RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   33 / 53

96K to 99K   out of 157.3K words

dun?ulallen abun ya sauka a cikinshi amma bakinshi ya bushe ?ayau, kamar mai azumi a lokacin da ake tsananin ?wallara rana.

Shi da ba mura yake yi ba, ba kuma kuka ya Wauki lokaci yana yi ba balle ace su suka zama sanadiyyar sha?ewar muryarsa. Ko da ya buWe baki da niyyar tambayar Hafizu da?yar maganar ta fito a dusashe ya ce
"Da gaske ne duk abinda ?ar'uwarka ta faWa? Ka sake ta tun washe garin ranar da kuka bar ?auyen nan?"

Sai a wannan lokacin da Baffa ya jefa mishi waWannan kausasan tambayoyin guda biyu, sannan ya ji kamar an kwance duk wani dabaibayi da aka yi ma bakinsa, ?wa?walwarsa, da jikinsa. Cikin sauri ya motsa ?afafunsa da suka yi masa tsami sosai saboda doguwar tsayuwar da yayi ya zube a ?asa.

Ya sani, laifi ne ya riga da ya aikata shi. Yun?urin yin ?arya don kariyar kai ko kuma musanta abinda ta faWa duk ba shi zai hana tonuwar asirinsa komai daren daWewa ba. Don haka yaga gara kawai ya faWi gaskiya, tare da yi musu gagarumin sadaukarwar da a wancan lokacin da aka Waura aurensa da Zulai a karo na farko ya kasa yi musu.
"Da gaske ne Baffa. Na sani ni mai laifi ne sosai, domin na yi wasa da hankalinku. Amma don Allah kuyi ha?uri ku yafe mana kamar yadda Zulai ta ro?a mana. Sannan tunda yanzu lokacin da nake da damar mayar da ita ya wuce, na rantse da Allah yanzu a shirye nake in karSi aurenta da hannu bibiyu don in faranta muku rai..."

Saukar wasu tagwayen maruka a kuncinsa dama da hagu shi yasa shi rufe baki ba tare da ya shiryawa hakan ba. Duuummm! Shi ne ?arar sautin da yake ji a kunnuwansa na tsawon wasu da?i?u. A idanunsa kuwa babu abinda yake kallo sai gilmawar wasu ?ananun taurari masu tsananin haske da she?i.

Da saurin gaske ya rufe idanunsa don tsoron kar hasken taurarin su illata mishi ?wayoyin idanu. Da farko, ya zaci ya kurmance saboda ?arar duuummm Win da yake ji a kunnuwansa ya daWe bai daina ji ba. Sama-sama kuma sai ya fara jiyo muryar Innaye tana mishi magana kamar daga can nesa kafin maganar ya matso kusa da kunnensa sosai.

A tsorace, ya buWe idanunsa yayi arba da Innaye da Baffa suna tsaye a gabansa suna huci. Da ganin irin tsayuwar da suka yi ba shi bu?atar a faWa mishi daga hannun su wa tagwayen marukan da ya amsa suka fito.

[2/11, 10:54 PM] Fareeda Abdallah: "Hafizu su wa ka mayar sa'anninka?"
Innaye ta sake jefa mishi tambayar da matsanancin Sacin rai a muryarta.
"Mu za ka wula?anta Hafizu? Mu? Mu za ka wula?anta?"
Izuwa wannan lokacin, muryarta rawa yake sosai, zafafan hawaye na sauka daga idanunta. Cikin fushi da gushewar hankali ta sake buWe baki ta ce
"Hafizu Allah..."

Da wani mahaukacin tsawa Baffa ya katse ta
"Keh Rahina kin yi hauka ne? ?an naki za kiyi ma baki saboda abinda bai taka kara ya karya ba?"

Ba Baffa kaWai ba ya shiga firgici da jin kalaman da Innaye ke ?o?arin furta ma Hafiz ba. Aunty Balira da Zulai ma sai da suka mi?e tsaye, hannayensu biyu Wore akai hankulansu a tashe.

Kamar ?aramar yarinya, haka ta fashe da kuka zuciyarta na ?una da raWaWi
"Ya zanyi Malam? Shin akwai inda na ragi Hafizu a tarbiyya ne da zai min wannan mummunar sakayyar? Ya zanyi?"

