RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 53

15K to 18K   out of 157.3K words

Zuciyarta cike da sa?e-sa?en yadda za ta canja tsarin zamansu a gidan kafin su bar garin Abuja.

Su ba wula?antattu bane, don haka bazai yiwu Bintu ta cigaba da Waukarsu a wula?ance ba. Ba maula suka je gidan ba balle ace za'a dinga ba su sadda aka so a hana su sadda aka ga dama.

Idan Bintu tana da ?anci a gidan lallai su ma suna da shi. Da wannan daliln kuwa ko da tsiya ko da tsiya-tsiya za ta ?watar musu ?ancinsu, idan Yaya Hafiz yaga dama, yayi ?uli-?ulin kubura da ita. Amma tsakaninta da matarsa ba sau?i ba sau?a?awa, shege ka fasa, Wan halak sai yanka.

Tana waWannan tunane-tunanen har ta ?arasa cikin falon gidan, watsar da tunanin komai tayi ta buWe idanu sosai tana kallon irin ?ayatattun kayayyakin da aka yiwa falon kwalliya da su. Duk da ba sanin kayayyaki masu tsada tayi ba, ido ba mudu bane amma ya san kima.

Kuma da ganin kura za ta ci akuya, ko da ganin kayayyakinnan ma?udan kuWaWe suka ja ba ?an kaWan ba.

Haka kawai, ba tare da sanin dalili ba sai hoton gidansu na can ?auye tun daga soro har zuwa falo da uwarWakin Innaye ya faWo a cikin idanunta. Babu mahaWa ko kusa, amma da ta tuna nisan tazarar da ke tsakanin rayuwar birni da na ?auye sai ta ajiye tunanin komai ta ?arasa cikin kicin Win.

"Baba Rabi an gama abincin ne?"
Ta tambaya da yanayin fuska kadaran-kadahan bayan sallama ?asa-?asa da tayi a ?ofar kicin Win.

"Ba'a gama ba Auta."
Ta amsa da sauri cikin girmamawa, domin maganganun da yarinyar tayi Wazu kafin ta fice daga kicin Win tana kuka sun tsaya mata a rai.

Da wannan dalilin yasa ta ?uduri aniyar in Allah ya yarda ta Sangarenta dai baza ta sake yin wani abu da zai nuna wula?antarwa ga tsohuwa da yarinyar ba, duk da daman dai tana yin komai ne don guje ma kuskurewa UwarWakinta. Don ta ?ara warware ma Zulaikha yadda tsarin girkin abincin ke tafiya sai ta cigaba da cewa
"Kin san yanzu ranar ta fara Wagawa, kuma a ?a'idar da Hajiya Bintu ta tsara zuwa uku na rana ne zan dinga raba abinci. Shi yasa na tsara komai yadda aikin zai dinga tafiya kan lokacin da ta tsara..."

"To madallah!"
Zulaikha ta katse ta tun kafin ta aje numfashin maganarta.
"Yanzu ya za'ayi? Me za ki samar ma Innaye mai Wan sau?i? Daga asibiti ta dawo kuma ta bar gidannan ko karyawa bata yi ba."

"Assha! Jikin ya motsa ne? Allah ya ?ara mata lafiya. To ko dai za'a haWa mata Tea ne? Domin ya saSa ma ?a'idar Hajiya Bintu girka wani abu daban saSanin wanda za'a dafa gaba Waya..."

"Wai wace ce kuma Hajiya Bintu da kike ta sako min sunanta a cikin maganganun da muke yi? Ya ina miki maganar mahaifiyar Maigidannan ta fita bata karya ba kina min zancen wata Hajiya Bintu da ta tsinci mai gidan a sama da ha?waransa talatin da biyu? Dan Allah ki aje maganarta gefe kiyi abinda ya kamata. Ko Indomie ce da ?wai ki dafa mata yanzunnan, idan kuma baza ki iya ba kina tsoron saSa umarnin wacce kike ma aiki, ki kunna min abin girkin ki nuna min inda kayayyakin abincin suke, ni sai in dafa mata da kaina. Ko da nake ?ar ?auye kin san dahuwar indomie dai ba za ta gagareni ba."
Zulaikha tayi maganar tana ?ara harhaWe girar sama da ?asa. Zuciyarta cike da haushin Baba Rabi yadda take ma Bintu wata irin biyayya ta musamman kamar wacce ta girme mata a shekaru.

