MAI DAKI BOOK 1 HAUSA NOVELS BY SODANGI.docx

Author :  Hafsat C Sodangi Category :  KDP NOVELS

Chapter   4 / 7

9K to 12K   out of 19.3K words

na sauran kwanakin.

Don haka na shirya mishi abin karyawa.

Ya fara ci kenan ya kalle ni Na baki

mintina goma kI shirya na sauke ki a

gida."

Ban san sanda na fara godiya ba, duk da

cewar mintina goman ba 1sa na za su y ba.

Na riga nayi wanka don haka atamfata

na dauko Exclusive na daura da gyalenta

da set din takalmi da Jaka 'yan taly, sai

yan canji na da ba su fi Naira dubu daya

ba.

Da wasu yan abin kwalam da nake

ajiyewa idan ya kawo sun ban sha'awa na

karewa dakin kallo na rasa abinda zan

kaiwa Umma.

66

Don haka na bude akwatin aurena da

zannuwa suke ciki na dauko mai kyau na

fara nadewa ban san ya shigo ba ya ce

"Me za ki yi da ita? "

Na rasa abinda zan ce, ya ce To

mayar. Na sake budewa na mayar

gwiwata a sanyaye.

A kofar gida ya ajiye ni na shiga rabona

da gidanmu watanni biyar. Haka na Umma

da Babana. Gani na rinka yi kamar ba ni ba.

Haka nan Umma ta rinka ina ta ka saka

da ni. Ta zuba mun ido ko kyaftawa bata

yi. Ni kuwa kunya duk tà kama ni.

Farin ciki mai yawa Umma ta nuna na

ganina. Ita ma na ganta tayi kyan gani ba

kadan ba.

Na bude Jakata na ciro ma su Tasi'u

Bueno cakulet da biskit kwali biyu na

mika musu suna ta murna, wanda iyakacin

kuma abinda na riko nusu kenan.

67

Ni ce na tashi yau ma nayi mana girkin

rana muna ta yar hirar mu da Umma.

Wacce ganin irin murnar da take yi ne

yasa ni kasa gaya mata mnaganar da ke cina

a cikin raina.

Wato maganar Makarantata. Ba zai

yiwu na dakushe mata wannan farin cikin

da take ciki na ganina ba.

Karfe hudu da rabi daidai sai ga

sallamar dan aika wai na fito na dauko

gyalena na zo inda Ishak ke hakimce a

cikin mota na dan risina ta gefe na ce "Ai

na dauka zaka shigo ku gaisa da Umma ne

ko da ba za ka bar ni na jira dawowan

Babana ba."

Ya ce, A'a ba zan shiga ba, fito

kawai. Na ce, "To." Na koma na ciro "yar

Naira dari taran da nake ta nuku-nuku na

kasa bai wa Umma, na mikawa su Tasi'u

nayi wa Umma sallama na fito zuciyata

kamar ta fashe.

68

Muka iso gida ya ajiye ni ya juya, ni

kuma na shiga kicin da nufin dorà abincin

dare.

Tunani nake yi na yadda zan rinka

taimakon iyayena, don kuwa ba zai yiwu.

na zauna a haka ba. Ishak ba ya bani ko

sisi zan iya cewa tun bayan aurena a shi

sile biyar bata shiga tsakanina da shi ba.

Haka nan duk wani abu na amfanin gida

shi ke kawowa bani da wata hanya da zan

bi na samu kudi da zan iya yi musu wani

abu. Ya zama mun dole nasan abin yin.

Tun daga ranar da na samu matsala da

Ishak kan zuwana gidan su Hindu ban

sake ba, sai dai da yake ya daina kulle ni

bayan na roki yayi mun hakan, to ita takan

shigo.

Mafita daya ce shi ne na dan rinka

taimaka musu da dan abinda za su ci

wanda shi kam ina da shi, don haka da

Hindu ta shigo na roke ta ta gayawa

Mominsu ina son aikanta gidanmu.

