Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 48

9K to 12K   out of 143.8K words

MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


*SHAFI NA BIYAR*

Juwairiya zaune a gefen Mama ta na yi mata kitso,Ibrahim ya na zaune a gefenta ya na wasa.Baba ya buWe labulen Waki ya fito dai-dai lokacin da Baba Sani ya kwaWa sallama daga nesa da su.Ganin sa Juwairiya ta zabura kamar za ta gudu,tun lokacin abin ya faru ta ?ara matu?ar tsoron shi ganin shi take kamar kumurci.

Baba Sani ya kalle ta da wani irin kallo wanda shi kaWai ya san ma'anar sa,sannan ya mi?a ma Baba takadda yace."Gashi na gaji da biyan kuWin wuta ni kaWai,yau za su zo ka biya ko kuma a yanke na ka."Ya faWa ya na kallon bangaren Juwairiya da ta rintse idanunta tun bayan da lamarin ya faru ta yi katanga da shi,ko ina ba ta zuwa islamiya ma ta ha?ura gara ta din ga zama a gida da ta gan shi.

Baba ya yi kasa?e ya na kallon sa na tsawon lokaci sannan yace."Ka sa su yanke nawa in dai baza ka iya biya ba,bani da shi kuma na ga ko waya babu wanda yake da shi a cikin mu hasken kawai muke amfani da shi."

" Oho ko ma me zaka ce kace na gaji da wahala."Ya sa kai ya fice ya na bambami.
" Ikon Allah na rasa me ke damun shi ya canza gabaki Waya.Allah ya ganar da shi."Yace sannan ya Wauki gatarin sa ya fita.Juwairiya ta yi shiru ta na tunani a ranta zuwa can ta mi?e tare da shiga bayi ta saka kuka.

Mama ba tace komai ba illa ba?in cikin halin da yake nuna musu,wanda ta san tsananin ?iyaryarta ya sa yake nuna musu hakan.Idanunta suka kawo ruwa amma sai ta yi ?o?arin sharewa,ba tare da Ibrahim ya gani ba.

Juwairiya ba ta fito ba sai da ta sha kukanta ta ?oshi sannan ta wanke fuskarta ta fito,a ranta ita kaWai ta san halin da zuciyarta take ciki.Duk da Mama ta gane kuka ta yi ba tace mata komai ba,domin ita ma da za ta samu dama kuka za ta yi ko zuciyarta ta rage raWaWin damuwar da take ciki.

Yanayin rayuwar da Juwairiya take ciki babu daWi ji take kamar ta na rayuwa a gidan kurkuku!Kusan kullum sai ta yi kuka ta na matu?ar bakin cikin halin da iyayenta suke ciki,burinta bai wuce ace ta samu aiki ta na taimaka ma iyayenta ba.

Tsakanin ta da Baba Sani tun faruwar lamarin take jin wani tsanar sa mai tsanani ya na ?ara shiga cikin ranta,ko muryar shi ta ji sai ta yi ta'awizi a cikin ranta tsananin mamakin mugun halin sa take.

Duk yadda ta so ta taimaka wa iyayenta abin ya ci tura har takai su kwana basu ci ba,tashin hankalinta yadda Ibrahim yake yi,amma ?iri-?iri Baba Sani ya hana matar sa basu abinci.

Ganin halin da suke ciki wani lokacin ta yi kuka kamar numfashin ta zai rabu da gangar jikinta.
Mahaifin Juwairiya na tsaye ya rataye gatarin sa a kafaWa hankalinsa baya jikinsa,tunani yake sosai a cikin ransa ga wata irin yunwa dake ?wa?ularsar.Tunani fal a cikin ransa ya na tunanin kuWin aikin da za'a yi ma Ibrahim aiki a ?afar sa.

Ya daWe a tsaye ya na tunanin mafita daga bisani yaci gaba da saran iccen da yake yi cikin rashin kuzari,tare da rashin madafa sai tsa?a da warwara yake a cikin zuciyar sa.

Ya Waga gatarin sa a sama ya na can ya na tunani bai ankara ba sai ji ya yi gatarin ya dawo tsakiyar kansa! "Innalillahi wa inna ilaihir ra ju'un."Iya abin da yace kenan ya zube a ?asa a sume jini na ta zuba kamar famfo!

Hankalin Malam Audi dake gefen icce ya na bayar da iccen ya fahimci abin da ke faruwa, da sauri ya iso garesa ya na salati cikin tsananin razana tamkar zai fasa ihu ganin halin da yake cikin.
Mutanen dake gurin suka yo kansa suna salati ganin abin da ke faruwa,kama shi suka yi aka saka shi a cikin mota suka nufi a sibiti da shi.

