Ranar Wanka Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 23

6K to 9K   out of 66.9K words

Ko da kika ga na fi shaƙuwa da ita ina yi ne saboda ita ce mace ta farko da aka fara haihuwa a gidan, amma bayan wannan babu wani abu saɓanin hakan."

"Munafuki duk mai hankali daga kallonka zai fahimci ƙaunarta kake. Ballantana ni mahaifiyarka da na raine ka na san abin da kake so da wanda ba ka so." Ta ce a ranta a fili kuwa cewa ta yi.

"Na dai gaya maka sai ka kiyaye." Ta ce tare da ficewa.

Ransa ne ya ɓace idanusa suka yi ja sai ya juya ya fice ba tare da ya kalli kowa ba.

Yana fita Ummu da ke ƙoƙarin haye sama ta saki ajiyar zuciya tana jin wani irin tashin hankalin da yana saukar mata da ciwon kai ta nufi ɗakin Abu.

Duƙawa ta yi ta saki kuka sosai wanda 'yan'uwanta suka yo kanta suna rarrashinta

Kuka ta saka masa tare da faɗawa jikinsa wanda hankalinsa ya yi matuƙar ta shi ya fara rarrashinta.

"Yaron nan daga dawowarsa yana son ya cigaba da sani cikin damuwa. Na yi tunanin shekarun da ya ɗauka zai sa ya daina haka, amma abin ci gaba ya yi.

"Lafiya mai kuma ya yi?" Ya tambayeta cikin mamaki wanda ya sa ta share hawayenta ta ce,

"Shaƙuwar da bana son yan nuna mata dai yake nunawa. Wallahi bani da kaffara mahaukacin yaron nan sonta yake. Ko a ina ya taɓa ganin an so wacce babu aure a tsakani? I don sonta da ƙyawunta yake ruɗarshi har yake jin ƙyashin wani ya aureta, ai akwai mata waɗanda suka fita kyawu sai ya je ya nema, amma ba wai ya tsaya yana nuna wa 'yar'uwarsa wacce suka fito ciki ɗaya soyayya ba."

"Haba Laila, har yanzu hasashe kike baki tabbatar ba, kuma bai taɓa gaya miki ba. Yana da hankali ba zai aikata hakan ba. Duk kyawun da take da shi ai dole wani ya aureta tun da babu aure a tsakaninku. Ku dai mata kuna da sauran camfar abu don babu komai a tsakaninsu sai shaƙuwa. Tun suna yara ya kamata ki raba shaƙuwar ba wai sai da suka girma ba don hakan zai yi miki wuya."


"Shiyasa na ce ayi musu aure kawai! Tun da ya dawo a haɗa aurensu tare ga Wajnaah har ta gama karatu aiki take yi. Ta yi haƙurin jiransa."

"Eh, zan yi mishi magana amma ita Hilah gaskiya ba yanzu ba sai ta gama makaranta." Ya ce tare da ɗaukar agogonsa zai ɗaura wanda ta taso ta ƙarɓa tana ɗaura masa.

"Ina kashedi da jawo hankalinka da ka da yaron nan ya kasa controlling emotion ɗinsa ya aikata ba.."

"Haba ke fa uwace don Allah ki daina faɗin haka domin in sha Allahu hakan ba zai taɓa faruwa ba." Ya katseta cikin tsawa wanda ya sa ta yi shiru amma a ranta ita tasan abin da take tunani.

Sai kuma ta ce"Haka ne Allah ya shige mana gaba." Tare da ɗaukar wayarta da ba ta san me za ta yi daita ba sai juya ta take yi.

Huwais, zaune a kan kujera cikin ofis ɗin abokinsa kuma amininsa Doctor Khair.

Kallonsa yake yana jin bayanin da yake masa wanda ya ɗora da cewa,

"Sam bana shawartarka da ka cigabada shan irin waɗannan maganin it been for a while kana sha wanda a shawarce bai kamata ba ace kana sha ba. Duba ga illolinsa da abin da zai haifar nan gaba, saboda za ka kai mizanin da za su zamo maka illa..