69

Na debi shinkafa mudu biyar da su

Taliya da cous-cous, man gyadan (Turkey)

da soyayyen nama da sauran abubuwan

amfani na hada mata rigijif ta kai ta dawo.

ow Zuciyata tayi mun dadi naji sanyi na

dan yi wani abu. Sai dai babban abin

takaicin shi ne, bayan kwanaki biyu kawai

da faruwar hakan sai naji wa'azi a Rediyo

ana yi na matar da ta yi wa miji kyauta da

abinci ba tare da ya sani ba, irin

hukuncinta.

Sai dai har idan ta tabbatar da shi din

ma zai yi hakan, to sai tayi da nufin Allah

ya ba shi ladan.

Nayi shiru a raina ina tunanin to shi zai

yarda da hakan ko kuwa shisshigi nayi? Ba

zai yiwu na gaya mishi ba kada na Ballo

wa kaina liki, tunda dai an ce haramun ne

gara kawai na nemi hanya da zan nemi

nawa ita ce ta hanyar dinki tunda na iva,

kuma ina da keken yin dinkin.

70

Sannan unguwarmu sabuwar unguwa

ce, da alama za a samu alheri idan mutum

ya ce zai yi wata sana'a.

Washegari asabar don haka Ishak yana

gida da rana. Sai da na gama aikace-

aikacena na gida sannan nazo falon da

yake na zauna na fara yi mishi magana kan

tunanin da nayi na dinki tunda na iya.

Amsar da ya bayar a gajarce ce, ita ce

idan ina gidanshi to ba zan yi dinki ba. Ba

zai lamunci irin wadannan abubuwan na

nuna karanta ba.

Ba ni da abin fada, don haka naja

bakina nayi shiru. Kamar yadda shima ya

yi. Bani da wani abu da nake yi da ya

wuce aikin gida da girki.

Wannan a yanzu nake rayuwa akai babu

abinda yafi damuna irin tsayawar karatuna.

Ba zan ce Ishak ya yaudareni da

1yayena ba, don kuwa matsayj shi ya

wuce hakan mijina ne.

71

Sannan babu wanda zai kalle ni ya ce

Ina da matsala don kuwa a bayyane yake

na samu canji. Kana kàllona ka san ina

cikin wadata,

Sai dai to iyavena fa? Wannan shi ne

babbar matsalata.

Yau ma zama nayi da nufin jiran

dawowar Ishak na nemi i2inin zuwa gida a

washegari don kada ya ce ban fada mishi

da wuri ba.

Ina matukar kewar Babana saboda zan

iya cewa tun da aka yi aurena rabona da

shi, a yanzu kuma wata na bakwai nake

ciki.

Na jira shi har na gaji na hau kan

doguwar kujerar dake dakin na kwanta.

Bai shigo ba sai karfe goma sha biyu

daidai.

Na mike zaune saboda jin motsin da

nayi na kuma yi mishi sannu' ya amsa: Ban

tsaya zancen kawo mishi abinci ba don

72

kuwa ma a yanzu idan ya dawo ba yaci ko

na kawo mishi,

Ban yi mishi maganar ba sai da ya

kammala shirin kwanciya sannan na fara

kokarin yi mishi maganar.

Bai bar ni ba saboda dago mun hannu

da yayi alamar dakatawa.

Wai ke ba ki da wata magana ne sai ta

gidanku? Mits! Yayi tsaki ya yi

kwanciyarshi.

Sai mutum ya wuni aiki amma idan ya

dawo gida a maimakon a barshi ya huta

wai sai a tasa shi a gaba da surutan banza.

Ya ja abin ruhuwarshi ya kwanta.

Na riga na saba da dabi'un Ishak, don

haka a yanzu ba su cika damuna ba.

Washegari har na gama mishi shirinshi na

karyawa da sauran abubuwan shi na tafiya

aiki a raina ina tunanin zai yi mun

maganar zuwana gida da nayi mishi bai ce

komai ba ya tafi.

73

A duk 1ökacin da ya tafi aiki na kan

dauki wayata na kira Hindu ta taya ni hira,

hakan ne yasa muka yi wata irin shakuwa

ba kadan ba.

