RANAR NAKA COMPLT BY FAREEDA ABDALLAH

Author :  FAREEDA ABDALLAH Category :  African Stories & Novels

Chapter   21 / 53

60K to 63K   out of 157.3K words

ba, tabbas da babu abinda zai hana shi lallasa Zulaikha a gurinnan. Sanin ba shi da wannan damar yasa shi yin ?wafa ?asa-?asa, yayi ta maza gurin rage girman Sacin ransa.
"Kuyi ha?uri, lokaci na tafiya. Duk yadda ake ciki idan mun isa za muyi waya da ku."
Yayi maganar da sanyin murya.

Ba tare da Sata lokaci ba duk suka ja baya daga jikin motar, Aunty Rakiya ce ta rufe ?ofar baya na motar inda suka zaunar da Zulaikha bayan ta cusa kanta cikin motar ta raWa ma Zulaikha magana a kunne.

Fatan alkhairi da addu'ar Allah ya tsare gaba Waya suke mishi haWe da Waga mishi hannu, har direba ya tayar da motar suka Sace ma idanunsu basu koma cikin gida ba.

"Ubangiji Allah ya kaWe fitina, ya bada zaman lafiya da Zuriya masu albarka."
Indo, babbar ?a a Wakin Umma Laminde tayi addu'ar.

"Ameen ya Allah"
Suka amsa gaba Wayansu.


***** ******

Da Sacin rai sosai a muryarsa ya Wan waiwaya baya ya kalli Zulaikha da har lokacin yake jin shesshe?ar kukanta ?asa-?asa ya ce
"Kin san Allah? Idan bakiyi mana shiru ba a tsakiyar dajinnan da babu gida gaba babu gida baya zan saka a sauke ki. Kuma kin san halina sarai, tsaf zan iya aikata fiye da haka."

Maganar na dira a kunnuwanta Wif! ta tsayar da kukan da take yi kamar Waukewar ruwan sama. A tsorace ta Wan Wago kanta daga cikin hijabi ta saci kallon gefe da gefen hanya.

Sai taga kamar yadda ya faWa ne, a cikin daji suke tabbas! Kuma ta san mugu ne na ?arshe in dai a kanta ne, kaWan daga cikin aikinsa ne ya yasar da ita a gurin, balle ma a yanzu da yake ganin ta zame mishi ?arfen ?afa. Kuma kasancewarsa gogaggen Wan boko da ya saba da ?arya ?ir?irar abinda zai faWa don wanke kansa a gurin iyayensu bayan ya Satar da ita ba abu ne da zai mishi wahala ba.

Tana jin shi ya ja ?wafa mai ?arfi, sannan yayi dogon tsaki. Ga dukkan alamu dai bai so tayi shiru ba.
'Mugu! Aniyarka ta bi ka. In Allah ya yarda har mu raba gari muguntarka ko na matarka bazai taSa tasiri a kaina ba. Allah nake ro?o ya cigaba da bani kariya daga dukkan sharrinku.'
Tayi maganganun a zuciyarta.

Kasancewar ta daWe tana kuka, kuma daren jiya gaba Waya barcinta raba da rabi ne. Don haka bata Sata lokaci cikin tunani ba nannauyan barci yayi awon gaba da ita.

Kamar a mafarki, ta ji saukar wani zazzafan duka a gefen kafaWarta. A firgice ta Wago fuskarta idanu a warwaje ta ce
"Wayyo Allah Innaye..."

Cike da jin haushi ya kai hannu zai make mata baki, Allah ya taimake ta taga tahowar hannunsa, da saurin gaske tayi gaggawar kawar da fuskarta can gefe Waya.

"Idiot! Kina barcin ma baki san idan an tashe ki kiyi salati ba sai ihu."
Ya faWa da Sacin rai yana harararta.

?asa-?asa ta mayar mishi da martanin hararar da yayi mata, duk da bata san cikakken fassarar kalmar 'Idiot' ba ta san zagi ne, domin malamansu na boko suna yawan faWa ma Waliban da basa jin magana. Bakinta a gaba a zuciyarta ta ce
'Ni dai ba Idiot bace.'
A fili kuma cewa tayi cikin guna-guni
"Yaya duka na fa kayi ba tashi na ba... Kuma da zafi sosai. Bayan Innaye ta ce amana maci amana maye..."

