Chapter 6 Reading NAZLAH Baƙin Ƙaddara by Salmaj HN Novels

NAZLAH Baƙin Ƙaddara by Salmaj

Author :  Salmaj Category :  KDP NOVELS

Chapter   6 / 11

15K to 18K   out of 30K words

""ta fada tana kallonshi, taSe baki ya yi, tare da cewa ""Lallai Yayah, ashe ta dawo shine bata fada min ba, ta kyauta ai"", ya fada yana mikewa."

"kallonshi tayi, tare da cewa ""ina zuwa haka?"", dan tsayawa ya yi, tare da cewa ""gida zanje Hajiya, zuwa"

"Anjima zan dawo"", ya fada yana yin gaba, fatan sauka lafiya ta mishi, kafin ya fice."

"Yana fita ya tarar da Yaranahi, zazzaune suna cin Abinci, suna ganinshi suka zabura suka mike gaba"

"dayansu, suna sara mishi, kowa gurin mota ya nufa, murmushi ya musu, kafin yace ""ku zauna ku gama cin Abin cin, in kun gama ku shiga da kayan ciki, ni zan tafi gida, in yaso in kuka gama kwa taho"", ya fada yana wucewa."

"Abbas ne ya yi, saurin bude mishi mota ya shiga, shima shiga ya yi mazaunin driver, tare da kunna motar,"

"tafiya ya fara yi, tun kafin ya karaso bakin get aka bude musu, yana zuwa ya fice, kan titi ya hau, kasantuwar Unguwar kusan gaba dayanta titi ne, dan Unguwar Sarakai ce , da manyan Yan siyasa, basu wata tafiya sosai ba suka ™araso Barhim ."

"Tunda suka tun karo Unguwar zuwansu , ya isar da Yan Unguwar, hakan yasa kowa ya shiga taitayinshi,"

"dan baya wasa da mutum, in ka mishi iskanci ko ka nemi yiwa wani to taka maka wuya zaiyi ba abun da yasha mishi kai, Suna karasowa getman din ya wangale musu get din gidan suka shige."

"sai da Abbas din ya dai-daita parkinga kafim ua fito, yana sha™ar daddar iskar da take kaWawa, cikin izza ya"

"fara takawa cikin gidan, bai ko damu da Sojojin da suke sara mishi ba, yana zuwa jikin kofar ta bude da kanta,"

™afarshi na taka shiga cikin palon yaci karo da Plate a ™ofar shigowa palon.

"da mugun Mamaki yake kallon cikin palon, ganin komai a hargitse, da alama Sa tunda ya tafi babu abun da aka gyara cikin gidan, da Sallama ya shiga cikin palon, da sauri Sadiyya ta mike tana kallonshi, fuskarta ta bayyana"

tsantsar farin cikin ganinshi.

"gurinshi ta nufi tana washe baki, cikin muryarta mai dadi tace ""barka da zuwa, saukar yaushe?"", ta"

"fada tana karSar brief case din da yake hannunshi, sakat mata ya yi, ya shige ba tare da yace mata komai ba."

*********

"""Ke! Nazlah tashi kizo ki shirya, ki tafi Makaranta dan su Salamatu tun dazun naga sun wuce Amma ke baki"

"da Niyyar mikewa ki tafi"", tura baki Nazlah tayi, tare da cewa ""to kema Umma mi Wallahi na gaji"", ta fada tana , ci gaba da yanka kyallayen da suke gabanta."

"Haleem ne da ya shigo yanzu, ya daka mata tsawa, tare da cewa ""Zaki tashi ko sai na tattakaki Sakarar"

"Yarinya, "" ya fada kamar zai duketa, da sauri ta mike tana diddira ™afafunta ta shige Waki, ta kusa Minti goma da shiga amma bata fito ba, ""zaki fito wai ko sai na shigo Wakin"", Haleem ya fada cikin muryarshi mai dadi da kuma Amo, a hankali ta bude labulen Wakin ta fito tana share hawaye, fuskarta tayi jargwab da hawaye, gabanshi ta tsaya tana cuno dan karamin bakinta."

