Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 48

18K to 21K   out of 143.8K words

kallon hanya,ganin ta ya saka shi sakin ajiyar zuciya mai ?arfin gaske.
"Shigo mana Juwairiya hankalina ya tashi matu?a na yi zaton wannan mara kirkin Baban nan naki ya hanaki zuwa "Yace da ita ganin ta dogare a bakin ?ofa,ta Wan tsaya ta na kallon shi sai kuma ta ?ara haWe fuska haushin sa take ji don shi ya yi shishshigi a lamarinta,har ya saka Bab Sani ya yi mata wannan tozarcin.

"Gaskiya ban ji daWin abin da ya faru ba!Haba sai kace ba ?anin mahaifinki ba.Lamarinsa ya tsoratani ba?in cikina yadda ya?i yadda da maganata akan ina sonki da aure.Kawai ki gaya min dangin ku naje can na nemi aurenki."

Yace da ita ya na kare mata kallo don ya fahimci a wani hali take,takaici ya kamata jin abin da ya faWa sai ta mi?e hanyar kicin ba tare da tace mishi komai ba.

Gabanta ya sha tare da ri?e mata hijabi yace."Na fa fara ?osawa da halin ko in kula da kike min haba waike dutse ne a ?irjin ki ba zuciya ba!Ki ji tausayina ko don halin da kike ciki ki zaSe ni a matsayin mijin ki hatta mahaifiyarki ba za ta zauna a wannan gida ba.

Takai hannu da nufin ta ?wace hijabinta sai ya ri?e hannun cikin kalar tausayi ya na jin kamar ya yi mata kuka,ganin sam ba ta da rangwame akan soyayya.Baki ta buWe da nufin ta yi magana sai suka ji sallamar Anty Naja ta shigo da sauri da alamun gajiya tare da ita.

Da sauri ya saki hannunta ya matsa gefe ya na zare ido,ita ma cikin tashin hankali ta tsaya ta kasa haWa ido da ita ta na jiran tashi n hankalin da za ta fuskanta.
Amma sai dukansu ta basu mamaki ta faWa kan kujera ta na lumshe ido "Wash Allah! Na gaji matu?a Juwairiya bani ruwa don Allah."Tace cikin sakin fuska ba tare da ta fahimci komai ba."
Da sauri Juwairiya ta shige kicin ta na mamakin sokanci irin nata haba ta ya ya za'ai tace bata fahimci komai ba.Bayan ta kawo mata ruwan ta haWo har da abin motsa baki,ta shige kicin ta ci gaba da aiyukan ta can sai ga shi ya shigo yace."Ina jiranki in kin gama zaki tafi ina hanyar da nake tsayawa sai mu ?arashe tautaunawar.

Ganin ba zai saduda ba Mama tace ta ha?ura da aikin in ta bata kuWin aikin ta na wata haka kuwa aka yi,bayan ta yi mata albashi ta ?ara mata harda zannuwa masu kyau biyu nata sai Waya Mama ta Winka,kasancewar suna da biki a family Win su kuma tare da Juwairiya za su tafi garin Kano.

Hankalin Anty Naja ya tashi matu?a ganin ba ta zo aiki ba,ta shiga ruWani ta din ga tunanin ko ta yi mata wani abu amma bata gano ba.Shi ma hankalinsa ya tashi sosai duk da yaso sai sun gama daidaitawa a tsakanin su sai tabar aikin,amma ta yi sauri gashi ya na son yaje gidan ya na tsoron tijararren ?anin mahaifinta

Sai ya azalzala ma Anty Naja ta shirya ya kaita har ya na mata barazana da ya na nan akan bakan sa in dai ba Juwairiya ba sai dai ta bar aikin,ai kuwa ba shiri ta shirya suka taho ya ijeta a kofar gidan ta shiga ciki ya zauna da yaransa ya na jiran ta fito,burin sa ya ga Juwairiya.