Hindu wayayyiyar yarinya ce ba kadan

ba, haka nan yanayin irin gidajen da muka

tashi ma ba daya ba ne.

Don kuwa kamar yadda nake "yar talaka

ita kuwa ya ce ga babban Ma'aikacin

Gwamnati, Mominsu ma wayayyiyar mace ce.

Wunin da nake yi da ita a cikin gida

yayi matukar taimaka mun kwarai da

gaske kan al'amurana. Ban taba zama na

fada mata wani abu game da mijina ba,

amma sai ta gane hakan.

Wanda yasa ta yi mun magana, ban

saurari abin ba don ganin da nake yi mata

na cewa ita din ko da muke kusan sa'o'in

juna ita ba macen aure ba ce.

74

Haka nan kullum Umma tana gaya mun

na rike sirrina. Don haka ko da ta yi mun

magana murmushi kawai nayi.

An dan dade kafin na samu Ishak ya

bani izinin zuwa gida. na zaune cikin

motar daidai ya tsaya a kofar gidanmü na

ce mishi "Ko za ka bar ni ne zuwa dare

don na gaisa da Babana?"

Bai ce komai ba, nima kuma ban sake

yin magana ba. Hira sosai muka yi da

Umma ina mata korafin ba a taba kawo

min su Tasi'u ba

Tayi murmushi ta ce, "To sai ki gayawa

Babanku tukunna. Na ce, "To." Babana

ba karamin jin dadin ganina ya yi ba.

Yayi ta murmushi ba iyaka, yana ta dan

yi mun tambayoyi ina ba shi amsa tare da

jaddada tambaya daya da yake yi min.

Babu matsala dai ko Hauwa'u? Na

ce, "A'a babu." Ya ce, "To ki yi ta hakuri

kin ji, shi zaman tare hakuri ake yi."

75

Na ce, "To Baba." Kamar na danne

abinda ke damuna sai dai na kasa. Na ce

"Baba sai dai maganar Makarantata ne har

yanzu shiru.

Nayi mishi bayanin yadda muka yi da

Ishak ya dan yi shiru zuwa can ya ce, "Too

babban al'amari a wurin mu ai shi ne ki

zauna lafiya a dakin aurenki.

Kuma ga dukkan alamu kina da

kwanciyar hankali. Ita maganar karatu tana

zuwa ne daga baya.

Amma tunda dama can yasan da

maganar ina ganin bari ni da kaina nayi

mishi tuni muji abin da zai ce."

Tun kan Ishak yazo daukana nayi wa

Babana magana akan ina bukatar su Tasi'u

su zo min kwana biyu, ya ce "To."

Ba a wani dade ba rannan kawai da rana

sai ga Yaya Auwalu da su Tasi'u da dan

kayansu a kullin leda.

76

Murnata bata boyuwa, na rasa inda zan

ajiye su. Nan da nan na shiga kicin na fara

ajiye musu dan abinda nake dashi.

Muka yi hira da Yaya Auwalu sosai

daga ni kuma ya yaba da inda nake don

kuwa bai taba zuwa ba shima sai yau.

Ya jima sosai kafin yayi mun sallama

ya tafi, ya bar mun Tasi'u da Sadisu akan

za su y1 mun sati guda.

Muka wuni muna harkokinmu ba kadan

ba cikin raha da jin dadi. Hindu kuma tazo

ta debe su ta kai wa Mominsu suka gaisaa

suka dawo tare da kaninta Abubakar.

Da daddare kuwa hira muka sha ba

kadan ba, nayi dariyar abubuwan da suke

bani labari har na gaji.

Rabon da naji dadi irin a yau har na

manta. Ba su yi barci da wuri ba saboda

kallon da suke yi sai wajen karfe goma na

dare kafin nan kuwa ni kaina na gaji.

Nayi wanka na gyara na hau gadona na

kwanta, kan ka ce meye har nayi barci

77

abinda ya hana ni jin dawowar Ishak don

kuwa ban farka daga barci ba sai da naji

kiran sallar Asubahi,

Da sassafe Ishak ya fita wanda shi ne

dalilin da ya sa ban tuna gaya mishi zuwaan

su Tasiu ba sai bayan tafiyarshi.

