Sakacina Ko Halin Maza Complete Hausa Novel

Author :  Jamsy Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 48

90K to 93K   out of 143.8K words

yi mugun Waga masa hankali duk da bai wani fahimce ta ba.
Tashi ya yi zaune ya na mata wani mugun kallo.

" Wallahi baki da mutunci ga shi na tashi gaya mini damuwarki,amma ki sani in na ji maganar ba ta da mahimmanci kin san sauran."

Ya faWa da muryar gargaWi ganin ta hana shi bacci.

Hararar shi ta yi tana faWin" Oh koma me za ka ce kai ka sani tun da ka zama munafuki, ka bani mamaki fir'auna a zuci Annabi Musa a baki." Ta faWi hakan ne don ta gane ko ?arya Lantana take mata don har yanzu ta kasa yadda da abin da ta faWa mata.

Bai ce mata komai ba ya ?ara watsa mata mugun kallo na na gargaWin ta iya bakinta.

Cikin tsanani mamaki A.m ya ji ta watso mishi tambayar da ya girgiaza shi ta ce.

" Mene ne ala?ar ka da Juwairiya?"

Ya shiga cikin tsanani tashin hankali ya ruWe matu?a ya kuma razana domin jikin shi rawa yake ayi,jin tambayar da ta watso mishi ya shiga damuwa Baba Sani ya faWo mishi a rai yana tunanin ko shi ya faWa mata,ya san zai iya don ya na shakkar sa ba shi da mutunci na ?arshe.

Allah ya so babu wadatacciyar haske a Wakin sai fitila mara haske na bacci dake kunne mai kama da babu,domin da a kwai ya tabbata babu abin da zai hana ba ta gano gaskiya ba,saboda jikin sa ya ji?e sharab da gumi sai zufa yake karyo mishi,ya na ji a ran sa in Allah ya haWa shi da Baba Sani sai dai Allah zai raba su.

Shirun da ya yi sai zuciyarta ta karye ta fara tunanin to ko gaskiya ne.
A.m da yaga zai tona a sirin kanshi da kanshi sai ya dake cikin wata irin murya ya ce." Mai ya sa kike min wannan banzar tambayar waye ita kuma meye haWa ni da ita? ?ar aikin ki fa kike danganta ni da ita kin cuce ni,mai zan yi da ?ar matsiyata jinin talauci kin taSa ganin na kula wata mace duk da damuna da suke yi balle ita.

Wani irin sanyi ta ji ya kamata jin abin da ya faWa dama ta san ce wa babu yadda za ayi ya kulata,amma don kar ta yi saurin sauko wa ta ce." Ba wani nan munafiki ai ni ka bani mamaki ka rasa wacce za ka kula sai ita,to bari ka ji na rantse maka ba ita ba ko wace mace ka kalla nine ajalinta saina illata rayuwarta,yadda ko waWanda suka kawo ta duniya ba za su so su ganta ba balle kai kana tunanin zaka haihu ne ni bana haihuwa."

A.m da ya koma ya kwanta jikin sa a mace hankalin sa ya tashi sosai,ya Wan ji daWi da ya fahimci ba Baba Sani ya gaya mata ba,don in da shine duka zai Sata lamarin ya tabbata sai ya kunna mata wannan recording da ya yi,amma a ran sa ya na mamakin wane munafukin ne ya gaya mata,ya san ce wa A.k ba zai taSa gaya ma matar sa ba."

Domin ya cire mata shakku sai ya mi?e cikin Waga murya ya ce.

" Look Zainab na lura baki da hankali ko kuma kin sha wani abu ko kin fara Waukar zigin ?awaye,in baki yadda da ita ba mai zai hana ki daina yawo ki zauna ki kula da ni,wanda ni kaina zan fi bu?atar haka,bawai ki tsaya kina zargina da wata kucaka ba,kamana kike tunanin zan iya kula ta mai take dashi kuma waye ubanta a duniya."

Ya yi ?uta ya ci gaba da magana da ?arfi ganin maganganun sa suna tasiri a kanta saboda ta yi shiru ta na sauraren sa.

Janyo ta ya yi zuwa jikin sa." Zainab please trust me."

Ya ?ara marairaice murya ya na shafa bayanta da ta yi lamo a jikin sa kamar wata mage ta na ?ara jin madarar son sa na ?waranya a zuciyarta.

A.m da ya ji ta yi lamo a jikin sa ya saki gwauron numfashi,ya na tunanin yadda zai yi ta amshi yaron da Juwairiya za ta haifa masa,amma ya saka a ran shi dole ta karSa ko ana ha mata ana ha maza.