"Anya...?"
Baba Rabi ta faWa cike da taraddadi da tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. Sai kuma ta ?ara da cewa
"Ko da yake, shi kenan. Bari a dafa mata, Wan bani mintuna goma kacal. Je ki dawo, yanzu zan gama dafa mata."

Gefe guda taja ta tsaya tana bin duk inda Baba Rabi tayi da idanu, akan idanunta ta kunna Gas Win girki, daman shi kaWai ne take ga baza ta iya amfani da shi ba a kicin Win. Tana biye da ita har ta buWe store, ta Wauko duk abinda za ta bu?ata sannan ta fito ta kulle. Abu na biyu da taga yadda ake kunnawa ayi amfani da shi blander ne, don haka ta kura idanu sosai taga yadda ake anfani da shi.

Tana kallon komai tana k'ara kwasar ilimin yadda ake amfani da kayan girkin 'yan birni, har zuwa lokacin da Baba Rabi ta gama dafa lafiyayyiyar indomie da ta ji kayan had'i. Ta soya kwai guda hudu kamar yadda Auta ta umarce ta, sannan ta kwashe komai a kula Mai kyau sabanin Wanda ake zuba musu abinci ta mika ma Auta.

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke lokacin da ta karbi abincin. Ta haske Baba da wani lallausan murmushi, a tausashe ta ce
"Na gode, Allah ya biya ki da alkhairi."

"Amin ya Allah. Ki gaida Innaye, Allah ya kara sauki."
Baba Rabi ta amsa bayan ta mayar mata da martanin murmushinta.

Ko da ta koma can bangarensu, akan darduma ta tarar da Innaye, hannunta da casbaha tana ja amma tana gyangyad'i. Sallamar da tayi ma bata amsa ba sai da ta ce
"Innaye barci kike yi?"

Firgigit! Tayi ta farka, ta bude Baki za tayi magana wata k'atuwar hamma ta k'wace mata.

"Sannu Innaye. Kiyi ha?uri, na barki kina jira na ko? Ba'a gama dafa abincin gidan bane shi ne nasa aka dafa miki Indomie..."

"WaWannan siraran taliyar Auta? Kin san dai ko a gida ke ce kike ?wazzabar a siyo miki ita gurin Isa mai shayi ki ci, ko ki karSo a shagon Isiya ki dafa, ni kam bata WaWarani da ?asa ba."

"Innaye, wannan haWi na musamman aka yi gurin dafuwarta. Ba irin ta can ?auyenmu bane, na tabbata za ki ji daWinta. Kuma kin ga fa har wata faffaWar ?wai aka soya miki da za ki dinga yaga kina haWawa da taliyar a gayance irin na ?an birni. Bari in zuba miki ki WanWana ki ji."
Bata jira umarnin Innaye ba ta zauna dirshan a gabanta, ta Wauki faranti da cokali ta buWe kular ta zuba mata mai Wan dama a faranti, daga yadda take fitar da daddaWan ?amshi tun bayan buWe kular, duk su biyun sai haWiye miyau suke yi.

Da farko ?wan gaba Waya ta Wora akan abincin Innaye, sai da ta ce mata ta rage, sannan ta yanka biyu da cokali ta bar mata rabi. Daman tun a frige Win falon can cikin gidan ta Wauko musu ruwa da lemon kwali, a kofi ta zuba mata sannan ta tura mata abincin a gabanta.

Ta tura abincin gabanta ta mi?a mata cokalin, Bismillah tayi ta fara ci a hankali ita kuma tana janta da hira, labarin samarinta na can ?auye da Innaye bata taSa sanin tana da su ba take ba ta, tana faWa mata yadda suke nacin bibiyarta ita kuma tana karta musu rashin kirki da kashedin kar wanda ya kuskura ya bi ta gida, a cewarta, duk basu yi mata ba.

Sai dariya suke yi kamar babu wani abu da yake damunsu. Cikin ?an?anin lokaci sai ga Innaye ta cinye abincin tas! Bata ankara ta cinye ba sai da Auta ta ce
"Innaye in ?ara miki?"