"kallo ya ™are mata tare da cewa, ""shige ji tafi, kuma Wallahi na fito na gsnki a hanya kina wasa ko kin"

"tsaya sai na Sallaki"", ya fada yana dungure mata kai, kuka ta fasa tare da ficewa, tana kukan ita an tsaneta komai sai ace dole tayi, a haka ta kama hanyar zuwa Makarantar , babu nisa sosai daga gidansu zuwa Makarantar sai dai, sai"

"an tsallaka titi, tana cikin tafiya ta haWu da wani Yaro dan Unguwarsu mai suna Idi, ganin tana kuka yasa ya fara mata"

dariya.

"da sauri ta Wago kanta tana kallonshi, cikin hasala da jin haushi, kan Yaron tayi da gudu, tana zuwa ta cukwikuyeshi"

", ta hadashi da bango, tare da fara gwara kanshi, tana zazzaga mishi ruwan masifa, yakushinta Yaron ya fara yi yana neman hanyar guduwa."

"damkarshi tayi, tare da kafa mishi cizo a wuyanshi, ta rike ta cije , ta™i saki, ihu Yaron ya saki, yana son ta"

"sakeshi, amma ta gama du™un™uneshi, mutane ne suka fara taruwa, suna son rabasu, amma ta™i rabuwa dashi, ta™i sakin Yaron ga wuyanshi har ya fara jini , wani Mutum ne, yazo ya fisgeta daga jikin Yaron tare da dalla mata mari."

"Tsautsayi yasa Yatsan hannun mutumin ya fada cikin bakinta, wani wahalalan cizo, mai ratsa kwanya ,"

"wsnda yake bi ta cikin jijiyoyin jiki ta sakar mishi, wanda yasa mutumin, ba shiri ya saki ihun azaba, tana ganin idanun mutane sun fara yo kanta, ta saki hannun mutumin da gudu, kamar iska haka ta tsallake titi zuwa Islamiyarsu."

"Tana cikin gudun ta haWu da wani tsoho Daga mata hannu ya yi, itama ta daga mishi, cikin kwala"

"murya yace ""ki kula ana Taro Makarantarku, kar ki bari a duke ki, ki gudu"", ya fada yana juya baya."

"babu wanda ya lura da lokacin da ta shige ciki, ruWewa Mutumin ya yi, yana cewa ""Aljana! Wallahi Aljana ce kun gani ta Sace Sat"", ya fada cikin ruWu da tashin hankali, wani Matashi ne yace ""Wallahi Alhaji ba Aljana"

"bace, mutum ce, Allah dai ya shirya, dan fitinar Yarinyar nan tayi yawa"", ya fada yana jinjina kanshi."

"itana shiga cikin Islamiyyar tasu ta tarar da Malam Arabi na dukan latti, tsuru² tayi da ita, ba abin ta"

"koma waje ba tasan boom din da ta haWa, gashi bata kaunar bulala ko kaWan dan har in aka mata to ranar bata kwana lafiya, take dubura ta faWo mata, ana dukan wata ta mike, tabi bayanta, kasantuwar suna da yawa wanda aka du™a, ba lallai ne a iya ganeta ba, har ta gota Malamin wata Yarinya tace ""Malam Arabi ga Nazlah chan ta ruga baka bigeta ba"", da hanzarinshi ya juyo, tare da kwalala mata manya²n idanunshi masu kama dana Nufawa."

"""Ke! Uban wa yace ki tashi ban dukeki ba ki gudu?"", ya fada yana zazzare mata idanunshi, cikin jin haushi"

"tace ""Malam Arabi ka daina zagar min Uba kaga dai babu abun da ya maka"", ta fada tana dalla mishi harara dan arayuwar ta tsani zagi, ""Ke! dan Ubanki ni kike cewa haka?, Nace Uban wa yace ki tashi ki tafi?"", cikin dakiya da nuna rashin tsoro, ta kawar da kanta tare da cewa ""Ubanka ne"", ta fada tana karkaWa kanta."

"Ware idanunshi ya yi, da mugun Mamaki, cikin Azama ya damki wuyan hijab dinta tare da cewa ""Kutumar"

"Uba, dan Ubanki ni kike zagi?, Ashe Yau zan ci Ubanki kuwa"", ya fada yana zuba mata bulala a gadon bayanta."

