Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 48

39K to 42K   out of 143.8K words

faWa sai ya ji kamar bai fahimci maganar ba kuma har ga Allah a cikin zuciyar sa ya gasgata hakan da bai ji ba.


" Ikon Allah bayin Allah don Allah ka ?ara maganar wallahi ban ji me ka ce ba yadda ka san ciwon kurumta ya kamani,a lokacin da ka yi maganar sake faWi kamar yadda ka faWa kuma da Hausa don Allah ba turanci ba.


A.k ya so ya yi dariya jin ya ce ya yi magana da Hausa ?ila in ya ?ara maganar da larabci zai ce ya yi mishi,A.m ya mai da wayar sa a aljihun rigar sa shi bai ga dalilin da A.k zai tsaya ya na Wan waken zagaye ba,ya san a ran shi irin abin da suka zo mishi da shi bai isa ya hana auren Juwairah ba



" Auren Juwairiya kuka zo nema!" Ya maimaita hakan ya fi sau ba adadi daga bisani ya mi?e zubbur ya na faWin." Haba dama na yi tunanin a lokacin da na ganku irin yaran manya ne da suke shaye-shaye su yi Satan kai su dami mutane,kun ga tunanina ya zama gaskiya ga ku kamar mutanen kirki ta waje amma ta ciki ba hali."


Ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya ba su ikon koda jan numfashi ba." Wallahi na Wauka wani abin ya kawo ku ko ba sa rana akan Juwairiya a bazan taSa yadda ta auri wani daga cikin ku ba,bare na ba da Juwairiya yanzu haka bikinta saura sati Waya don haka ku wuce ki bani guri ?an ?waya kawai."


A.m ya harzu?o ya na faWin." Wa kake ce ma ?an ?waya kai ne mugun Wan ?waya da ka kasa gane mutanen kirki da na banza,ba giya muke sha ko kuma kamfanin ?wayar muke haWiya."



"A.m ya kamata ka saukar da fushin ka kasan me muka zo nema."


A.k ya ce mishi tare da kama shi ya zaunar ya na dafa kirjin sa.
" A'a ka barshi ya yi min rashin kunya ya biyo ni har gida zai gaya min magana,a Wakina fa kake.To bari kaji ko mutuwa za kai sai dai ka mutu, kai ko maka mutu ne aka fito da kai a ?abari,a ka ce na baka auren Juwairiya numfashin ka zai dawo wallahi sai dai a turbuWaka a cikin ?asa ta rufe maka ido."
" Wai tsaya kun ma san me kuka zo min da shi?Juwairiya da na tsana a rayuwata shi ne zaka kazo ka na da kuWi ka aura taS wallahi ina."


Da aka kai wannan gabar sai A.m bai ce komai ba ya rintse idanun shi kawai don aikin A.k ne.Amma sai ya ji A k ya yi shiru ya na kallon Baba Sani da yake faWin ?iri-?iri ba ya son ?ar wansa ta ?aru,kai wannan wane irin mutum ne an ya a kwai zumunci a duniya saboda son duniya ko ya ce son kai,mutane sun manta zumunci bayan Allah ya gaya mana zamu tsallaka siraWi mara zumunci ba zai sha ba.


A.m ya buWe baki zai yi magana ganin A.k ya?i magana dai-dai lokacin da Baba Sani ya sausauta murya ko me tuna ya sa ya yi sanyi ya ce." To kai in ban da ku me za ku yi da mace irin Juwairiya yarinyar da ta gama zagaye duniya ta na yawon aikatau kuma duk mazan gidan sun san ta,sam ba ta da hali mahaifiyarta ta koya mata bin maza har sata take yi ka tambaya har kulle ta a ka yi a prison."