Juwairiya na tsakar ta na girki Mama ta na zaune ta na jan carbi ta yi sallama ta shigo,da sauri Juwairiya ta saka hannu ta rufe fuskarta ta na dariya.
Anty Naja ta harareta ta na kallon Mama tace."Da ma Mama haka Juwairiya take bata da kirki? Kawai ta guje mu ba tare da mun yi mata wani abu ba,hankalina ya tashi ?warai Mama gaskiya ba ta kyauta ba."

Ta ?arashe maganar ta na kallon Juwairiya sannan ta Wora da cewa "Ko mun yi miki wani abu ne?Ai gaya mana ya kamata ki yi ba ki Wauke kafafunki ba.Ni da yara da Daddyn su Abnaj duk hankalin mu ya tashi."

Mama ita ba tace komai ba tace komai ba sai dariyar ya?e take mata,bayan sun shiga Waki suka yi gaisuwa a tsakanin su sanann shiru ya biyo baya.Sannan Anty Naja ta katse shirun tace."Me ya faru Mama kwana biyu bata zo aiki ba na yi tunanin ko wani ba lafiya,amma da nazo naga kowa lafiya.Ko na yi laifi ne Mama."

Matu?ar kunya sai ya lulluSe Mam ta ji kamar ta nitse ta rasa yadda za ta fara mata bayani,har Juwairiya ta yi sallama ta shigo,ganin Mama ta kasa mata bayani ta kalli Juwairiya tace."To ko auren ne ya zo,in kuma wannan ne Mama ai ni ce me haWo kayan Waki ko?"Ta ?arashe maganar ta na me tsigar tambaya.
I ta dai Juwairiya ba tace komai ba ta na ta wasa da yatsunta,Mama ta daure tace."Ba shi bane ban san dai yadda zaki Wauki zancen bane shi yasa na kasa sanar miki,amma ranar wanka ba'a Soyan ciji."

Gaban Anty Naja ya faWi daram!Sai ta ji zuciyar ta ta raya mata lai-lai a kwai abin da suke Soye mata,duk da bata san ko menene ba amma taji ta firgita Allah ya sa ba wani lamari me girma ya faru ba.
Ganin ta yi shiru ba tace komai ba jikinta ya yi sanyi Mama dai ta daure tace."Dama mijinki ya bijiro da wata magana ya na son auren Juwairiya har ya shigo da maganar gida,mu kuma muka ga rashin dacewar haka saboda irin halaccin da kika yi mana shi yasa nace ta dakata da aikin kawai ki nemi wani."Tace ta na karantar fuskarta.







Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na Tara.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga n??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????umba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zaka?uran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.








*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA TARA*

Abin mamaki da yake macece wayayyiya sai bata nuna komai ba duk da irin tarin luguden da zuciyar ta take mata,ta na jin kamar ta fita ta sha?o shi munafiki kawai haba ya kamata a ce ta Wago tuntuni saboda yadda yake yabon ta da kalamai magana Waya biyu ya sako sunanta,amma da yake ba ta da wayo sai ba ta Wago ba ta danganta kular da yake bata a dalilin ta na kular mishi da yara,sam ba ta yi tunanin zai ce ya na sonta ba ganin basu da komai ?ar Malam Shehu.
Wayancewa ta yi ta na dariyar ya?e tace."Haba Mama ni na yi tunanin wani lamari ne me girma yasa kika hana ta,amma akan wannan Wan ?aramin abin zaki hana ta,in dai a kan wannan ne karku damu ai gara ya auro wacce na sani da ya Wauko min wata.Kuma karku manta shi fa mijin mata huWu ne,don Allah karku ce zaku hana mishi aurenta."


