RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   30 / 53

87K to 90K   out of 157.3K words

kuma bata saba saka su ba. Don haka ta nemi guri ta adana akwatin, ba tare da tunanin ranar da za ta iya saka Waya daga cikin kayayyakin ba.

Kwanaki bakwai na cika cif! Da kanshi ya samu Mummy a Wakinta ya sanar da ita ya amince.

"To Madallah! Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Sai ka dage kayi ?o?arin neman soyayyarta..."

"Soyayya kuma Mummy? Sai kace wani ?aramin yaro?"
Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.

Da?uwa tayi mishi da ?an yatsunta kafin ta amsa mishi da
"A'a kai ka yanke ma ?asa cibiya saboda tsufa Baban Imam! To ina tabbatar maka idan baka nemi soyayyarta ba baza ta taSa aurenka ba, kana zaune garin kallon ruwa kwaWo zaiyi maka ?afa. An faWa maka irin waWannan kyawawan yaran masu nutsuwa ana sake da su ne? Uhmmm! Ka zauna nan dai, sai dai kaji wufff! Wani ya yi awon gaba da ita..."

"Haba Mummy... wannan fa kamar kina min baki ne. Bayan kuma ke da kanki kika kwaWaita min aurenta a raina."

"Eh! Duk da haka kuma ai ban ce zan tilastata ta so ka ba. Idan kana son ta ka zubar da duk wani girma ka nemi soyayyarta, na faWa maka."

Da haka suka rabu da Mummy, ya fice daga Wakin yana tunanin shi ta ina ma zai fara?
Bayan Sata hankalin dare da yayi yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin kwarkwanta notikan Autar Innaye cikin kwanaki ?alilan. Mataki na farko da ya fara bi shi ne karSan lambar wayarta ta hannun Karima.

"Yaya?"
"Lafiya kuwa?
"Allah yasa dai ?anwar tawa ba laifi tayi ba?"
Ta jera mishi tambayoyin a firgice.

"Kin shiga uku da sa'ido Karima. To tambaya zanyi mata akan Imam."

Har za ta sake jefa masa wata tambayar, wani Wan tunani da tayi kuma yasa ta sakin murmushi. Katse kiran tayi, cikin ?asa da minti Waya ta tura mishi lambar Zulaikha, a ?asan lambar ta ?ara da
"Allah yasa mu ji alkhairi Yayana."

Dariya kawai yayi, ya amsa addu'ar a fili amma bai mayar mata da martani ba.


******


Sannu a hankali cikin kwanaki ?alilan sha?uwa mai ?arfi ya shiga tsakanin Abban Imam da Umman Imam. Kamar yadda Zulaikha take kiranshi shi ma yake kiranta, amma ?arfin sha?uwar tasu ta fi a waya, gurin chatting da kuma kiran da yake yawan takura mata da shi da cewar ya kira ne suyi hira, yana gidan ko ba ya gidan.

A cikin kwanakin ya hana ta da zuciyarta sakat! Duk inda ta bi da tunaninsa ma?ale da ita, saboda yadda yake yawan sakota cikin al'amuransa. A cikin hirarrakin da suke yi, cikin hikima ya bata labarin kaso saba'in cikin Wari na rayuwarsa.

Yanzu har an kai matakin da idan ya tafi gurin aiki kafin ya dawo zai kira ta ya faWi abincin da yake so ta dafa mishi. Ita kuma bata taSa ce mishi a'a ba, yana dawowa zai tarar da abinda yake so an jera mishi a dining Win Sangarensa. Sai dai ba ta taSa yarda ta ?etara iyakar addininta wajen mu'amala da shi, a ta?aice ma, ta fi sakewa da shi suyi hira sosai ta waya, a fili ba ?aramin kunyarsa take ji ba.

Tana zama a inda yake suyi hira ne kaWai idan su Mummy suna gurin, duk yadda yaso su dinga keSewa ta ?i bashi damar hakan. Shi kuwa bai takura ta ba, ko a hakan ma ya gode, kuma kan tafe kan isa watarana jariri ango ne.


******

Duk yadda ya so ya yakice tunaninta a zuciyarsa ya kasa. Ga wani matsanancin ciwon kai da yake ta addabarsa tun da asubah. Har ya Wauki jakarsa ta zuwa wurin aiki ya ajiye, ko takalmin ?afarsa bai samu sararin cirewa ba ya faWa rub da ciki a kan gado, ?afafuwansa na lilo a ?asa.

