Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   36 / 48

105K to 108K   out of 143.8K words

matan na ka ya sa ka fara shaye-shaye ne? Haba bacci har sha biyu da ?an mintina sai ka ce wanda ya yi sabon aure.

Shafa kansa ya yi ya ce." Kai fa banza ne bari na watsa ruwa mu tafi."

Yana ?o?arin hawa Juwairiya ta fito da nufin ta shiga kicin ta Wora girki kanta a sunkuye ta gaishe da A.k da ya yi tsaye yana kallon Am da yake shafa kansa.

" Kai amma ka ci uwar Wan rainin wayo ka bar ni ina can ina ta neman ta,Baba Sani ya tasa ni a gaba ashe kana nan ka na cin amarci har da makara."
Tsaki ya yi ya harare shi daidai lokacin da ta shige kicin ya sausauta murya ya ce."Nima ganinta na yi ta dawo."

Ya na taSe baki ya yi maganar ya Wauki remote ya kunna tv bari na yi sauri na watsa ruwa ka rage zama.
" Allah ya yi munafuki anan ka yi sauri ka fito kai ka sani da gulmarka."
Dariya ya yi ya bugi bayansa." Da babu ai gara ba daWi."Ya ce tare da haye wa sama.

Kusan sati biyu tun da Zainab ta tafi Lantana ba ta zoba,sakamakon yarta da take aure ta haihu an yi mata aiki ta tafi jinya.Hakan ya ba su damar sakewa suna jutawar su.
Kullum ranar duniya sai A.m ya kira Zainab amma ba za ta Waga ba, kuma yana ta biko gurin iyayenta,sai wula?anci suke masa daga ?arshe mahaifinta da kan sa ya kira Daddy A.m a kan ya daina zuwa gidan shi Zainab sai ta huta za ta dawo.Da zarar ta dawo za ta dawo Wakinta don haka ya daina damunsa.

A.m ya yi fushi sosai sai ya yi zuciya ya ?yaleta musamman da ga matar wucin gadi,ta dage tana faranta masa ko ba komai zai yi maleji kafin ta dawo.

Juwairiya ta yi amfani da wannan damar ta saka rayuwarta a cikin ta A.m duk da irin gwasaleta da yake yi, yana yabon Zainab amma da ya fita zai kira ta yana gaya mata ya yi missing hawayenta na banza don Allah ta yi mishi kukan zai siya.

In ya faWi haka dariya take mishi ta ce ashe kukan banza ya ?ara matsayi tun da har siye ake son ayi.Haka dai suke zaman su cikin girmama juna da kulawa.

Washegari Z???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ainab ta kira lantana aka ta je ta gyara mata gidan ta,saboda tun da ta tafi kewar sa ya dame ta ko bacci kasa yi take yi,duk kiran da yake mata rungume wayar take yi tana kuka,amma shegen girman kai ya hana ta Waukar wayar in ta tuna kuma da abin da ya yi mata sai ta ji duniyar ya yi mata zafi.Ita tunanin ta A.m zai biyo ta ?asar ne.


Sai dai tana tunanin yadda za ta iya danne zuciyarta,ta zauna da Juwairiya bayan ta gane amanarta suke ci,duk da A.m ya yi mata rantsuwar yana shan magani ne saboda ita, amma kuma bai ?aryata numbarsa a wayar Juwairiya ba,sai dai ya nuna sam bai san zancen ba wata?ila son sa take don kwanaki ana kiran sa da ba?uwar numba,bai dai taSa Wagawa ba ne shi yasa bai fahimci komai ba.

Zainab ta gane sam ba za ta iya rayuwa babu shi ba,amma dole ta canza zaman su domin sai ya gane kuran sa,ita kuwa Juwairiya Momi ta ce ta bar lamarinta a hannunta don sai ta yaba wa aya za?inta.

Lantana ta shigo gidan da mamakin ?ofar a buWe duk da ta ga motar A.m a gidan,amma ta san ba' abarin ?ofar falon a buWe.

Tura ?ofar ta yi ta shigo tana ?arema gidan kallo yadda yake tashi da ?amshi da gyara komai tsaf,jikinta ya bata a kwai mace a gidan.

Tsaye ta yi tana Wan tunani sai kawai taga Juwairiya ta rugo da gudu daga sama tana dariya,jikinta daga ita sai yar bes fara da wando fari tirikwata wa da A.m ya siyo mata da suka fita,saboda shi yana koyi da hadisin ma'aiki wanda yake mana koyi da saka fararen kaya.

