RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 53

18K to 21K   out of 157.3K words

ratsa zuciya da gaSSan jikinta.



*******
Duk matsananciyar fara'ar da ke fuskarta lokaci Waya Waukewa tayi Wif! Sakamakon ganin wasu setin kuloli har guda uku da ya nuna mata da cewar a cikinsu za a cigaba da zuba ma su Innaye abinci. SaSanin waWanda ta ware guda biyu masu matsanancin arha da sau?in kuWi, ta kuma tabbatar ma Rabi duk halin da ake ciki in dai ba ita ta canja ba kar a taSa canja su wajen zuba ma Innaye da Autarta abinci.

"My Dear? Lafiya kuwa? Me ya canja yanayinki lokaci Waya haka?"
Ya tambayeta cikin kulawa da tarairaya, lokaci Waya shi ma yanayin fuskarsa ta Wan canja saboda damuwar da ta shiga duk da bai san ko ta mece ce ba.

Duk yadda ta so wayancewa kasawa tayi, sai kawai ta Sug??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e da cewa
"Uhmmm!"
Sai kuma ta sake wul?ita idanunta kan kuloli biyun da ya siyo a matsayin nata kulolin, canjin wancan da ya kai ma Innaye abinci irinsa sak sai banbancin kala da kuma wani sabo mai zane daban da ya siyo mata don faranta zuciyarta.

A hankali ta mi?a hannu ta Wauki Waya daga cikin kwalin kulolin wanda ya kasance irin nata, reciept na kuWin kular da ke manne a jikin kwalin ta duba, dubu Wari da hamsin ya siya, ita kuwa da yake Oder ne da kuWin kawowa da komai a dubu da ashirin ya iso mata har gida.

Ajiyewa tayi ta Wauki Waya kwalin kular, ita kuma dubu tamanin da biyar take. Ba kunya ba ta sake duba kulolin da suke matsayin na su Innaye sai taga Waya dubu arba'in, Waya dubu talatin da biyar, Waya dubu arba'in da takwas.

Duk da kuWaWen da aka siyo kuloli ukun basu taru sunyi kuWin nata guda biyu ba, ta rasa dalilin da yasa ranta yayi mummunan Saci da ganin kulolin a matsayin na su Innaye.
'Bintu ki nutsu fa... Idan kina son komai ya tafi miki dai-dai sai kin saka siyasa a ciki.'
Wani sashe na zuciyarta ya ankarar da ita.

Wannan tunanin da tayi yasa da sauri tayi ?o?arin kawar da damuwar fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi.
"Uhmmm!"
Ta sake cewa a karo na biyu.
"Allah dai ya ?ara mana imani da lafiya Sweethert. Wallahi yau na ga abubuwa kala-kala masu Waga hankali a asibiti, ni da nake ta damuwar ciwon Innaye sai naga ashe tana cikin nagartattun tsoffi masu lafiya da ?warin jiki sosai a wannan zamani da muke ciki. Allah ya ?ara mata lafiya da nisan kwana."

"Amin ya Allah."
Ya amsa da sauri yana sauke ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali.

"Kuloli sunyi kyau gaba Waya Sweethert. Allah ya ?ara buWi da arziki mai albarka."

"Ameen."
Ya sake amsawa cikin jin daWi da farin cikin da ya gaza Soyuwa a zuciyarsa.

Ledar magani da alluran Innaye da ke ajiye kusa da ita ta janyo ta fara nuna masa tana mishi ?arin bayani a rarrabe.

'Daman arashi akayi, bata yi tsammanin dawowarsu zai zo lokaci Waya ba sai ga shi tana shiga da motarta cikin gidan shi ma direba ya shiga da tasa. Lokacin da misalin ?arfe biyu da minti arba'in da biyar na rana.

A yadda ta saba idan tana aikin safe kuma ta tsara tun tana hanya, idan ta isa gidan ko a gurguje ne za ta samar mishi da lafiyayyen abincin da zai ci idan ya dawo. Tunda ?a'idar lokacin dawowarsa a kullum huWu da rabi ne zuwa biyar na yamma. Sai dai idan da wata ?wa??waran dalili yakan Wauki askis a gurin aiki kamar dai yau Win da ya dawo ba lokacin da ya saba ba, duk da bata san dalilin dawowar tasa a yau ba.

