Domin abu biyu suka haɗe masa tare da rikita ƙwaƙwalwarsa.


Cikin dare sam baya bacci, yana tunanin rayuwar da zai yi da Wajnah da kullum ƙara tsanarta yake a cikin zuciyarsa. Sannan ga shi Hilah ta takura masa kan yazo bikin. Abin duniya sun haɗu sun yi masa yawa. Gabakiɗaya ya rame ya fita hayyacinsa, wanda ya tsorata iyayensa, amma kuma hakan shi ne kawai zai kawo maslaha.


Wata shawara ta bijiro masa take ya amince da zai zo. In ya so ranar ɗaurin auren sai ya yi mata wani ƙaryar. Duk da ya san cewa za ta yi fushi dashi mai tsanani, amma ba za ta iya rabuwa da shi ba, saboda kamar yadda yake jin sonta a cikin zuciyarsa, ya tabbata tana jin kwatankwashinsa duba ga yadda take gaya masa yadda ta damu da shi, kuma ya san Hilah ba za ta taɓa gaya masa ƙarya ba.

Hilah tsaye a kicin tana dama kunun gyaɗa da ta ke son ta kai masa. Har cikin zuciyarta tana matuƙar tausaya masa domin rashin masoyi babu daɗi. Tana ji a ranta yadda take son mahaukacin masoyinta, matuƙar aka raba ta da shi za ta iya shiga kwatankwacin halin da yake ciki.

Bayan ta dama masa kunun ta ɗauka ta nufi sashinsa. Yana kwance da waya a hannunsa. Hotonta yake kallo yayin da hawaye suka taru a gefen idanunsa.

Ƙwaƙwansa ƙofar ta yi tare da kiran sunansa wanda ya yi maza ya aje wayar.

Yana buɗewa suka zura wa junansu idanu.Tausayinsa da damuwa da halin da yake ciki suka ƙara kamata

Tsayawa ta yi cikin yanayi na jimamai, sai kuma ta ɗauke idanunta ganin ya ƙi cire nasa.

"A haka za ka yi angwancin?" Ta yi masa tambayar cikin tausayi.

Ƙaramin tsuka ya ja jin tambayar da ta yi masa.

"Ya Huwais, ka ga yadda ka koma? Dubi gashin ƙasumba da ka tara. Don Allah ka cire komai a ranka ka yi addu'a kar ka janyo wa kanka cuta mu shiga uku."

"Ina jin zuciyata tana zafi! Ummu ba za ta gane ɗacin da na ke ji ba, saboda auren soyayya ta yi da Abu. Hilah, Ummu ta gama kashe mini farincikin rayuwata tun da ta hana ni da wacce zuciyata ba ta muradinta."

"Please, ka daina faɗin haka. Aurenku sai family ɗinmu sun yi alfahari da shi. Anty Wajnah na da kirki ba za ka yi dana sanin zama da ita, kuma Ya Huwais, Allah ya ba ka damar ƙarin aure, in har ka samu damar auren wacce kake so za ka iya ƙara aure."

"Ta yi mini nisa ba za ta aure ni ba, amma na san sonta shi ne ajalina."

"Ka so abin da ka san za ka samu ba wanda ba za ka samu ba. Na ce ka gaya mini inda take zan je na gaya mata yadda kake son ta na kuma roƙe ta ta aureka."

A ransa ya ce,"Ke ce Hilah! Kece wacce zuciyata take mafarkin samu a matsayin mata, amma kuma ba zan taba mallakarki ba."

A fili kuwa zura mata idanu ya yi, wanda ya sanya ta ɗauko kunun gyaɗar ta iba ta miƙa masa a baki.

Kauda kansa ya yi, yana faɗin,"Ba na jin ɗanɗanon abinci na rasa ɗandanon bakina."

"Ka ci kar ka yi wa kanka horar yunwa."

Babu musu ya karɓa jin abin da ta ce. Yana cikin sha su Abidin suka shigo.