Yanayin yadda take maganar ya nuna da ?arfin hali kawai take yi,amma ta na ?o?arin ?a?alo dariya.
"Haba ?ar nan ai ana barin halas don kunya kawai ya nemi wata,amma Juwairiya ba tsarar auren sa bane."
Anty Naja ta dage ta ri?e kishinta ta na ba ma Mama baki akan ta ha?ura ta yadda ayi auren,sannan ta Wora da ko ba zasu bashi ba don Allah Juwairiya ta dawo aiki.

Daga ?arshe ta yi ma Mama sallama ta fita har ta na tonon Juwairiya ta fito tare suke da angon ta yazo biko,ita dai ba tace komai ba a ranta take mamakin wani irin hali take dashi.Bayan ta jaddadawa Juwairiya tazo aiki ta yi musu sallama ta fita.

Bayan ta fita ta buWe murfin mota ta shige tare da haWe girar sama da ?asa a ranta ta na mamakin raina mata wayo da ya yi wato ya turo ta ta yi mishi bikon budurwar shi,bayan ta sheda Juwairiya yarinyar kirki ne sai tace amanarta suke ci.
A yadda ya ga yadda ta fito sai hankalinsa ya tashi don bai yi tunanin za su gaya mata abin da ke tsakanin sa da ita ba,sai ya yi dana sani da tuntuni ya tare ta da maganar.
Bayan sun fara tafiya ya kalleta yadda ta ?ara cin magani fuskarta ba rahama yace cikin ?arfin hali ya yi mata tambayar."Ya take ko ba ta jin daWi ne?"

Haba kamar jira take ya yi tambayar lokacin da take kallon waje ta fara bala'i in da take shiga ba nan take fita ba tace."Munafiki da zamu taho ai da ka gaya min biko zan je na yi maka.Da ma amanata kuke ci kai da ita da ta amince ?ila sai dai in ji ta tare a gidana ko."

Nan ta Salle ta na gaya mishi kalamai zafafa mara sa daWin ji,in da take shiga ba ta nan take fita ba a hanya ta zage shi tatas! Ta yi mishi wankin babban bargo.Shi dai shiru ya yi mata don ya san ya ibo ruwan dafa kansa kuskuren shi Waya da bai sanar mata ba,kuma bai Wauka su Juwairiya za su yi suSul da baka su gaya mata ba.
A haka suka kwana sam ba ta barshi ya rintsa ba,shi kan shi bai san ta iya rikici ba,sai ayau ya san ta na da zafi mata da kishi humh ba'a magana.
Washegari Juwairiya ta na zaune ba ta da ninyar zuwa aiki amma Mama ta matsa mata akan taje.Sai dai yadda ta ga gidan ta san ba su kwana lafiya ba.

Tun daga falon take kallon yadda ya hargitse ko ina an birkita shi sai gabanta ya fara faWi ta san cewa a kwai wani girman lamari da ya faru.
"Munafuka kema me ya kawo ki gida!Maza fita matsiyaciya me kwacen miji kawai,in banda ke jahila kina ?ar talaka za kiyi tunannin mijina zai aureki."Anty Naja take magana cikin zafi sannan ta Wora da cewa."Fita kar na ?ara ganin ki a gidana,sai abi wani sarkin amma mijina yafi ?arfin ki.

Ko da ta dawo ta sanar ma Mama tace."To shikenan Allah ya sa haka yafi alkhairi.Hankalin Baba Sani ya kwanta ganin Juwairiya ta bar aiki kullum ta na gida,hakan sai ya yi masa daWi musamman da yake tunanin yanzu komai zai kwaSe musu.
Juwairiya ta yi tunanin Baban Abnaj zai biyo bayan ta,amma shiru kake ji Malam yaci shurwa wato matarsa taci ?arfinsa.Ganin haka sai suka kama sana'a sosai da kuWin da Baban Abnaj yake basu,yanzu har abincin siyarwa suke yi Ibrahim ya na kai wa ?ofar gida.Kuma suna samu ba laifi don da shi suke cin abinci.