Bayan ta yi masa sannu da zuwa tun a tsakar gidan, jakar hannunsa ta Ofis da wayoyinsa biyu ta karSa ta wuce masa da su ciki, duk da farko so tayi su jera amma ya ce ta shiga ciki yana tafe.

Da kanshi ya dinga shiga da kwalayen kulolin yana ajiyewa a gabanta bayan direba ya gama aje masa su a ?ofar falon har ya gama shiga da su gaba Waya.

Tun ma kafin yayi mata bayanin kulolin, har fuskarta ya cika da matsananciyar fara'a tana jin ?arin matsananciyar ?auna da soyayyarsa a zuciyarta. A tunaninta, gaba Waya kuloli biyar Win ya siyo ne don wanke zuciyarta daga laifin da yayi mata na jiya.

Tun kafin ya ce komai, ta bashi kyakkyawan runguma da sumbata biyu a kuncinsa dama da hagu, ta kuma ?ara da godiya da addu'ar Allah ya ?ara buWi. Ranta bai fara Saci ba sai da ya ware biyu a matsayin nata uku kuma na mahaifiyarsa. Domin a idanunta, da sa?ar wani Sangare na zuciyarta, sai take ga kamar ba asalin kuWaWen kulolin da ya kira na Innaye aka rubuta a jikinsu ba. Kamar dai sun nin-ninka haka, kamar dai an rubuta kuWi kaWan ne domin a ninke ta a baibai. Idan ba haka ba taya za'a ce kuloli masu sau?i haka yanayin zane da ?ayatuwansu har sun fi na ta masu tsada kyau a idanun mai kallo?'

?o?arin kawar da tunanin komai tayi a zuciyarta ta tsayar da hankalinta guri Waya ta cigaba da yi mishi bayanin magunguna da alluran.
"Alhamdulillahi! Duk sakamakon gwaje-gwajen nata sun fito yau. Irin ciwukan da mukai hasashen samu a jikinta ma ba'a samu ba. Ba ta da ciwon suger kuma babu hawan jini, ba ta ulcer, hanta ma da ake tsammanin za'a samu a jikinta duk babu. Ka ga amfanin yin gwaje-gwaje sosai kafin a fara shan magunguna ko?"
Ta ?arasa maganar idanunta cikin nashi tana sakar mishi murmushi.

"?warai kuwa Dr. Bintu."
Ya amsa bayan ya mayar mata da martanin murmushinta.

Hararan wasa da soyayya ta jefe shi da shi kafin ta cigaba da cewa.
"Izuwa yanzu abu biyu zuwa uku dai muka tabbatar suna damun Innaye. ?an typhoid ne kaWan, sai maleria, sai kuma rashin hutu da bata cika samu ba. Duba da yanayin shekarunta, a yanzu ta kai matakin da ba ko wane irin aiki da ta saba yi ada can za ta cigaba da yi ba. Lallai tana bu?atar ta dinga hutawa sosai. Ka ga waWannan su ne magunguna da alluran da zan Wora ta akai, in sha Allahu cikin ?an?anin lokaci duk wani ciwo da yake damunta za mu neme shi mu rasa."

"Ma sha Allah! Allah yasa haka My Dear, don dai Allah ya sani waWannan ?ananun ciwo ce ciwo cen da suke addabar Innaye cikin satittikannan suna matu?ar Waga min hankali."

"Kar ka damu. Za ta warke da wuri in Allah ya yarda."
Ta amsa a fili. A zuciyarta kuwa cewa tayi
'In sha Allahu ta kusa macewa gaba Waya ma kai ka huta nima in huta.'

Ruwan gora me madaidaicin sanyi da tun kafin shigowarsa ta Wauko a cikin frig ta tsiyaya a kofi ta kafa mishi a baki cike da soyayya, kallon ?wayar idanun junansu suke yi cike da shau?i a zukatansu, don haka bai ma san lokacin da ya shanye ruwan ba sai da ya ji ta janye kofin daga bakinshi.