Hannunsa ya laluba ya janyo filo guda Waya ya Wora kansa, sannan ya sake Wauko wani filon ya kifa a kansa. Lumshe idanu yayi, a zuciyarsa yake ta addu'ar Allah ya kawo barci ya Wauke shi ko na awa Waya ne.

Cikin hukuncin Allah kuma sai addu'arsa ta karSu. Barcin ya Wauke shi, amma irin rikitaccen barcinnan mai tafe da wasu irin birkitattun mafarkai. Kamar dai yadda ya faru da shi cikin dare, wani al'amari da tun bayan rasuwar marigayiya da ya tattara batun aure ya ajiye gefe Waya bai sake faruwa da shi ba sai yanzu.

Yanzu Win ma kuma akan Zulaikha, Aunty Zulan da duka-duka tsawon lokacin da ya san da wanzuwarta a duniya basu taka kara sun karya ba. Haka ya farka a firgice, ko da ya fahimci abinda ya sake faruwa a karo na biyu tsakanin daren jiya zuwa yanzu wani matsanancin kunya ne ya lulluSe shi.

Filon da ya Wora a kanshi ya janye ya rungume tsam-tsam a ?irjinsa, ya janyo lallausan bargon da ke ajiye a gefen gadon ya lulluSa har kansa. ?ara matse filon yayi, zuciya da gangar jikinsa cike da wani irin matsanancin shau?i da son aure ?arara.

Shi kaWai, ya kwaSe fuska kamar zai saka kuka. A hankali ya ce
"Na shiga uku, Allah na tuba ka yafe ni. Wannan yarinyar za ta lalata ma Mummy Wa."

Shi kaWai, yayi ta juyi akan gadon yana ?ara jin yadda sabon al'amarin ke ?ara amsuwa a dukka sassan jikinsa. Ga kansa da yake matsanancin ciwo har lokacin bai sassauta masa ba. A jejjere yake ta sauke ajiyar zuciya. Da?yar ya yun?ura ya mi?e ya nufi banWaki, ko da ya tsaya a gaban madubi, sai yaga idanunsa sun yi ja sosai.

KaWa kai kawai yayi hannunsa Waya dafe da mararsa yana tafe a hankali har ya shige banWaki. Ruwan sanyi ya sakar ma kansa da tsammanin zai samu sassauci a yanayin da yake ciki, ashe bayan tiya akwai wata cacar, yana gama yin wankan kuma ya fara rawar Wari. Alamun zazzaSi na shirin kawo masa farmaki.

Da?yar, ya iya janyo Waya daga cikin rigunan wanka masu kauri da suke ajiye a banWakin ya saka a jikinsa, ya lallaSa a hankali ya fice daga bayin. Kan gadon ya sake komawa ya ?udundune jikinsa gaba Waya da bargo, ha?oransa sai haWuwa suke gaf-gaf.

Ya Wauki tsawon lokaci a cikin wannan hali yana ta jan duk addu'o'in da suka zo zuciyarsa. Hankalinsa a tashe, ga shi ya kasa mi?ewa tsaye balle ko waya ce ya Wauka ya kira cikin gida a kawo mishi Wauki.

Sannu a hankali kuma sai barci ya fara fisgarsa, haka yayi barcin a jigace, da yake akwai bashin barci a idanunsa fiye da awa Waya yana barci sannan ya farka. A lokacin kuma zazzaSin ya sauka, zufa ya lulluSe gaba Waya jikinsa.

Hamdala yayi sannan ya janye bargon daga jikinsa ya mi?e tsaye, gurin kayansa ya nufa ya Wauki wasu kayan marasa nauyi ya canja. Ko da ya kalli agogo, ?arfe goma sha Waya da kwata ne na safe.

Mai ya shafa sama-sama ya fesa turare. Ya yaye zanin gadon da ke shimfiWe akan gadonsa ya canja wani, sannan ya sake hayewa kan gadon ya kwanta bayan ya Wauki wayarsa.

