Author : Hafsat C Sodangi Category : KDP NOVELS
kuwa na fara fidda rai abinda
kwata-kwata ban saba yi ba kenan.
26
Dabi'ata ce kullum Zan yi bitar
littattafai na koda nake da matsala wajen
biyan kudin Makaranta ni din ina cikin
daliban aji da suke da matukar kokari.
Tunda har Malamaina ma sun shaida
hakan, to amma ya zan yi? Malam Ali ya
taso ni a gaba, bana kuma ganin laifinshi
tunda aikinshi yake yi.
Duk wadannan tunanina ne kafin
wayewar gari, don kuwa tsintar kaina nayi
da fara shirin Makaranta, har na fito tunda
sammako nayi ina yiwa Babana sallama
wanda a yau din zan riga shi tafiya.
Ya ce, "Ke Hauwa'u ba Ummanku jiya
ta ce mun satin nan kaf idan ki ka je
Makaranta koro ki ake yi ba?
Na ce, "Eh haka ne Baba." Ya ce, "To
amma a hakan ke gara miki kiyi ta zuwa
ana korarki? Maganar gaskiya shi ne nayi
niyyar baki wani abu ki kai Makarantar
taku.
27
To sai dai mu mamatsalar wurin aikin
mu yawa ce da ita tunda wannan watan shi
ne wata na wajen uku da ba a bamu
albashi ba, amma daga zarar an bamu wani
abu zan ba ki ki kai musu ko da babu yawa
ne. Sai ki ba su hakuri yau din idan kin
je."
Na ce, "To Baba." Na fito daga gida ina
tafiya tare da tunanin maganar Babana ni
ba abin in ce mishi ai yanzu ta kai ma ko
saurarona basa yi ba.
sli Babu amfani tunda ba da gangan yake
Rin biya ba.
Na shiga aji na zauna a darare ganin har
karfe tara tayi Malam Ali bai zo ba, sai na
waiwaya bayana inda Sadiya Tanimu ke
zaune.
Saidai ban ganta ba, don haka na ce wa
wacce suke zaune tare rmai suna Zubaida.
DunsDon Allah dan bani aron littafinki ná
Chemistry na dan fara kwafa kafin a
tashi.
28
Ta kalle ni ta dan tabe baki tare da
girgiza kanta kafin ta ce, "A'a a gaskiya ba
zan miki karya ba, ba zan iya ba haka
kawai azo a kore ki na manta ki wuce mun
da littafi.
Bari dai wacce ta saba baki tazo don
naga itama kamar ke karatun ba damunta
yayi ba, bambancinku kawai ita ana biya
mata kudin Makaranta."
Na juyo na ci gaba da wasu sabgogin ba
tare da na tsaya bai wa Zubaida amsa ba.
Ba a ko kai mintina biyar ba bayan nan
sai kawai Malam Ali ya shigo. Tun kafin
ya fara kiran suna na mike na kamo hanyar
dawowa gida, zuciyata cike da kunci da
6acin rai.
Har naZO zan shiga gida sai naji ana
kirana,Abdussamad ne. Na tsaya ya
karaso inda nake.
Hauwa'u kenan, yau ma kin kasa zama
ne kiyi karatun har zuwa lokacin tashi?
29
Wani gululun bakin ciki ya taso ya
tokare ni, wai wannan me yake nufi ne?
Na dago kaina da niyyar ba shi amsa.
Sai dai na kasa saboda dama kiris nake
jira, don haka da na lura kawai kuka zai
kubucemun sai na shige gida ba tare da na
sake sauraronshi ba.
Ina shiga gida wurin Umma na wuce na
durkusa, kuka na kama yi babu
kakkautawa, ba tace mun komai ba sai da
nayi ya ishe ni ina share hawayena sai ta
ce "To ni kam Hauwa'u ai bani da abin yi
miki da ya wuce na ki hakura da wannan
sintiri da ki ke yi ana koro ki ba tare da
fashi ba.
Ki dan saurara kema ki samu nutsuwa
amadadin wannan zirga-zirgan da ki ke yi.
Idan Babanku ya samu kudi ai ya gaya
miki zai ba ki dan wani abu ki kai musu
ko? Kafin karshen wata muga abinda
Allah zai yi."
30
Na dawo daki na debi kayan wanki na
fitar na hado da na su Tasi'u gaba daya na
fara yi, sai wajen Azahar na gama nayi
wanka na nemi wuri na zauna da niyyar
hutawa a ka yi sallama da ni.
Na riga nasan Abdussamad ne, don
haka kamar ba zani ba sai kuma na dauki
gyalena na fita.
Yana tsaye a kofar gidanmu sanye da
wandon Jeans da riga shirt fitted na gaishe
shi a dake.
Ya ce, Hakuri nazo baki don naga
kamar dazu na bata miki rai, kiyi hakuri
ban yi da nufi ba. Na ce "Babu komai.
Ya ce, "Kin tabbata?
Na dan yi murmushi na ce, "Uhum!"
saboda yanayin yadda ya yi tambayar. Ya
ce, "Ban san dalili ba Hauwa'u, sai nake
ganin kamar ni din ina da ruwa a cikin
al amarin karatunki.
Don kUwa ko babu komai ai ke kanwata
ce. ko ba haka ba? Na ce, "Eh haka ne.
31
Ya ce, "To 1dan mutum ya samu halin yin
abu to baya sakaci da wannan damar har ta
kubuce mishi.