Lokacin da labari ya riske Juwairiya hannunta saka a ka sai kuma ta yi ?o?arin da?ile zuciyar ta da take ninyar kwarma ihu,ta fara salati ta na faWin."Inna lillahi wa inna ailaihir raji'un."Sai hawaye bayan ta yi nasarar faWin haka ta yi koyi da faWe na ubangiji da ya umurci bayin sa da su faWi haka duk lokacin da wata musiba ta same su.

"Wayyo Allah rayuwa ta me ya sa daga wannan sai wannan?"Ta tambayi kanta cikin tsananin ruWani.Gabaki Wayan su sun ruWe ganin halin da yake ciki kai ya kumbura kamannin sa ya canza,sannan an Waure kansa da bandeji duk ya Sace da jini.

A lokacin da suka je ko magana baya yi idanunsa a rufe ba ya iya ko buWe idanunsa,daga ganinsa ya na cikin wani hali babu alamun numfashi tare da shi sai bugun numfashin sa da yake sauka a hankali a cikin tsananin wahala.

Rintse idanunta ta yi a jikinta take jin kwatankwacin zafin ciwon dake jikin Baba,ta kasa kuka sai hawaye da yake gasar sauka a ?uncinta ba tare da sanin ta ba.

Suna zaune har tsawon wani lokaci amma bai farka da ga baccin da yake ba,saboda allurar baccin da aka yi masa.Har misalin tara na dare sai a lokacin Baba Sani ya shigo ya na ta zare ido,a cewar sa yanzu ya dawo gida ya ji labari.

"Ni na rasa wannan lamari na ka Yaya kamar wani mai bakin uwa,kullum rayuwarka ?ara taSarSarewa take.Haba wannan wane irin musifa ne! Tun ba yau ba nake maka maganar kabar yin faskare amma ka?i ga shi nan abin da ka jawa kanka."

Ire-iren kalaman da yake faWi kenan ba tare da nuna tausayi a fuskarsa ba,sai dai nuna rashin damuwa da faWin maganganu mara tsari.Juwairiya da ta kifa kanta da akan gadon asibitin ta na wani irin kuka.

Hankalin su ya yi matu?ar tashi ganin halin da yake ciki,Juwairiya kamar ta mutu haka take ji,?iri-?iri in aka bu?aci kuWi Baba Sani yake ?in bayar ba kullum da uzurin sa da yake faWi.

Da ga baya Baba Sani yake zuwa ya na kwana da Baba.Baba Sani tsaye akan Yayan na sa da misalin ?arfe Waya na dare,kallon sa yake da mugun nufi a ransa.Filo ya janyo tare da danne masa kai.

Allah Sarki bawon Allah da yake kwance a cikin mawuyacin hali ya fara mutsu- mutsu da ?afafun sa,bai jima ba ya yi dip alamun babu numfashi a jikinsa.

" Gara ka mutu kowa ya huta kullum cikin wahala nake da kai da iyalan ka,sannan Wan bu?ata ta da nake son na biya na rasa.Kaje kawai Allah ya haWa mu a kiyama!Abin da yace kenan ya kwanta da ninyar da safe ya fasa ihun ya mutu.

Washegari da safe Juwairiya tun da asuba take azalzala wa Mama da su je asibiti,irin mugayen mafarkin da take yi akan mahaifinta ya sa hankalinta ya tashi sosai.Mama ce ta Wan ?arfafata har suka dama koko suka sha,duk da dai Juwairiya ?urSar kokon take wanda ko siga babu hankalinta na gurin mahaifinta.

Ko wanka ba ta yi ba ta Wauki ruwan kokon ta na addu'ar Allah ya sa ya iya sha,Mama dai ba tace mata komai ba duk da ranta babu daWi.Ko da suka isa asibitin gaban Juwairiya ya yanke ya faWi ras!Sai ta kira sunan Allah ta ri?e kofin kokon ta na wani irin tafiya zuwa Wakin da yake tamkar wacce ?wai ya fashe mata a ciki.

Gabaki Wayan su suka yi mutuwar tsaye ganin Baba Sani tsaye, a Wakin ya Wora hannu a kansa ya na ?wala ihu, da kuruwa tamkar yadda jahilan farko suke yi yayin da wata musiba ta afkawa Wayan su.

Sautin kukan sa yake tafiya tare da bugun zuciyarta,ta rintse idanunta ta na addu'ar kar Allah ya sa mafarkinta ya zama gaskiya!In kuma da gaske ne ya za suyi da rayuwar su a duniya bayan ba mahaifin su?

Sai kawai ta fara ja da baya ta na girgiza kanta tare da nuna mahaifinta, ta na faWin dai-dai lokacin da Mama ta saka kuka domin ta tabbata ya riga mu gidan gaskiya."A'a bai rasu ba wallahi mafarki ne!Don Allah kar kuce min mafarkina ya zama gaskiya.Mahaifina ya na raye bai mutu ba."