Hannunshi ta kama kamar ?aramin yaro suna tafe zuwa dakinshi tana ba shi labarin wasu dattijai biyu mata da aka kawo asubitinsu, shekarunsu bai kai na Innaye ba amma irin ciwukan da suke jikinsu sam ita ba ta d'auke da su.
"Ka ga wannan ke k'ara nuna mana ba wani gata ko rayuwa a cikin birni ke hana bawa ya kamu da cututtuka ba. Abin ikon Allah ne kawai da jarabawarsa, sai mu k'ara gode ma Allah da ya kawo mana na ta jarabawar da sauk'i. Allah ya k'ara mata lafiya."

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke na k'ara samun kwanciyar hankali da maganganunta. Kafin ya amsa da
"Amin ya Allah My dear. Haka ne kam, na ji dadin maganganunki. Ina tsananin son ki matata..."

"Ni ma ina son ka Mijina."
Ta katse shi da amsar tun kafin ya aje numfashin maganarsa, fuskarta cike da murmushi.

Kamar ko da yaushe in dai ya dawo tana gidan, ita ta taya shi ya rage kayan jikinsa sannan ta shige bandaki ta hada mishi ruwan wanka. A zuciyarta take dariyar yadda ta iya kirkirar zancen an kawo tsofaffin da suka fi Innaye jin jiki don kawai ta kwantar da hankalinsa.
'Yo miye a ciki? A fakaice dai ta isar mishi da sakon ba rayuwa a birni ko kauye ke sa mutum ya kamu da cututtuka ba. Duk da dai ita da kanta takan kiyaye tu'ammali da kayan kauyen da kuma 'yan kauyen don gudun kamuwa da cutuka. In jifa ya wuce kanta ya fada kan ko ma waye, gara su can sun saba rayuwa a haka.'

Ko da ta gama haWa mishi ruwan wanka, kafin ta fice a Wakin sai da ta fitar mishi da ?ananun kayan shan iska da zai saka idan ya fito daga wanka, ta fesa turare, ta ajiye a gefen gadon sannan ta fita zuwa kicin a gaggauce domin samar musu abinda za su ci.

Baba Rabi ta gama rabon abinci kenan ta shiga cikin kicin Win, kamar ko wane lokaci in dai ta shiga a irin wannan lokacin, bubbuWe kular abincin kowa tayi taga yadda aka zuba masa.

Idanunta ?ur akan miyar su Innaye da aka zuba tsokokin nama masu yawa saSanin yadda aka saba sakawa.
"Rabi?"
Ta kira sunanta bayan ta janye idanunta daga kan miyar suna kallon juna cikin ido.

"Na'am Hajiya"
Ta amsa a ladabce.

"Yau hannunki ne ya suSuce kika loda nama haka da uban yawa a miya har aka rasa yadda za'ayi da shi?"
Ta tambayeta tana ?ara tsattsare ta da idanu.

"A'a Hajiya. Kawai dai ji nayi Auta ta ce Innayen ba ta da lafiya, shi yasa nayi sha'awar in Wan ?ara musu naman... kuma ma fa da yanka biyu ne kawai na ?ara kam ukun da kika ce in dinga zuba musu."

Fuska a Waure ta buWe baki za ta daka ma Rabi tsawa ta tuhumi ina ruwanta da ciwon Innaye sai Zulaikha ta sanyo kai cikin kicin Win, bakinta Wauke da siririyar sallama. A hannunta ri?e da kular da aka zuba ma Innaye indomie.

"Barka da dawowa."
Ta faWa a ta?aice, bayan ta yi ma Bintu kallo Waya ta kawar da kanta. Kai tsaye ta nufi gurin ajiye kwanonin wanke-wanke ta ajiye kular hannunta.

"Baba Rabi sannu da aiki. An gama abincin ne?"
Ta tambayi Rabi wacce tun bayan shigowar Zulaikha da kulolin ?irjinta ke bugun tara-tara.

Ko kaWan bata so shigowar Auta da kulolin a daidai lokacin da Bintu take cikin kicin Win ba. A yadda ta so, bayan ta kai musu abincinsu ne za ta Wauko kula da farantan ta shiga da su cikin gidan ta wanke a sirrance kamar yadda ta wanke tukunyar da tayi amfani da ita ba tare da Bintu ta san an dafa ma Innaye indomie ba.

