RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 53

30K to 33K   out of 157.3K words

mai jiki, bai Sata lokaci ba ya fice daga cikin Wakin.

"Ta ci abinci kuwa?"
Tambayar da Hafiz ya fara yi kenan bayan ya zauna, idanunsa na kan Innaye shi ma yana karantar cigaban da aka samu a lafiyar jikinta.

"Eh! Ta Wan ci, amma ka san bakin babu WanWano, dole cin abincin kaWan-kaWan ne."
Yaya Balira ta amsa mishi.

"Haka ne! Allah ya ?ara sau?i. Yanzu kafin shigowata na duba Chemis Win Habu ban ganshi a ciki ba, sai dai idan ya buWe sai in kira shi yayi mata allura. Yanzu bari a fara ba ta magungunan..."

"Magani kuma Hafiz? Anya baza'a ha?ura da magani da allurannan ba?"
Aunty Ladidi da bata cika magana ba a cikinsu ta faWa idanunta a warwaje. Da alamun har lokacin bata manta labarin da Zulaikha ta basu ba.

Kallonta yayi, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallonsu hannunsa ri?e da ledar maganin Innaye. Yana jin yadda kaso hamsin cikin Wari na Sacin ransa da ya sauka sanadiyyar nasihar da mahaifinsu yayi musu yana ?o?arin dawowa sabo fil a zuciyarsa.

Yaya Balira da ta kasance babba a cikinsu ne ta gyara zama ta fara yi mishi ?arin bayani cikin tausasa kalamai.
"Kayi ha?uri Hafizu, ka kwantar da hankalinka. Kar ka bari ranka ya Saci dalilin maganar da Ladidi tayi. Allah yana ganin zukatanmu ba wai mun raina ?o?arinka da na iyalinka bane.

Amma abu Waya da nake so ka fahimta shi ne, ko da muke mutanen ?auye, daidai gwargwado ka san Baban Yasin (Mijinta) a baya ya Wauke ni munyi zirga-zirgan asibitoci da yawa na cikin Kaduna saboda matsalar haihuwa da nayi fama da shi. Ina yawan ganin idan magani yayi ma mare lafiya ?arfi canja mishi ake yi. Idan kuwa likita ya ?i canja ma mare lafiya magungunan da suka mishi ?arfi shi mare lafiyan yana da ikon ya canja asibiti don ya gana da wani likitan ko warakarshi anan take. Mu kanmu haka mukai tayi har dai daga bisani muka mi?a ma Allah al'amarin, sai daga baya kuma waraka tazo mana daga Indallah.

A lamarin ciwon Innaye ma yanzu kam shawarar da muka gama yankewa kenan, ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kamar yadda na faWa maka da farko, ba don mun raina ?o?arin Bintu bane za mu Wauki wannan matakin. A bayyane yake waWannan magungunan sun yi ma Innaye ?arfi, don haka gobe da sassafe idan Baban Yasin zai fita da mota zamu tafi da Innaye asibitin dutse ko Barau Dikko a cikin Kaduna a sake dubata a canja mata magunguna..."
[12/27, 5:16 PM] Fareeda Abdallah: "Na fahimce ki Yaya Balira. Babu komai, Allah ya kaimu gobe da safen. Ki shirya da wuri sai mu wuce da ita asibitin."
Ya faWa a nutse ba tare da fuskarsa ta nuna Sacin rai ko kaWan ba.

Gaba Wayansu sun ji daWin yadda ya nuna sau?in kai da fahimta cikin ?an?anin lokaci.

"Allah yayi maka albarka Hafizu."
Innaye ta faWa cikin sanyin murya, da alamun ita kanta ta ji daWin amincewar da yayi a sau?a?e.

"Amin Innaye. Allah ya ?ara miki lafiya."
Ya faWa da bayyanannen farin ciki a fuskarsa, sosai yaji daWin saka albarkar da tayi masa. Ko babu komai a yanzu zuciyarsa ta ?ara gamsuwa Innaye bata ?ullace shi ba kan abinda ya faru.

Dukkansu ?a?an Innaye mata sun so su kwana a gurinta amma mahaifinsu ya fatattake su zuwa gidajensu.
"Sai ka ce a garin gaSa-gaSa muke? Ca nake acan Habujan ma Zulai ita kaWai take kwana da ita babu abinda ya faru balle nan gida cike da mutane? Kwanan da za kuyi a gurinta ya isa yasa ko hana Allah ikonshi ne?"