Ya ?ara sausauta murya ya matsa kusa da A.k don ya fi A.m sau?i ya fara magana kamar zai yi mishi raWa amma A.m ya na jin me yake faWi." Ina da yara sun yi karatu na boko in kuma so Juwairiya ba ta san komai ba har talla yi take yi,ai da ka aure ta gara na yi maka fatan ka mutu ba aure.

" Juwairah nake so kuma zan aureta ko da ace duk mazan duniya sun san ta a matsayin ?a mace."A.m ya ce ransa a Sace.


" To ba zan ba da ba kuma kamar maganar ta ita matar wani ne na rantse,a yau zan Waura mata aure ba sai an jima ba don ina zargin ku za ku iya sace ta.To ni sai in ce kamar an yi maka baki kamar ka mai zai saka ka auri Juwairiya uban ta har ya mutu faskare yake yi, a gurin faskaren ya sara ma kansa ya mutu shi ne za ka ce ka na sonta.


" Nima ba son ta nake ba ban taSa jin ina son wata ?a mace bayan matata ba,kai ma in ka furta ina sonta ka yaudari kan ka don duk faWin unguwarku ban ga macen da zan ji ina son ta ba."


Kawai sai ya yi galala ya na kallon shi a ransa tunani yake to uban me zai yi da ita,koma dai mene ne ba za ba shi ba in ma ya na son ya yaudare shi ne ya ba shi aurenta,yadda ya rantse Juwariya ba ta ba jin daWi a duniya tun da ta kange kwaWinsa a kan ta gara ya ba ma wannan tsohon ya wula?anta rayuwar ta.

" Ku faWi ko me za ku ce ni ba yaro ba ne kuma ba zan baku auren ta ba yanzu ma zan Waura mata aure don haka ku cire wanann tunanin."

A.k ya karkace ya zaro makullin mota ya ije masa a gaban sa sannan ya janyo cek da ga aljihun sa ya ije na kimanin miliyan biyar.


Wayyo Allah zo ka ga ido sai ya zare ido can kuma ya fara mitsinan kansa ya gane ko mafarki yake." Ka bar cutar da kanka ta hanyar mintsnin kanka ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya lamarin ke faruwa,in har ka bamu haWin kai har gida zan canza maka rayuwar ka ta dawo sabuwa in har zaka ba ni auren ta."

A.m ya ce da shi ya na kallon sa yadda ya ruWe kamar zai zare." Ikon Allah don Allah in mafarki nake ku dake ni sai na farka wai ni ne zaku ba wannan kuWin don ku auri Juwairiya an ya ku ba ?an cin kai ba ne?"

Ya faWa ya na ?arewa A.m kallo tunanin sa shi ne babba a wurin cin kai saboda ya fi A.k jiki da faWi."Ko ma duniya muke ci ba ruwan ka in mun cinye ta tunna ba ?aunarta kake ba."

A.k ya ba shi amsa amma kuma sai A.m ya kalle shi ya ce.

"Ka daina danganta mu da wannan mu mutane ?warai ne kawai fatanmu ka amince da bu?atarmu."

Ga mamakin su sai suka ga ya tattara kuWin ya saka a aljihun wandon sa har da makullin motar ya fara zare ido. " Duk da cewar na tsane ki saboda wani ?udiri na wa ba na fatar in da za ya huta ta ji daWin aure,amma ba zan bari wannan damar ta wuce ni ba Juwairiya sai dai wallahi ina tsananin ba?in cikin faruwar lamarin da na Waya daga cikin ?ata kuka nema Allah bari na kira ta sai dai Juwairiya ta nuna mata kyawun halitta amma ta na da hali."


Mi?ewa ya yi sai A.k ya kamo hannunsa ya zaunar da shi." Ka barshi ba bu?ata ita dai Juwairiyar ya gani yake son ya aura na wucin gadi,shekara Waya tak za ta yi zai rabu da ita don a cikin sirri za' a Waura auren."