Hannayenta biyu ya ri?e ya ja ta ya zaunar akan kujera. A tausashe ya fara mata magana
"Kiyi ha?uri. Hannunka ba ya taSa ruSewa ka yanke ka yar. Ki yafe masa, ita kuma Zulai mu cigaba da yi mata addu'ar dacewa da wanda ya fi shi alkhairi."

Hannayenta ya saki ya koma gurin Hafizu da kallo Waya za a mishi a fahimci ba ya cikin hankalinsa.
"Ka je, je ka Hafizu. Babu komai ai, wani zamani ne Allah ya kawo mu da kuyanga take haifar uwargijiyarta. Je ka, mun sallama, mun kuma yafe maka. Allah ya haWa fuskokinmu da alkhairi."

Yana gama faWin haka ya koma kusa da Innaye ya zauna, tafukan hannayensa biyu yasa ya rufe fuskarsa. Kamar yana kuka, amma a zahiri ba kukan yake yi ba, nauyayan ajiyar zuciya yake ta sassaukewa akai-akai. Ba ya ko son ganin fuskar Hafizu, shi kanshi in banda ?arfin zuciya da mazantaka babu abinda zai hana shi furta mummunan kalami ga Hafizu kamar yadda Innaye tayi niyya.

Hankalinshi a tashe, maWaukakin tashin hankali irin wanda tunda ya zo duniya bai taSa shiga kwatan-kwacinsa ba. Da rarrafe, ya fara muskutawa da nufin ?arasa gurinsu Baffa a fusace Aunty Balira ta dakatar da shi.

Hannunsa ta kamo, ta mi?ar da shi tsaye a fusace, yana waigen su Baffa yana cijewa a haka ta ja shi har sai da ta fice da shi daga cikin Wakin. Bata ?yale shi ba sai da ta kai shi har gurin motarsa.

Direba da tun Wazu yake jiran fitowarsa yana ganinsu ya buWe ?ofar, tura shi ciki Aunty Balira tayi sannan ta cusa kanta cikin motar suna kallon juna
"Kayi ha?uri. Mu kam su kaWai muke da, ba mu da makwafinsu a wannan duniyar. Gara kai, ko da sun mace kana da Tauraruwa Bintu da gudan jininka Aadilu. Kaje kawai, domin cigaba da ganinka kaWai ya isa yasa zuciyar Innaye da Baffa bugawa. Mun sallama ka ga Bintu Hafizu."

Fuuuuu ta wuce zuwa cikin gidan ba tare da ta saurari ko zai ce mata wani abu kamar yadda taga bakinshi na motsi ba.

A Sangarensa har ya yun?ura zai bi bayanta, sai kuma ya tuna wasu daga cikin maganganunta gaskiya ta faWa. A yadda ya Sata ma Baffa da Innaye rai lallai ya kamata ya basu iskar da za su huce ko na kwana Waya ne.
"Mu je."
Ya faWi haka ga direba da?yar! Sannan ya janyo ?ofar motar ya rufe, ya lumshe idanunsa ya jingina da jikin kujera, yana jin yadda kanshi ke wani irin matsanancin sarawa kamar zai faWo.


****** ******


Kwanaki bakwai da suka biyo baya wasu irin zafafan kwanaki ne suka kasance ga Baffa da Innaye da Aunty Balira. Duk da labarin mutuwar auren ya bazu ga sauran dangi, amma waWannan mutane uku su ne waWanda al'amarin yafi yi wa mugun dukan da in banda Allah ya kiyaye tabbas da sun samu matsala a lafiyarsu.

Innaye da Baffa jininsu ne yayi mummunan hawa, gara ma Innaye daman an san tana da hawan jini, shi kuwa Baffa da ba'a taSa sanin yana da shi ba sai yanzu Allah ne ya tsare shi amma da ya kamu da cutar mutuwar Sarin jiki.

Kasancewar yanzu an samu gagarumin cigaba a asibitin ?auyen, duk ranar litini da talata da laraba, akwai babban likita da yake zuwa daga kaduna ya duba marasa lafiya. Kuma an zuba ma'aikatan jinya ?wararru a asibitin, cikin hukuncin Allah da taimakon wannab likitan na kyawawan magunguna da ya rubuta musu, da kuma nasiha da tunatarwa kan muhimmancin yarda da ?addara daga bakin babban malaminsu Zulaikha Baffa da Innaye har ma da Aunty Balira suka cigaba da rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Kaso sittin da biyar na damuwarsu ya ?aura, musamman ganin yadda Zulai ita da kanta take iya ?o?arinta wajen rarrasarsu da kalaman kwantar da hankali.