Da sauri duk suka girgiza kai fuskokinsu a dame. Domin ba haka suka so ba, amma baza su iya mishi musu ba saboda tarbiyar da aka Wora su akai. Abinda suka sani ne ko sun tafi gida hankulansu ba kwanciya zai yi ba, Zulaikha ta faWa musu ciwon Innaye cikin dare ne yake tashi gadan-gadan, ba fata suke ba idan wani mummunan abu ya faru da ita a bayan idanunsu fa?

Kamar ya san tunanin da suke yi sai ya ?ara da cewa
"Don haka ku kwantar da hankalinku. Babu abinda zai faru sai alkhairi in Allah ya yarda. Ku tashi yanzu ku koma gidajenku, gobe idan Allah ya kaimu da safe kafin tafiya asibiti sai ku sake neman izinin mazajenku ku zo ku duba ta. Allah ya tashe mu lafiya."

"Ameen Baffa"
Haka suka fice daga gidan jiki a sanyaye bayan sunyi ma Innaye da Abokan zamanta sallama. A hanyar raka su zuwa ?ofar gida da Zulaikha za ta yi ne suka jaddada mata lallai komai dare idan ciwon Innaye ya tashi ta kira wayoyinsu ta sanar da su.

Kamar yadda Innaye ta saba kwana cikin matsanancin zazzaSi da kwankwatsar ?ashi ako wane dare, yau ma duk da bata sha magungunan dare ba haka ta kwana cikin azabar ciwo, kamar ma ya fi na kullum a ganin Zulaikha.

Baffa da yake da turakarsa yana ta safa da marwa yana duba halin da take ciki, sauran abokan zamanta ma ba'a barsu a baya ba gurin zirga-zirga duba halin da take ciki. To abu ne da babu yadda suka iya sai abinda Allah yayi, addu'o'i suka yi mata sosai kafin suka koma Wakunansu.

Baffa da nauyinta yake a kanshi a ?arshe dole ya bar turakarsa ya koma Wakin Innaye, tsawon mintuna goma sha biyu ya Wauka zaune kusa da ita yana tofe ta da duk addu'ar da tazo bakinshi, hankalinshi a tashe. Duk da faWin Mal Bahaushe ciwo idan yaji dare ya fi tashi a iya tsawon rayuwar da yayi da Rahina bai taSa ganin ta yi ciwo makamancin wannan ba. Irin yadda take jan numfarfashi a wahalce tana saukewa ga gurmususu da take yi kamar mai na?uda shi ne abinda ke ?ara Waga mishi hankali.

Ita kuwa Zulaikha tana rakuSe a gefe tana ta hawaye kamar yadda ta saba, hannunta ri?e da ji?a??en tawul da take goga ma Innaye a jiki don rage mata zazzafan zafin zazzaSin da yake jikinta.

Daga bisani Baffa cikakken alwala ya Wauro ya shimfiWa dadduma a tsakar Wakin ya fara jero nafilfili, yana nema mata sau?i da rangwame gurin mahaliccin sammai da ?assai.

Kamar aikin asiri, sai gaf da asubah zazzaSin ya sauka, nannauyan barci ya Wauke ta kamar ko wane lokaci. Ko da Hafiz ya shiga cikin gidan duba jikinta bayan sun fito daga masallaci irin labarin da mahaifinshi ya bashi na tashin ciwon bai ji daWinshi ba ko kaWan.

Ya zaci sau?in da ya gani a yammacin jiya zai Wore, kuma rashin shan maganin dare da bata yi ba ya ?ara saka shi sakankancewa yayi barci hankali kwance. Tunda ai an ce magungunan da take sha ke tayar da ciwon, tunda bata sha ba menene dalilin tashin ciwon a wannan dare?

Haka yai ta sake-sake a zuciyarsa da tulin tambayoyin da ba shi da amsarsu. Ko bayan ficewar Baffa zuwa turakarshi don ya kimtsa zuwa asibitin shi ya kasa ficewa. A falon Innaye ya zauna ya zuba tagumi da hannu bibiyu, ?wa?walwarsa a cunkushe. Ya ma rasa wani irin tunani ya kamata yayi?