"Idan kika sake min maganar Innaye anan sai na Sata miki rai. Za ki fito ko sai na sa an kulle ki cikin mota?"

Kafin ta fito, sai da ta waiga ta tabbatar ba'a tsakiyar daji suke ba. Mamaki ne ya kamata da taga ashe har sun isa gidanshi a Abuja, bata ce komai ba sai girgiza kai da tayi. A maimakon ta fito ta Sangaren ?ofar da yake tsaye yana jiran fitowarta, muskutawa tayi zuwa can Waya ?ofar ta buWe da sauri ta fita tun ma kafin ya sake cewa komai.

Mi?a tayi haWe da salati a hankali, a zuciyarta take ayyana ?arshen tika tiki tik! Ga ta dai a cikin gidan, kuma a matsayin matar mai gidan. Sanin irin wainar da za'a toya kuma a cikin gidan Allah kaWai ya bar ma kansa sani.

Da saurin gaske ta Waga ?afa ta bi bayansa ganin har ya kusa isa bakin ?ofar shiga Sangarensu ba tare da ya ?ara ce mata kanzil ba. Har ta kusa cimma inda yake, sai ta tuna da jakar kayanta da yake cikin boot Win mota. Ba tare da kunya ko jin nauyin jikinta da ta kasance irin yarannan masu ?iba ba ta juya da gudu zuwa gurin motar.
"Mal Musa jakar kayana da wayata a cikin mota."
Ta faWa da ?arfi kuma cikin karaWin da yasa hatta Hafiz sai da ya tsaya a inda yake ya waiga yana kallonta.

"Wawuya kawai."
Ya faWa a fili haWe da jan tsaki ganin irin gudun da take yi.

"Afuwan ranki ya daWe. Ai da ma kin shiga daga ciki sai in Wauko miki jakar kayan naki."
Mal Musa ya faWa cikin girmamawa, domin tun a ?auye yasan matsayinta a gurin maigidansa yanzu tudu biyu ne.

Dariya ne ya kamata ganin yadda yayi mata magana, har da wani Wan dur?usa mata irin bayar da girman nan. Duk yadda ta so fuskewa ta ci magani kasawa tayi, sai da ta Wanyi dariya kafin ta ce
"Ka ga Mal Musa, ni fa ba wata ba?uwar zafi ba ce. Kar ka wani Waura min girman da ko kusa bazan iya Wauka ba. BuWe min mota kawai in Wauki wayata da jakar kayana."

Yana buWe boot Win motar, bata tsaya jiranshi ya ciro jakar kayan ba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? da sauri ta ciro abarta, ta buWe gidan baya na motar ta Wauki wayar da Aunty Balira ta bata sannan ta nufi Sangaren masu gidan. Idan tayi taku Waya, biyu, sai ta waiga ta kalli hanyar Sangaren BQ inda aka sauke su ita da Innaye.

Haka kawai tsoro ya mamaye zuciyarta
"Allah yasa dai ba a can Sangaren za su ce in zauna ni kaWai ba."
Tayi addu'ar a fili, zuciyarta cike da tsoro.
"TaS! Ai Wallahi idan Yaya ya ce in koma can ni kaWai bazan je ba, sai dai yasa a maidani Fa?o, haka kawai ni kaWai ?wal kamar mayya za su tura can gurin? TaS! Bazai yiwu ba."
Ta sake faWa a fili tana Wan murguWa baki kamar Yayan yana gabanta.

A daidai lokacin ta isa ?ofar shiga Sangaren masu gidan, bata tsaya wani ?wan?wasawa ba kawai ta murWa hannun ?ofar tare da cusa kanta cikin falon, bakinta Wauke da siririyar sallama.

Cak! Taja ta tsaya tana ?are ma tan?amemen falon kallo, babu kowa a ciki. Matsanancin mamaki ne ya kamata ganin gaba Waya falon an canza kayan ciki da ta sani, wasu tsadaddun setin kujerun aka canja da kayayyakin more rayuwa kala daban-daban. Duk da daman can falon mai bala'in kyau ne, amma yanzu sai taga ya ?ara ninka kyau fiye da yadda ta san shi a baya.

