Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 48

126K to 129K   out of 143.8K words

ciwon kai ba."Ta faWa tare da fara janyo kayanta.

" Momi don Allah ki bar ni a nan ba na son na koma gidansa."Ta faWa sai kuma ta kama kuka saboda tana tunanin yadda zaman su zai yi a gidan,sannan wa zai rin?a tarairayarta kamar yadda su ke mata.

"Momi ba zan ?ara ba don Allah ki bar ta anan yanzu ta zama ?azamiya ba ta komai zuwa za ta yi ta Sata mini gida."Ya ce da ita saboda yana tsoron kar Zainab ta ji tana gidan,shi da yake son ta dawo in ta ji komai zai Sace.

" Oho ko mai za ku ce yau za ku tattara ku bar mini gidana."
Ta?wala ma mai aikinta kira ta ce." Kwaso mata kayan abinta su tafi,sai kun bar gidan nan zan fita."

Da ya fahimci da gaske take yi sai ya Wauki jakar da Momi ta tilasta mi shi ya Wauka,yana hararar ta da take ta matsar ?walla.

A mota sun yi shiru babu wanda yake tari a cikin su,A.m ya so ya yi mata magana amma da ya ga ta shigo,sai ta zauna a gidan baya ta Wauki Wankwalinta Waure hancinta da shi,wato alamun har yanzu warin yake mata.

Kamar kurame babu wanda ya yi magana sai shi da yake ta jan tsa?i.

Ko da suka shiga falon zaune ta yi a falo ba tare da ta kalle shi ba,ta janyo wayarta ta kunna data ta haye whatsapp da Hamdiya ta buWe mata,don ita da chert kwata-kwata bai dame ta ba.

" A Wakin masu aiki za ki ci gaba da zama kamar da,don har yanzu matsayin ki na nan bai canza ba."Ya ce mata yana mata wani mugun kallo.

Ba tare da ta kalle shi ba ta ?ara sautin ?arar wayarta da tsa?wanni ke ta shigowa rututu,sai da ta nisa ta ce." Ni ma ba na bu?atar ya canza kuma ba zan zauna da mutum yana mini warin jaSa ba,gara na ?arashe sauran watannin da zan yi ba tare da na kusanta kaina da kai ba,don haka kar ka damu na zaSi in da na saba zama."

" Hakan ya yi ai sai ki ci gaba da zama kayan Wakin kawai zan canza don Wana ba zai kwanta in da talawa suke rayuwa ba."Ya ce tare da Waukar wayarsa ya fara hawa sama.

" Aiko sai ya kwana don ba shi da mara ba da talakawan a jikin ?ar talaka ya fito ka ga shima dangin matsiyata ne."

Da sauri ya sauko ?asa kamar zai isa gareta amma sai ya fasa ya yi mata wani mugun kallo.
" ?arya kike yi ko da ya a fito a jikinki sai da na saka kuWina na siye ki da ma?udan kuWi,kuma kar ki manta wacce zan ba ma wa gaba da bayanta arziki suka gada ba tsaya ba."

" To dangin ?aruna ai dai ba a canza ma tuwo suna."Ta ce tare da Waukar goruba ta fara ci don ta san ya tsani ya ganta tana ci.

Tsaki ya yi ya haye sama ba tare da ya ?ara ko kallonta ba.

Juwairiya na zaune a cikin falon ta ga ana shigowa da kayan Waki masu kyau,har aka gama jerawa suka tafi sannan na shiga ya yi kyau sosai.

Kwanciya ta yi ba ta tashi ba sai gabda magariba,wani irin ?ulululu ta ji cikinta ya yi na yunwa,sai ta far hawaye da ta tuna irin gatan da suke mata.

Kicin ta shiga ta don ta yi faten da ya zama kamar al'ada ku san shi ne abinta a kullum.

Sai dai ko da ta shiga kicin Win warin gas ya hana ta yin komai,duk da toshe hancinta da ta yi ta kasa zama a kicin Win.

