Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   39 / 48

114K to 117K   out of 143.8K words

gane wace ce mahaifiyarki sam ba zan bari hakan ta faru ba,ko da ace zan yi yawo tsirara ne! Kin san wace ce mahaifiyarki ya kamata ki zama jaruma.Irin zuciyata ya kamata ki Wauka,ba in aka yi miki abu ki ce za ki rama ta kisa.Sab ba haka jarumi yake cin nasarar sa ba,dagewa za ki yi ki saka makamanki ki ya?i duk wanda ya zama garna?a?i a cikin rayuwarki."

Ta faWa yayin da ta yi shiru tana kallonta don ba ta fahimci mai take cewa ba." Bari na baki labarina wanda baki taSa sani ba Zainab.Mahaifin ki yaso wata mace kamar ransa yana jin zai iya mutuwa in bai same ta ba,ita kuma ?awatace da muka haWu a makaranta.
Mun sha?u sosai muna shiri da ita,duk ?an'uwanta na san su,don har zuwa nake na kwana a gidan su.Mahaifinta hamsha?in mai kuWi ne sosai suna da kuWi,yayin da ni ina karatu a gidan kawuna shi ya Wauko ni ya sani a makaranta iyayena talaka.

Tun da na fara mahaifinki na Wauki son duniya na Wora mishi sosai,sannan ina son na canza rayuwata daga ?angin talauci.

Matar kawuna ta yi mini hanyar wani malami ya ta kaini gurin sa,don ya janye hankalin sa daga gareta,amma sai dai in na yadda da sauran ?wayayen haihuwana za'a yi asirin,in da za'a bar Waya kawai wato Wa Waya zan haifa a duniya.Ba tare da damuwa ba na amince.A lokacin har an saka ranar auren su biki ya rage kwanaki aka fasa auren,in da ya zo gidammu da fari iyayena sun ?i,amma ganin zai haukace dole aka Waura aurenmu wanda dalilin haka ta aikata suicide. ta mutu.
Sai dai na fara nadama bayan aurenmu duk lokacin da hankalin sa ya dawo jikin sa,sai ya kasance ina yawan zuwa a juyar masa da hankali,a haka muka rayu har na haife ki bayan na haife ki sai Allah ya saka mi shi tsananin sonki,domin yana son yara sosai ya sha gaya min zan haifa masa yara da yawa."

Momi ta yi nisa tana kallon Zainab da ta yi zuru ta zuba mata ido tana kallonta cikin al'ajabin labarin da take gaya mata.

" Na yi matu?ar dana sani sosai da na yadda aka yi amfani da sauran ?waina,saboda dangin sa sun takura mi shi akan ya ?ara aure,sai dai na yi ruwa na yi tsaki har yau ya kasa ?ara auren.Don haka ki share hawayen ki A.m bai isa ya zauna da wata mace ba bayan ke,ke kaWai ce za ki zauna da shi har abada,na yi miki wannan al?awarin in...."

" No Momi don Allah kar ki saka wani abu daban a cikin aurena! Ina son A.m ina burin na rayu da shi har abada,kuma kin san ni ba na son waWannan halayen da kike yi,don haka in ba za ki taimaka min ba,kawai ni zan watsa mata acid ko na Wauketa a garin."Ta ce da Momi cikin shagwaSa tana kallonta yayin da hawaye suke ?ara turereniya a fuskarata.

" Banza shashasha! Ita kin san abin da ta yi har A.m ya kula ta? Ki zauna garin kallon ruwa kwaWo ya yi miki ?afa,kuma Allah kin ji na rantse miki ko ke baki yadda da hakan ba,dole mu zamu Wauki mataki."

"Haka ne Momi ki yi ha?uri amma gaskiya ba zan amince da abin da kike so ba,zan kira Anty Lubna na san za ta ba ni shawara."