Ga kuma wasu tan?ama-tan?aman hotunan Yayanta da Anty Bintu da jaririnsu da aka kafa a kusurwoyin falon. Saboda tsabar ?auyanci bata san sa'adda ta saki jakar kayanta a tsakiyar falon ba, ta fara zagayawa a hankali tana Wan tattaSa abubuwan kwalliyan da tunda aka haife ta bata taSa ganin irinsu ba.

Baza ta ce ga iya adadin mintunan da ta Sata tana kallon ?auyancin ba, kafin daga bisani ta tsaya gurin wani ?aton hoton Jariri Aadil da yayi kyau sosai kuma ya fito fes a cikin hoton kamar Wan turawa. A hankali ta mi?a hannunta ta taSa fuskarsa a cikin hoton, ita kaWai sai sakin murmushi take yi tana shafa fuskarsa kamar a gaske shi take shafawa.

Allah ya sani tana son yara, musamman yara masu kyawu tun suna jarirai, shiyasa ko a ma?wafta in dai aka haifi yaro ko yarinya kyakkyawa ta dinga jelar Wauko yaron yana yini a gurinta kenan.

"Keh! Wace ce ke?"

Saukar gigitaccen tsawa da tambayar Bintu a kunnuwanta yasa ta Wauke hannunta a jikin hoton da sauri tare da waigawa baya a tsorace. Da yake ta ba hanyar saukowa daga matattakalar baya ne, shi yasa tun daga saman benen bayanta kawai Bintu take hange ba tare da sanin ko wacece ba sai yanzu da ta juyo suka yi ido biyu.

Da maWaukakin mamaki sosai a fuskar Bintu take kallonta, domin ko da suSutar baki Hafiz bai faWa mata tare da Zulaikha yake ba. Farin cikin ganin kyakkyawar zinariyar matarsa da Wansa mafi soyuwa a zuciyarsa ya mantar da shi duk irin Wunbin damuwar da ya kwana ya yini da shi.

Tunda suka haura sama wanka kawai yayi suka yi musayar sumbata da rungumemeniya tsakaninsa da matarsa ya Wauki Wansa yana ta mishi wasa kamar wani babba. Saukowar nan da Bintu tayi ma ta sauko ne da nufin ta Wauko mishi abubuwan motsa baki kafin ta ?arasa mishi abinci ashe rabon tayi tozali da Sacin rai ne.

Yo Sacin rai mana, idan ba Sacin rai da takaici ba me zai kawo Zulai gidanta a irin wannan lokacin bayan ko sati gayyar na'ayyen danginsa basu yi da komawa can ?auye daga taron sunan da suka zo ba.
"Ke ce?"
Ta tambayi Zulai da murya mai bayyana fushi ?arara tana harhaWe girar sama da ?asa.
"Me ya kawo ki gidana?"
Ta sake tambayarta a tsawace ba tare da ta jira amsar tambayar farko ba.

?asa-?asa Zulaikha ta galla mata harara, zuciyarta cike da tunanin irin cin kashin da Bintun tayi musu wancan karon zuwansu gidan ita da Innaye. Tana kuma ayyana lallai wannan karon baza ta taSa Waukar wula?anci daga Bintu ko Yayanta ba sai dai duk abinda zai faru ya faru.

Sai da ta kawar da fuskarta gefe Waya, da ta?ama-ta?ama a muryarta ta amsa ma Bintu da cewa
"Gidan Yayana dai. Kuma tare da shi muke tafe, abinda baki gane ba shi za ki je ki tambaya ba ni ba."
[1/21, 8:22 PM] Fareeda Abdallah: Har ta buWe baki za ta yi magana, sai kuma ta katse maganar ta hanyar jan ?a??arfan tsaki. Da sassarfa ta juya ta fara haura matakalar benen bibiyu ranta yana ?ara Saci, har ta isa Wakin Hafiz. Tsabar yadda ganin Zulaikha ya tunzurata ta ma kasa tsayawa ta rage girman Sacin ran da ke bayyane ?arara a fuskarta, ko kuma tayi ?o?arin saisaita yanayin kalaman bakinta.

"Hafiz? Zulai na gani a falo? Me ya kawo ta gidana?"
Ta tambayeshi cikin Waga murya ba tare da damuwa da barcin da taga ya fara yi ba, Aadil na kife a ?irjinshi shi ma yana barci.