Ta kalli farantin, ta kalli Auta idanu buWe, lokaci Waya sai suka sake kwashewa da dariya.
"Lallai kam Auta kinyi gaskiya, wannan dahuwar taliyar ba irin jagwalgwalon da kike yi acan ?auye bane. Ta yi daWi sosai, na daWe rabon da in ci abinci mai yawa irin haka, lallai komai na birni ya fita daban da na ?auye. Ko don ina jin yunwa ne?"

"A'a Innaye. Ta bakinki ne, tsarin dahuwar ba irin tamu bace amma duk indomin iri Waya ne. Kar ki damu, ai na zuba idanu sosai na koyi yadda ake dafa irinna ?an gayun. Idan muka koma gida, irinta zan dinga dafa miki..."

"Kya dai dinga dafa ma mijinki. Domin muna komawa gida zan tura Baffanku ya tuntuSi Idi, Hamisu, da sauran duk masu son ki da kika gama ba ni labarinsu yanzu. Anya Auta? Ashe daman kina da masu son ki kika bari muna ta Waga hankalinmu akan ko Aljani ne ya aure ki kika rasa mashinshini? Yayyinki na ta safa da marwa gurin Malam Usaini suna karSo miki dafa'in farin jini da na kore shaiWanu?"

?irjinta ne ya buga daram! Sai a yanzu ta fahimci irin suSul da bakan da tayi a dalilin son janye hankalin Innaye har ta ci abinci sosai. ?wal-?wal tayi da idanunta ta sunkuyar da kanta ?asa, domin ta san duk abinda za ta faWa a yanzu dai Innaye baza ta taSa fahimtarta ba.

Kamar an buWe famfo, haka Innaye ta cigaba da faWa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Domin al'amarin rashin auren Zulaikha abu ne da ya daWe yana ci musu tuwo a ?warya, kawai dai don ba su da yadda za suyi ne.
"Shekarunki sha bakwai fa. Saboda Allah duk faWin ?auyenmu ki faWa min wace yarinya ce yanzu sa'arki a shekaru da ba'a yi mata aure ba? Ke ko kunya bakya ji? GanWan-Wan da ke ni da nake Gyatumarki ina tafe muna jera kafaWa a cikin gida? In banda akwai zaman lafiya tsakanina da su Laraba ai da tuni sun fara yada min habaici da ba?a?en maganganu.

Yanzu sa'anninki fa daga masu ?a?a uku sai biyu, Hanne ta gidan Mal Bala kuwa ita da yake kwainika take yi ?a?anta huWu. Saboda Allah kin yi ma kanki adalci mu ma kinyi mana adalci kenan?"
Saboda yanayin lafiya da yayi mata ?aranci a ?an kwanakin, nan take ta fara numfarfarshi sama-sama saboda faWan da take yi ba ?a??autawa.

Da sauri Zulaikha ta matsa kusa da ita ta ri?e hannayenta, a tausashe ta fara magana idanunta cike da hawaye.
"Ayya mana Innaye Allah sarki. Don Allah ki kwantar da hankalinki, kin ga ba wani wadataccen lafiya kike da shi ba. Kar ki manta, ke kike yawan faWen aure lokaci ne, kamar layin markaWe ne idan yazo kaina ko ina so ko ba na so sai an ni?a min..."

"Au! Da waWannan maganganu biyun kika dogara yasa kika ?i mayar da hankali kan abinda ya kamata kina gani kullum hankalinmu a tashe?"
Innaye ta jefa mata tambayar fuskarta na bayyana Sacin rai. Sai kuma ta Wan sassauta muryarta yayi rauni ta sake cewa
"Auta ko dai so kike in koma kushewata ba tare da na ga ?a?anki ba?"

"A'a! A'a! Wallahi ba haka bane Innaye. Don Allah kiyi ha?uri."
Ta ?arasa maganar tare da gangarowar hawayen da tun Wazu take ri?ewa a cikin idanunta.

"Idan ba haka bane to yaya ne? Sanin kanki ne babban burinmu a yanzu ni da Baffanki da ?an'uwanki mu hannanta ki a hannun miji na gari wanda muka yarda da nagartar halayensa. Me yasa baza ki sadaukar da farin cikinki don ki cika mana burinmu ba?"