"Yauwa Hilah, dama neman ki muke a cikin gida. Tun ɗazu muka kawo masa break amma ya ƙi ci. Yaya yana son ya yi mana asarar kansa, bayan ya san in har babu shi ba zamu iya rayuwa." Affan ya ce tare da zaunawa a gefensa


Tausayin ƙannin na sa ya kamashi ganin yadda suka nuna tsantsar damuwarsu.

Hankalinsu bai kwanta ba, har sai da ya shanye tas! Hilah ce ta miƙe don ta gyara ɗakinsa.

"Bari muje zamu karɓo ɗinki mu a gurin tela. Hilah ki kula da shi."

Murmushi ta yi tare da ɗaga kanta ta ci gaba da gyara falon.

Tana aikin duk ta ɗago idanunta sai ta ga yana kallonta.

"Gaya mini Hilah in har mahaukacin masoyi ya bayyana yana da mata zaki aure shi?"


"Mai yasa ka tambaya Yaya?"

"Saboda ni ma na gane, in har wacce nake so ta ji ina da mata za ta iya aurena." Ya ba ta amsa jin tambayar da ta yi masa a maimakon amsar wace ya yi mata.

"Eh, zan iya aurensa saboda ina matuƙar sonsa, in har zan auresa matuƙar ya cika duk sharuɗan da ya kamata na aure shi a addini ban damu ba."


Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423




*RANAR WANKA...*



NA



JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"



☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 15

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Gaya mini Hilah in har mahaukacin masoyi ya bayyana yana da mata zaki aure shi?"


"Mai yasa ka tambaya Yaya?"

"Saboda ni ma na gane, in har wacce nake so ta ji ina da mata za ta iya aurena." Ya ba ta amsa jin tambayar da ta yi masa a maimakon amsar wace ya yi mata.


"Eh, zan iya aurensa saboda ina matuƙar sonsa, zan auresa matuƙar ya cika duk sharuɗan, da ya kamata na aure shi a addini ban damu ba."

Da fari murmushin jin daɗi ya yi, amma da ya ji ta ce sharuɗa, sai ya tuna da matsayinsa a gurinta, wanda ya faɗar masa da gaba.

Ba tare da ya ce komai ba, ya kwanta a kan kujera bayan ya ɗora filo a samar ƙirjinsa.

Bayan ta gama gyaran ɗakin ta ja masa ƙofa ta fice ganin bacci yake yi.

Ya rage saura kwana biyu biki, Hilah ta cika da matuƙar murna. Shirye-shiryen haɗuwa fa mahaukacin masoyi take ta yi.

Ta je ta gyara kanta, ta yi ƙunshi mai matuƙar kyau. Sannan har dilka ta sanya aka yi mata. Duk lokacin da ta shigo masa tana murnar zasu haɗu da mahaukacin masoyi sai hankalinsa ya ƙara tashi.

"Yaya, zan ɗauko maka hotonsa, na san zai kasance kyakykyawa kamar kai." Ta furta mishi lokacin da take bashi indomie da ta dafa masa.

Murmushin yaƙe kawai ya yi masa, amma yama jin babu daɗi sosai.

"Ya ce zai gaya mini sunan shi, kuma na san cewa sunan yana da daɗi. Ni fa ina jin kamar na sanshi, domin na tana zuwa gasar musabaƙa ƙawata ta ce wani matashi ya tambaye ta sunana da inda nake. Jikina yana ba ni shi ne."

"Huhm!" Ya ce cikin damuwa yana mata kallon tausayi.

Miƙewa ta yi ta ce,"Yaya, bari na je na yi wanka. Za muje walima gidan su Anty Wajnah."

Ɗaga mata kai ya yi ta fice tana ɗaga masa hannu.