Har ya lalubo lambarta zai kira sai kuma ya yanke shawarar bari ya fara dubawa ko tana Online. ?wa??warar magana yake so suyi guda Waya, tsakanin jiya zuwa yau irin abubuwan da suka faru da shi sun bashi tsoro, bai san idan ya cigaba da jan lokaci yana lallaSata me zai iya faruwa a gaba ba.

Gara kawai ya fito fili ya faWa mata halin da zuciyarsa take ciki game da ita. Yana da kyakkyawar ya?inin in sha Allahu za ta fahimce shi, za kuma ta bashi damar da yake bu?ata, ayi komai a gaggauce a wuce gurin kafin shaiWan ya jefa shi a halaka.

"Hi Beb!"
Ya fara tura mata, zuciyarsa cike da fatan tana kusa da wayar, ya sani in dai taga sa?onsa za ta amsa mishi a gaggauce.

Minti biyu tsakani ya tsura ma suna da lambarta idanu kafin yaga ta buWe sa?on, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga alamun tana typing daga can Sangaren.


"Abban Imam! Ya aiki? Fatan ka isa Ofis lafiya?"

"Ban fita ba fa, ba ni da lafiya Wallahi. Har na Wauki jaka kawai na ajiye na koma na kwanta."
A ?arshen sa?on, ya ?ara da hoton kan gwaigwai (Emoji) mai nuna alamar shagwaSa, da mai nuna zama abin tausayi, da mai kuka ya tura mata.

Mamaki ne ya Wan kamata, domin tun sassafe suka yi waya, bayan gaisuwa da tambayar yadda ta wayi gari ya tabbatar mata a ranar bazai karya a gida ba. Zaiyi sammakon tafiya Ofis ne, akwai wasu muhimman ayyuka da bai ?arasa jiya ba, yau zai ?arasa ya tura su Lagos.

Da damuwa a fuskarta kamar yana gabanta ta ce
"Subhanallahi! Me yake damunka Abban Imam?"

"Ke ce!"
Ya amsa mata kai tsaye, ba tare da wata kwana-kwana ko Soye-Soye ba.

Da mamaki sosai ta tura mishi da kan gwaigwai na zare idanu. Sannan ta ?ara da rubuta mishi
"Ni kuma?"

"Eh"
Ya sake amsawa, sannan ya tura mata da alamar zuciya mai motsi.

"Allah sarki ni... Me nayi kuma?"
Ta aika mishi da tambayar. Acan Sangarenta, sake gyara kwanciya tayi akan katifar Hajja tana ?ara ri?e wayar ?am-?am a hannunta. Ta rasa dalilin da yasa duk cikin mutanen da take mu'amala da su lamarin Abban Imam na musamman ne a zuciyarta.

Ko a waya idan suna magana, ko kuma idan suna chatting, irin yadda yake riritata, yana nuna mata ita Win ta musamman ce. Yana mata raki da shagwaSa-shagwaSa kamar wani Imam, ita kaWai ta san irin yanayin da take ji a jikinta. Bakinta bazai taSa iya fasalta irin yadda take ji ba, shi yasa ako wane lokaci cikin jin kunyarsa take. In dai ba akwai su Mummy a gurin ba gaskiya ba ta jin kunya zai barta ta iya sakewa da shi suyi magana ko da na minti biyar ne kacal.

Amma a waya, ko kuma ta kafar sadarwa, tunda ba ganin idanun juna suke yi ba shi yasa har take iya sakewa da shi suyi hira haka.
[2/6, 12:04 AM] Fareeda Abdallah: "Kin hana ni nutsuwa Beb! Kin hana zuciyata samun nutsuwa tun sa'adda na fara yin tozali da kyakkyawar fuskarki. A yanzu kuma Wan barcin da nake samun yi raba da rabi ma kina neman hana ni. Don Allah ki barni in huta mana Beb."

?urum! Doguwar sa?onsa ya faWo cikin wayarta. Jikinta na Wan rawa ta buWe, domin ko da ta ji shi shiru, kusan mintuna biyar bai ba ta amsa ba. Tayi tunanin ko ya sauka ne.

A yanzu da sa?onsa ya shigo da sauri ta buWe don jin laifin me tayi masa? Ko da ta gama karanta dogon sa?on, jikinta ne gaba Waya ya Wauka Wummm! Sannu a hankali ta Wora lumshe idanunta.