"ihu mai karfi ta saki, tare da cewa, ""ba kaine kace Uban wa ya sani guduwa ba, kuma ai Ubanka na haWu dashi yace min in naga ana taron Makara na gudu, kuma dan na fada maka shine zaka duke ni"", ta fada tana ™o™arin"

"kwacewa, zuba mata bulalar ya kara yi a tsakiyar kanta, wadda ta zago har fuskarta, tuni shatin bulalar ya tsaga fuskarta ya yi, wani jaaa lokaci daya abunka da farar mace."

"jin yarda bulalar ta ratsa mata cikin jikinta, da kwanyarta har tana barazanar illata mata jinta da ganinta"

"yasa ta faWi kasa, yana ™o™arin riketa, ya mikar da ita, ta shige cikin rigarshi Yar shara,Makalewa tayi tana gunjin kuka, ™o™arin fiddota ya shiga yi, amma ta manne."

"gefen Mararshi ta samu, ta gasa mishi wani Lalataccen cizo, mai illata yan hanjin ciki, ri™e gurin tayu kam"

"ta™i sakinshi, zufa ce ta fara karyo mishi, cikin jikinshi, ba abin ya yi, ihu ba ace Malam na kuka, gashi kuma ya kasa cirota daga cikin jikinshi, haka ta ringa bi tana mammana mishi cizo duk inda ta samu, yakushi kuwa, babu inda bata ya kusa ba, ™o™arin cire rigar ya fara yi, amma ta rike kam taki sakin rigar, taki kuma daina cizonshi."

"ganin Yana niyyar kashe kanshi, yasa ya saki ihu tare da cewa ""Wayyo Jama'a ku kawo dauki, wannan"

"shegiyar ³ar zata kashe ni, wayyo Marata wayyo"", ya fada yana ™o™arin guduwa, hardewa ya yi, ya fadi cikin filin makarantar."

"birgima ya fara, yana kokarin cireta, amma abu yaci tura, hakan yasa yaci gaba da zunduma ihu, tuni"

"Malaman Makarantar sunzo sun zagayesu, dakyar da jibin goshi, suka samu suka fito da ita daga jikin Malam Arabi, ana fitar da ita ya fice daga makarantar da gudu, yana haki,bai tsaya ko ina ba sai da yaje gida, zubewa ya yi a tsakar gida yana haki, Matarshi ce ta kalleshi, tare da cewa ""Lafiya Malam"", girgiza kanshi ya fara yi, alamar ba lafiya, sai dai ya kasa yin magana."

"ruwa ta kawo mishi, dakyar ya sha, yana sha ya fara cewa ""Wallahi ba Mutum bace! ba mutum bace!! nace"

"miki Aljana ce"", ya fada yana zazzare idanu tare da le™en hanyar waje, ita kuwa ta kasa gane maganar da yake yi, sai binshi da kallon mamaki take, ganin sahun cizo na ha™ora raWo² akan fatar cikinshi, fa yakushi har kan kirji."

"sai lokacin ta lura da babu komai jikinshi sai gajeran wando, ""Malam ina rigarka?"", ta fada tana mishi"

"kallon tuhuma, ""na fada miki ba mutum bace"", cikin tsawa tace ""kai Malam yimin shiru, ashe halin da ka koma kenan, kwartanci ka fara, shine har da zuwamin ba riga, to ai na gani basai ka karamin wata magana ba, maci Amana kawai, kuma Wallahi naji dadi da aka maka haka, naso ma da sun gurguntar da kai, kaga kwartanci ya yi rana"", ta fads tana mikewa daga gurin ta shige Waki abinta."

************

"Bulali Malaman suka sanya aka cicciro musu, suka sanya Nazlah Office, zasu duketa, hankalinta in ya yi,"

"dubu ya tashi da ganin irin bulalan da aka zagayeta dasu, FaWuwa tayi a gurin , jikinta na wani kyarma, daga baya kuma ya saki bata ko motsi, daya daga cikin Malaman ne ga zabga mata bulala, akan ™afafunta, tare da cewa ""tashi Munafu™a yau sai kin gane kurenki, na abubuwan da kike yi, dama dama muke jira, yau kuma gata ta samu, ba Aljannu ba, ko Uban Aljannu ne yau sai mun ci ubansu"", ya fada yana yin ball da ™afafunta."