Sai ta ruga za ta fita waje tashin hankalin ta ta ya ya mahaifinta zai mutu ya bar ta da azzalimi!Mutuwar sa na nufin ya yi nasara akan ta zai cika mummunan nufin sa kenan?

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haWu a shafi na shidda dan har yanzu shinfiWa ne har ba'a fara ba.Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.




*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA SHIDDA*


Duk yadda Juwairiya ta so ta kwantar da hankalinta akan mutuwar mahaifinta, abin ya ci tura!Da ta tuna mugun nufin Baba Sani sai ta ?ara rikicewa,irin yadda ta nuna na rashin tawakkali ya so ya fara tunzura Mama tun ta na ba ta ha?uri, ta taushe tashin hankalinta domin Juwairiya ta natsu amma ta kasa,sai uhu take ta na furta sunan Baba.

Ganin irin abin da take yi sai Mama ranta ya Sace matu?a,ta saki hannun Juwairiya dake son a kyaleta ta fita da gudu kamar wata kamun aljanu tace."Ku kyaleta ta yi duk abin da ta ga dama,ban san baki da tawakkali ba sai yanzu Juwairiya!Na Wauka saboda ?arfin imanin ki ni zaki din ga ba ma ha?uri,tare da jawo min aya akan na Wauki ha?uri domin duk mai rai mamaci ne."

Juwairiya ta du?a tare da ?ara sakin wani kuka dai-dai lokacin da Baba Sani ya ?araso gun ta ya na mata wani kallo,mai kama da tausayi ko akasin haka tare da sausauta murya yace."Ku kyaleta rashin mahaifi abu ne mai ciwo na tausaya miki matu?a,domin hakan da kika yi sai kika tuna min lokacin da mahaifin mu ya mutu ina kuka mahaifinki Yaya Ahmed shi ya dinga lallashina!"

Sai ya saka kuka ya na faWin."Allah Sarki!Allah ya ji?an ka Yaya."Ya nufo Juwairiya dake kuka tamkar ranta zai fita,da nufin zai ri?e ta ya lallasheta.

Da sauri ta matsa ta na wani irin kuka kamar za ta shiWe,ja da baya take kamar ta ga dodo.Ganin haka sai ya kyaleta a ran sa kuwa murmushin mugunta yake mata.Bayan an gama cuku-cuku aka ba su gawar Baba da har ta fara sandarewa.

Hankalin Juwairiya bai ?ara tashi ba sai da suka dawo gida ta ga inda yake kwanciya,wani ?arin abin tausayi tun da Ibrahim ya ji mutuwar mahaifinsa ya Wauke numfashi ko motsi ba ya yi.Lamarin sai ya jagule ma Mama ta rasa in da za ta sa kanta ta ji sanyi,ga wani irin kuka da Juwairiya take yi ta?i ta yi shiru.

Bayan an yi wa Baba sallah aka kai shi gidan gaskiya gidan da ko wane bawa yake da gadon sa domin ba'a wahala gurin mallakar sa.Cikin dare Juwairiya ta na kwance ta kasa bacci!A ranta ji take kamar mahaifinta kashe shi aka yi musamman yadda ta ga Baba Sani bai nuna tashin hankali game da mutuwar sa ba.

Ta na lura da shi har shinkafa ya siyo a dafa ma ?an zaman makoki,wanda ko mutuwa za su yi ba zai taimaka musu da shi ba.

Kwana ishirin da rasuwar Baba amma har yau sun kasa manta shi a kullum ta ranar duniya sai sun yi kukan rashin sa,musamman Juwairiya da yake sokanar ta duk san da zai fita ya na cewa Allah ya nuna mi shi ranar auren ta,a she ba shi da rabon gani.

A lokacin da Baba ya yi arba'in Juwairiya ta saka ma ran ta za ta yi fito na fito da Baba Sani duk abin da ya shirya a shirye take ita ma.Tun lokacin da Baba ya rasu bai ?ara shiga sabgar ta ba,duk da cewar ba ganin ta yake ba don ba ta fita ko ina.

Ganin ba su da cin yau bare na gobe sannan Mama ita ma kwana biyu ba lafiya take da shi ba,ya sa za ta gaya ma Mariya ta nema mata aiki ta din ga yi don da yunwa ya kashe ta gara dukan Baba Sani ya kasheta ita kaWai.Ta san ya na hana su abinci ne don kawai ya cutar da rayuwar su ko ya samu biyan bu?atar sa,amma ba wai don ba shi da kuWi ba tunna aikin gwannati yake yi.

Ranar da Baba ya yi arba'in sun sha kuka bayan sun yi mishi saukar alkur'ani suka ha?ura da kukan suna mishi addu'ar Allah ya ji?an shi.