Gabaki Waya kayan sawarta suka kwashe ita da Momi,bayan ta kira mahaifinta ta sanar masa take ya buga ma Daddy A.m waya saka yi kaca-kaca.

Jikin Daddy ya yi sanyi to fa asiri ya tonu ya san cewa a kwai daru saboda shi ya saka hannu aka Waura auren.
Jikin shi ya kama rawa saboda irin zagin da mahaifin Zainab ya din ga yi mi shi,ya san dole ya kira ainihin mahaifin shi ya gaya mi shi.

Wani irin zufa take tsefo masa don ya san Allah kawai zai fidda shi,sai yanzu yake ganin mugun wauta da ya yi har suka yi galaba ya amince da aure.

Wayar sa ya zaro ya don ya kira A.m cikin fushi.A ran sa yana ba?in cikin halin dukan mata da A.m ya Waukar wa kan sa.
**********
" Wai mene ne haka ne A m ka san mai kake yi kuwa a asibiti muke,kuma ka duba idanun mutane a kan ka suke sam ba ka da kunya."

A.k da ya yi wa Juwairiya rumfa da take kwance kan gado,ya kuma tura hannun sa a cikinta wai zai ji in da yaron yake.

Juwairiya da wani irin kasala ya rufe ta zuciyarta tashi take yi,kamar wani aman yake son ya zubo mata.


Da sauri ta ture hannun sa ji ta yi kamar an Wora mata wuta a in da ya Wora mata hannu a cikin.

Ita ji ta yi da ya matso ta kamar wani irin wari za ta ce ko ?amshi mara daWi yake mata.

Hannunta ta saka ta toshe hancinta da jin wani amai zai taso." Don Allah ka matsa kusa da ni sam ba na son jin ?amshin ka kusa da ni."Ta faWa da muryar kuka tana jin wani ?unci a tare da ita.

A.m ya yi turus kamar zai saka kuka ya juya ya kalli A.k da ya zuba masa ido sosai cikin son dariya.

" To fa baban baby ka ce kai ma ka shiga daga ciki kenan."
Ya faWa a ransa yana tunanin kamar Juwairiya tana daga cikin jinsin matan da Allah ya halitta,a lokacin da suka samu ciki sai Allah ya jarabce su da tsanar miji tsana mai tsanani,yayin da suke ?aurace ma mazajen su wasu har suna cutar da kan su.

Don matar sa tana daga cikin irin masu wannan halittar,duk sanda ta samu ciki shikenan zaman lafiya ya yi ?aura a gidan su har ta haihu.

" Humh ka na ji fa wannan yar rainin wayon take faWin na matsa,ai ita ta san in da ba babyna da yake jikinta ba babu abin da zai saka na matso kusa da ita,bayan ta san babu macen da nake so irin matar so."Ya faWa yana hararar ta sosai ganin ta hana shi jin motsin baby.

Ga mamakin sa sai ya ga ta mayar masa da hararan da ya yi mata,don ita har ga Allah ta ji wani irin tsanar shi a cikin ranta,ba wai don abin da ya faru ba,sai dai wani canji da ta ji a jikinta,saboda in ya matso wani irin wari take ji har da ?arni-?arni a jikin sa,wanda yake tado mata da hararwa.

A.k da ya yi tsuru yana kallon abin al'ajabi ganin yadda suka Wauki fushi,bai taSa tsammanin Juwairiya tana da tsiwa ba.

" Ikon Allah yau kuma irin murnar da za ku nuna kenan,bayan yau Allah ya kusan cika muku burin ku.Kai zaka samu magaji,ita kuma za ta koma gurin Mama kamata ya yi ku nuna ma Allah godiyar ku."

A tare suka harari junan su sai ta ji wani irin kewar Mama da son ganin ta ya kamata.

Hawaye ta soma zubarwa wanda ya Waga hankalin A.m,cikin Waga murya ya daka mata tsawa.

" Ki yi ma mutane shiru so kike Wana ya gado shegen kukan ki na rashin dalili."