Kamar a mafarki, haka muryarta ya sauka a kunnuwanshi da wani irin tsawa-tsawa. A hankali ya buWe idanunsa da suka fara canja launi saboda gajiya da kuma barcin da ya fara Waukarsa.
"Me kika ce Sweetheart?"
Ya tambayeta a nutse, a ?o?arinsa na ?aryata zuciyarsa da take ta raya mishi kamar fa Sacin rai yake gani a fuskar Bintu kuma tsawa tayi mishi yayin magana don kawai ta ga Zulai ?anwarsa a cikin gidan. Wai a hakan ma don bata san matsayin Zulai a gare shi ya ?ara sama daga ?anwa zuwa mata ba.

"Zulai na gani a falo. Na tambayeta me ya kawo ta tace min in tambaye ka. Shi ne nake neman sanin abinda ya kawo ta da ?aton jakar kaya bayan ko sati Waya ba'ayi da su Aunty Balira suka koma ba..."

"Don su Aunty Balira sun zo suna sun koma wata a cikin dangina ba ta da ikon zuwa bayansu?"
Ya katse ta da tambayar tun kafin ta aje numfashin maganarta, mamaki mai girma bayyane akan fuskarsa.

Suuu tayi a tsaye guri Waya, sai da yayi mata wannan tambayar ne yasa ta jin kamar fa ta kwafsa a yanayin yadda ta zo mishi da ?orafin. Narai-narai tayi da idanunta kamar za ta saka kuka, muryarta a raunane ta amsa da
"A'a ba haka bane. Kawai dai na yi mamaki ne."
Har ta yi shiru sai ta ?ara da
"Kuma dai My dear sanin kanka ne Zulai ba ta wani ?aunata, ba shiri muke yi ba. Saboda Allah sai ka rasa wacce za ka Wauko ta kwana biyu a gidannan sai ita? Ka sani sarai ni raini ne ba na so... Amma idan maganganuna sun Sata rai Allah ya baka ha?uri."
Shar... hawaye suka sauko daga idanunta, a sanyaye ta juya za ta fice daga Wakin.

Bata san sa'adda ya kwantar da Aadil akan gado ba sai ji kawai tayi ya ri?o hannunta na dama. Ko kafin tayi wani yun?uri har ya kwantar da ita a ?irjinsa, a tausashe, ya fara shafa bayanta alaman rarrashi.

Ita kuwa hawaye ne suka Salle mata kamar an buWe famfo, sai tsiyayar da su take yi a ?irjinsa zuciyarta na ?ara zafi. A yadda take ji, kamar ta buWe baki tayi ta kwarma ihu ko za ta samu sau?in damuwarta amma babu hali.

Allah ya sani, ta tsani mu'amala ta kusa ko ta nesa ya dinga haWa ta da dangi da iyayen Hafiz. Wai me yasa baza su sakar mata mara tayi walwalarta bane tunda dai shi da ya kasance dolen-dole a gare su yana zuwa can ?auyen? Da gangar tun bayan komawar Innaye ?auyen ta ?i zuwa, duk sa'adda ta ji ya fara zancen zai je duba iyayensa za ta fake da laulayin ciki, ko kuma ta ce cikinta baiyi ?wari ba a matsayinta na likita baza ta iya jure doguwar tafiya a cikin mota ba don gudun abinda zai je yazo wanda ba'a fata.
Shi kuma da yake Allah ya jarabce shi da masifaffen son cikin haka yai ta mata uzuri bai taSa matsa mata ba har Allah ya sauke ta lafiya. Kullum idan yaje, da irin uzurin da zai ?ir?ira ya faWa ma iyayen a matsayin abinda ya hana Bintu zuwa duba Innaye. Su kuwa da yake dattawan arziki ne ko a fuska basu taSa nuna mishi Sacin ran rashin zuwan nata ba, tunda dai shi da yake nasu yana zuwa akai-akai, to Alhamdulillahi.

"Beb kukan kuma na menene?"
Ya tambayeta da mamaki bayan ya Wago fuskarta yaga hawaye kaca-kaca har ta ji?a mishi gaban lallausar rigar shan iskar da take jikinsa.