Kayan ciye-ciyenta ta kwaso ta dawo falo tare da kunna kallo ta zauna tana ci.Gidan ta ji ya yi mata faWi saboda babu kowa a gidan sai maigadi,A.m kuma tun da ya fita bai dawo ba.

Bayan ta yi sallar magariba da ?yar ta jira isha'i tana gyangyaWi,akan daddumar ta kwanta sai bacci.

Sai misalin tara ya shigo ganin bai ganta a falon ba sai ya yi mamaki saboda da sai ta kai ?arfe sha Waya tana kallo.

?akinsa ya shiga ya yi wanka kafin ya zo ya yi sallama da ita,don haka ko turare bai shafa duk da yana jin wani iri,amma gudun rigimarta ya ha?ura.

Dariya ya yi ganin yadda ta dun?ule kanta tana bacci a dadduma sai ya shafa mata addu'a ya Waga ta cak ya kwantar akan gado tare da rufo mata ?ofa ya fita.

A.m dake ta juye-juye a Wakinsa shi kaWai yana jin kewa na damunsa musamman na Zeey Win sa shida yake hutawa da matansa biyu,amma Waya ta gagare shi,don haka ba tare da wani tunani ba ya fice daga Wakin,bayan ya fesa turaren da take so a Wakin.

Cak ya Waga ta don ya san ba za ta amince ta biyo sa ba,sai dai kafin ya isa da ita ta farka tana mi shi bore amma bai kula ta ba,har sai da ya dangana ta da Wakin ya kwantar dare da rufe ?ofar.

" Ki kwanta har na fara bacci Momi ta kira ni ta ce kar na sake ki kwana ke kaWai a Waki,saboda gudun matsala."
Bakin sa ya taSe yake magana ba tare da ya dube ta ba,ganin yadda ta ci magani tana mi shi bore.

" Amma ka san ba na son ?amshin jikinka ba zan iya kwana da kai Waki Waya ba,sannan na yi al?awarin babu abin da zai ?ara kawo ni Wakin nan,saboda na gama aikin da aka biya ni."

" Na sani ni ma ba wannan ya sa na kawo ki ba ko da ha?uri nake yi nake kula ki don na samu baby,amma kin san ai na wuce ajin da zan kula ki.Fatana matar so ta dawo mu ci gaba da zamanmu lafiya." Ya ce tare da kwanciya can gefen ta.

" Oho ko ma me za ka ce ba ni da matsala Allah ya sa matar ladan gona nake a gareka bai shafe ni ba."Ta ce sannan ta fara mi shi bore tana yatsina fuska kan za ta bar Wakin.

" Kin san Allah ko aman me za ki yi ba zan raba kwana da ke ba,sai matar so ta dawo gara ki kwantar da hankalin ki ki kwanta ya fi mi ki."

Juwairiya da ta gaji da ta kwanta bayan ta Waure bakinta don ta lura komai zai ta yi mi shi ba zai mai da ta Wakinta ba,sai ta kwanta don babu yadda za ta yi.

A.m da ya kasa bacci yana ta mutsu-mutsu yana jin tana ?orafi har ta gaji ta yi bacci,amma shi ya kasa bacci.

Wani irin juyi ya yi sai ga shi ya rungumota ya matseta a jikin sa.
Da sauri ta ture jikinsa cikin Sacin rai." Don Allah matsa za ka takura mini ina bacci,ka san ba na son na ji na raSe ka."

Ba tare da ya buWe idanunsa ba ya ?ara matseta a jikinsa yana jin zafin jikinta ya yi masa daidai da sanyin jikinsa.

" Ki kiyayeni har yanzu a matsayin matata kike don haka ina da ikon da zan taSa ko ina a jikinki."Ya raWa mata a kunninta.

" Ai ba ka isa ba in ba haka ba amai kake son ka yi wanka da shi do.."