A yau mna wuni muka yi muna

harkokinmu. Nayi mana abinci mai dadi

dafadukar taliya da taji hanta ga kuma

farfesun kayan ciki, don kuwa nasan babu

abinda suke so irin taliyar.

Yau ma sai da muka yi hirarmu wajen

karfe goma sannan na shinfide su a dayan

dakin na gyara musu komai na fito na hau

gadona ina tunani a raina irin kewar da zan

ji ranar da su Tasi'u za su koma gida.

Idan da da hali da na roki Umma ko

Babanmu su bar mun su Tasi'u.

Kwanciyar nayi da nufin na yiwa Ishak

maganar idan ya amince to, tunda muna da

wadatar waje.

78

Yau ma ban san sanda ya dawo ba

saboda barci mai nauyi da ya dauke ni.

Can cikin barcina naji kamar ana kirana.

Na bude ido cikin sauri saboda gane ba

mafarki nake yi ba. Sadisu ne. Sai dai ba

ni kadai ce na tashi ba har da Ishak.

"Menene ya faru Sadisu? Ya ce,

"Aunty zan yi fitsari ne." Na mike cikin

sanyin jiki saboda irin kallon da Ishak

yake yi mun, na dawo dakin da suke nasa

shi a bayan gida yay.

Na sake shimfide shi ina kara jaddada

musu in sun ji wata bukata ba sai sun tashe

ni ba su shiga bandaki kawai su yi.

Na kuma gaya musu hakan tun kafin su

kwanta amma kuma sha'ani irin na yaro.

Na shigo dakin, Ishak yana zaune a kan

bakin gadon nayi nufin wucewa naje na

kwanta, duk kuwa da sanin da nayi na

cewa ni yake jira.

79

Sai, dai yanayin shi da ke sani cikin

faduwar gaba. "Zo nan. Abinda yace mun

kenan.

Na nemi wuri a kasa na zauna. Me

wadannan yaran suke yi mun a gida?

Lafazin da yayi amfani da shi yasa na rasa

abunda zan ce, ko kuma ta inda zan fara.

Cikin daga murya ya ce, "Ba ki ji

abinda na ce ba ne ko ya ya? Na ce, "Eh

naji, ba ka gane su ba ne? Su Tasi'une fa

da Sadisu kannena.

"Hala kin ga alamar makanta ne a tare

da ni ko? Nayi maza na ce "A'a ba haka

ba ne."

Idan na ce zan tsaya fadin irin tashin

hankalin da na gani ranar a tare da lshak to

nayi karya. Duk kuwa da irin bayanan da

nayi mishi wanda ko saurarona bai yi ba.

Maganar kuwa da muka wayi gari da ita

ita ce, ta bai yarda su sake kwana mishi a

gida ba, maza-maza na sa a mayar da su

kwana biyun da suka yi ya isa haka.

80

Bai ci komai ba ya fita. Bai bani kudin

motar mayar da su ba, duk kuwa da yasan

banida ko asi.

Nayi iyakacin kokarina wajen juriya

kada 'yan yaran nan su fahimci wani abu.

Tasi'u bai fi shekara shida ba, shi kuwa

Sadi yafi uku amma bai cika hudu ba.

Yan kannena da nake da su amma wai

Ishak ba zai iya mu'amalla da su ba.

To sai da wa? Ko da yake ni din ma da

ya aura ga irin yadda yake tafiyar da ni.

Sanin hakan da nayi bai hana ni bakin ciki

mai yawa ba. Biye mishi zan yi?

Ko kuwa dai zan nemi mafita ne? Na

gama ayyukana nayi lullubi tare da rufe

gidan na shiga gidan su Hindu.

Mominsu tana daki nayi sallama na

shiga, na bar su Tasi'u a wajen yara suna

wasa. Ban boyewa Momi komai ba.