Ya Wan kalle su a fakaice ya tabbatar da gaske suke yi ko fim suke son shirya wa suka yaudare shi haka." Tabbas haka maganar abokina yake ni zan aureta na shekara Waya matata ce ba ta haihuwa,shi ne nake son ka aura min ita bayan ta haihu zan Wauke Wana na sake ta ita ma zan biya ta kamar yadda da na yi maka."

Wani irin daWi ya cika mishi rai ya kama hannun A k ya ri?e ya na faWin." Kasan Allah ko auren kwana Waya kake son yi da ita zan baka, kai duk abin da za ka yi da rayuwar ta ba nida matsala in har za ka bani kuWi sai dai da sharaWin komai ya din ga biyo wa ta hannuna."

" Wannan kuma ba zai yiwu ba za mu baka duk jin daWi na rayuwa,amma Juwairiya na cikin wani hali a yanzu ina da labarin mahaifiyarta da ba lafiya kuma za 'ayi mata aikin zuciya ka?i ka taimaka,ga ?aninta da yake da matsala tun mahaifinta na raye yake da burin a yi mishi aiki don haka zamu fitar da shi da mahaifiyarta,ita ma mu saya mata gida,sannan ba su da cin yau bare na gobe ka ga ya dole mu inganta rayuwarta wanda da shi zamu ci ?arfin ta har ta amince da auren."



Baba Sani take ya haWe rai jin baza a ba shi na Juwairiya ba da ya rantse ba zai ba ta da yawa ba,amma sai ya Wan saki fuska ya na ce wa." Ni ma ki yi min uzuri ba ni da shi ne da na taimaka mata,wannan aikin wahala kawai nake yi ai nima abin a taimaka min ne."

A.k tsaya wa ya yi ya na mamakin sa ya sani ce wa a kwai mutane masu son kuWi amma wannan ya wuce tunanin sa an ya na da imani kuwa.



Yauwa a matsayin ?ar aikin gidana za ta zo wanda za ka gaya ma mahaifiyarta za ta aiki na tsawon shekara Waya ta koya wa matata girki,wanann dalilin ya sa na ingamta rayuwar ta haka."Ba ka da matsala in ma a matsayi ?ar gadi za ta zo ai wallahi sai an yi auren,na san yadda zan yi da su duka hatta mahaifiyar ta tunna ka ba ni kuWi ba ka da matsala.


Yace ya na tare da zaro makullin motar ya kalla sai kuma ya maza ya mayar lokacin da A.m ya mi?e a tunanin sa ?wacewa zai yi don ya ga ba shi da kirkin Waya.


" Oh Juwairiya ban sani ba a she ke jarina ne mahaifin ki ya mutu ya bar min dukiya nima na yi kuWi!Ai wallahi ?an mata biyu zan gallo a rana Waya wayyo Allah!Ashe dama zan yi kuWi Wallahi mutane za su ga rashin mutunci ehe."


" Yauwa ina motata kuma a ina gidan yake sannan kamar yadda ba ka son matar ka ta sani haka iyayenka kenan ni ne waliyin ku duka ba matsala in ma ka na son a Waura yanzu ba matsala."

Tsabar takaici ya sa A k ya?i ce wa komai don ya fahimci jahili ne ku kuma son kuWin ne ya rufe mishi ido yake faWin ya zama waliyin su duka,sai shi ma ya mi?e ba tare da ya ce mishi komai ba A.m ne ya mi?a mishi takadda ya ce ga shi duk abin da kake son ka sani ya na ciki.


Zai fita A.k ya kalle shi ya ce " Ai ya kama ta a kira Juwairiya mu gaya mata ko in ce ka yi mata bayani ka san wa?a a bakin me ita tafi daWi."

A.k ya ce mishi cikin gatsali shi har ya fara jin kunyar ta tun kafin ta fito haka kawai daga haWuwa sau Waya sai su zo mata da wanann tatsuniyar.