" Bai kamata ki yadda da zugin ma?iya a kanmu ba ki tuna na yi miki halacci har yau babu wanda ya san ke ce bakya haihuwa,kuma na kasa haWa wata mace da ke na ri?e al?awarin da ba yi miki duk da ina son naga ?waina a duniya fiye da rayuwata,hakan ba zai sa ki yadda da ni ba?"

Zainab jikinta ya mutu murus duk da ta yadda da shi,amma ta Wauki aniyar cusgunawa rayuwarta da wula?anta ta agaban shi,domin ta cire Wan shakkun da take yi a zuciyarta kuma in ta gane gaskiya Lantana ta kuka da rayuwarta.

" Ka yi ha?uri zauji zuciyata ce ta kasa gasganta hakan bayan na san halinka fiye da kaina,amma in sha Allahu ba zan ?ara maka irin wannan tuhumar ba, kuma ni ma na fahimci ma?iya ne suke son su raba mu sai dai su mutu don ni da kai mutu ka raba."


Rungumota ya yi ya ce." Wannan dalilin ya sa nake matu?ar son ki auren mu da ke sai mutuwa za ta raba ni da likitar likitoci.

Yauwa bari na siya kwalliyar da aka hana ni siye bayan daga kallo Waya na siya babu ta yi gashi yanzu har ta yi arha."Dariya ta saki suka manta komi .

A.m bai tambayi wanda ya gaya mata ba amma ya zama dole ya ?ara saka tsaro saboda someone is behind ko kaWan bai yi tunanin Lantana ba ce.

Cikin tsananin mamaki Baba Sani ya tsaya a ?ofar gidan sa ya na kallon Maama da ke tsaye da ?an sanda guda biyu a bayanta.

" Yauwa ranka ya daWe ga shi nan ku kama shi."Ta faWa fuskarta babu walwala.

" Ranka ya daWe don Allah kar ku kama ni na rantse gobe Juwairiya za ta dawo na gaya mata,amma ta ?i ji duka yau sati biyu da shekara ta yi kuma wannan bawon Allah ya taimaki rayuwarta."Ya faWa ya na zare ido.

" Ok kin ji abin da ya ce ki yi ha?uri in har ba ta dawo ba sai mu Wauki mataki."?aya daga cikin Wan sandan ya faWi.

" Ba komai Allah ya kaimu goben in kuma ba ta dawo ba zan kai gaba,ko da kuwa baku ?wato min ha??ina ba."

Ta ce ta kalle Baba Sani cikin Sacin rai ranta ya na faWa mata a kwai abin da Juwairiya da Baba Sani suke Soye mata.

A daren da suka yi maganar da misalin ?arfe biyu na dare Mama na zaune a sallaya ta na karatun kur'ani bayan ta idar da sallar nafila.

Sai ta ji kamar ana buWe get Win gidan tsoro ya hana ta motsi zuwa can ta ji an shigo.

Wasu ?attin maza majiya ?arfi guda uku suka shigo.
Da sauri ta mi?e ta na salati kafin ta furta komai sun sha?a mata wani abu a fuska ta zube luuu a ?asa.



TO FA MASU KARATU NA IJE BIRONA SABODA TSORON WA?ANNAN MUTANE INA TUNANIN SU WAYE.

KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



SAKACINA KO HALIN MAZA


TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY





Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu bu?atar shiga cikin group Wina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ?ofa a buWe take na ?orafi gyara ko ?arin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga za?auran marubuciya,kuma ?awata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ?ara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.










*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 26*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


A cikin motar da suka zo da ita suka sakata,sun yi tafiya mai nisa gaske sannan suka tsaya.

Duk nisar tafiyar da suka sha amma Mama da Ibrahim ba su farfaWo ba.

Wani ?aton gida suka shiga da su tare da kwantar da su,sannan suka fice daga gidan.

Kusan awa Waya Mama ta yi sannan ta farka cikin tsananin razana tana salati.Ta kalli in da take yayin da take tsananin mamaki,idanuwanta suka firfito tana mamakin in da ta tsinci kanta.

Ibrahim dake kwance ta rungume tana jijjiga shi,cikin tashin hankali tana mamakin ganin ta a wannan gida.

Ko da ya buWe ido sai ya cika da tsananin mamaki ya kalle ta ya ce.

"Mama ina ne nan kuma mai ya kawo mu wannan gida?"

Mama dake cikin tashin hankali ba ta ba shi amsa ba,sai mi?ewa da ta yi tana ?arewa gidan kallo.

Duk da rashin ?arfin jikinta amma haka ta mi?e ta kama hannun Ibrahim suka fito waje.

" Madam lafiya ina za ki je."