*********

Kimanin shekaru huWu da auren su suna zama cikin so da ?aunar juna,sai ?an saSanin da ba'a rasa ba a tsakanin ma'aurata.Kullum A.m ya yi kasa?e ya ji Zainab tace mishi ta na da ciki amma hankalinta ba shi a gurin tunna ba ta taSa yi mishi maganar baby ba.


Lamarin sai ya fara damunsa musamaman da ?annin shi da sa'annin shi suna da yara,amma shi matarsa ko Satan wata ba ta taSa yi ba.

Sai kuma Allah ya Wauki son ?ara ya Wora mishi in ya gan su kamar ze zare.Ya na matu?ar son yara kullum ya na hanyar gidan ?an'uwan shi ya na manne da yaransa.Daddy Win shi ya fara ?orafi ya na tsoron kar A.m ya Wauko rashin haihuwa sai ya fara mishi ?orafi sosai kullum ya na kiran waya akan suje likita ya duba su.

Ganin yadda ya Wauki son yara ya Wora ma kansa sai Zainab ta yi gum da bakinta ba ta taSa suSutar baki ta nuna mishi ita ce ba ta son ta haihu take shan ?wayoyi ba.
Sun Wan fara samun saSani yadda yake kwaso yaran ?an'uwan shi ya kawo gidan ya siyo musu kayan wasa.Ranta Saci yake sosai ta na ganin hakan kamar takuratawa rayuwarta ne,duk yaran da ze kwaso ba ta musu komai sai masu aiki.Gaskiya Allah ya jarabce shi da son yara sosai.

Wataranar Alhamis Zainab ta tashi da ciwon ciki kamar za ta mutu,hankalin A.m ya tashi matu?a ganin a sume ya Wauke ta ya saka a mota suka nufi asibiti.
Bayan an karSe ta aka yi mata ?an gwaje-gwaje tare da turata Wakin hoto,duk abin da ake ta na kwance kamar gawa ba ta san in da kanta yake ba.Likita ya gano mahaifarta ce ta samu matsala sakamakon tarin ?wayoyi da ta din ga Winkira ma kanta masu ?arfi na hana haihuwa.Wanda sakamakon haka mahaifar na gabda ruSewa in da likitan ya ba A.m shawarar ayi mata aiki a cire mahaifar.
Tsananin tashin hankali A.m ya shige shi ya din ga kallon likitan kamar ?arya ya yi mishi."Me yasa Zainab za ta aikata hakan?Hakan na nufin ba ta son shi ne har take shan maganin hana Waukar ciki don kar ta haihu?"
Irin tarin tambayoyin da yake yi ma kansa kenan amma ba shi da amsarta,daga bisani ?e?eshe zuciyarsa ya yi kan ?aryata likitan ya san Zainab ba za ta aikata hakan ba,musamman yadda ta ga Daddyn shi ya mutu akan ya ga ya haihu,sannan yadda yake nuna mata ya na son ta haifa mishi baby ta na nuna masa Allaha ne be kawo ba.To hakan na nufin yaudararsa take.

Sai ya yi zuru ya na kallonta da take saukar da numfashi cikin rashin haiyaci ta na bacci,sakamakon allurar baccin da likita ya yi mata.Sai ya shafi fuskarta ya na me tausaya mata halin da ta shiga.

"Gaskiya ban yadda da maganar likita ba ina ta ya ya zan rayu ba tare da na ga Wan cikina ba,duk da na san Allah ya ba jarabtar bayinsa amma gara wata jarrabawar ba wannan ba.Ya na ganin halin da Daddy Win shi yake shiga saboda rashin Wa duk dukiyar da ya tara ya tafi a banza.In in haka ne ya zan yi da shares Win da na saka ma yarana tun kafin su zo duniya a ?asashen waje.

Nan take zuciyarsa ta?i amincewa da abin da likitan ya faWa duk da ya san asibitin su ?wararru ne.
Kusan awa Waya ta na baccin wahala sannan ta buWe idanunta.Da sauri ya ri?e mata hannu ya na shafar kanta."Kin tashi babyna sannu. Yace ya na ?o?arin temaka mata tashi ta zauna.