" Baku da matsalar ga ya mata ita Win banza ai gaba ta kai ta."Ya Wan matso ya na cewa." Dama wannan Wan iskar tsohon ba ya bani wasu kuWin kirki yau zan mayar mishi da kayan tsiyar shi,ana harkar kuWi me za' ayi da tsiya ai ni mutuwar mahaifin ki gaba ta kai ni gobarar Titi a Jos."


" Ga ra dai ka kira ta shi ya sanar mata."A.k ya ce shi dai A.m bai ce komai ba sai dai ya ji wani iri lokacin da Baba Sani ya fita daga Wakin ya na faWin bari na dubo ta shegen yawo ne da ita ai kai da zama za ka yi da ita sai ince baka dace mata ba."

Juwairiya ta na du?une a murhun gawayi ta hira wutan yafi sau ba adadi amma da ta hura sai ya mutu muWis,kusan kuka take son ta yi don har ta fara hawaye ganin wutar ta ta?i kamawa ta mi?e tsaye tare da zura mata ido,ji take kamar ta Wora hannu aka ta yi ta ihu.

Ta takaici ta kalli ledar taliyar da take son ta dafa ma Mama ba ta jima da dawowa daga asibiti ba take son ta Wora musu abinci da ruwan zafi ta kai musu.


Kawai sai ta ki muryar Baba Sani ya na magana tare da ?o?arin shigowa duk da ba ta ji me yake faWi ba,amma ta tsorata matu?a gani take kamar zai ce ta dafa taliyar ya Waura aurenta.


" Juwairiya ina kike ashe dama ke jarina ne?Oh ikon Allah dare Waya Allah kan yi bature."Oya maza biyo ni kika abin mamaki aike kin samo mana can jin rayuwa Juwairiya yarinya Wiyar albarka."


Cikin rashin hayyaci ta tsaya ta na kallon shi sam taka sa fahimtar wai yau Baba Sani yake ce mata ?ar albarka,sai ta fara shakkun ko ya zare ne jikinta ya fara rawa ta matsa nesa da shi,ta na karanto duk addu'ar da ta fito bakinta.


" Ke ban san hauka maza wuce kina da ba?i a falona kuma wallahi in kai min hauka,zan iya ajalin ki kin san bani da wasa akan kuWi gara ma ki kiyaye!Maza wuce."


Da sauri ta ruga zuwa shashinsa jikinta na kyarma haka kawai jikinta ya ba ta Alhaji Taminu ne ya zo,sai ta rintse idanunta ba ta son ganin shi a haka ta faWa Wakin tare da sallama wanda na yi tsammanin a zuciya ta yi,don ko ita kanta ba na tunanin ta ji.


Tsayawa ta yi a Wakin ta kasa buWe idanunta sam ba ta son ganin fuskar sa mai kama da biri.

Wani ?amshi wanda ta sha?e shi a rayuwarta wanda ba za ta taSa manta mamallakin ?amshin, ba har iya tsawon rayuwarta,tun daga ranar da ta sha?e shi take jin ?amshin a jikinta har zuwa yau da ta ha?i?ance ma kanta lai-lai wannan mamallakin ?amshin,mai sanyaya zuciya da kawo nishaWi ga duk wanda ya sha?esa ya na kusa da ita,musamman da ta ji sautin da zuciyarta take ta na bugawa da ?arfi kamar za ta fito fat!Fat!!Har sai da ta dafe gurin.


A hankali ta sauke idanunta da suka kaWa sukai jajur saboda wahalar hura wuta da tasha,duk da taji an kira sunan ta wanda ta gane ba muryar sa ba ne saboda ko tari ya yi za ta gane muryarsa,amma sai ta tsinci kanta da Wora idanunta a kansa yayin da idanunnata sukai rau-rau sun canza kala suna ba da wani tarwatsi a cikin su.