A cikin waWannan kwanaki bakwai, zuwan Hafizu sau uku ?auyen, amma sam ko kusa ya kasa samun yadda yake so. Lallai wannan shi ne BAYAN TIYA AKWAI WATA CACA. Sa'adda ya yanke ma kanshi shawarar rabuwa da Zulaikha salin-alin don samun kwanciyar hankalinsa da na iyalinsa ko kusa bai hango ma kansa faruwar wannan ?alubalen ba.

Shi dai kam Allah ya sani ko na da?i?a Waya bai taSa jin soyayyar Zulai a zuciyarsa ba. Kuma tun da aka Waura aurensa da ita ya shafe kwanaki biyu ne cif cikin zazzafan tunanin ta yadda zai iya fara gudanar da rayuwar aure tare da Zulai.

Bai hango ma kanshi zai iya ko da kwatantawa ba. A ganinsa, zaman aure da Zulai zaluntarta kawai zaiyi ?arara, ba ya son ta, Bintu ita ce zaSin zuciyarsa. Ta yaya zai iya kwatanta adalci a tsakaninsu? Ya gama ha??a?e ma kansa zama da Zulai tamkar jefa kansa a halaka ne.

Sake tunawa da babu Wa'a ga abokin halitta wajen saSa ma mahalicci yasa shi rubuta ma Zulai takardar saki bakinshi ?anin ?afarshi. Kuma ko a yanzu, baiyi da na sanin sakin Zulai ba, domin har yanzu shi ba ya jin sonta a zuciyarsa.

Amma kuma irin gagarumin farin cikin da ya gani a fuskar iyayensa, lokacin da suka je Fa?o shi da Zulai, yasa shi ji a ransa lallai zai iya yarda a sake Waura mishi aure da ita su zauna a wani gida daban ba tare da sanin Bintu ba ko don Worewar faffaWan farin cikin da ya gani a fuskar iyayensa.

Ko da Zulai bata tona asirin abinda ke faruwa ba, shi da kanshi zai bayyana abinda ke faruwa idan lokacin da ya tsara yayi, cikin hikima da iya magana ta yadda al'amuran baza su taSarSare haka ba.

Shi yanzu ta ina zai Sullo ma wannan al'amari? Sai da yayi kwanaki huWu a Kaduna kafin ya koma Abuja saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki, ya san ko ya koma Abuja Bintu, Wansa, da gurin aikinsa da sauran abokan arziki baza su taSa samun nutsuwarsa ba. A cikin kwanaki huWun da yayi a Kaduna zuwanshi Fa?o sau biyu, ya koma Abuja a daddafe cike da damuwa yayi kwana uku sannan ya sake tafiya Fa?o, nan ma dai babu wani cigaba.

Gaba Waya iyayen sun ?i sauraransa, duk yadda yake tunanin girman al'amarin ya wuce haka. Ko da yayi tunanin bi ta hannun ?annen Baffa su Baba Abubakar su ma gaba Waya sun ?i masa hannu. Haka ma ?an'uwan Innaye sun ?i sauraransa.

A zuwansa na huWu ne ya tara Aminan Baffa da waWanda yasan Baffa yana jin maganarsu har da ?wallarsa ya ro?i don Allah su shige mishi gaba wajen sasanta shi da iyayenshi.

Sun yi mishi faWa sosai kamar za su ari baki. Shi dai kanshi yana ?asa, sai ha?uri yake cigaba da bayarwa yana sharar ?wallah, tunda matar na tuba ba ta rasa mijin aure.

A ?arshe Mal Liman ya kira Baffa a waya ya ro?e shi alfarman ga su nan zuwa gidan, yana so zaiyi magana da su shi da Innaye. Baffa zai musa Mal Liman ya haWa shi da Baba Lurwanu a wayar, a dole ya amince da ziyarar tasu.

Ko da ya gansu tafe da Hafizu baiyi wani mamaki ba,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? gaba Wayansu suna zaune ne a falon Innaye saboda ya fi girma. Hankalin Hafiz bai ?ara tashi ba sai da yaga yadda Baffa da Innaye suka ?ara ramewa sosai a cikin kwanakin, kuma wani abu da ya lura shi ne sam ba sa ko ?aunar kallonsa, a Wazu, matso ?wallar dole yai tayi a gaban su Mal Liman, a yanzu kuwa kukan na gaske yake yi.