Shiru ya yi cikin tunani ganin bai ce komai ba ya ɗora da cewa.

"Please, ka daina shan maganin ɗauke sha'awa ka yi aure. Wata ƙila perception ne kawai na ka kan babu macen da za ka ji feelings a kan ta sai ita. Ta iya yiwuwa negatives ne ba gaskiya bane. Kai namiji ne cikkake mai ba dutse bane, bana tunanin za ka iya kaɗaicewa da mace ba tare da ka ji wani ba. Ka ga ƙila albarkacin auren ya ɗauke maka sha'awarta da ƙaunarta, don ƙila sheɗan ne yake saƙa maka hakan don ya yi nasara a kanka ka aikata ba daidai ba, saboda tun da nake ban taɓa jin wanda ya kamu da son yar'uwarsa biologically.

"Ya zan yi, ya kake son na yi Khair? Ba ka san abin da nake ji game da ita ba shi ya sa kake cewa haka. A irin yadda na ke jin sonta sai zuciyata take kitsa mini akwai lauje cikin naɗi, amma na kan kore hakan ina tuna da rayuwarmu bakiɗaya. A gabama aka haife ta na raine ta ta girma. Ni na san soyyayarta ita ce ƙaddarata wace za ta kai ni kushewata lokacin abai yi ba." Ya ƙarashe maganar cikin murya mai rauni tare da saukar hawaye masu zafi kan ƙuncinsa.

"Yanzu me kake son yi?" Ya tambayesa cikin tsananin tausayinsa na jararabawar da Allah ya yi masa.

""Ban sani ba! Ni ma ban sani ba." Ya faɗa yana watsa hannunsa cikin damuwa sai ya ɗora da cewa,

"Amma sai dai ina jin zuciyata tana bani shawarar da zai iya zama mini ƙadangaren bakin tulu a rayuwata, domin zabbi shawarar da take bani, wataƙila bayan lalacewar lamarin sai na samu mafita a cikinsa. Zanbi makauniyar zuciyata domin samun mafita, duk da ance son zuciya, ɓacinta."

"Karka je ka aikata abin da za ka yi dana sani. Ka amince da aure kawai shine mafita."

Kallonsa ya yi ba tare da maganarsa ta shigesa ba.

"I understand, I know that you are trying to help, amma ka sani kurmar zuciyata ta riga ta yi nisa ba ta jin kira, domin a shirye take ta yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada! Matuƙar za ta samu muradinta ko da na wucin gadi ne."


Tabbas ya yarda so mahaukaci ne domin ga shi ya mai da amininnasa mahaukaci yana tunani ba tare da ya hangi abin da zai je ya dawo ba, ganin yadda zuciyarsa take masa ingiza mai kantu ya aikata lamarin da ya tabbatar xai yi dana-sani mara amfani.

"Na fahimce ka duk da cewar ba na amince da ka ci gaba da sha bane, amma babu yadda zan yi da kai, don haka ga maganin ka ci gaba da sha Allahu ya kawo maka ƙarshen matsalarka."

"Thanks." Ya ce tare da karɓar maganin ya fice yayin da zuciyarsa ke gasganta masa hakan shine kawai mafita a gare shi.

Hilah ta shiga cikin tsananin damuwa na maganar da suka yi da shi. Tunaninta wa yake so, kuma mai ya sa yake faɗin ta yi masa nisa? Kan me zai ɗauki son mace ya ɗora ma kansa har yana tunanin in ba ita ba ba zai iya rayuwa ba. Bayan namiji ne wanda ko bai samu soyayyar mace ba zai samu wacce ta fita.

A ɗan tunaninta sai take ganin duk ba matsala bace wanda zai tashi hankalinsa har ya saka shi cikin ƙunci domin shi ɗin namiji ne da Allah ya ba shi damarmarki da dama.