Ta ji muryar wani mutum wanda yake tsaye a get Win gidan,ya na sanye da kakakin sojoji da bindiga Wauke a hannunsa.

Mama ta ja baya da sauri tana kallon sa da tsoro a fuskarta.

" Waye kai kuma mai ya sa kake tambayata?Zan koma in da kuka Wauko ni."

Ta ba shi amsa da muryar tsoro a fuskarta,tana ja da baya saboda ta tsorata ?warai da ganin sa.

" Madam ki yi ha?uri oga bai ba mu izinin ki fita ko da ?ofar gida ba ne."

Ya ce cikin Waure fuska ba tare da ya kalle ta ba,balle ya ga tashin hankalin da ke Wauke a fuskarta.

" Waye kai mene ne haWina da kai har za ka ce ba zan fita ba,sannan waye agan ka ina ruwana da shi."

Ta jera masa tarin tambayoyin da take tunanin ba zai amsa mata ko Waya ba.

" Wannan kuma sai ki jira har sai ya zo ki yi mi shi tambayoyi,amma ba ni da masaniya ina kan aikina ne kawai.

Mama da fari ta Wauka wasa yake mata amma da ta dage kan dole sai ya buWe mata,sai ta ga ya Waure fuska ya Waga zungureriyar bindigar sa,ba tare da ya ?ara kallon ta ba.

Da sauri ta kama hannun Ibrahim suka koma ciki,saboda ta tsorata da shi gani take kamar zai harbe ta.

" Inna lillahi!
Wai me ke faruwa ne na kasa gane komai ya Allah ka fahimtar da ni,na san cewa Baba Sani ba zai taSa killace ni a gidan nan ba don kawai na bu?aci Juwairiya ta dawo."

Ta faWa cikin tashin hankali tare da rashin madafa tana ji kamar ta yi hauka.

" Ina Juwairiya mai ya sa ita ba'a taho da ita ba?"
Ta tambayi kanta da tsananin mamaki yayin da ta rasa ta in da za ta fara tunani,domin lamarin ya Waure mata kai sosai.

" Ko masu garkuwa da mutane ne suka sace mu?"

Ta faWa tana kallon Ibrahim da ya cika da mamaki ya na kallon daular gidan da aka kawo su.

A jiyar zuciya ya yi mai nisa sannan ya sauke tagumi ya kalli Mama,da fuskarta ya nuna tsantsar tashin hankalin da take ciki.


" Ba na tunanin za'ayi garkuwa damu har gida sannan aka wo mu cikin wannan daular Mama! Ki duba irin wannan gidan na masu kuWi ne sosai.Ni dai ina zargin a kwai wata a ?asa.Tabbas a kwai lauje cikin naWi."

" Haka ne Ibrahim zuciyata ta fara hasasomin haka,sai dai ina zargin duk abin da ya faru a kwai saka hannun Baba Sani a ciki.Zuciyata ta fara zargin in da ya tura Juwairiya ba alkhairi ba ne,sai dai ina Wan jin sanyi ne, in na tuna da Juwairiya yarinyar kirki ce,na yadda da tarbiyar da na ba ta sam ba na tunanin za ta aikata abin da nake zargi,duk da cewa ba'a shedar Wan yau."

Hannu ta Wora a ka yayin da gabanta ya faWi ras!Sa'ilin da wani tunani ya faWo mata.

" Kar dai a ce Baba Sani ya yi mini ?arya ne akan aiki zai kaita,ya saka ta a hanyar banza?"

Ta tambayi Ibrahim da take tunanin bai fahimci abin da take nufi ba.
Mama ta saki ?ara tare da zubewa a ?asa tana faWin." Ya Allah na kasa samun natsuwa zuciyata,na shiga ruWanin halin da Juwairiya take ciki,kar a ce Baba Sani ya Sata mini tarbiyar da na gina ta akai,ya saka ta a harkar banza.Kar a ce da kuWin da take aikata alfasha muke ciki."

Sai ta girgiza kanta tana kuka da ?arfi ta ci gaba da faWin. " Iya tsawon yaushe zan zauna a wannan gidan ba tare da na san gaskiya ba,in har Juwairiya ta canza tarbiyar da na ba ta tabbas ba zan iya yafe mata ba,domin na ci burin na ga na aurar da ke Juwairiya kar ki yi mini haka."

Da sauri Ibrahim ya tas???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?o ya rungumeta yana rarrashi ganin tana son ta fita hayyacinta.