Hankalinshi ba ?aramin sake tashi yayi ba ganin duk irin nasiha da kyawawan kalaman da aka yi ta faWa ma su Baffa sun ?i cewa komai. Har dattijan suka gama duk maganganu da nasihar da za suyi, suna ?o?arin rufe taron da addu'a. Baffa bai ce komai ba, balle Innaye da tun Wazu fuskarta ke lulluSe cikin hijabi.

"Baffa, Innaye, don girman Allah ku yafe min. Na san na aikata kuskure mai girma a gare ku, bazan sake ba in Allah ya yarda. Kuma a shirye nake a sake Waura min aure da Zulai in ri?e ta..."

Da sauri Baffa ya katse shi da cewa
"Hafizu, a madadin Rahina zan ari bakinta in ci mata albasa. Mun yafe maka. Amma daga yanzu, zancen aure tsakaninka da Zulai ya haramta har abada, kar in sake jin ta daga bakinka. Ina fatan ka fahimce ni?"

"Na fahimta Baffa."
Ya amsa jikinsa a sanyaye.

Godiya Baffa yayi ma dattijan da Aminansa sannan Mal Liman ya rufe taron da addu'a. Bayan shafa fatiha suka fice daga Wakin Hafiz ya bi su a baya yana ?ara yi musu godiya. Ko da ya koma cikin gidan, ya zaci ko Wan kaWan ne zai ga canji a fuskar Baffa da Innaye, sai yaga ba wani canji.

Bayan kashaidi mai girma da Baffa ya kora mishi cikin Sacin rai akan kar ya kuskura ya sake tattaro mishi mutane kan matsalar da shi kaWai ya jaza ma kanshi ficewa yayi daga falon Innaye yana jan ?aramin tsaki.

Ita kuwa Innaye ko kallo bai isheta ba, mi?ewa tayi daga falon ta fice tsakar gida, don ma kar ta shiga Waki ya ce zai bi ta da wani magiyarsa na banza da wofi. Ba komai yake ?ara Sata mata rai da lamarin ba face idan ta tuna yadda Hafiz Win yayi wasa da hankalinta, tsawon watanni tana harhaWa mishi tsaraba da abubuwa da yawa kan cewa ya kai ma Zulaikha ashe sam ba sa tare da juna.

Don tsabar ya raina ta har yana zuwa da matarsa tana ?ara jaddada mata lallai suna zaune lafiya da Zulai. In dai Wan da ta haifa a cikinta zai iya yi mata irin wannan rainin wayau wanene ma a duniya bazai raina ta ba? Babu!

Tabbas ta yafe ma Hafizu kamar yadda Baffa ya nema, amma ba ta ji a ranta ko can gaba za ta iya sakewa da Hafizu ta yarda da shi kamar yadda suke a baya. Abu ne da bazai taSa yiwuwa ba.

Haka Hafiz ya ?araci zamansa a Wakin ya fito yayi musu sallama ita da sauran matan gidan duk zuciyarsa a jagule. Fatan Allah ya kiyaye hanya suka yi masa ba wani walwala da ?auna irin ta da a muryoyinsu ya fice yana jan ?afafu.

Ko da yaja motarsa kamar zai kai ma Aunty Balira ziyara, amma sai ya tuna yadda suka rabu baram-baram a wancan zuwan nasa, da kukanta har tana mishi Allah ya isa kan Waukar ha??inta da yai tayi yana ce mata lafiya ?alau suke zaune da Zulai.

Anty Ladidi da Anty Rakiya kuwa tun da suka haWu a gidan Baffa ya gaishe su babu wacce ta amsa mishi ko kusa baiyi gigin zuwa gidajensu ba, ya san idan ya je duk munin abinda suka yi mishi shi ya siya da kuWinsa.

Haka yabar garin Fa?o zuciyarsa cike da sa?e-sa?en sabbin hanyoyin da ya kamata ya bi don daidaitawa da iyaye da ?an'uwansa.
"To Alhaji ina ga me zai hana tunda duk an fahimci juna a Waura auren kawai a wuce gurin?"

Da fara'a sosai a fuskar Abba Lurwanu, Kamal, Alhaji Musa suka Waga fuskokinsu suna kallon Baffah.
"Da gaske kake yi Malam Aminu?"
Abba Lurwanu ya jefa ma Baffa tambayar don kore tantama.