Da gudu take saukowa tana dariya shi kuma ya biyo ta cakulkuli yake mata wai kan dole sai ta yi mishi kuka yaga hawayen banza.

Kamar yadda Lantana ta yi tsuman tsaye tana kallon su haka suma suka zuba mata ido cikin firgici.


TO FA NIMA IDANU NA ZUBA MUSU TARE DA BASU LOKACI DOMIN NA GA REACTION ?IN SU



KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.






*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 29*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Juwairiya kunya ta kama ta matu?ar gaske ji ta yi kamar ta nutse a ?asa,juwaya ta yi za ta koma ciki,amma sai A.m ya janyo ta tare da haWa ta da ?irjin shi.

" Ke! Wace irin mahaukaciya ce da za ki shigo gidan ma'aurata kai tsaye sai ka ce Wakin gidan ku."

"Lantana jikinta ya kama rawa kamar mazari saboda tsawar da ya daka mata,ta yi mugun firgita ba ta gane abin da ya ce ba.

" Ka yi ha?uri yallaSai wallahi ban san ka na ciki ba,kuma Hajiya Zainab ta ce na zo na gyara gidan za ta dawo."

Ta faWa jikinta na rawa kanta na asa ta na mamakin abin da ta gani don ta firgita.

A.m ya yi farin ciki sosai jin abin da ta ce sai ya Wan ture ta daga jikinsa,ya kalli Lantana da har yanzu idanunta a ?asa suke,ba ta son ta ?ara ganin abin da ta gani,domin ?ila ?arya suke mata.

" Ok sai ki je ki yi aikin ki munafuka na sha mamaki da Zainab ta tunume ni akan ina tare da Juwairiya,a she ke ce munafukar da take son raba aure.
Wallahi kin ji na rantse miki in har kika yi gigin faWa mata abin da idanun ki suka gani,kaf ?an gidan ku ni ne ajalin su don bom zan siya na tashi gidan."

Ware idanunta ta yi tsananin tsoron sa ya kamata saboda idanun sa sun tabbatar mata da zai yi fiye da haka.

" Ba ke kin iya munafunci ba to bari na ?ara miki da abin da zai kashe ki,don ba za ki iya faWa mata ba duk munafuncin ki saboda in ban kashe ki ba,to ita za ta yi ajalin ki kin ga gulma ta yi riba kenan."


Ya ce da ita ya na zare mata ido domin haushi take ba shi,tun da ya ji ita ta faWa mata komai,ga shi yanzu ta korar masa da matar so.

"Juwairiya matata ce wanda na aura a bisa wasu dalilai da ba zan gaya miki ba,saboda bai shafe ki ba."

Ya ?ara matse ta sosai a jikin sa kiss ya sakin mata a kumatunta,ya na mata wani irin kallo da ya saka ta kauda idanunta saboda kunyar Lantana.

" Kin ga in ta dawo sai ki gaya ba mata yau ?in ?ara gani ba kuma iyakan runguma ba,ki sanar mata duk abin da kika gani kar ki rage."

Lantana da sauri ta shige kicin tare da rufe ?ofar.

" Innalillahi na shiga uku!"

Ta sauke ajiyar zuciya mai ?arfi yayin da kanta ya kulle ta rasa in da za ta fara tunani.

" Wallahi wannan mutumin ya rikita ni na rasa mai zan fara tunanin,a halin yanzu zuciyata ba za ta iya fahimtar komai ba,domin ya saka ni a cikin ruWu."Ta ce yayin da ta Wora hannu akanta.

" Da gaske ya ke faWin matar sa ce ita?A 'a lamarin nan a kwai rikitarwa! Ji fa yadda ta koma tamkar wata gilas,saboda tsabar kyau kai Zainab shashashar mace ce,wai ta je hutu ai kuwa ki dawo za ki ga sakamakon hutu."

" Wa ni ai komai na ga kuna yi ba zan iya gigin gaya mata ba,haka kawai ku da holewa ni da shan bugu.Kai amma fa A.m ?arshe ne gurin rashin mutunci don ko kaWan Zainab ba ta yi tunanin ta na gidan ba."

Irin maganar da take yi a zuciyarta kenan ta buWe ?ofar a hankali ta na le?en su,sai ta ga sun ?ara rugawa da gudu sun yi ciki.

" Allah ya kai mu ki dawo gidan nan za mu
sha kallo!Allah ya sa kar ki yi shigowar dare in ba ma idanuna abinci,sai ki gane sakaci kika yi ko halin maza A.m yake nuna miki."Ta faWa sannan ta kama aikinta zuciyarta cinkushe da tunani kala-kala.