Bayan ya haWa mata tea ya ba ta tasha ta lumshe idanunta ta na ji har yanzu wani abu ya na karta mata a cikinta,ita kaWai ta san irin tarin azaba da raWaWin da take kwankwaWa.

"Ya jikin sannu kin ji abin da likita yace game da ciwon ki?"Ya tambayeta da murya mai sanyi ya na gyara mata Waurin Wankwalin ta da yake son ya warware.Ba tare da tunanin komai ba tace."A'a hubbina."A ta?aice ta ba shi amsar don ba ta son dogon surutu.

Ya Wan ja numfashi ya fesar ya jinjina girman lamarin baya so ya gaya mata,bai san yadda za ta karSi lamarin ba cewar ba ta haihuwa mahaifarta ya fara ruSewa wanda dole sai an yi mata aiki.To amma ya na son ya gane shin da gaske ita tasha maganin hana Waukar ciki har ta illanta musu kanta,ba yan haka da ya bari sai ta warke.

"Likita yace ba zaki taSa haihuwa ba yanzu ma mahaifarki za'a yi miki aiki a cire."Yace da ita ya na son yaga yadda za ta ?arSi lamarin.
"Inna lillahi.Tace tare da bayyano wani tashin hankali a fuskarta nan take fuskarta ta sauya sai hawaye,ta yi ?asa da kanta ta na son ta yi magana amma ta kasa sai hawaye dake ta gasar sauka a fuskarta.A zuciyar ta kuwa illa tarin nadama da faWin"Na cuci kaina!"
"Ina son na sani da gaske ke kika illan ta mahaifar ki Zeey sabosa bakya son ki haihu da ni,ko dama ba kya sona ne ko a kwai wani ?udiri a ranki."Yace bayan ya yi ?asa da kan shi dai-dai da kunninta saboda baya son aji me yake faWi.

Ta dago ta kalle shi fuskarta cike da hawaye ganin yadda fuskarsa ya bayyana da tashin hankali,don in ba ta yi ?arya ba har hawaye ta gani a fuskarta.
"Na shiga uku yanzu in yace ya na son ya haihu ga shi ni bana haihuwa ya zan yi?Kuma wallahi ba zan taSa iya lamun ce na gan shi da wata mace ba.Gara ma ace na ga ranar mutuwata!Tace a zuciyarta ta na kukan nadama.

"Ka yi ha?uri hubbi ka yafe min na san na yi wa rayuwata illa ba zan taSa haihuwa ba!Girman lamarin ya yi wa zuciyata girma.Duk akan sonka ne ina son karka juya min baya inna fara haihuwa na saki sanann jikina ya canza,kuma na sha jin kana faWin baka son jikina ya canza kafi son na kasance yadda nake.Kuma a wannan lokacin ban shirya haihuwa ba gani nake yara kamar takurane a gareni duba ga irin yanayin aikina."Sai ta fashe da kuka ta na ?arawa taci gaba da cewa."Wallahi ba zan iya buWe idanuna na ga wata mace a matsayin muharramar ka!In kuwa ranar ta kasance to kasa a ranka zan kashe kai na na kasheta sannan na kasheka.In ta?aice maka mutuwar kasko za muyi,don ina sonka ba zan juri wata a kusa dakai ba."
Tsananin tashin hankali ya shige shi tare da nadamar furta mata waWannan kalamai da yake na baya son yanayin ta ya canza,duk da be yi tunanin za su yi tasiri a gareta ba har ta aikata wannan abu su yi dana sani.

Ya zura hannun sa a aljihun wandon sa ya na kallon yadda fuskarta ya canza zuwa tsabar tashin hankali,ita kanta ya san ta yi nadama amma kuma mara amfani.
Ganin be ce mata komai ba ya na

7 / 48