Sai a yanzu ta ?ara zurfafa tunaninta akan irin yanayin da take ji akan Abban Imamu. Duk da a iya tsawon rayuwarta bata taSa faWawa cikin kogin son wani mahaluki a faWin duniya ba. A yanzu kam ko rantsuwa tayi babu kaffara wannan yanayin da take ji a jiki da zuciyarta ba komai bane face alamomin So.
"So dai?"
Tayi ma kanta tambayar a fili tana mamaki.

"So kuma? Wa ake so ko kuma wa yake so?"
Hajja da fitowarta kenan daga banWaki zancen da Zulaikha tayi ya dira a kunnenta tsulum ta saka bakinta.

"Hajja ba fa magana nayi ba... zancen zuci ne kawai ya fito fili. Wani labari nake karantawa a facebook ya Wauki hankalina."
Ta amsa ma Hajja da sauri tana ?o?arin buWe wayarta da taji ?arar sa?o ya sake shigowa.

"Beb! Baki ce komai ba... Ki agaza ma ?an Mummy kar kiyi kisan kai... Da gaske nake yi fa..."
Sa?on da Abban Imam ya ?ara turo mata.

Lura da tayi shau?in da take ji na Soyayyar Abban Imamu zai iya saka ta yanka ihu a Wakin Hajja, sawunta a likkafa ta sauka akan gadon.
"Hajja ina zuwa, ki gama shiryawan zan dawo yanzu in lallaSe miki kan."
Ta fice da sauri tun kafin Hajja ta amsa.

Sai da ta shige Wakinta, ta mayar da ?ofar ta rufe, ta jingina da jikin ?ofar sannan ta iya ba shi amsa
"To ni me zan ce? Ni dai babu ruwana... Kar ma ka bari wani ya ji wannan wasar da kake min."

"Wallahi, Summa tallahi ina son ki Zulaikha."
Ya tura mata da sauri sa?onta na isa gare shi.
"Da gaske nake yi, ina bala'in son ki."
Ya sake tura mata.
"Don Allah, don girman Allah kar ki ce min bakya so na."
A karo na uku ya sake tura mata.
"Na sani akwai tazarar shekaru masu Wan yawa a tsakaninmu, amma na miki al?awarin zan so ki, in riritaki, in shagwaSa ki, in ji da ke, har ma fiye da saurayin da kike tunanin aura."
Sa?on shi ya sake sauka a karo na huWu.
"Ki taimakeni Beby ki so ni, ko da rabin son da nake miki ne. Ke ni ko bakya jin so na a yanzu, ki bani dama don girman Allah in koya miki so na. In Allah ya yarda baza kiyi da na sani ba."

Tsananin yadda maganganunsa suka kassara mata sassan jiki, yasa bata san sa'adda ta zame zuwa ?asa ba. Saboda jin ?afafunta tayi kamar an zare mata duk wasu ?asusuwa da suke cikinsu. Ta karanta sa?on, ta ?ara maimaitawa, a karo na uku ta sake bitar manya-manyan maganganunshi. Da ta rasa abinda za tayi, kawai sai ta fashe da kuka.

Da saurin gaske ta kashe wayar a daidai lokacin da kiranshi ya fara shigo mata. Da?yar, da jan mazaunai, da muskutawa, da rarrafe, taja jiki zuwa gefen gadonta. Da tayi iya ?o?arinta ta kasa mi?ewa ta hau kan gadon kawai sai tayi kwanciyarta a gurin, har lokacin hawayen idanunta basu daina tsere kamar an buWe famfo ba.


******


Mamaki mai girma ne ya bayyana a fuskarsa lokacin da yaga kiranta na shigowa cikin wayarsa. Abu ne da bai taSa faruwa ba tun da ya Wauko ta daga Fa?o zuwa Abuja. A yau da ya faru kuwa kun ga dole yayi mamaki.

Da fari, ya tsammaci kiran daga Aunty Balira ne kamar yadda ya ga sunan, Sai da ya lura babu New a ?arshen sunan Aunty Baliran, sannan ya gane tsohon layinta ne da ta bar ma Zulai. Kenan a yanzu, Zulai ke kiransa.