"Mama mu bi abin da sannu-sannu kar ki aibata ta,na san cewa sam Anty Juwairiya ba za ta aikata haka ba,tabbas a kwai abin da ke faruwa.Kuma duk wanda ya sa aka kawo mu cikin wannan daular,to a kwai saka hannun Baba Sani a ciki don zuciyata ba ta yadda da irin sanyin da ya yi ba,lokaci guda ya zubda duk wani makaman sa akanta."

Mama ta shiga cikin tsananin ruWani ?warai ta yi ihu ta yi kuka,tana ro?on mutumin da ya taimaketa ya gaya mata abin da ke faruwa,amma ko kallon ta bai yi ba don ba'a ba shi izinin haka ba,bayan haka shi bai san komai game da lamarin da ya faru ba.

Ganin irin kukan da Mama take yi tana kiran sunan Juwairiya ta ?i shiga cikin gidan,a farfajiya ta tsaye tana kuka sosai ya kalle ta ya ce.

" Hajiya ba ni da nufin na cutar da ke gara ki koma ciki,don wallahi ko kukan mutuwa za ki yi ba zan buWe miki ki fita ba.

Jin haka Mama ta ?ara sakin wani kukan ta zauna a gurin ta ?i motsiwa,sai kuka da take yi domin kanta ya kulle.

*****

A ranar da aka Wauke su Mama Juwairiya ta yi wani irin bacci mai nauyin gaske,ba ta tashi ba sai da ta Wauki tsawon lokaci tana bacci mai kama da na mutuwa.

BuWe idanunta ta yi cikin tsananin mutuwar jiki don ji take ko Wan yatsa ba za ta iya Wagawa ba.

Sai da aka Wauki tsawon lokaci sannan ta samu ta iya tashi zaune.

?aga idanunta da ta yi ta kalli agogon da ke manne a bangon Wakin,da gudu ta mi?e tana salati saboda tunawa da ta yi ko sallah ba ta yi ba.

" Na shiga uku mai ya faru yanzu fa ?arfe Waya har da kwata,wane irin bacci na yi ko dai mutuwa na yi na dawo?"

Ta tambayi kanta domin wannan bacci da ta yi bai yi kama da na lafiya ba.

Da sauri ta mi?e ta shige ba yi tana tunanin to wane sallah ya kamata ta fara.

Bayan ta idar da sallah sai ta yi sauri ta ruga zuwa falo,saboda kiran curoma da cikinta yake yi.A haka dai ta ?arasa tana mamakin jin gidan ya yi shiru,kamar ba mutane a gidan.

Ta shiga cikin tsananin tashin hankali da ta duba lungu da tsa?o ba ta gan su ba ,sai ta fara kuka da salati tana dubawa cikin tsoro.Ta Wauki tsawon lokaci amma ba ta ji Wuriyar kowa ba.

Tana tsaye a farfajiyar gidan motar Baba Sani ya sawo kai.Da sauri ta ?arasa gurin shi cikin muryar kuka don tunaninta ya fara ba ta yana da saka hannu na rashin ganin su,ko kuma shine ya Wauke su.

" Baba Sani ina Mama na duba ko ina ban ganta ba."

Wata irin tsawa ya daka mata ya ce."Ku ji min munafuka ban sani ba,duk abin da ke faruwa ba da saka hannunki ba za ki raina min wayo."

Zare idanunta ta yi ta ce."Wallahi ba ni da masaniya akan komai mai ya faru?"

Kallonta ya yi sai ya matso kusa da ita ya fara magana cikin Waga murya." Jiya A.m ya sameni ya ce kun yi da shi zai kai Mama wani gari har zuwa lokacin da za ku rabu,saboda na gaya masa ta kawo min ?an sanda."

Ya faWa ranta a Sace da ba?in ciki ?arara a fuskar sa." Wallahi sam ba haka na so ba na so a ce yabar mini komai a hannuna,saboda na yi ba?in cikin irin daular da ya kaita."

Juwairiya ta kaWu da jin abin da ya faWa sai ta saka kuka sosai,ganin yanzu Mama ta san abin da ta aikata.

A ?asa ta zauna tare da ?ara sakin kuka." Na shiga uku ba zan iya ?ara gaWa ido da Mama ba,wane irin kallo za ta yi min wallahi na yi dana sani ?warai,yanzu idanuwana ba za su ?ara ganin ta ba har saina haifa mi shi yaro."Sai ta ji hawaye na sintiri akan fuskarta.

Sosai ta shiga tashin hankali ta na jin ba za ta ?ara iya haWa ido da Mama ba,don ta san daga ranar da ta ji abin da ke faruwa za ta tsaneta na har abada.

Ganin irin kukan da take yi sosai kamar ranta zai fita a ranta ta na jin ba?in ciki matu?a.

Baba Sani bai duba halin

31 / 48