"Kiyi ha?uri Innaye."
Ta sake faWa cikin kuka mai tsanani.

Duk da matsanancin tausayinta da ya cika zuciyar Innaye bata bari yayi tasiri a fuskarta ba. Haka ta cigaba da tsattsareta da maganganu masu karya zuciya har sai da suka kai gaSar da Zulaikha ta Waukar mata al?awarin suna komawa gida za ta ba masu sonta damar fitowa neman aurenta. Kuma duk wanda su iyayenta suka tabbatar ya fi nagarta ko da zuciyarta ba ta so za ta amince a Waura musu aure.

"Allah yayi miki albarka Auta ta. In Allah ya yarda baza ki taSa yin da na sani ba a auren da za muyi miki. Allah yayi miki albarka."

Duk yadda addu'a da saka albarkar suka yi mata daWi a zuciya ta kasa amsawa a fili sai a zuciya. Sunkuyar da kanta ?asa sosai ta sake yi wasu sabbin hawayen na sake Salle mata, don Allah ya sani, Aure, ta bar gaban Innaye zuwa gidan wani ?aton gardi haihata-haihata shi ne abu na ?arshe da bata fatan ya faru a kanta.

Kuma ita da kanta idan za'a Wora mata wu?a a ma?ogwaro baza ta taSa cewa ga dalilin da yasa take ?in aure a rayuwarta ba.


****** ******



"Uhmmmm! In faWa miki gaskiya Bintu? Kin ga duk irin matsananciyar soyayyar da kike ganin tana gudana tsakaninki da Abdul-hafiz? Wallahi baza ki taSa samun kwanciyar hankalin mijinki da nutsuwarsa guri Waya ba matu?ar tsohuwar nan tana raye. Iya zallar gaskiyar magana kenan, babu wani Soye-Soye ko kwana-kwana.

Kar fa ki manta, duk lalacewarta da ?auyancinta mahaifiyarsa ce. Akwai wannan ?auna da soyayyar ta musamman da Allah ya saka tsakanin Wa da mahaifiya, to ke wacece da za ki ce dole ya fifita ki akan mahaifiyarsa?

Ai in faWa miki ?awata kin riga kin baro shiri tun rani. Yo uwar miji na birni ma ya aka ?are da ita ballantana ta ?auye? WaWanda tun asali sun riga sun ginu da rayuwa akan makirci da matsanancin sa'ido na tsiya ga bin ?wa??wafi? Ai fa ina sake jaddada miki sai dai kiyi ha?uri, shi yasa ni bana taSa ganin laifin ?an matan da suke ture soyayya su ?i auren saurayi muddin mahaifiyarsa tana raye.

Uwar miji???!! Uhmm! Ciwon zuciya da hawan jini ake faWa miki ?awata. Ko ni abinda yasa baki san Wan ?aramin biki da cikan da muka kwasa da tawa ba kafin Allah ya Wauki rayuwarta don dai baki yi aure bane a lokacin, ko na faWa miki irin matsalar da nake ciki ba lallai ki fahimci inda na dosa ba. Da Allah kuma ya dubi zuciyata sai ya raba mu tun kafin tafiyar tayi tsawo, shi yasa kika ganni yanzu hankalina kwance, kamar tsumma a randa.

Don haka idan za ki Wauki mataki tun wuri gara ki Wauki mataki, musamman a yanzu da wasu ?an damarmaki suke a hannunki..."

"Kamar ya? Me kike nufi Raudha? Don Allah buWa min bayanin sosai yadda zan gane."
Ta katse ta da tambayar a Wokance, a zuciyarta take jin kamar wata gwaggwaSar mafita Raudhan za ta faWa mata wanda zai haura da ita tudun mun tsira a cikin ?an?anin lokaci.

?an dariya Raudha tayi tana karkaWa ?wayoyin idanunta, sai kuma ta gyara zama ta cigaba da cewa
"DaWina da ke Bintu wani lokacin duk wayewarki kanki kullewa yake yi, jiya fa kika gama cika mana bakin mu ?yale ki, ke kin san yadda za ki bi da komai daki-daki ki warware matsalar da ke gabanki. Yanzu kuma me ya canja miki ra'ayi kike neman mafita a waje na?"