A.m da ya ji shigowar ta duk da ba ta yi sallama ba amma ya ji an buWe kofa an shigo,sanann kiran sunan ta da A.k ya yi sai ya kasa Waga idanunsa ya kalleta,duk da ya na son ya kalli wacce yake so ta zamo Wa ga abu Waya tal mafi soyuwa a gareshi don ko sun rabu aba' a sake ma tuwo suna.



"Ya ilahi! Allah na ro?e ka ka farkar da ni daga mafarkinsa da nake,kuma wanann ya zama na ?arshe tunna na kusa zama matar wani."Ta faWa aranta ta na ?o?arin mai da hawayen da suke son bayyana Soyayyaen lamarin da ke cikin zuciyarta.


" Juwairiya ki zauna mana."

A.k ya ce ganin hankalinta ya tafi wani gurin ga mamakinsa sai ya ga ta nemi ?asa ta zauna tare da saukar da kanta ?asa.

Gaishe su take son yi amma ji take kamar babu harshenta a cikin bakinta ta ?ara buWe bakinta amma ta kasa.

Ganin sun yi shiru duka sai ta ?ara ?asa da kanta ta na kallon kafen Win dake Wakin tamkar ta na son ta gano ko an maguWi gurin yin sa.

A.k ya mi?e ya kalli A.m da yake ta danna wayarsa amma a zahirin gaskiya bai san me yake dannawa ba, tunanin sa ta ina zai fara kuma ta fahimce shi,shirun da ya yi ya na son ko A.k zai yi mata bayani amma sai ya ga ya mi?e.


" Bari in jira ka a mota in kun gama tautaunawar ina mota."


Ya fice ya na girmama lamarin da suka zo da shi. " Juwairaah! Babu gaisuwa wata?ila kin manta ni ko."Ya faWa don rashin sanin ta in da zai fara.

Ta Wago idanunta ta zuba mishi amma ba ta ce mishi komai ba,sai dai a ranta ta ce." Ta ya ya za'ai na manta da kai bayan ka tafi da zuciya da ruhu gangar jikina kawai ka barmin,amma to mai ya kawo shi gidammu wanda har Baba Sani ya yadda na zo gurin sa.Aurena yake son yi?".

Ta tambayi kanta sai ta yi saurin kawar da wannan bahagon tunanin ta ce " Kai ina wutsiyar ra?umi ta yi nesa da ?asa."


"Wai ni kurma kika zama bayan rabuwarmu?Ko kina mamakin ganina ne"

Ya Wan tambaye da hasala a ranshi ganin yadda take basar da shi kuma ya tsani hakan.

" A'a ai ba'a mamaki da ikon Allah."

Iya abin da ta ce kenan ta ?ara naWe bakinta ta yi shiru tanani fal a zuciyarta.


Ganin ta tafi wani tunanin daban sai ya ce " Haka ne ba'a mamaki da ikon Allah don haka kar ki yi mamakin na zo nai man aurenki amma fa na kwangila auren shekara Waya nake son mu yi dake kuma cikin sirri."


Juwairiya ta Wago kanta da sauri ta kalle shi a wannan karan ba tare da ta ji nauyin sa ba." Aurena zai yi amma na kwangila mai hakan yake nufi?Sannan kuma cikin sirri to suwa ye ba' a son su san auren?"


Tambayar da ta yi ma kanta kenan a cikin zuciyarta wanda ba ta san maganar ciki ta fito fili ba.Ya gyara gilashin idanun sa ya mi?e tare da juwa mata baya.

" Yes abin da kika ji hakan nake nufi kin san ke ba sa'ar aurena ba ne,na tabbata kina tunanin me ya sa zan aure ki?Kamana Wan gayu kuma Wan masu da shi yayin da ke kina talaka kucaka dake.Ki kalle ni mai aji kama na ban yi kama da wanda zai aure ki ba."

Ya numfasa ya juyo ya na kallonta ganin yadda ta saki baki hanci ido ma'ana

14 / 48