Author : Hafsat C Sodangi Category : KDP NOVELS
ce, "Uhm, Allah dai ya samu a
124
danshinku. Na ce, To Amin. Kin san
kuwa ban taba tunanin zuwanki ba.
Ta ce, Yaushe kuwa za ki yi tunanin
zuwana? Ai ke kam Hauwa'u ba ki da
kirki, daga kin yi aure sai ki ki mutane?
Na ce, Ayya, ba na samun fita ne. Ta
ce, Eh ai ban ga laifinki ba ko kadan ko ni
nayi aure na samu wadata haka ina za ni?
Ai sai kawai nayi zamana na yi ta shan
gara.
Na mike don kawowa Sadiya abinci da
kayan shaye-shaye da ciye-ciye saboda
hirar tata ba wani dadi take yi mun ba.
Don nasan Ishak yana jinta. Tana nufin
kenan don ka samu gidan miji mai wadata
shi kenan babu ruwanka da sauran
mutane?
Yan uwanka, 1yayenka da abokan
arziki. Idan kuma ya zamana shi ba shi da
lokacinka kamar Ishak fa? Sai ka yi ta
rayuwa kai kadai takamar ya wadataka'
125
Lalura kuma idan ta same ka fa? Na
debo abinda zan kawo mata na ajiye a
gabanta tana tambayana maigidan yana
nan ne?
Na ce, Eh yana barci. Na mike na shiga
dakin Ishak na zauna kusa da inda ya ajiye
kanshi don nayi maganar da zan yi a
hankali.
Na ce, Za kủ gaisa ne? bai ce mun
komai ba har na gaji da zamana na fito na
dawo falo muka ci gaba da hirar mu.
Na ce, Sadiya ya Makaranta? Ta ce, Ga
mu nan mun usa gamawa muna ta shirin
zana jarrabawa, Malam Ali kuwa kullum
sai ya tambaye ki.
Na ce, To da yake tambayata ai sai ki ce
mishi iyayena sun dauki shawarar da
kullum yake ba su sun kuma aurar da ni.
Tayi dariya, Ke Malam Ali fa
shakiyanci kawai yake yi miki. Amma ke
kin zauna kenan ba za ki koma Makaranta
ba?
126
Ke kina ganin hakan ya yi miki daidai?
Yanzu fa watan gobe ne za mu rubuta
jarrabawa kowa kuma sai ya kama
gabanshi a yi ta tafiya babu ke.
Karatu ai shi ne adon mace a duk
lokacin kuma da ta rasa shi to tayi babbar
asara, don kuwa ko aure ki ke yi ai ba kin
rinka zama ke kadai ba kenan wata rana za
a yi miki kishiya ki ka san wacce za a auro
miki?
Na yi nufin katse Sadiya na ce, Ke
Sadiya bar wannan maganar haka muyi
wata kuma. Na dauko wata hirar ina
tambayarta, Ni kuwa ina Zubaida?
Ta tabe baki ta ce, Uhum, tayi aure ita
ma har ma ta haihu ai tsiranku babu yawa.
Kema dai da alama cikin ne da ke tunda
gashi nan har ya fito.
Aini kam yanzu idan nayi aure family
planning zan yi kafin na gama karatuna
sannan na fara haihuwa. Na ce To idan
mijin naki bai yarda da hakan ba fa?
127
Ta ce, To yaushe dama zan sanar da shi,
ai tuni zan je nayi abina bai ma san lokacin
ba.
Ke! Cikin saurina waiwaya Ishak ne a
tsaye cikin wani irin bacin rai. "Tashi ki
fita a gidan nan."
Sadiya ta fara kokarin gaishe shi,
"Common get out, idiot! 'yan banzan yara
kawai marasa kunya."
Sadiya ta mike sum-sum-sum ta fita, ni
kuwa jikina sai bari yake yi ga kunya ga
takaici, "Ke kuma." Yana nuna ni da dan
yatsarshi "Ki kiyaye ni na gaya miki.
Ki san irin mutanen da za ki rinka kawo
mun gidana. Wanene Malam Ali?" Cikin
kuka na fara kokarin yi mishi bayani.
"Shut up dalla kiyi mun bayani. Na ce,
Malamin mune na Makaranta. "Menene
gaminki da shi da take yi miki maganar shi
iye?"