"Uhmmm! Baza ki gane bane Raudha. Wallahi da farko duk yadda nake hango girman matsalar kamar bata kai haka ba. Allah ya sani ko ?aramin kular abincina Sweetheart ban taba tsammanin zai iya dauka ya kai ma tsohuwar nan ba, sai ga shi ya goge min hadda ta hanyar kwasar abincin da na Wauki fiye da awa biyu ina shirya mishi kuma na zuba a cikin tsadaddun kuloli ya kai ma ?auyawan can. Allah ya gani wannan abu ya bakanta min rai ba kadan ba. Yanzu dai duk ba wannan ba, warware min maganar da kika yi ta karshe yadda zan gane sosai."
Ta ?arasa maganar fuskarta na bayyana takaici, kamar a lokacin ne take kallon kulolinta a Wakin Innaye.

Dariya sosai Raudha tayi kafin ta matsa da bakinta kusa da kunnen Bintu ta rad'a mata wasu maganganu, lokaci daya Bintu ta waro idanu warwaje had'e da bude baki a mamakance. Da sauri ta janye kunnenta hannunta dafe da haSa ta ce
"Ke Raudha !!! Anya kuwa zan iya? kina ganin wannan mafita ce da za ta samar da hanya mai Sullewa? Ni dai gaskiya tsoro nake ji"

"Oho miki! Sai ki je kiyi ta jin tsoron. Ni dai shawara na baki, ko ki dauka ko ki cigaba da zama a cikin matsaloli ba ma matsala ba. Sai ma nan gaba idan ita da kanta tsohuwar da tsohonsa suka nemi dawowa gidanku da zama gaba Waya..."

"Haba-haba-haba-dai! Su ma baza su fara ba. Sai ka ce a garin gaSa-gaSa."
Bintu ta katse ta da sauri hankalinta a tashe.

"Kina ganin bazai yiwu ba? Su ai daman a garin gaSa-gaSan su ke. Kuma ma kanki farau zama gida Waya da iyayen miji? Kin san dai Wansu na da wannan ?aton gidan da duk ?auyensu babu irinsa, kuma mai Sangarori da yawa baza su taSa yarda ya kama musu haya ba. Yanzu dai tashi ki tafi Ofis, daga baya ma karasa maganar..."

Ita kaWai a cikin Ofishinta ta gama tunanin irin maganganun da suka tattauna da Raudha kafin ta ?araso asibitin. Da farko, sam bata ji a zuciyarta za ta iya aiwatar da shawarar da Raudha ta bata ba, amma a yanzu da ta ?ara yi ma al'amarin karatun ta nutsu sai ta fahimci lallai fa ya kamata ta Wauki mataki tun kafin wankin hula ya kaita dare. Kuma a yanzu dai babu wani mataki da take gani a matsayin mafita ta gaggawa face bin hanyar da Raudha ta Wora ta akai.

A hankali, ta mik'a hannu ta dauki takardar da ke ajiye akan teburin gabanta, sakamakon gwajin da aka yi ma Innaye ne don ganin ko tana da ciwon suger ko babu.

Ba tare da ta buWe ta ga me sakamakon ya ?unsa ba ta keta shi gida biyu, hakan be ishe ta ba, sai da ta ?ara yayyaga shi gutsi-gutsi sannan ta watsa a cikin abin zuba sharar da ke cikin ofishin.

Tattara yan karikitanta tayi ta zuba a cikin jaka, ta Wauki wayarta da ke ajiye a gefe ta gyara zaman mayafinta sannan ta fice daga cikin Ofishin.

Bata Sata lokaci ba tayi sallama da sauran abokan aikinta bayan ta hannanta komai ga likitan da ta karSe ta ta shige motarta ta bar asibitin.

Kafin ta ?arasa gida, sai da ta biya wani babban shagon sayar da magani ta sayi magunguna da alluran da za ta Wora Innaye akai a matsayin na ciwukan jikinta sannan ta wuce gida. A gefe guda, tana jin wani nutsuwa na musamman yana

6 / 53