Siraran hawaye masu tsananin zafi suka wanke masa fuska." Haƙiƙa na zama mayaudari, kuma na biyewa zuciyata na sanya ƙanwata cikin wani yanayi. Ban san ya ya za ta ji ba, in har na ƙi zuwa." Ya furta maganar cikin nadama da damuwa.

"Ka yi kuskure Huwais, tun farko sai da na gargaɗe ka da hakan, babu abin da zai haifar sai ɗa mara ido." Amin ya furta cikin wayar ransa a ɓace.

"Ban san ya zan yi ba Najib, ko na yi ninyar daina kiranta, sai na ji ba zan iya rayuwa ba in ban ji muryarta ba." Ya furta jin abin da ya ce.

"Ka daure ka karya layin, sannan ka daina kiranta ka rungumi matarka da za a aura maka. Wajnah na da kyau za ka sota. Sheɗan ne ke yi wa rayuwarka ingiza mai kantu don ya kai ka duniyar nadama."

"Kana da gaskiya Najib! Kuma in sha Allah zan bi shawarar ka." Ya ce tare da rintse idanunsa da suka yi masa nauyi.

Rana ba ta ƙara, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. A yau ranar Juma'a ya kasance family ɗin gidan Alhaji Nadabo suke cikin matsanancin farinciki. Ganin dubban mutanen da suka fara zuwa don halarta bikin Huwais da Wajnah.Kowa fuskarsa ɗauke da farinciki. Gurin ya cika maƙil da manyan mutane. A masallacin Juma'a za a ɗaura auren, daga nan sai a wuce gurin cin abinci.

Abu zuciyarsa fara ƙal tamkar gonar auduga. Sai haba-haba yake da mutane yana tarbarsu cikin karamci.

Ummu kuwa tafi kowa murna, domin ji take babu wanda ya kaita farinciki. Tun safiyar sai dai kawai ta ji hawaye sun zubo mata na farinciki. In ta tuna dargar da ya sanya ta da tashin hankalin da ta fuskata kafin bikin, da ƙalubalen da ya rinƙa faruwa sai kawai ta zube ta yi sujjada shukuriya. Shikenan daga yau ta huta Huwais ba xai ƙara sata damuwa ba, don ta gama yadda sha'awace take damunsa wanda kuma ya ɗora kan ƴar'uwarsa.

A ranta duk ta ƙosa a ɗaura auren ya tattara ya bar mata gidanta.

Najib ne zaune a cikin ɗakin Huwais, da sauran abokanansa suna ta fama da shi ya shirya, za su inda suka kama don masaukin baƙinsu bayan ɗaurin auren amma ya ƙi.

Cikin ɓacin rai Taufiƙ ya kalle shi,"Wannan abin da kake yi sam ba ka kyautawa Huwais, ni wallahi zan iya yarda da aljana da aureka, saboda babu yadda za a yi ka kai har wannan lokacin baka yi aure ba." Ya tsagaita ko zai ce wani abu, amma sai ya ga ko kallon arziki bai samu ba.


"Please, ka tashi."

"Ka barni domin babu inda zan je."

Caa suka yi masa ganin ya ƙi tashi ya yi wankan ballanatana su sanya ran za shi.


Banza ya yi dasu, yana ta tunanin halin da Hilah za ta shiga, in har ta kira wayarsa ta ji a kashe, domin saura minti talatin lokacin da suka sanya za su haɗu ya cika.


Ganin sun kaɗa sun raya, amma ya ƙi tashi sai Najib ya kalle su ya ce,"Ku ƙyale shi na san wanda za ta sashi ya yi wankan."

Wayarsa ya ɗauko tare da fara neman numbar ta. Huwais ya ɗauka Ummu ce har zuciyarsa ta fara bugu.


"Yauwa, ƴar halak ƙin ƙi ambato." Ya furta lokacin da ya ji muryar Hilah na yin sallama.

Jin an bata damar shigowa ya sa ta shigo cikin natsuwa.

Gabakiɗaya idanunsu suka hau kanta. Wani irin tsau ta ji tare da kunya ta lulluɓe ta.