?ici-Sici yayi da fuska saboda tsananin takaicin kiran da tayi masa, kamar tana gabansa, a fusace ya ce
"Ko uwar me take nema da take kira na ina tsaka da aiki oho!!"
Ya faWa a fili. Kiran na gaf da tsinkewa ya Waga wayar, ya kara a kunnensa, har lokacin fuskarsa a Waure tamau babu walwala ya ce.
"Menene kike kira na a irin wannan lokacin da kika san ina tare da iyalin..."

"Madallah Yaya mai iyali. Kana tare da iyali ko bakwa tare ba abinda na kira in ji ba kenan."
Ta katse shi da sha?a??iyar muryar da ke bayyana alamu biyu, ko dai tana fama da matsanancin mura, ko kuma ta yi kuka sosai don tana cikin matsanancin damuwa.

Kafin ya sake kwaSo mata wata ba?ar maganar don ba abinda ta kira shi taji kenan ba tayi saurin sake cewa
"Daman tambayarka zanyi, gobe asabar za ka je Fa?o ne...?"

"Bazan je ba. Ko zan je ma ba abinda ya dame ki bane."
Ya katse ta a fusace.

"To ni kam zan tafi gobe in sha Allah. Zanyi sammakon zuwa pack in hau motar haya. A gobe, babu abinda zai hana ni zuwa ga Innaye da Baffa sai dai wani ikon Allah. Daman na zaci za ka tafi ne, in shirya ka biyo ka Wauke ni mu tafi tare don cigaba da rufuwar asirinka. Amma tunda baza ka je ba ni kam zan tafi..."

"Zzzzzaaaa ki tafi Fa?o kike cewa? Da izinin wa za ki tafi?"
Ya tambayeta bakinsa na rawa, da wani irin bayyanannen tashin hankali a muryarsa duk da yana ?o?arin Soyewa.

Izuwa lokacin, acan Sangarenta ranta ya fara Saci. Amma tana ta ?o?arin dannewa don ba ta so su raba hali kamar yadda suka saba, duk da haka, bata san sa'adda taja mishi wani dogon tsaki ba kafin ta ce a fusace
"Har wani izinin waye zan nema don zan je ganin iyayena? Look Yaya Hafiz, kana iya fitowa gobe ?arfe bakwai da rabi na safe ka Waukeni mu tafi Fa?o a mutunce, kana kuma iya shantakewa kayi zamanka ni kuma in tafi a motar haya. Sai dai kyakkyawan albishir a gare ka shi ne duk abinda ya biyo baya kar kayi kuka da kowa face kanka da son zuciyarka..."

"Zulai??? Umarni kike ba ni?"
Ya jefa mata tambayar a tsawace.

"Ba umarni nake baka ba Hafiz."
Ta kira sunanshi gatsatsau abinda bata taSa yi ba.
"Ina faWa maka abinda zai faru ne tabbas! Ko da son zuciyarka, ko babu son zuciyarka. Domin kai baka isa kasa ko ka hana ni yin abinda zuciyata ke so ba."
?it! Ta katse wayar ta barshi sake da baki, ?irjinsa na wani irin bugawa sauri-sauri saboda tsananin kaWuwa da firgita da irin kalaman da ke fita a bakin Zulai.

Kamar ba ita ba? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Me yake shirin faruwa ne?


****** ******
Neman aurensa da Aisha mahaifiyar Imam, nema ne da iyaye suka fara nuna sha'awar ?ulluwar dangantakar. Kafin daga bisani da zancen ya isa kunnuwansu suka ri?a da hannu bibiyu, kasancewar duk su biyun masu biyayya ne da bin umarnin iyaye.

Don haka a wancan lokacin bazai ce ya WanWani za?i da guban da ke cikin soyayya ba, duk da dai jagoran aurensa da Aisha babu ?iyayya ko kaWan, zallar ?auna ce da biyayya suka haWu wajen samar da sassanyar soyayya da sha?uwa mai tsayawa a zuciya.

Amma a yau, da ya gama fallasawa Zulaikha sirrin zuciyarsa ta bar shi a ma?ale, ba tare da ta amsa mishi da eh ko a'a ba duk da yana matu?ar tsoro da fargabar jin kalmar a'a daga bakinta. Ya daWe bai shiga cikin mummunar yanayi na gagarumin tashin

30 / 53