Kwanciya ta yi tana tunanin halin da yake ciki. Tana wannan tunanin har bacci ɓarawo na yi nasarar sace ta.

Zaune yake kan sofa daga shi sai gajeren wando. Duk da sanyin A.C da ya cika ɗakin sai yake jin zufa na kama shi ta cikin jikinshi, sakamakon abin da yake son aikatawa.

Miƙewa ya yi, ya ɗauko ƙaton hotonta da ya zana ya rungume a ƙirjinsa cike da begenta. Ya ɗan ɓata lokacin yana rungume da hoton sai kuma ya miƙe ya ɗauko maganinsa ya ɓalla tare da haɗiya bisa ƙa'ida wanda a hankali ya fara aiki ya daina jin sha'awarta.

Sabuwar wayar da ya siya da da sabon layi ya sanya hannunsa ya ɗauko. Bayan ya gama deciding da yanke hukunci zartacce akan lamarin ya aminta da komai ya faru in the future zai ɗauka, domin tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan duka.

Sa layin ya siya wanda ba shi ya yi rigister ba ya ɗauko sai ya kunna wayar yana kallon wayar da ta gama serching ta kunnu.

A hankali ya danna numbarta a cikin wayar da nufin ya yi mata magana ta whatsapp sai kuma ya fasa ya kashe wayar ya koma ya xauna yana tunani.

A ƙalla sai da ya yi haka sau biyar da ga ƙarshe ya yi nasarar tura mata tsaƙo kamar haka:

"Na kasa natsuwa na kasa sukuni kullum zuciya cikin begenki. Kar kinyi mamakin hakan, domin na riga na gama a concluding son ki da ya mai dani mahaukaci shi zai yi ajalina, amma kafin na mutu, akwai buƙatar ki san wani yana can yana begenki da fatan ki zamo ta sa na har abada. Na ki mahaukacin masoyi."

Ya tura mata da hakan tare da kashe wagarsa gabakiɗaya yana jin yadda zuciyarsa ke bugu tamkar za ta fito waje! Ko wanda ya yi gudun kilometer 1000. Bayan ya tura mata alert na naira miliyan ɗaya.

Hilah na zaune cikin hall ɗinsu tsaƙon ya shigo wanda ba ta duba ba, saboda lectured ɗin da ake musu hankalinta na kan malamin, domin sam ba ta wasa da sauraren lecturer in yana lecturing.

Bayan ta fito sai ta nufi cafateria don ta ci abinci saboda yau a makare ta haɗa karin kummallon ba ta samu damar da za ta yi breakfast ba.

Tana zaune ita da ƙawarta Nihal suna cin abincin sai ta tuna da tsaƙo ya shigo cikin wayarta, wanda ta ɗauko wayar da ke cikin jakarta don ta duba.

Da sauri ta miƙe tana kallon alert na one miliyan da ya shiga cikin wayarta tun lokacin.

"What!" Ta ce cikin mamaki tana kallon alert ɗin.

"Miliyan ɗaya a ka turo mini! waye ya turo?" Ta yi tambayar cikin mamaki tana nuna wa Affrin wayarta da ta tsaya tana kallonta cikin mamakin abin da ya sanya ta razana.

"Waye shi Hilah?"

"Ban sani ba domin kamar ba da account ɗinsa aka tura ba ta banki ne."

"Ok, kuma babu tsaƙon da ya turo? Ki duba wataƙila ya tura miki baki gani ba."

Ba tare da musu ba ta shiga cikin inbox ɗinta jikinta na rawa.

Ganin saƙon ya ɗan sanyaya zuciyarta amma ganin an rubuta anonymous sai ta ɗan ji faɗuwar gaba.

"Ga message na gani sai dai da alamar wanda ya yi turo tsaƙon, ba ya son bayyana kansa domin anonymous ne." Ta ce tare da buɗe tsakon wanda ta fara karantawa sai dai ba ta ƙarasa ba ta tsaya cikin tsa




Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*



NA



JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"



☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation


*GARGAGAƊI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.