Kanta ta duƙar ƙasa cikin sanyaruar murya ta gaishe su.

"Wow! Huwais ƙiri-ƙiri ka hana ni auren ƙanwar nan na ka." Ya furta yana mata kallo tamkar zai cinyeta.

Zumbur ya miƙe cikin ɓacin rai ya ce,"Ba na hanaki shigowa ba in na yi baƙi?"


"Ka yi haƙuri Yaya, zan tafi ne kuma ina ta kiran wayarka ba ka ɗaga ba."

Muryarta ba shi kaɗai ba, duka mutanen ɗakin sai da ta ɗauki hankalinsu.

Sai a lokacin ya tuna wayarsa, na cikin bedroom ɗinsa, tun safe da Wajnah ta kira ya yi wurgi da wayar.

Hannunta ya ja cikin tsananin jin haushin yadda suke kallonta. Bedroom suka shiga.

"Kai anya na taɓa ganin mace mai kyau irin ƙanaar Huwais?" Adnan ya faɗa shakku.


"Dole ya rinƙa kishinta sosai. Wannan fulawar tun da babu aure a tsakaninsu, dole ya kula da wanda zai ba shi ya amanarta." Sudais ya ce.

"Yayana, zan tafi saura minti ishirin mu haɗu da mahaukacin masoyi."

Idanu ya zura mata na tsawon lokaci ya kasa cewa komai. Kwalliyar da ta yi da kyaunta, suka tafi da imaninsa. Ji yake kamar ya rungumeta ta rarrashe shi.


"Har kin yadda da shi, da ya ce zai zo? Gani nake kamar yaudararki yake yi. Kuma in har da gaske yake yi gida ya kamata ya zo. Ki haƙura da shi ki manta shi a cikin rayuwarki."


Raurau ta yi za ta yi kuka, sam ba ta son ya hana ta tafiyar."Don Allah ka barni na je, ni da Afrin zamu. Kasan Ummu ta hana ni kula sa, matuƙar ta ji ina tare da shi ranta zai ɓace."Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa.


"Ok, ni ban ce kiyi mini kuka ba." Ya ce yana xare hannunsa.

"Yauwa Yayana, sai na dawo. A ɗaura aure lafiya."

Tsaya ya yi, tare da zura hannunsa a cikin aljihun wandon, kayan baccin da yake sanye da su ba tare da ya ce mata komai ba.


Har ta buɗe ƙofar za ta fita, sai kuma ta tsaya tare da ƙare masa kallo.

"Yayana, ango sukutum guda bai yi wanka ba?"

Ɓata fuska ya yi, jin abin da ta ce tare da gyara tsayuwarsa.

"Yauwa, gara ki san ya shi ya yi wankan, domin tun ɗazu muke fama da shi, ga kayan shi can wanda Affan ya kawo ya ƙi sakawa." Cewar Najib da ya shigo.

Ɓata fuska ta yi tare da kama hannunsa."Don Allah ka yi wanka..."


"Je ki kar ki ɓata masa lokaci kinga lokaci ya kusa."

"Pleas.."

"Hilah, ki je na yi miki alƙawarin zan yi."


"Promise?"

"Sure," Ya ce mata to sai ka shiga bari na haɗa maka ruwan wankan.


Da sauri ta nufi bayinsa, wanda ko minti uku ba ta yi ba ta fito.

"Yayana, na haɗa maka. Ka yi mini addu'a zuciyata na bugu."


"Fatan alkhairi sis." Ya furta cikin wani irin yanayi.

Ba tare da ta kula ba ta fice da gudu.


Kallon ƙofar da ta fice suka yi." Ka cutar da yarinyar nan Huwais! Shin me kake tunanin za ta ji in har ba ta gan shi ba?"


"Za ta ji babu daɗi na yi kuskure, amma yanzu zan tura mata da tsaƙon

14 / 23