A haka Yaya Balira tayi sallama a ?ofar Wakin ta shiga ciki ta same shi zaune cikin damuwar da fuskarsa ta gaza Soyewa.
?irjinta ne ya buga daram! Da sauri ta saki jakar kayan da ke hannunta a ?asa ta ?arasa gurinshi hankalinta a tashe.
"Hafizu me yake faruwa? Ina Innaye?"
Bata jira ya amsa mata ba ta nufi cikin Wakin da sauri, ganin Innaye tana barci ga Zulaikha zaune akan dadduma tana gyangyaWi yasa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta zauna a hankali a gefen gadon tana ?ara kallon Innaye don tabbatar da barcin take yi ko?
Bata daWe da zuwa ba Aunty Rakiya da Aunty Ladidi suka isa gidan. Duk yadda suka so suyi sammakon tafiya asibiti bai yiwu ba saboda dole suka jira Innaye ta tashi barci don kanta, aka tarairayeta zuwa banWaki aka yi mata wanka. Suka shiryata a nutse, tayi sallah a zaune, suka ba ta abin kari ta karya sama-sama kafin suka Wauki hanyar tafiya zuwa asibiti.

?a?an gaba Waya suka so tafiya asibiti, a dole suka ha?ura saboda Baffa ya hana. Daga Aunty Balira sai Hafiz sai Baffa da Innaye da direban da ke tu?a motar suka tafi asibiti.

Kasancewar safiya ce babu go slow a hanya, kuma basu haWu da sharrin ?arfe irinna jiya ba. Nan da nan suka isa asibitin Barau Dikko cikin garin Kaduna. Da yake tafe suke da gogaggen Wan boko Hafiz sai basu sha wata wahala ba, shi ya shige musu gaba gurin yin komai, layi na zuwa kansu aka shigar da file Win su suka samu ganawa da babban likitan da yake aiki a lokacin.

Bayan ta?aitaccen binciken da likita yayi akan Innaye, da kuma yanayin galabaitaccen jikinta da ya gani, nan take ya rubuta za'a basu gado. Sannan ya rubuta takardan gwaje-gwaje kala-kala ya dam?a ma Hafiz.

?aki na musamman Hafiz ya bu?aci a kwantar dasu, kafin ya tafi Sangaren biyan kuWin da aka bu?ata na gwaje-gwajen da za'a yi mata.

Da yake ya saka ma ransa son sanin takamaimai abinda ke haddasa ma Innaye waWannan cututtukan cikin daren shi yasa ko bayan gama Wiban jininta don gwaji, aka Waura mata ?arin ruwa bai bar asibitin ba sai da ya tsaya jiran fitowar sakamako. Wasu sakamakon sun fito a ranar, wasu kuma an tabbatar mishi sakamakonsu sai washe gari za su fito, sannan wani gwajin sai washe gari da safe za'a yi mata.

Nan take direba ya tu?a su zuwa cikin gari bayan ya dubo hotel mai kyau da tsada a wayarsa suna isa ya kama musu Wakuna, shi, mahaifinshi, direba. Kayayyakin da za su bu?ata na kwana Waya zuwa biyu ya shiga babban shagon da ke jikin hotel Win ya siyo musu sannan ya koma ciki. Lafiyayyen abinci mai rai da lafiya yayi musu Oder suka ci sannan kowa a cikinsu yayi wanka ya canja kaya.

Duk yadda yake jin gajiya a jikinshi bai zauna ba, Wakin da Baffa yake ya shiga sai yaga har yayi barci. A hankali yaja mishi ?ofar ya nufi Wakin da ya kama ma direbanshi.

Ko da ya shiga sai ya tarar da shi ya gama cin abinci, yana kishingiWe akan kujera yana sakacen ha?ori. Ganinshi yasa direban mi?ewa tsaye da sauri bayan ya amsa sallamarshi.
"Oga barka da yamma. Allah ya ?ara arziki yaba tsohuwa lafiya. Za mu fita ne?"
Ya ?arasa da tambayar a ladabce.