"wani Uban ihu ta kwarara, tare da fara wani Yare wanda duk cikinsu, babu wanda ya iya gane mai take"

"cewa, Malamin ne ya dagota tare da haWata da bango, ya dago bulala zai zabga mata, wani Wula™antaccen kallo ta watsa mishi, tare da sanya hannunta dauki wata bulala da take kusa da ita, ta zabga mishi akan sankonshi , a ruWe ya saki bulalar hannunshi, yana dafe kanshi da yaji kamar an sauke mishi shi, kafin ya yi wani yunkuri, ta kara zabga mishi a gadon bayanshi, gantsarewa ya yi, tare da sakin ihun azaba,"

"ganin tana dukanshi, yasa gaba daya Malaman suka yo kanta, tama cikinsu tayi, tana dukanshi suka dukanta, abun ka da Jinnu , karfi ba daya ba, tuni ta haWa musu jini da Majina, cewa take ""Uban waye yace ku taSa mana GoWiya, yau sai kun gane baku da wayau, dama ku Bil Adam dinan baku da mutunci, bakusan kawaici ba, kuma baku da kunya, daga Yau ko wani ne yace ku kara taSa ta zaku ga abin da zai faru da ku, marasu kunyan Wooofi kawai"", wata murya da sam batayi kama da tata ba ta fada, tana zazzare musu idanu, karatu suka haWa baki gurin yi mata."

"dariya ta she™e, da ita, tare da karasa musu karshen Ayar da suka dauko, haka suka dunga yi, tana dukansu suna karatu tana karasa musu, duk surar da suka dauko ita take karasa musu."

"da gudu, suka bude office din suka fice, ita kuwa Hamma ta buga tare da sulalewa a gurin Summamiya,"

"Malamai kowa ya kama gabanshi, Šaliban ma ganin Gwagwarmayar da akeyi yasa kowa warewa, dan babu mai zama anan wannan badaqalar............"

"Ga duk mai so, zai iya min magana ta number na kamar haka "