" Allah ya sa abin da ya fi mai za ki yi amma saina matso kusa da ke,ko ranar da kika yi mini ba kashe ni ya yi ba,in ma da gayya kika yi,sannan ki korar mini matar so sannan ki barni maraya,ai ba ki isa ba,yanzu Win maneji zan yi kin san ba kamar ta kike ba."

Ba tare da ta ji ba?in cikin abin da ya ce ba sai ta saka mi shi kuka sosai,jin abin da yake mata sannan tana jin duk in da ya taSa na jikinta kamar yana Wora mata garwashin wuta.
" Ai in har ka taSa ni ba zan yi wanka ba don ba na son na saka ruwa a kaina."

" Wannan kuma ke ya shafa matsalar ki ne ke da Allah."Ya ce mata ba tare da ya fasa abin da ya yi ninya ba.

Ganin da gaske yake ta ture jikinsa da ?arfi za ta mi?e,amma sai ya saka ?arfin tuwonsa ya ri?e ta ?am.
" Ka rabu da ni sadda ka je neman aurena cewa ka yi in samu ciki in haihu ai baka nuna bayan cikin a kwai abin da zai shiga tsa?aninmu ba."

Dariya ya yi jin abin da ta ce sannan ta ?an?ame jikinta sosai,sai ya tsaya cak ya kalle ta ransa ya fara Saci.

" Har yanzu matata kike so ki kiyaye ni karki kai ni bango in yi miki dole gara ki saki jikinki."

"Mugu azzalimi wallahi gobe gidan Momi zan koma ko na Wauko Hamdiya mu rin ?a zama tare."Ta ce da shi jin ya kai mata wani wawan kis.

" Allah ya ba ki sa a dama ki na da hali mai kyau da za ta karSe ki,na san mugun halinki na ?azanta ya saka Momi ta kore ki,ita Hamdiyar ba mahaukaciya ba ce kamar ki."

Ganin abin da take mi shi ya tashi zaune da Sacin rai ya ce." Juwairiya ki fita idona ina tausayinki ne don babyna na rantse da yanzu jikin ki ya gaya miki."Ya ce mata ran shi a Sace.

" To meye sabo a gareni ka duki matar so balle ni ai halinka ne."Da Sacin rai ya kalleta ganin ta ?i yadda sai ya sausauta murya.

" Kar kiji ina ro?on ki gaisawa da babyna zan yi kuma maneji zan yi da zarar Zainab ta dawo ko kallonki ba zan ?ara yi ba."

Ganin ba za ta kula sa bai saurara mata ba sai da ya samu natsuwa ya matsa gefe.Juwairiya da sauri ta mi?e tana kwara amai da fari biriss ya yi da ita amma gani yadda ta ke ?a?ari sai ta ba shi tausayi ya isa gareta tare da kama jikinta.

" Karka taSa ni dama na san ka tsane ba ka sona duk abin da zai cutar da ni shi kake so."

Tsaki ya yi ya koma ya kwanta kuma ya ?i buWe mata kofa da ta gaji ta kwanta ita ma.

A.m da ya jima bai yi bacci ba yana ta tunanin canjin da ya ji a jikinta domin ta canza kamar ba ita ba,komai na jikinta ya zama wani iri wanda shi kan sa ya kasa tantance komai.

Hunnunsa ya tura cikin gashin kanta yana murmushi mai Wauke da ma'anoni wanda shi kaWai ya san me yake nufi.

Haska fuskarta ya yi da wayarsa sai yaga ta yi bacci tana saukar da numfashi a hankali,yayin da fuskarsa take wani irin haske mai walwali.

Murmushi ya yi kamar ya rungumota su kwanta amma ya san mai zai faru sai ya kwanta cikin annashuwa,tare da tofa mata addu'a ya kwanta da tunani barkatai a zuciyarsa.

" A.m ka tashi don Allah."


Juwairiya ta ke bubbuga shi a hankalinda wata irin murya,amma sai bai ji ta ba kasancewar bai ya daWe bai yi bacci ba.