Ya sani idan za su sake kwana su yini suna yawo a mota da Mal Musa ko a fuska bazai taSa nuna mishi ya gaji ba. Amma adalci shi ne ko da mutum yana maka hidimar da kake biyansa, yadda kake jin gajiya a jikinka shi ma yana ji, rai dangin goro ne. Haka kawai lokaci bayan lokaci yana da kyau ka dinga nuna ma hadiminka shi ma fa Wan'adam ne mai ?anci. Da wannan dalilin yasa shi sakin Wan ta?aitaccen murmushi, ya ce
"Ameen. A'a Mal Musa. Shigowa nayi kawai inyi maka ban gajiya. Fita zanyi yanzu amma ba tare da kai ba, Baffa yana Wakinsa yana barci. Kai ma ya kamata ka huta, sai na dawo."

Cikin fara'a yayi masa a dawo lafiya da addu'ar Allah ya tsare sannan ya mi?a mishi makullin mota. Ya karSa ya fice daga Wakin shi kuma ya cigaba da kishingiWarsa, a zuciyarsa yake jinjina kirki da karamci irinna Ubangidansa.

Ko da ya koma Wakinsa, wayarsa ya Wauka ya kira lambar Aunty Balira ta faWa mishi duk abubuwan da suke bu?ata. Bai Sata lokaci ba ya fice daga Wakin, kasuwa ya shiga ya lodo musu siyayya a wadace. Har ma da abinda bata ce mishi suna bu?ata ba aka loda mishi a bayan mota ya nufi asibiti.

Da yake Wakin da aka kwantar da su kwanciyar mutane biyu ne, shi yasa basu rasa inda za su zuba kayayyakin da ya siyo musu kamar bai san zafin kuWi ba.

"Allah yayi albarka Hafizu. In Allah ya yarda baza ka taSe ba."
Minti Waya biyu kalaman da ke fita daga bakin Aunty Balira kenan, fuskarta yalwace da farin cikin yadda bai taSa nuna gajiya wajen Wawainiya da su ko mahaifiyarsu.

Da fara'a a fuskarsa a amsa addu'ar. Gefen Waya gadon da babu mara lafiya akai ya zauna, yana kallon Innaye wacce tunda aka Waura mata ?arin ruwa da allurai da aka zuba a cikin ruwan barci take yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Bai daWe sosai ba saboda magriba da ta kawo jiki yayi ma Aunty Balira sallama ya fice daga Wakin. Yana hanya, kiran Bintu a karo na uku ya shigo mishi amma bai samu sararin Wauka ba, sai da ya isa Wakin da ya kama sannan ya bi bayan kiranta.

Ringing Win farko ana biyu ta daga wayar ba tare da jan aji ba kamar yadda ta saba.
"My dear..."
Ta kira sunan da take yawan faWa masa da wata irin raunanniyar murya.
"Laifin me nayi?"
Ta sake tambayarsa tub kafin ya amsa da muryar da ke bayyana matsananciyar damuwa.

In ji Mal Bahaushe ya ce me kaza a aljihu ba ya jimirin as! A tsammaninta li?in da ta fara yi ne ya Salle, shi yasa tun da ya tafi jiya da yau ko wayarta ba kasaifai yake Wauka ba. Idan ta ci sa'a ya Wauka kuma ko ya biyo bayan kiran da ta yi mishi kamar yanzu sam ba ya bata wani nutsuwarsa yadda ya kamata.

Tsoron ko asirinta ne ya fara tonuwa har yake ?ullace da ita yasa kawai ta sakar mishi kuka a raunane, irin kukan nan mai bayyana tana cikin matsanancin damuwa da tashin hankali.

"Kiyi ha?uri Sweetheart."
Ya faWa a tausashe.
"Don Allah kiyi shiru, ki kwantar da hankalinki. Kin san kukanki na Waga min hankali."
Ya faWa cikin rarrashi da muryar da ke bayyana damuwa.

A hankali ta fara ?asa-?asa da kukan har tayi shiru gaba Waya, amma bata ce komai ba, sai sauke ajiyar take yi irinna kuka.

"Kin san ko da kinyi min laifi zuciyata baza ta iya jimirin fita daga al'amarinki ba. Kiyi ha?uri, al'amarin ciwon Innaye ne yake Waga min hankali... Tun da muka iso jiya ba ni cikin nutsuwa ta. Jikinta har yanzu baiyi sau?i ba..."

"Subhanallahi. Allah sarki Innaye. Allah ya bata lafiya. Tana shan magungunanta kuma ana yi mata alluran safe da dare kuwa?"
Ta tambaye shi daga can Sangaren.