Bini-bini za ta le?a ta na kallon sama amma sai ta ji shuru kamar bacci suka yi.

" Ha ina tausayin ki yarinya ba ri Zainab ta dawo."Ta ce ta na aiki cikin mamakin lamari da al'ajabi.

" Humh namiji bunun ?aya."

Abin da take ta nanatawa kenan a cikin zuciyarta.


A.m ya rungume hannun shi ya na kallonta da ta kwanta akan cinyar shi,ta Wora filo a ?irjinta idanunta lumshe kamar ta na bacci,sai dai a zahirin gaskiya ba bacci take yi ba.

Zuciyarta cinkushe da kishi da tunani jin Zainab za ta dawo,domin a yadda take jin son sa da kishin ta ba za ta iya Soye kanta ba,kamar yadda ta yi a farko ta na jin ko sama da ?asa za su haWe za ta nuna kanta a wannan karon.

Kamar yadda take tunani shi ma haka zuciyar sa take cinkushe da tunani,ga shi ya gagara samo mafita.

Duk da cewa zuciya da gangar jiki sun yi kewar Zainab,amma in ya tuna za ta dawo gaban sa yake wani irin yankewa ya faWi.

Ya sani a yanzu babu wanda zai kalle ta yabce ita yar aiki ce,duba ga yadda ta koma tamkar wata tarwaWa.

Ya na ta tunanin ko ya Wauke ta daga gidan sai dai ya na jin ba zai iya jure rashin abincinta ba,saboda har yanzu ya kasa iya cin abincin Lantana.

Wayarsa ya zaro ya gwada wayar Zainab da ya daina kira,saboda ?in Wauka da take yi.

Sai dai ringing Waya ya ji ta amsa tare da sakin kuka.
" Ka daina sona A.m ban taSa tunanin a kwai ranar da zan yi fushi da kai ka ?yale ni ba."

Ta amsa daga Sangarenta ta na wani irin kuka da yake tafarfasa masa zuciya.

Tsam Juwairiya tami?e daga jikin sa ta fice daga Wakin ba tare da ta kalle shi ba,yayin da zuciyarta ke mata luguden bugu na kishin sa.

Binta da kallo ya yi ganin ta canza kalar fuskarta kamar ba wacce ya sani ba.

Sai da ta fice daga Wakin ya saukar da nauyayyar ajiyar zuciya.

" Ya kike son na yi kin mai da ni kamar wani ?wallo don kawai kin ga Allah ya jarabce ni da son ki?Kawai na ba ki dama kije duk abin da kika yi ninya ki yi,ni dai har yanzu ba zan fasa gaya miki ina sonki ba."

Ya ce da ita ya na jin tsananin haushinta da kuma fargabar abin da zai faru,domin ya na ji a jikin sa kamar lokaci ya yi da zai gaya mata zaman Juwairiya a gidan su,don su daina samun saSani,duk da ya san zai sha wahala kafin ta amince.

" In har ka na sona da gaske A.m ka daina kawo rigima a cikin aurenmu,sannan ka tuna da al?awarin da ka yi min don Allah karka canza."

Shiru ya yi bai ce komai ba ya rufe bakin sa da hannun sa ya na jin saukar kukan da take yi.

" Ka yi shiru ba ka ce min komai."Ta faWa cikin muryar kuka.

" Mai kike son na ce miki Zainab wane irin halacci ne ban yi miki ba! Ki dawo a kwai wata magana mahimmanciya wace za mu tautauna,kuma in kika fahimce ni in sha Allahu ba za mu ?ara samun tarna?i a aurenmu b."

" A.m a kwai matsala ne don Allah ka faWa min?"

Ta tambaye shi da za?uwa jin muryar sa ta canza." Babu kuma kar maganar da na ce miki za mu yi ya Waga hankalinki domin alkhairi ce."
" Ok to shikenan baby ba matsala,amma fa ka canza gabaki Waya,domin da ace babu wata matsala cewa za ka yi in jira ka mu taho tare."Ta ce da shi da wata kalar murya.

" Wata?ila da izinana kika tafi?"

Ya ce da ita a ?ufule kawai sai ta ji ya datse wayar, a lokacin da take faWin.

" Tun da ba za ka zo ba sai ?arshen za mu dawo,saboda zamu tsaya mu yi siyayya."

Mi?ewa akan gadon ya yi tare da shafa gemun sa da ya ?awata masa fuska.

Wani irin damuwa ya ji ya lulluSe shi sosai.