Ganin haka kawai sai ta saka mi shi kuka da ?arfin ta.Da sauri ya buWe ido tare da kunna fitila,ya kalli agogo ?arfe biyu da kwata.

"Lafiya mai ya same ki?"

Ta ri?e cikinta tana hawaye ganin haka ya ruWe ya kamo ta jikinsa.

Ture shi ta yi ta ce." Cikina ke ciwo kuma na kasa bacci."

" Mai ya faru take ciwo ko ba?in ciye-ciyen ki za ki ja mini asara."Ya ce da ita cikin Sacin rai da ta tashe shi da tsakar dare,saboda bacci ne a idanunsa.

" Yunwa nake ji kuma Wanwake zan ci."Ta ce tana fargabar abin da zai ce mata.

"Abinci da tsakar daren nan an ya ki na da hankali kuwa?"
" Yunwa nake ji sosai kuma ba zan iya bacci ba sai na ci abinci,ko da na dawo banci abinci ba,sannan kai ba ka damu dani ba,balle ka tambayeni."

Sai ta saka kuka tana." Allah Sarki ni dai kawai ka mai da ni gidan Momi na fi son na zauna acan,saboda kai ba ka iya komai ba sai zalinci da mugunta."

A.m tun yana tunanin ko wasa take masa har ya gane da gaske yunwar take ji,tashi ya yi da sauri ya na dana sanin Wauko ma kansa jangwam da ya yi,ya buWe mata ?ofa ya ce cikin tsawa." Malama dallah zo ki fita gabaki Waya daga dawowarki kin tada hankalina ki bari gobe in na kira ki sai ki yi mini abin da kika ga dama.Ai kin san in da kicin Win yake sai ki je ki girka tun da kin zama cin yau,in ban da iskanci da tsakar dare za ki ta she ni,Allah ya sa ki yi girki da aljanu su tsorata ki."Ya ce a fusace yana kallonta kamar ya sha?ure ta.

Turo bakinta ta yi ta ce." Babu in da zan ni anan zan kwana kuma ni ba zan iya girki da kaina ba,saboda warin gas ba ya barina na yi kuma in dai na yi girki ba ya mini daWi,don haka kai za ka girka mini kuma Wan wake zan ci."

Tsananin mamaki ya sa shi kasa magana a ransa yake mamakin yau she ta raina shi haka da har za ta kalli tsabar idanun shi ta ce shi zai dafa mata abincin da za ta ci.

" A she za ki mutu don ko da rana ba ki taSa ganin na shiga kicin na yi ma matar so girki ba balle ke yar karan kaWa miya,kuma in ban da kin raina,ni zan yi miki girki kici da tsakar dare ko ba ki kalli agogo ba."

Ya yi tsaki ya koma ya kwanta yana jin haushin tashin shi da ta yi.

Juwairiya ta takura ta saka ?ara domin har jiri take gani saboda yunwa,sai ta fara kuka ganin ya kwanta.
" Ai kuwa mutuwan kasko za ayi ni da abin da ke cikina don har na ji ya daina motsi,kuma tabbas in banci abinci ba mutuwa zan yi ka ga kai ka rasa ko banza Mama tana da Ibrahim,kai kuwa matarka juya ce ba ta haihuwa"

A.m da yake ji kamar ya sha?ure ta saboda takaici a she Momi wahala suke ji shi ya sa ta haWosa da ita,amma jin abin da ta ce sai ya mi?e yana murza idanunsa,ya kalli cikinta da sauri ya ce.

" Amma kin san ban iya kunna gas ba kuma ban iya Wanwake ba."

Ta so ta yi dariya ganin yadda ya yi maganar da tausayin kan sa a fuskarsa,sai ta ?ara gasganta maganar da Hamdiya ta yi mata cewar duk abin da ta saka shi zai yi,saboda cikin in ko hakane duk sai ta wahalar da rayuwar su duka.