Har ya buWe baki zai faWa mata gaskiyar abinda yake faruwa sai kuma ya tuna gargaWin da mahaifinsa yayi masa.
'Hafizu, kar ka kuskura ka faWa ma iyalinka an daina ba mahaifiyarka maganin da ta siya mata. Ba don komai ba kuwa sai don za ta ga kamar an raina ?o?arinta da kulawar da ta ba mahaifiyarka ne. Idan kunyi waya kar ka kuskura ka faWa mata ma mun taho asibiti. Ina fatan ka fahimce ni?'

Tunanin wannan maganar yasa shi amsa mata da cewa
"Eh! Ana bata komai kamar yadda kika nuna min. Jikin ne dai har yanzu ba sau?i sai na musulunci, ki taya ni addu'a..."

"Ka kwantar da hankalinka My dear. Za ta samu sau?i sosai in Allah ya yarda, don Allah ka kwantar min da hankalinka. Ya kake so inyi idan ciwo ya kama min kai?"
Ta tambaye shi a shagwaSe. Kafin ya amsa ta sake cewa
"Ka dai san idan kana ciwo ni ce ke jigatuwa ko?"
Ta sake tambayarsa.
"To yanzu ba ni kaWai zan jigata ba My Dear. Har da Babynka Wan wata biyu da yake kwance a mahaifata. Ko za ka so ka zama silar da Wan tayinka zai bi rariya tun kafin ya fito duniya yayi tozali da fuskar kyakkyawan mahaifinsa...?"

"Mmmmme kike nufi Sweetheart?"
Ya katse ta da tambayar muryarsa na rawa.
"Ban... gane ba? Me kike nufi? Kina nufin ke Bintu kina Wauke da Wan tayin cikina a jikinki?"

Ta daWe da sani, shi Win mutum ne mai son yara sosai. Tun kafin suyi aure ya sha faWa mata shi fa yana son yara da yawa, ko da suka yi aure duk sa'adda ba?onta na wata yazo sai ya Wanyi ?orafin har yanzu ?wallonsa bai shiga raga ba? Ya kamata tayi wani abu a matsayinta na likita.

Shi yasa a yau da ta samu tabbacin tana Wauke da juna biyu sanadiyyar amai da tashin zuciyar da ta tashi da shi har ya kai ta ga yin gwaje-gwaje ta a ranta bai kamata ta Soye mishi wannan abin farin ciki da ya daWe yana jira ba.

"Eh My dear. Da gaske nake. Yanzu haka da nake zaune takardun gwaje-gwajen da suka tabbatar min ina Wauke da ciki ne ri?e a hannuna. Ka ce Alhamdulillah..."

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi ala ni'imatihi tatimmussalihat!!!"
Ya faWa a jere muryarsa da karaWin farin ciki tun kafin ta aje numfashin maganarta.
"Na ji daWin jin wannan kyakkyawar albishir Win Bintu. Lallai kin cancanci gwaggwaSar tukwuici a hannuna. Ina ma ace yanzu haka ina tare da ke? Lallai da kin ga yadda ake nuna matsananciyar murna da tarairaya. Na gode, na gode. Allah yayi miki albarka. A yadda na tsara a Wazu ko zan koma Abuja sai jibi, amma saboda wannan kyakkyawan albishir Win da kika yi min gobe da wuri ina nan tafe kin ji Sweetheart? Yanzu faWa min, me kike yi?"

Sai da tayi fari da idanunta kamar yana kallonta, sannan ta amsa a yangace
"Ina zaune ne a tsakiyar gadonka. Zuciyata cike da kewarka Mijina uban ?a?ana."

"Ni ma ina kewarki Matata. Yanzu me kike jin ci?"
Ya sake tambayarta a Wokance.

"Babu komai My dear. Tun Wazu zuciyata tashi take yi, ba na jin cin komai."
Ta amsa tana murmushi.

Da tarairaya da kulawa haWe da matsananciyar ?auna a muryarsa ya fara faWa mata tausasan kalamai.
"Ayya... Yi ha?uri Sweetheart. Sanadin Babyna kike jin haka ko? With time komai zai wuce kin ji? Yanzu dai faWa min, cikin ya fara motsi ne?"

A yanzu kam ta kasa hana kanta dariya, dole ta sake shi amma a sanyaye, da salon jan hankalin wanda aka yi dariyar dominsa.
"Dariya na baki?"
Ya

11 / 53