Ta tashi ta shiga daki ta dauko kudi

masu yawa ta bani ta ce "Ki koma gida

81

idan Hindu ta dawo zan turo miki ita sai ki

bata ta mayar da su gida.

Kiyi hakuri, ki kuma yiwa mijinki

iyakacin biyayyar da za ki iya idan har

bata sabon Ubangiji ba ce.

Kada ki să damuwa a ranki ko kuma ki

ce wai za ki yi fushi da shi kin ji ko?" Na

ce "Eh."

Na dawo gida na ci gaba da kwanciya,

don kuwana rasa kuzari tunani iri-iri a

cikin raina.

To da Ishak ya yi mun haka a kan

kannena shi nashi 'yan uwan baya tunanin

za su iya zuwa ko kuwa idan suka zo ya ya

yake so ayi?

Na sake yin shiru, to a zaman da nake

yi ma zan iya cewa bai taba yi mun wata

magana ta game da 'yan uwanshi ba kamar

yadda ban taba ganin wani yazo ya ce shi

abokin shi ne ba.

82

Nayi saurin mikewa na zauna ina wasu

yan anane-tunane a raina, tambayoyi iri-

iri da nake bukatar na samu amsarsu...

Sallamar Abubakar kanin Hindu ne ya

katse mun tunanina. Ya miko inun bakar

leda ya ce "Ga shi in ji Momi. Na karba

ina dubawa.

Littattafai ne na Hausa da alama ta bani

ne na samu na karanta ni ba ma'abociyar

karatun ba ne, amma sai naga barı na ajiye

kada ta ce na gwasaleta.

Na mike don samarwa kaina abinda zan

Ci tunda yamma ta fara yi. Chives kawai

na soya da kwai naci na sha shayi aka:

sannan nayi sailar Magriba.

Ina idar da saliah sai kawa naji

sallamar shigowar Ishak, mamaki ne yayi

Ihatukar kama ni, zan iya cewa tunda, aka

yi aurenmu ya koma aiki bai taba dawowa

kafin ayi saliar isha'i ba.

Asali na ya dawo karie tara yayi sauri.

Na mike ina nade dardumar sallah tare da

83

yi mishi sannu da zuwa, bai amsa ba don

dama nasan hakan ne zai biyo baya.

Saboda zai yi mun abu wanda zai sani

bakin ciki amma shi ne kuma mai yin

fushi idan har ba hakun na bashi ba, kuma

to ba zai taba saukowa ba.

Sai dai a wannan tunda dai nasan ban yi

mishi wani laiff ba, to nima ban shirya

bada hakurin ba.

Na shiga kicin cikin sauri nayi mishi

abinda zai ci, fried rice da farfesun danyen

kifi wanda duka aikin bai dauke ni awa

guda ba.

Na kawo na ajiye mishi. Sai dai ban

ganshi a falon ba. Na shiga cikin dakin

kwananmu nan ma hakan. buruntun da

naji a daya dakin ne yasa ni lekawa.

Gyarawa yake yi yana kakkawar da

wasu abubuwa duk da dai har da ba a wani

amfani da daki banabarin shi da datti.

Ine tsaye ina kallon 'irin gyaran da yake

yi na shiga daki na dauko wani zanin

84

gadon na shimfida akan gadon na sa

tsintsiya na share dakin.

Bai ce mun kala ba ya shiga asalin

dakinmu ya fara kwaso kayan shi yana

maida su daya dakin.

Aikin da ya dauke shi har karfe goman

dare, don kuwa tsinke nashi sai da ya

dauke ya kai shi daya dakin, kuma ya

gyare shi tsaf ina zaune a. falon ina

kallonshi.

Ya shiga bandaki yayi wanka ya bada

tea yasha bai ko kalli abincin da na ajiye

mishi ba ya shiga sabon dakinshi ya

kwanta.

Ba sai na jira an yi mun wani bayani ba

nima da kaina na fahimci abinda hakan

yake nufi, nima sai na shiga tsohon

dakinmu ko kuma na ce na asalin na

kwanta.

Al'amarin Ishak ba na

4 / 7