Amma yanzu ganin kular ta san dole Bintu ta tambayi me aka dafa saSanin wanda aka gama girkawa yanzu? Ganin ba ta da mafitar da ya wuce amsa tambayar Zulaikha yasa ta ce
"Eh! Na gama. Je ki, yanzu zan shigo muku da shi..."

"A'a! tunda ga ni mene na wahal da kanki? Sannu da aiki. Bani kawai in wuce mana da shi."
Ta ?arasa maganar idanunta na kan murfin kular miyarsu da ta gani a hannun Bintu, wacce take tsaye kamar mutum-mutumi, sai idanu kaWai take iya rabawa a tsakanin su biyun, fuskarta a tamke ?warai kamar bata taSa sanin wani abu dariya ba.

Tun ranar da suka zo gidan, a cikin wannan kular ake zuba musu abinci. Don haka bata tsaya jiran Baba Rabi da ke harhaWa abinda za ta ce mata ba don ta hana ta Waukar abincin kawai ta ?arasa gaban Bintu ta Wauki kular da aka zuba farar shinkafar, ta mi?a hannu za ta zare murfin kular miyar daga hannun Bintu da sauri ta janye hannunta tare da aika ma Auta wata matsiyaciyar harara.

"Waccan kular da kika shigo da ita yanzu, me aka zuba a ciki?"
Ta jefa mata tambayar cikin fushi tana aika mata da kallon tsana a fili.

Duk cikin dangin mijin nata ta fi tsanar yarinyar, ko don ta kasance a mafiyawancin lokuta tana yi mata abubuwa na gatsali da raini ne? oho!!

"Au! Wai wancan kular?"
Ta mayar mata da tambaya cikin tambaya a raine, da kuma irin salon da ta san Bintun ta masifar tsana. Sai kuma ta Wanyi murmushi tana kallonta cikin ido itama da yanayin kallon yadda ba kya so na ni ma ba son ki nake yi ba.
"Innaye, da kika tafi da ita asibiti ko karyawa bata yi ba kika yasar da ita a wula?ance, ita na saka aka dafa ma indomie da soyayyen ?wai. Bata isa ba ne ko ni Win ban isa in saka a dafa mata bane?"

Ta buWe baki za tayi magana cikin masifa da Waga murya sai ta tuna Hafiz yana gidan, duk da akwai tazara mai yawa tsakanin Wakunansu da kicin Win lallai idan ta ce za ta Waga murya zai iya jiyo ta. A matakin da ta Wauki aniyar Wauka kuwa, har su Innaye su bar gidan a fili dai baza ta taSa nuna mishi wani alamu na tsana da ?iyayyarsu da ke dan?are da zuciyarta ba.

Duk yadda ranta yakai ?ololuwa gurin Saci da tambayoyin rainin da Zulaika tayi mata sai kawai ta Suge da girgiza kai, ta saki ?arfafan ?wafa sau biyu. A wula?ance ta saki murfin kular da ke hannunta ya faWi ?asa sannan ta fice daga cikin kicin Win da sassarfa.

Tana da ?aramin kicin a jikin Wakinta da take amfani da shi ita kaWai, don haka can ta nufa zuciyarta cike da sa?e-sa?en yadda za ta saka aci mata uban Zulaikha la'ada waje kafin su bar garin Abuja, wannan al?awari ne ta Wauka ma kanta.

Fuska a dame Baba Rabi ta kalli Zulaikha ta ce
"Auta Ba kiyi kalar yara masu rashin kunya ba. Saboda Allah me yasa kike son Sata wayon ki da kyakkyawar tarbiyar da nake gani a tare da ke ta hanyar biye ma Hajiya.? Matar yayanki ce fa..."

"Ke baki ga yadda take mana bane Baba Rabi? Don kawai mu ?an ?auye ne sai mu zama ababen wula?anci da tozartawa a gurinta? In dai za ta taya na rantse da Allah ni kuma sai na sayar mata. Allahn da ya halicce mu bai wula?anta mu ba babu wata ?ar adam da zan zauna ta wula?anta mu."
Murfin kular ta Wauko ta rufe ta sungumi kular miyan cikin fushi bakinta a gaba ta fice daga cikin kicin Win.