Cikin sa'a bayan kwana biyu da gaya ma Mariya ta nema mata aikatau,ta zo da murnar ta an samu saboda ta na samun aikatau da dama kusan ita dillaliyar masu aiki ne.

Tafiyar da Baba Sani ya yi sai hakan ya ba Juwairiya damar ta fara aikin ta cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya sani ba.Duk da ita Mama taso ta bari ya dawo su tambaye shi amatsayin sa na mahaifi,amma ta?i ta kafe daga karke wasu irin maganganu ta jefa ma Mama wanda yasa ta ji babu daWi,a yadda take gaya mishi magana duk da ta san dama ba sa shiri,amma ko ba komai yanzu shi yake da matsayin mahaifinta kuma ko aure za ta yi shi yake da alhakin komai.

FaWa sosai ta yi mata don ganin ta a maganganunta har da rashin kunya,wanda hakan bai dace ba musamman shi da yake da matsayi mai girma a ranta.Juwairiya ta ji maganganunta amma yadda ta faWe su haka ta watsar da su a gurin a ranta take faWin."Ta ya ya za'ai na mutunta mutumim da yake da burin Sata min rayuwa,ko da mahaifina ne ya bijiro da wannan iyakan abin da zai yi mishi kenan Mama,domin babu biyayya ga abokin sabon halitta!Kema da zaki ji abin da yake so a gareni sai kin yi mishi fiye da nawa."

Matar da Juwairya za ta yi ma aiki likita ce a shika ta na da yara uku,a kwai wata mace tsohuwa wacce take mata girki ita kuma Juwairiya aikin ta kula da yaranta mata biyu da namiji Waya,in da za ta din ga mata aiki ta na tafiya har islamiya ta saka su tare da yaranta.Ranar da kuma take da aikin kwana za ta kwana da yaranta da safe ta shirya su ta tafi makaranta,wanda ta ba ta zaSi in ta gama shirya su za ta tafi gida duk da ita matar makaranta ta ba Juwairiya zaSi ta koma ta zana jarrabawar fita sakandiri.

Juwairiya ta ji matu?ar daWi na samun aikin duk da ta na jin tsoron abin da Baba Sani zai yi mata in ya fahimci ta na aikin.Ta?i amince mata kan shawarar da ta ba ta da ta koma makaranta,duk da ita ma ta na da bu?atar haka amma ta san Baba Sani ba zai bar ta ba.

Sai dai cewar da matar ta yi za ta dinga kwana da yaranta in ta na aiki ya so ya Wan tsorata ta,amma da ta gaya mata a kwai Baba tsohuwa sai hankalinta ya kwanta don ta yi tunanin tare za su din ga kwana.

Juwairiya ta ?ara son ta yi aikin jin an ambaci kuWi mai tsoka,sannan da suka tashi za su tafi sai ta ba ta kayan abinci da kuWi naira dubu ta sallami Mariya da tsoka,saboda ta yaba da hankalinta musammam da ta ganta ba ta da ?azanta.

Mama da ta ji aikin har da kwana sai ta fara yiwa Juwairiya faWa kuma tace sam ba za ta yi aikin ba,ta na ta faWa in da take shiga ba nan take fita ba.Ganin hakan sai ta saka kuka ta mi?e domin ta yi sallar magariba."Ba gara na zauna a gidan Anty Naja ba tunna na ji Mariya tace mijinta ustazi ne me gamu,akan ?anin mahaifina dake son ya Sata min rayuwa.

Juwairiya ta yi tunanin za ta shawo hankalin Mama,amma sai ta ga ta kafe a dokin na?i in da ta ?ara mata da cewar sam ata fau ba za ta yi aikin ba.

A ranar da suka shirya da Anty Naja za ta fara aikin,Mama ta kafe ko da Mariya tazo suka lallashi Mama shi ma bai yi wani tasiri ba ganin haka sai ta ha?ura,akan ta nema mata wani kawai wanda ba za'a din ga kwana ba.

Da maraice ta na zaune akan kujera ta na wanke-wanke sai suka ji sallamar Mariya da wata a bayan ta,da sauri ta Waga kanta duk da cewar ba ta yi ma Anty Naja kallon kirki a ranar ba,amma ta sheda ta.

A kunyace ta amsa mata sallama tare da yi mata jagora zuwa Waki,ta ibo mata ruwa a kofi ta ije mata sannan ta fice daga Wakin ta na jan numfashi ta ri?e turaren Anty Naja da ya baWe Wakin na su,wanda Juwairiya ta so ya dauwama a Wakin saboda daddaWar ?amshin sa.

"Ba ki sanni ba ko Mama?"Anty Naja tace bayan ta Wauki ruwan da Juwairiya ta kawo mata cikin sakin fuska,kuma ta sha ruwan sosai ba tare da nuna ?yan?yani ko tafi ?arfin shan ruwan randa,wanda hakan sai ya

4 / 48