07033371851

```DAGA TASKAR SALMAJI / ³AR LELEN ROYAL/ SARAUNIYAR YA˜IN MARUBUTA```

"[12/21, 12:10 PM] YAR LELEN ROYAL STAR CE : *NAZLAH* "

*DAGA AL[]ALAMIN*

SALMAJI/[]AR LELEN ROYAL STAR CE

"*WANNAN LITTAFIN DAGA FARKONSHI HAR KARSHENSHI, SADAUKARWAR NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF)"

"WANNAN LITTAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KIYI YADDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI, YA KUMA K'ARA RUFA ASIRI DUNIYA DA LAHEERAH...*"

* ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION *

{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

"*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad akarwa, ilimantarwa da kuma nishad antarwa_*"

_(R.S.W.A) Ruwa kad ai ke maganin k ishi_

*Alk alaminmu  yancinmu*

13-14

"""""""""""""""""""""""""""""Babu wanda ya kula da Nazlah kowa ta kanshi ya yi, babu kuma wanda ya yi tunanin zuws gidansu ya"

faWi halin da take ciki.

"Ummu tana ta jiranta, dan an kawo mata kashedinta har gida, hakan yasa take jiranta taji ba'asin Abun da"

"ya faru, kafin ta dauki mataki a kanta, shiru² Nazlah bata dawo ba har gabanin Magrib, hakan yasa hankalinta ya tashi, ta kasa zaune ta ™asa tsaye, tana cikin Safa da marwa, Yah Haleem ya shigo, kallonta ya yi tare da cewa ""Ummu Lafiya kuwa?"", ya fada yana kallonta, da sauri ta juyo gareshi tare da cewa ""Nazlah ce bata dawo ba, tun Wazun da ta fita Islamiyya, gashi Abbanku baya nan, kuma ya hanani fita in baya nan, ko zaka je ka duba min ita ?"", ta fada tana kallonshi, ""to Ummu bari naje na duba"", ya fada yana juyawa."

"cikin sauri yake tafiya zuwa Makarantar tasu Nazlah dan duhu har ya fara rufawa, cikin sa'a ko da yaje"

"makarantar a bude take, sai dai ba kowa a ciki, hankalinshi ya fara tashi, cikin da™iya ya fara dudduba Ajujuwan Makarantar, sai dai ba kowa a ciki, kuma duk a bubude, cike da tsananin mamaki yake kallon Ofishin Malaman da yake a bude , kuma makarantar ba kowa, hankalinshi ne ya kaiga wani waren takalmi da ya gani yashe a ™asa kusa da Ofishin, tafiya ya fara yi zuwa ofishin, da sauri ya shiga yana furta ""Innalillahi Nazlah! Nazlah!! Nazlah!!!"", ya fada yana jijjigata."

"A hankali ta fara bude idanunta, da suka mata nauyi, ""Yah Haleem..! ta fada tana shigewa jikinshi"", mikewa"

"ya yi, da ita jikinshi ya nufi hanyar waje, da ita rungume a jikinshi, hanyar gida ya nufo da ita, yana cikin tafiya yaji an kwala mishi kira, da sauri ya juya yana kallon Iya da take nufoshi, da sauri ta ™araso gareshi tare da cewa ""kaga"

"Nazlan?"", Nuna mata ita ya yi, tare da cewa ""gata bacci na tarar da ita tana yi, babu kowa a makarantar sai ita daya"","

"ya fada yana direta ™asa, ganin yarda take ta mutsu² da son ya sauketa."

"Yana sauketa, ta Afka kan Iya tare da cewa, ""Iya goyani bacci nake ji"", ta fada tana riketa, da mamakina"

"babu ko kunya Iya ta du™a Nazlah ta haye bayanta, zaro ido Yah Haleem ya yi, tare da cewa ""Iya dama har yanzu baki daina goyata ba,kar ta je ta karyaki fa"", ya fada yana yun™urin dauke Nazlah daga bayan Iya."

"kaSe hannunshi Iya, tayi tare da cewa ""mai yasha ruwanka da harkarmu, baka ji tace bacci take ji ba, "" ta"

"fada tana zare dan kwallinta, kyakyawan dogon gashinta mai kyau ne ya bayyana, wanda duk da tsufar da tayi amma yananan sumul sai dai furfurar da ba'a rasa ba akan tsoffafi."

"dakyar take takawa da Nazlah akan bayanta amma haka take tafiya, Yah Haleem ya yi, ya yi ta sauko da"

"ita amma ta™i, sai ma kara kankameta da Nazlah tayi ta rumtse idanunta."

*************

"Da sauri ta bi bayanshi, tana shiga ta tarar dashi zaune gefen bed dinshi, ya buga uban tagumi, zama tayi"

"kusa dashi, tare da cewa ""lafiya kuwa My Solder?"", ta fada tana dafa kafaWarshi."

"dago idanunshi ya yi, ya watsasu cikin nata , Cikin faWa ya ce""wai ke ba zaki chanja halinki ba, duk abun"

"da ake fada miki va zakiji ba, bayan rashin kula da ni , hanzu kuma har wani sabon salo kika koya ba rashin tsafta, duba wai nan Wakin Mijinki ne, amma kacha² ba gyara ba komai, yanzu wannan rayuwar da kika daukarwa kanki kina tunanin mai daurewa ce, ?"" ya fada yana kallonta."

"cuno baki tayi gaba, tare da daura kanta akan kirjinshi, ""to ba yanzu , zan tashi na gyara ba"", ta fada tana"

"mikewa, bathroom dinshi ta fara wankewa, wanka ya shiga, kafin ta fito har ta gyara mishi bedroom, kallon Bedroom din ya yi, jinjina kanshi ya yi, tare da cewa "" tab da matsala kuwa"", ya fada yana kara kallon bedroom din , dan kawai sunan ta gyara ne, amma babu abun da ta wani gyara, shara ce tayi , sharar ma bata yi ba, dan chan da datti chan share, chan datti haka sharar tayi. , kallon Bedroom din ya yi, jinjina kanshi ya yi, tare da cewa "" tab da matsala kuwa"", ya fada yana kara kallon bedroom din , dan kawai sunan ta gyara ne, amma babu abun da ta wani gyara, shara ce tayi , sharar ma bata yi ba, dan chan da datti chan share, chan datti haka sharar tayi."

"Da sauri tazo gareshi, ta rungumeshi tana shafa kirjinshi, wata uwar tsawa ya daka mata, tare da cewa"

"""zaki matsa min anan ko sai na babbalaki"", ya fada yana

6 / 11