A.k da yake kallon dirama dafa kafaWan sa ya yi ganin yadda ya daka mata tsawa.
" Haba A.m be a man. Baka ka san ba'a Waga ma mata masu ciki murya,irin shi ne suke haihuwar Wa motsi kaWan sai ya birkice."

Da sauri ya kalli A.k cikin razana ya kama hannun sa ya ri?e sosai." Da gaske kake?Ina ga zan duba duba google akan yadda zan kula da cikin saboda kar a samu matsala, ina son yarona ya fi Wan kowa a duniya,kuma ba na son ya yi kama da waccan abar mai emotionally fence."Ya ce yana nuna ta da bakin sa tare da galla mata harara.

Tura bakinta ta yi ba ta ce masa komai ba,don ita yanzu haushin sa take ji na rashin dalili

A.m ya ?ara hassala don ya tsani raini, karfa don ta ga ta samu ciki tace za ta yi mi shi rashin kunya,da kuma ya tuna abin da A.m ya gaya masa sai ya du?a kusa da ita.
" Kin san fa yanzu bake kaWai ba ce,don haka duk kulawar da zan ba ki babyna nake ma wa,ki kwantar da hankalin ki yarona ya sakata ya wahala ya yi ?atoto."

Ya ?ara sausauta muryar da ba ta taSa sanin yana da shi ba." Baby mai kake son ci?Ka faWi duk abin da kake so zan kawo maka shi."
Ture hannun sa ta yi ganin ya ?ara kawo wa "Don Allah ka ?yale ni ba na son cin komai."

" Ba ke na tambata ba babyna nake magana da shi don na san dole yana bu?atar abinci."
Ya faWa a kausashe don shi jin yake anya zai iya Waukar raini daga gare ta.
" Ka dai kula da abin da na ce maka, in ka din ga daka mata tsawa ta haifi yaron matsoraci, kai ka sani ka san dai wannan shikenan babu ?ari."A.k ya ce da shi.

Sosa kan shi ya yi." Na ji kuma zan kiyaye in sha Allah.Dole na samu babban likita wanda zai dinga Worani a kan yadda ake rainon ciki."

Juwairiya ta mi?e ta tana wani yatsina irin na masu ciki gabaki Waya ta ji wani canji a jikinta.Dambu da kalallaSa ta ji kawai tana son ta ci,amma ta san ko ta faWa masa ?ila ba zai nemo mata ba.

Amma kuma da ta ji son cin abincin zai saka mata amai,in dai ba ta ci ba kallon sa ta yi ta ce." Ni fa dambu zan ci da kalallaSa kuma yanzu nake so."
A.m ya zare ido ya ce." To yar rainin wayo gara dambu na san shi matar A.k tana yi,amma kuma mene ne kalallaSa?Ni fa kar ki raina mini wayo ?ila ba baby ba ne zai ci."
" Ko ma waye zai ci dole ka nemo ai wallahi tausayinka nake ji,don yanzu ka shiga hannu dole ka zama Wan siyayya."A.k ya ce mishi yana kallon doctor da ya turo ?ofa ya shigo.

" Yauwa doctor yau she zan dawo ka ba ni shawarar yadda zan kula da babyna."
Dariya ya yi suka tafa da A.k." Abinka da sabon shiga."Hararar A.k ya yi jin abin da ya faWa.

Wayar sa da take da can gefen Juwairiya ta Wauki ruri sosai.Gaban sa ne ya faWi don ya san kiran bai wuce daga gidan su.

" Please A.k Waga wayar ba zan iya ba na san bai wuce Daddy."Ya faWa yayin da fara'ar shi ta kau.