Mu je na nuna maka sannan Momi ta haWa mini garin Wan waken sai na zuba maka iya yawan ruwan da ake so ka kwaSa."

Tsaki ya yi ya zura duguwar jallabiya suka fice yana tafe yana tangaWi don bacci yake ji.Haka kuwa aka yi ta nuna masa sai da ta fita ya kunna,bayan ya zuba ruwa ya Wauko kayan garin kamar yadda ta ba shi umurni ya kawo mata tana zaune a falo da wayarta tana daddannwa ya ije mata fuskar shi babu fara'a ko kaWan.

Da ya kwaSa ya koma kicin yana mamakin kan sa." A she haka nake son Wana?"Sai ya yi dariya ya ?ara cewa." Na rantse duk ranar da ka fito zan rin?a kissing Winka wunin ranar shi ne horan da zan yi maka son."

Bayan ya saka su ?wama-?wama duk da ta gargaWe sa amma yana son ya ba?anta mata.
GyangaWi ne ya kama shi sai ya ji muryarta da ?arfi a bakin ?ofa ta ce." A.m."


Da sauri ya duba girkin har ruwan ya ?one saura kaWan ya yi sauri ya kwashe sannan ya kai mata.

" Ji don Allah wani irin Wanwake ne kamar an jefi ?ato."Ba tare da ya kalle ta ba ya fara tafiya zai haye sama.

" To ina za ka je nufin ka ni kaWai za ka bari a falo tsoro nake ji."

Dawowa ya yi yana harara ta." To ki zo mu je Wakina ki ci acan bacci nake ji."
" Allah ya kyauta ba zan koma Wakin ka ba ai ka sa cin abincin zan yi."Ta ba shi amsa a ta?aice.

Kan two seater ya zauna yana kallon yadda take cin Wanwaken tana ta kushewa.

Gabaki Waya sai ya ga ta canza kamar ba wacce ya sani ba,mai sanyin hali da ha?uri da kuka akan ya sota.
" Kai wai haka masu ciki su ke yi ko tashi ce ?ar rainin wayo?"Ya tambayi kansa zuciyar sa na tafarfasa.

Tun yana jiran ta gama har bacci ya kwashe shi a ta?aice a ranar anan suka kwana,sai da asuba kiran sallah ya tashe shi.
" Sai ki tashi ki yi sallah saboda iskanci kalli in da kika bar mu muka kwana kamar wasu marayu,kin takure guri Waya ji kuma kwanciyar da kika yi salon ki cutar mini da baby."Ya ce tare da fara tafiya zuwa Wakinsa don ya yi alwala jin amfara salla.

Haka suke zaman na su gabaki Waya ta mai da shi Wan aiki da ya fara ?orafi sai ta saka kuka ta ce baby,shi kuma sai ya ruWe ya yi duk abin da ta saka shi kullum gidan nan cike yake da kayan ciye-ciye,tun bai iya soya kalallaSa ba har ya ?ware saboda ?a'ida ne sai ta tashe ya yi mata Waya daga cikin su,tun yana ?orafi har ya saba,gabaki Waya ba ya samun bacci wadatacce,kullum cikin ?orafi take yi sannan duk wani turare ya saka Juwairiya za ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta so,?amshin wanda take so shi ya kama gidan ko ina,shi kan sa yana tsoron ranar da Zainab za ta shigo cikin gidan nan.


Kafin ta daina amai sun sha jarfa tun daga ranar da ta dawo duk dare sai ya Waukota da kan sa ,ta yi masa bore amma ya jure saboda shi kaWai ya san yanayin da yake tsintar kan sa,amai ne dai ?a'ida wanda kullum dare sai ta yi shi,amma hakan ba zai hana sa bin da ya yi ninya ba.

A.m ya rame sai hanci kamar shi yake laulayin saboda ba ta barin sa ya huta duk da ta yi mi shi ?orafin ya Wauko Hamdiya,amma ya ?i saboda ba zai iya Wauke idanunsa a kanta ba,kuma

43 / 48