?an muskutawa Baffa yayi, kafin ya kalli ?an'uwansa uku da Yayyen Innaye biyu da Malam Liman da su ma fuskokinsu ke bayyana farin ciki da nutsuwa da jin kalaman bakinsa. Sai kuma ya sake mayar da hankalinsa kan su Abba Lurwanu.
"?warai kuwa. Da gaske nake yi. Tunda dai duk na faWa maka muhimman abinda ya kamata ku sani dangane da Zulai, kuma kuka ce duk waWannan ba matsala bane. Wanda ke da alhakin aurenta ya rantse min da girman Allah shi ko a matsayin bazawara take yana son ta a haka, kuma zai ri?e min ita tsakani da Allah. To me za'a jira?

Kuma don yin kitso da ?war?wata a gabanku na kira yarinya na tambaye ta ta amince da auren Kamalu? Ta nuna kunya da murmushi wanda a gurinmu babbar alama ce ta amincewa.

Muhimmin abu kuma da fiyayyen halitta SAW ya umarcemu da yi kafin mu bada auren ?a?anmu shi ne bincike, kai da na yarda da kai Wari bisa Wari ka tabbatar min da nagarta da ingancin halayen wannan yaro. To me za'a jira bayan haka kuma? Ai ina ga kawai a Waura auren kafin ku tafi, ko zuwa nan da sati biyu ko uku sai ta tare a Wakinta in sha Allah.

Saboda mu kanmu abun ya zo mana bagatatan ne, bamu shirya komai na aurenta ba..."

"Alhamdulillah! Ma sha Allah! Baffah na gode, na gode, Allah ya saka da alkhairi. Ubangiji ya ?ara lafiya da nisan kwana. Ni Wallahi auren Zulai ma da za'a bani a sau?a?e haka ya fiye min komai, ita Win kawai nake bu?ata. Ba sai kun wahalar da kanku wajen siya mata komai ba."
Abban Imamu yayi maganganun da matsananciyar farin cikin da ya gaza Soyuwa a fuskarsa.

Ganin komai yake yi tamkar a mafarki. Sai ga shi cikin lokaci ?an?ani Alhaji Musa ?anin mahaifinsa ya zaro bandir na dubu Wari daga Aljihunsa, Abba Lurwanu ya ?ara wata dubu Warin akai suka zama dubu Wari biyu. Nan take aka mi?a ma Baba Abubakar a matsayin sadakin Zulaikha. Suka tashi daga zaman da cewa idan aka idar da sallar azahar sai a Waura auren, tunda a lokacin ?arfe goma sha biyu da rabi ne na rana.

Ko da labarin halin da ake ciki ya iske Mummy Saudah da Hajja a cikin gida Wakin Innaye zubewa kawai sukai goshinsu a ?asa suna godiya ga Allah. Bayan sun mi?e tsaye kuma Hajja ta karkace kai ta ri?e hanci ta fara rangaWa wata ?a??arfan guda kamar yarinyar mace.

Daga bisani kuma ta fara rera wa?a irin tasu ta mutanen da tana ?an raye-raye. Innaye dai tun tana kawaici tana Wan murmushi har ta sake ta fara dariya sosai. Cikin ?an?anin lokaci, Wakin Innaye ya cika da abokan zamanta da yaran gida, matan ma?wafta suna yi mata Allah ya sanya alkhairi.

Mummy Saudah kuwa uwar Wakin Innaye ta shige ta ciro wayarta a cikin jaka ta fara latso lambar ?an'uwa da abokan arzikinta tana faWa musu za'a Waura auren Baban Imam yanzu da bayan sallar azahar.
"Haba Hajiya Saudah? Wani irin aure ne haka na bazata babu ko gayyata? Ko sadaka aka bashi?"
KaWan kenan daga cikin ire-iren tambayoyin da mutanenta suke mata suna mamakin al'amarin.

"Tsaleliyar yarinya ce Waya tamkar da miliyan. Ba sadakarta aka bashi ba, shi da kanshi ya gano ta ya nace yana so, da yake dai iyayenta dattijan ?warai ne shi yasa daga zuwa tambaya suka ce za'a Waura aure nan da sati biyu sai ayi biki."
Amsar da take basu kenan, da matsananciyar murna a muryarta.

Ko a wannan

33 / 53