Shi kan sa A.m a tsorace yake ya san ayau Allah kawai zai raba su da shi.
Da ya Waga wayar sai ya saka ta a hands pree.
" Kaicona Abdurrahman! Yau na yi dana sani da na Wora ya?inina akan ka.Abin da ka aikata kenan?A she baka da hankali wallahi ban taSa sanin mahaukaci ba ne kai sai yau.Maza ka taho gida ina neman ka duk in da kake, da kuma yarinyar da Zainab ta ce ka dake ta saboda ita,don ni bazan ce matar ka ba ce sai dai kuma in ka canza iyaye bayan ni da Daddy Winka.Minti biyar na baka."

Mahaifin A.m ya faWa yana huci ya kashe wayar,yana kallon Daddy da ya yi tsuru-tsuru.

A.m jikin sa ya yi sanyi ya kalle ta duk tana jin abin da ke faruwa,amma ba ta nuna komai a ranta ba.

"Mahaifina ya na son ganina dotor ka sallame mu."
Ya faWa jikin sa a sanyaye saboda ya san a yau duk wanda yake da ?ima a idanun su, ?imar shi za ta zube,ya san mahaifiyar sa ba ta da wasa mace ce da ba ta Waukar raini,hankalin sa ya ?ara tashi da ya tuna ?annin sa ko ya za su kalle shi.

" Ka san Allah babu in da za ni, sai da na gargaWe ka amma ka yi mini rashin mutunci,yau sai ka ?waci kan ka da Daddy,amma babu in da za ni na san Daddy ya yi fushi sosa."A.k ya ce da ya ga yana kallon sa.

" Juwairiya tashi mu tafi sai ki jure duk abin da za ki gani,sau?inta ma siyen ki na yi da kuWina balle ki ce na kai ki in da za'a wula?an ta ki."

Hankalinta ya tashi gabaki ta fita hayyacinta ji take kamar ta ga ta Sace.

" Na shiga yau zan ga ahalin A.m wani irin tarba za su yi mini?Yau na san zan sha wula?anci wata?ila dukana za su yi."

Ta faWa cikin tashin hankali ganin yadda shi kan shi ya ruWe,sai ta raya a ranta babu in da za ta don ba za ta je su kashe ta ba.

Kamar ya san mai ta raya a zuciyarta ya ja hannunta,da ?arfi ya nufi mota yayin da gabansa yake dukan tara-tara.

A.k kuwa daga asibitin gida ya koma ko aiki ya ?i zuwa,tunanin shi Daddy zai iya bin shi gurin aiki,bayan ya shiga gida ya sanar da maigadin gidan sa duk wanda ya zo ace ba ya nan,ya rantse ba zai ?ara zuwa aiki ba sai ranar da aka gama wannan rikici.

A lokacin da ya gaya ma matar sa ta yi shiru,ta zuba mishi ido tana jin tatsuniyar da yake mata,zuciyarta na matu?ar mamakin sa,tsawon shekara biyu suka shirya hakan,amma ko wanka mai kama da jirwaye bai taSa yi mata ba,sai abin ya ?ara ba ta matu?ar mamaki ta din ga kallon sa tana son ta yi magana amma ta kasa.

Kofin gilas Win da ke hannunta ta saki tare da zare ido da ta ji ya ce." A yanzu Juwairiya na da ciki kuma Zainab ta gane,Daddy ya yi kiran sa tsoro ya sani na ?i zuwa don babu irin abin da ban faWa masa ba,amma ya yi kunnin uwar shegu da ni sann..."

" Na shiga uku wayyo Allah na! Oh Zainab mai ya kai ki aikata wannan kuskuren lallai kin yi sake."Ta ce da tsananin mamaki sai abin ya ba ta tsoro hararar A.k ta yi ta ?ara cewa.
" Amma wallahi kun munafunce mu gaskiya ba ku yi mana adalci ba,haba Baban Najwa yanzu watarana in za ka ?ara aure haka za ku munafunce ni."