SADAUKARWA

Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.



PAGE 4


BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM


Ganin saƙon ya ɗan sanyaya zuciyarta, amma ganin an rubuta anonymous sai ta ɗan ji faɗuwar gaba.

"Ga message na gani, sai dai da alama wanda ya yi baya son bayyana kansa domin anonymous ne." Ta ce tare da buɗe tsakon, wanda ta fara karantawa sai dai ba ta ƙarasa ba ta tsaya cikin tsananin mamaki.

"Waye wannan mahaukacin masoyi da ya tura miki tsako haka?" Afrin ta tambaya cikin tsananin mamaki.

"Tabbas ya cika mahaukacin masoyi! Domin babu mai hankalin da zai bayyana soyayyarsa a ɓoye da alamar matsoraci ne." Ta ce cikin tsananin mamaki. Sai kuma ta ɗora da cewa kafin Afrin ta yi magana.

"Kin ga shi ma da kansa ya sawa sunansa mahaukaci masoyi." Ta kashe wayar tare da maida ta cikin jaka tana jinjina lamarin lokaci guda kanta ya kulle ta shiga cikin duniyar tunanin.

"Ni fa ina tunanin wani ne da yake can yana fama da sonki, amma ya kasa zuwa gareki kin san ke ɗin ba kowane namiji, zai iya tunkarar ki da maganar so ba; saboda baiwarki da da ilminki uwa uba kyau tamkar ke kika yi kanki."

Shiru ta yi ba tare da kalamanta sun yi tasiri a ranta ba, domin hasashenta ne wannan. Besides, dukanninsu mutane ne kuma babu wanda ya fi wani a gurin Allah sai wanda yafi tsoron shi, don haka ba ta ganin wannan a matsayin hujja da zai sanya ya kasa bayyana kansa gareta.

"Wannan ba hujja bace, amma ko ma mene kyautar kuɗi da ya yi haka dole ya bayyana kansa, bari na je gida na sanar wa Ya Huwais, na san shine kawai zai bani shawara da mafita." Sai ta miƙe tana saɓa jakarta tare da cigaba da cewa,

"To amma ta ya ya akai ya samu account ɗina? Tunani nake ya san ni duk wanda ya turo wannan tsaƙon."

"Eh, ai ba abin mamaki bane saboda kamar yadda duniya ta sanki haka account ɗinki. Mutane nawa suke turo miki da kyauta su ce sun karɓa a musabaƙa da kika cinye."

"Haka ne." Ta ba ta masa sai suka fara tafiya tana cewa,

"Bari na wuce da wuya na dawo tun da surmiting assigment za mu yi, in ban dawo ba ga shi kawai ki ba da." Sai kuma ta canza shawara ta ce,

"Kai bari ma zan dawo kawai."

"Ok." Ta masa tare da miƙa mata assignment ɗin, wanda ta karɓa ta mayar cikin jakarta tare da ciro makullin motarta ganin sun iso gurin.

Da ta isa gida sai ta yi farking a ƙofar gida ta shiga cikin gidan wanda cikin sa'a Ummu na bacci.


Kai tsaye ɗakinsa ta nufa da yake kwance wayarsa a hannunsa ya rungume yayin da ya tafi duniyar begenta.


Ƙamshin turarenta ya dawo da shi da duniyar da ya lula.

Da sauri ya jawo laptop ɗinsa ya zauna ya buɗe tare buɗewa ya fara daddanawa fuskarsa a ɗan ɗaure.

Kallonta ya yi da ta yi sallama tare da ƙarasawa inda yake ta zauna.


"Lafiya sis, ba kin ce sai 4 pm za ki dawo ba?" Ya yi mata tambayar cikin tsannin mamaki duk da ya san dole ta dawo saboda shawarar shi kawai take nema, don baya manta ko a lokacin da ta fara menstration ɗin shi ta fara nuna wa mawa.