Sai da ta ja shesshe?a kafin ta iya danne zuciyarta ta amsa da
"Damuwar yadda na Sata maka rai daga dawowarka ne My Dear... Kayi ha?uri don Allah ka ji?"
Ta bashi ha?urin a shagwaSe. Kafin ya amsa ta ?ara da cewa
"Kuma zuciyata cike take da tsoron irin zaman da za muyi da Zulai, Allah yasa bata zo da nufin sauke min kwando-kwando na rashin kunyarta ba, domin ko yanzu daga tambayarta a mutunce baka ga wata uwar harara da ta aiko min ba..."

"Zan ja mata kunne sosai, ko kusa bata isa ta ce za ta maimaita iskancin da tayi mana lokacin zuwansu da Innaye ba. A gabanki zan gargaWeta."
Ya faWa a tausashe, zuciyarsa na ta canki-cankar ya faWa mata matsayin Zulai a gare shi yanzu ko kuma ya bari sai can gaba?

Duk da dai maganar da Innaye tayi mishi na bata yarda ya Soye ma Bintu matsayin Zulaikha a gare shi ba yana ta bugun can ?asan zuciyarsa.

"Shi kenan My dear. Ina mata barka da zuwa. Bari in je in kawo maka abin motsa baki."
Ta faWa da sanyin murya bayan ta goge hawayen fuskarta tsaf! Har ta kama hannun ?ofar za ta buWe ta fita maganarsa yasa ta tsayawa cak!

"Baffa ne yace in taho da ita zuwa nan da ki gama wanka, ko wasu ?ananun ayyukan ne sai ta taya ki da su, ko kuma rainon Aadil, don ita Win gwana ce gurin rainon ?ananun yara."

Da shi da yayi ?aryar don samun maslahar kai da kai, da ita da take saurarensa hankalinta a Wugunzume, a tare ?irajensu ya buga daram!

Lumshe idanu tayi tana jan Lahaula wala?uwwata illah billah a zuciyarta. Ko da ta buWe ido, bata yarda ta kalli fuskarsa ba balle yaga yadda wasu sabbin hawaye suka sake cicciko idanunta.

Da sha?a??iyar murya ta ce
"Allah sarki Baffa... Ai kuwa na gode sosai... Amma da an barta tunda ga Mashkura (?anwarta) har yanzu bata koma gida ba. Amma tunda an zo da ita ma bai Saci ba. My dear bari in je in dawo, na bar Zulai a falo ko ruwa ban bata ba."
Bata jira amsawarsa ba ta wuce da sauri don ma kar ya sake tsayar da ita.

Sai da ta tsaya a tsakiyar bene na sharSi hawaye na cikakkun mintuna uku kafin ta iya ?arasawa cikin falon fuskarta a Waure tamau. Turus! Ta ja ta tsaya ganin Zulaikha zaune akan kujera ta yi WaiWai, hannunta ri?e da babbar kwalin madarar hollandia tana WaWWaka, ko kofi bata samu zarafin Waukowa a kicin ba, haka take gwaSa bakinta a jikin kwalin tana sha babu abinda ya dame ta.

"Wani shegen ne yasa ki buWe min frig ki Wauki abu ba tare da umarnina ba?"
Ta tambayi Zulaikha ranta a Sace. Duk da zamanta akan kujera ya Sata ma Bintu rai ba kaWan ba, amma ganinta tana shan madara hankalinta kwance kamar a Wakin uwarta ya danne Sacin ran zamanta akan kujerar.

Kafin Zulaikha ta amsa mata, sai da ta lumshe idanu ta ?ara zu?ar madarar sosai da irin salon cusa haushin nan sannan ta kalle ta tana murmushi.
"Yaya ne fa ya siyo, saboda Allah Aunty Bintu a gidannan da irin matsayin da nake da shi har sai na nemi izininki kafin in Wauki wani abu da nake da tabbacin Wan'uwana ne ya siyo?"

Karaf! Maganganun suka sauka a kunnen Hafiz da yake saukowa daga bene. Ranshi a Sace, ya daka ma Zulaikha wani gigitaccen tsawan da yasa ta yarda kwalin madarar ba shiri, a tsorace ta Waga idanu tana kallonsa ?irjinta na bugawa akai akai har ya ?arasa saukowa daga benen.

Kai tsaye gurinta ya nufo kamar zai rufe ta da duka ya tsaya a kanta yana huci
"Sa'arki ce ita da za ki dinga

21 / 53