Taratsatsin bala'in da na gani a wajen
Ishak ranar ba kadan ba ne. Na lallaba na
128
hau gadona na kwanta, don kuwa na ga
da irin wadannan abubuwan.
Har hutunshi na sallah ya kare ya koma
bai yarda ya kai ni gida ba, wai a madadin
zuwan da nayi babu izininshi.
Yanzu kuwa kullum idan zai fita a gida
kullewa yake yi, ya yi tafiyarshi da nayi
mishi magana akan illar yin haka sai ya ce,
Idan ina da matsala nayi mishi waya ba zai
ji kuiyar zuwa ba, na ce To.
Don haka yanzu ni kadai ce nake wuni
a cikin gidan ko dan littattafan da nake
samu na daina.
A yanzu da nake cikin watanni na
takwas cikina ya bayyana sosai, kowa.
yana gani nima kuma ina matukar jin shi a
jikina, don kuwa abubuwa suna dan yi
mun wahala, kuma ba ni da mataimaki.
Shi kanshi Ishak ya lura da hakan,
amma ba zai iya hakura da halinshi ba.
Tashin da muka yi yau ba mai dadi ba ne a
wurina.
129
Don kuwa jikina yayi nauyi ba kadan
ba, da kyar nake motsawa. Ishak da kanshi
ya ce muje asibiti. Muna zaune gaban
Likita ya ce, Yaron a karkace yake
sakamakon da scanning dina ya bayar
kenan.
Don haka za a yi kokarin gyara mishi
kwanciya, don haka Ishak yaje gidanmu
ya sanar da Ummana, sannan ya dawo.
Ina zaune a bakin gadon dakin da aka
bani shi kuma yana zaune a kan kujera,
yanzu ya ya ki ke ganin zamu yi kenan
tunda dole naje wurin aiki, kina ganin ba
ki da wata matsala a kan hakan?
Na ce, Eh Umma zata zo ai. Ya ce, To
tunda haka ne bari na jira zuwanta kada a
bar ki ke kadai."
Sai washegari da safe ne aka yi mun
gyaran tare da kyakkyawan kashedin kada
na rinka aiki komai kankantarshi. Kwana
daya na kara a ka sallamo ni na dawo gida.
130
Da safe Ishak ne ya tashi ya hada mana
abin karyawa, ya share dakin gaba daya ya
shirya cikin sauri ya fita.
Na sha shayina na koma na kwanta,
wajen karfe daya sai ga dan aiken da ya
saba aikowa ya kawo mun abinci. Na bude
take a way ne na abinci mai kyan gaske."
Shinkafa fried rice da sálad da kuma
kwatan kaza. Da yamma kirana ya yi yana
tambayata abinda zai taho mun da shi, na
ce ni a koshe nake zan sha tea.
Duk da hakan bai fasa kawo mun wani
irin gashi ba na bankararren kifi da aka
gasa da lemon tsami yayi mun dadi ba
kadan ba.
Don haka na ci sosai. A daren yayi "yan
aikace-aikacen da zai yi bai kwanta ba sai
wajen karfe goma da rabi saboda wankin
da yayi na under wcars din shi.
Sanin halayyar Ishak yasa nake ta jin
shakkun yi mishi magana akan shawarar
131
da. nayi aina, sai dai duk da hakan ban
fasa ba.s
Ina kwanoe & gefehshi na ce, Ko zan yi
wa Umha magand ne ta samo mana wacce
2amu rinka. żarňa tare runda ka ga ni ko
wannan aikin ma da ka ke yi ba kai ne ya
kamáta kayi ba.
Ya ce, Kin ji nayi miki wani kora a
kan hakan? Na ce, To naji ba ka yi ba
amma idan naæo haihuwa fa?
Ya ce, Sai ki bari idan haihuwar tazo
kiyi magana, ba zan tsaya na yi ta jayayya
dashi ba don haka naja bakina nayi shiru.
llai ko ba a fi sati guda ba bayannan sa
na tashi da wani irin ciwon mara ma
musaltuwa, nayi ta wani irin murkususu ni
kadai a daki, don kuwa Ishak baya nan bai
dawo daga wurin aiki ba...
To bari mu jira dawowar Ishak din
muma, sai in ce mu hadu a littafi na biyu.
Taku;
Haj. Hafsat C. Sodangi
130