Dariya ya yi ganin ta birkice kishi ?arara a fuskarta." Baki fahimce ni ba A.m ya kashe ma?udan kuWi ya auri Juwairiya akan za ta ba shi baby in ta haihu su rabu ya bawa Zainab,wannan dalilin ya ije ta a gidan sa don tana haihuwa za su rabu,sakacin Zainab ya kusanta Juwairiya da shi,don tana da hankali ga kula da tsafta da iya girki ni kaina in na ci abincinta ina yabawa."

Ya numfasa sannan ya Wora da cewa."kuma kin san A.m da son kula shi ya sa nake kallon Zainab a matsayin wawiyar mace,saboda mijinta irin mazan nan ne masu son mace ta mai da su yaro,a yadda na kula da A.m zai iya barin mace ta yi masa komai na kulawa,wanda ita ta gaza hakan da haka Juwairiya ta samu ta saka sha?uwa a tsakanin su,duk da har yanzu yana kan bakan shi na rabuwa da ita,ni dai lamarin yana Waure min kai sosai ina tunanin yadda za ta haihu ta ba wa wata mace Wanta.Sannan ba lallai ba ne Zainab ta ri?e."

" Humh wannan lamari a kwai rikitarwa har yanzu zuciyata ta kasa yadda da kai,don kun yi matu?ar ba ni mamaki,ashe duk ?us-?us da kuke yi maganar auren ne,in na yi maka magana ka ce kuna maganar kampani,ai ga shi nan kun ibo ruwan dafa kan ku,sannan ba ka kyauta ba da ba ka je ba."

" Wa ni wallahi babu in da zani tsuntsun da ya ja ruwa."
Bugun ?ofa ya ji da sauri ya shige cikin Waki bayan ya ce " Don Allah ko wane ne ki ce ba na nan,kar na zo na fito Daddy ya zo."

Dariya ya ta saki a ranta tana mamakin wannan girman lamari da ya faru da ita.
" Ikon Allah duk cika da isar Zainab ta?ama da kuWi! Yau ita ce da kishiya kishiyar ma talaka da take wula?antawa."

Sai kuma ta nisa ta kuma cewa." Allah sarki Juwairiya kin yi wauta ina tausaya ma rayuwar ki ko ya ya iyayen A.m za su karSe ki waWannan ?an nuna isa da raina talaka."Wayarta ta Wauka ta shige Wakinta.

A.m da yake jin bai taSa jin matsananciyar kunya irin ta yau ba,da ya yi hon maigadin gidan su ya buWe masa get.

Sai ya ji kamar ya koma lokacin da ya yi parking ya fito.

" Ki biyo ni."

Kawai ya ce hankalinsa a tashe ya nufi cikin gidan yayin da take taku cikin tsoro,ganin irin daular duniyar da ya kawo ta sai ta raina kanta.

Juawairiya ta tsaya cikin tashin hankali tana kallon mahaifin A.m da ko ba'a gaya maka ba,za ka nuna sa ka ce shine saboda sun yi matu?ar kama kamar har ta Sace.

Ta kuma kallon sauran mutanen da ke falon sun taru da yawa sun zuba mata ido.

Kyawawa da su masu zubin larabawa kamar A.m da su ta yi yawa.Sai tsananin kunya ta kamata ba ta taSa jin ta muzanta irin na yau ba.

" Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un! A she da gaske ne ba ?arya ba A.m ya zama uban kan sa ya yi aure?Ko kuma karuwa ce ya ije a gidan sa?"

Mahaifin A.m ya faWa ganin Juwairiya ta Soye a bayan sa,sannan sam Zainab ba ta gaya musu ba ta haihuwa da kuma maganar ciki ba.

Gani suka yi Daddy ya yanke jiki ya faWi sharab! Gabaki Waya suka saka kuka suka yi kan shi.


TO FA MASU KARATU GA DAI JUWAIRIYA TA BAYYANA CIKIN FAMILY ?IN A.M SHIN ZA TA ?AR?U KO YA YA?



KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO

39 / 48