"Haka ne Ya Huwais, amma ba zan iya zama har lokacin ba domin tsakon da aka tura mini." Sai ta ciro wayarta ta nuna masa tsakon ta ɗora da cewa,

"Abin da yafi bani mamaki shine har da kuɗi ya tura mini miliyan ɗaya."

Zare idanunsa ya yi cikin tsananin mamaki tamkar bai san abin da ke faruwa.

"Miliyan ɗaya! Waye shi kuma mai yake so daga gare shi, ko kin san shi kike ɓoye mini?" Ya yi mata tambayar cilkin ɗan ɗaga murya har lokacin idanunsa a xare.


Rau-rau ta yi da idanunta lokaci guda hawaye suka fara sintiri kan kyakykyawar fuskarta.

"Kaicona! Sai na yi tur da ni in har zan fara ɓoye maka sirrina." Ta faɗa tana kallonsa.

"To mene ne abin kuka?" Ya ce tare da jawo tissue yana ɗauke mata hawayen

Hannunsa ta kama ta riƙe gam wanda sai da ya ji ɗumin jikinta, har cikin bargon jikinsa, ya rintse idanunsa yana jin yadda yake jin ɗumin na ratsa ko ina na jikin shi yana saukar masa da natsuwa, wanda ya sanya shi zare hannun da sauri yana istigifari da ta'awizi kan Allah ya kawo masa ɗauki tunkafin sheɗanin da ke ƙoƙarin galaba a jikinsa ya yi.

Ba tare da ta fahimci halin da ya shiga ba ta ƙara kama hannun a karo na biyu ta riƙe sosai.

"Ya kafahimce ni wallahi bani da masaniya kan lamarin nan."

"Ok." Ya ce cikin basarwa ya cigaba da aikin shi yana tunanin mai zai ce mata.

Ganin shirun da ya yi ya sa ta fara magana da cewa,

"Ko ma waye wannna tabbas ya cika mahaukacin masoyi, domin ina ya taɓa ganin an yi soyayya a ɓoye? Wataƙila kuma mahaukaciyar zuciyarsa ta gaya masa zai iya siyen soyayyata da kuɗi ne, ba tare da ya san bani cikin makwaɗaitan matan da suke sayar da rayuwarsu saboda kuɗi ba. Namiji mai ilmin addini da boko nake nema, wanda zai amfani da ilminsa duka a cikin rayuwar aurenmu. Kuma ai ina da wanda zai aura don haka ya kama kansa."

Wani kallo ya juyo ya watsa mata, take zuciyarsa ta fara zafi na kishinta, sai kuma ya juya zai ci gaba da aikin wanda ya sanya ta kama hannunsa.

"Yaya, ka yi shiru ba ka ce komai ba."

"Me kike so na ce domin na ga lokacin da Hammad ya ce yana sonki ba ki gaya mini ba." Ya jefo mata maganar cikin bazata.


"Bani da zaɓi ne, bisa umurnin Ummu da ta ce kar na sake na gaya maka, ganin yadda kake tada hankalinka kake nuna kai xaka saɓa mini miji da kanka. Cewarta shi na gida ne, kuma ya cika criteria da kake son mijin da zan aura ya cika." Ta ba shi masa.

Shiru ya yi dama ya san tursasawar Ummi ne har ta fara kula wani ba ta gaya masa ba.

Karɓar wayar ya yi daga hannunta ya ɗan tsaya yana karanta tsaƙon tare da dogon nazari game da abin da zai ce mata.

Bayan ya gama nazarin sai ya ije wayar saman cinyarsa yana ƙare mata kallo ganin yadda ta wani firgice.

Tattara dukkan hankalinsa ya yi gareta ya ce,"Wa ki ka gaya ma wa?"


"Babu kowa sai Afrin ƙawata, bayan ita babu wanda ya sani."

"Good!

3 / 23