Tana zuwa falo, suka yi kiciSis da Hafiz shi kuma ya sauko daga sama inda Wakunansu suke. Duk da yadda ?irjinta ya buga daram saboda tunanin yadda ya gaji da buga ?ofa ta ?i buWe masa da safe har ya gaji ya tafi. Ko kaWan bata bari fuskarta ya nuna tsorata ba, sai ma ?ara murtukewa da tayi ta ?ara turo baki gaba kamar zai taSi bango. Ja tayi ta tsaya tana kallonshi kamar yadda yake kallonta.
"Sannu da dawowa."
Ta faWa cikin guna-gunin da ba ta da tabbacin ya ji ko bai ji ba.

A Sangarensa kuwa, da mamaki sosai a fuskarsa yake kallonta. Bai manta yadda jiya ya kora mata kashaidin kar ta kuskura ya sake ganinta a Sangarensu ba. Hallau bai manta yadda ya so ya lakaWa mata dukan tsiya kafin ya fita ofis Allah ya taimaketa ta hanyar kulle ?ofar da tayi ta bar makulli a jiki ba.

Haushin jiya da yau ne suka taso suka ?ara turnu?e shi, don haka cikin tsawa ya ce mata
"Me ya kawo ki nan? Ban faWa miki kar in sake ganinki a Sangaren nan ba...?"

Da sauri ta katse shi tun kafin ya aje numfashin maganarsa
"Ni ma fa ba son raina na shigo nan Win ba. Innaye ce ta ce lallai daga yau ni zan dinga zuwa karSa mana abinci, idan mun gama kuma in kwaso kulolin in shigo da su, idan kuma baka yarda ba, sai ka je ka tambayeta."

"Barka da dawowa Uban Wakina."
Muryar Baba Rabi a ladabce ya sauka a kunnuwanshi.

Harara ya galla ma Zulaikha sannan yaja tsaki ?asa-?asa. ?o?arin sassauta murya yayi ya amsa gaisuwar Baba a mutunce kamar yadda ya saba. Karaf! Idanunsa suka faWa kan sabbin kulolin da ya siyo anan falon, inda ya barsu har lokacin a gurin suke.

Umarnin kwashewa zuwa kicin yayi ma Baba Rabi bayan ya nuna mata waWanda ya siyo ma Innaye, ya kuma gargaWe ta kar a sake zuba ma Innaye abinci cikin tsaffin kuloli saSanin sababbin da ya siyo.

Ko da ya waiga inda Zulaikha ke tsaye, babu ita babu dalilinta. Abinda bai sani ba tun da ya fara amsa gaisuwar Baba Rabi saWaf-saWaf ta fice daga cikin falon.


*******
?abi'a ce da suka taso suka tarar da Innaye a cikinta jiran sallah tun kafin lokacinta ya ?arato. Har yanzu kuma da ta manyanta bata bar wannan kyakkyawan Wabi'a ba, sai ma ?ara ?aimi da tayi.

?arfe shida da minti goma ta shige banWaki ta Wauro alwala. Wuf! Zulaikha tayi ta Wauki flask Win da ake zuba musu ruwan zafi ta fice daga Wakin, daman damar da take jira kenan.

Hatta hijabin jikinta da kusan ko wane lokaci ba ta rabo da shi a jikinta sai a hanya ta sanya. Kai tsaye ta nufi can cikin gidan ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, tana tafe tana kalle-kallen yadda kyawawan shuke-shuken fulawoyi suka ?ara ?awata tsakar gidan, kuma da yake suna samun kyakkyawan kulawa daga mai aiki na musamman da aka Waukar musu, luf-luf suke gwanin ban sha'awa kamar a lokacin damina.

Ko da ta isa ?ofar babban falon, sau Waya ta danna ?ararrawar neman izini kafin ta murWa hannun ?ofar ba tare da jiran izinin shiga daga can ciki ba.

Kasancewar lokaci ne da in dai suna gida su biyun za'a same su cikin nishaWi ne da yanayi na soyayya. Ko a yanzu, suna zaune akan doguwar kujera, fiye da rabin jikin Bintu gaba Waya a jikin Hafiz

7 / 53