" Gaskiya na canza shawara ina ganin kawai zan Soye Juwairiya duk san da ta samu ciki,sai na saka Zainab ta yi cikin ?arya a zuwan ita take da ciki in ta haihu Wan ya zama Zainab a zuwan ita ce ta haihu."

Take ya amince da shawarar sai ya mi?e da sauri ya saka takalmin sa ya fice zuwa Wakinta.

Ta na tsaye a gaban mirrow ta juya bayanta tare da Wan jingina kanta da gefen mirrow,a ranta ita kaWai ta san mai take tunani,domin iya tsananin damuwar dake kan fuskarta na hango.Ba tare da ta san ya shigo ba ya fara magana.
Kallon sa take yi da wani irin canji a fuskarta har ya gama mata bayani,ba ta tanka ba illa kallon sa da take kamar ba?o a gare ta.

Ganin ba ta da ninyar magana sai ya saki tsaki ya juya ya na faWin." Ina fatan kin ji mai na ce."

Ko kaWan A.m bai canza mata ba wai don Zainab za ta dawo,haushin da take ba shi duk ya yi mata maganar abin da ya tsara sai ta yi shiru ta zamar masa kamar wata kurma.

Zaune suke a falo sun dawo daga siyayya A.m ya ce ta raka shi a kwai turaren da yake son ya siya.

Sun zaune a falon ?asa sun baje kayan ciye-ciye suna ci

Turaren da ya siyo ya na son ya yi haWa da wanda yake shafawa,saboda turaren ya tafi da imanin sa gashi ba zai iya canza wanda yake fesawa ba.

A hannunta ya kama ya fesa mata a hannun ya ce." Matar shige ki ji ?amshin sa ya yi daWi ko?"

Juwairiya har ga Allah ?amshin bai yi mata ba,kallon sa ta yi ta Sata fuska tare da toshe hanci." Humh ni ban ji wani ?amshin daWi ba don ni warin almiski ya yi mini,kuma ni ba na son almiski."

" Allah ko ka ji gulma wannan turaren ko shugwaban ?asa ya sha?i ?amshin sa ba zai kushe ba,balle ke ni na san gulma ce irin ta ki don ko wanda na ke shafawa ba ki taSa cewa ya na daWi ba."

Dariya ta yi lokacin da ta toshe baki ganin haka sai ya ji haushi sosai ya biyota ya na faWin." Allah sai na fesa shi a jikin ki duka."
Zagaye falon suke yi har ya kamata zai fara fesa mata turaren,yayin da take ro?onsa don har ga Allah bai yi mara ba.

Wayar sa da take aljihun wandon sa ta fara ?ara da sauri ya ciro,jin kiWan da ya saka ma Zainab ce.

" Hello gani a airport ka zo ka Wauke ni."

Ya kalli Juwairiya da ta ji abin da Zainab Win ta ce saboda ta na jikin sa ya Waga wayar.

Da ido ya yi mata magana sannan ya Wauki key Win motar sa ya fice.

Ta na ganin sa ta faWa jikin sa tare da sakin kuka sosai." I miss you honey."
Da so ya yi ya ture ta ganin irin shigar da ta yi duk da cewar a da in ta yi shiga wani lokacin ya na ?orafi,amma yau ganin ta da gyale ta yi roling Win sa,sai ran sa ya Sace sosai,domin shi da za ta fara shigar Juwairiya ya na so,saboda ya gane hijabi wani sirri ne da Allah ya bawa mata duba ga jikin Juwairiya da yake mamakin ?irar sa.

Ga mamakin ta sai ta ga ya yi shiru, bai cika magana ba sai kallon hanya da yake yi,hakan bai saka ta damu ba saboda ta yi tunanin ko har yanzu fushi yake yi da ita,duk da cewa ita ya kamata ta ?i masa magana,amma sanin hali sai ta kama bakinta ta yi shiru.

Wayarta ta Wauko ta yi kiran Momy ta gaya mata jirgin su ya sauka lafiya.

Ko da suka isa gida wanka ta shige saboda ta gaji matu?ar gaske,kanta har wani sarawa yake yi saboda ciwo,in da Allah ya taimake ta ta ci abinci a jirgi,so babu abin da za ta nema illa ta yi sallah ta bi lafiyar gado.

Ya shigo da dubuwar farar rigar bacci wanda ya Waure igiyar ta bayansa,ganin ta kashe fitilar Wakin ya kunna fitila mara haske.

"Zainab ki tashi magana za mu yi kuma mai mahimmanci."

Ya ce da ita don yau yake son ya gaya mata komai,gudun kar ta ganta a gidan lamari ya jagule,saboda

36 / 48