Kiyi amfani da kuruciyarki ki taimaki
kanki kiyi karatu. Muka shiga wata hirar
ta daban, yana tambayata wasu abubuwan
ina ba shi amsa har Babana ya dawo.
Yau ma ya gaishe shi ya wuce na biyo
shi a baya yana tambayataYau an bar ki
kin yi karatun ko kuwa an sake koro ki?
Na ce, An koro ni Baba. Ya ce,To
sai kiyi hakuri muga abin da Allah zai yi."
Na ce, "To.
Har satin ya kare ban koma Makaranta
ba, haka nan kullum bayan sallar La'asar
Abdussamad yana zuwa mun hira.
Ranar Lahadi da yamma kwatsam sai
ga Sadiya Tanimu, na tare ta cikin farin
ciki ba kadan ba. Makwabtanmu na tura
aka sayo mun Zobo mai tsabta,
32
Na kuma yi sa'a dafaduka muka yi ma1
Kyau ta kuma yi dadi na kai mata dakina
bayan sun gaisa da Umma.
Tana cin abincin muna dan hira tana
bani labarin abubuwan da suka faru bana
nan, da irin gwajin da aka yiyyi a aji.
Naji wani iri a raina. Ta tashi zata tafi
na mike da niyyar yi mata rakiya. Da nisa
sosai na kaita har kusan barin unguwarmu
gaba daya.
Ta wuce ni kuma na kama hanyar
dawowa gida.
Baiwar Allah salamu alaikum. Jin
yanayin sallamar ne ya sani juyawa, wani
mutum ne a tsaye sanye cikin farar shadda
jamfa da wando.
Na amsa tare da nufin ci gaba da tafiya.
Dan dakata mana yanmata. Tun daga
dan nesa fa nake bin ki ban dai yi miki
magana ba ne saboda ganin yanayinki.
Na san ba yarda za ki yi ki tsaya cikin
mutane ba, shi yasa ban tsaida ke ba sai da
33
naga mun zo nan wurin. Sunanki nake so
ki fada mun.
Na ce, "Hauwa'u. 99 Ya ce, Gidanku
fa? Ba tare da yin wani dogon tunani ba
na yi mishi kwatance.Ya ce, "To ya
gode. Na dawo gida na ci gaba da
harkokina.
Har a yau Monday ma ban yi nufin
zuwa Makaranta ba, saboda maganar da
Babana ya yi mun na jiranshi zuwa
karshen wata don ganin abin da Allah zai yi.
Da yamma ne aka yI sallama da ni,
cikin zuciyata Abdussamad ne, don haka
hijabina na dauko na fito ga zatona
Abdussamad din ne, Sai kawai naga
mutumin jiya.
Yau ma sanye yake cikin tafafe na
kamala, jamfa da wando, rigar half jamla
ta matukar yi mishi kyau.
34
"Ina wuni? Na fara gaishe shi cikin
girmamawa, don kuwa ba karamin yaro ba
ne.
Lafiya Hauwa'u, yaya karatu? Na ce,
"Mun gode Allah."
"A aji nawa ki ke a Makaranta? Na
gaya mishi ya dan yi murmushi "Kina da
saura dai ashe." Muka dan yi hirar karatu
kadan, abinda ya sa na saki jiki da shi.
"Kina da sha'awar yin karatu mai zurfi
ne? Ko za ki tsaya ne daga gama
Secondary?" Na ce, "Idan na samu halin ci
gaba haka nake so."
Ya ce, Eh yana da kyau, kin san
karatun 'ya mace ba karamin abu ba ne ga
ya'yanta, da kuma mijinta baki daya.
A daidai lokacin ne Abdussamad yazo,
ganinmu yasa shi juyawa ya tafi. Mutumin
ya kalle ni yana dan murmushi.
Ina fata dai ban tsarewa saurayin naki
wuri ba'? Na ce, "A'a ba saurayina ba ne.
Ya ce, "Menene, abokinki ne?"
35
Na dan yi murmushi, ya dan yi ajiyar
ZUciya ya ce, "To Malama Hauwa'u, ni dai
kin ganni ba yaro ba ne karami, don haka
ya kamata ki gane ba da wasa ko yaudara
nazo wajen ki ba.
Na gan ki ne na yaba da halinki da
kuma dabi'arki ta nutsuwa da na gani a
tare da ke. Ni ba mutumin garin nan ba ne,
nazo wani dan aiki ne wanda nake ganin
kamar zai dauke ni tsawon shekaru uku
zuwa hudu.
Sunana Ishak, ina kuma aiki ne da
Ma'aikatar noma wato (Ministry of
Agriculture). Ina fata zan samu hadin kan
da nake nema a.tare da ke?
Ina so na gaya miki ba zan tauye ki na
hana ki karatunki ba, don kuwa kina da
kuruciya sosai. ldan aka yi miki hakan ba
a yi miki adalci ba.
Don haka ina so kiyi tunani mai yawa a
kai zan dawo rana ita yau din nan don jin
abin da ki ke ciki.
36
Na ce, To. Y asa hannu ya miko mun
kudi, ya ce "Ungo wannan. Na dan yi jim
kamar ba zan karba ba, ya ce "A'a karbi
kawai."
Na ce,To na gode. Sannan ya bude
bayan motar shi ya sauke mana doya
manya goma da buhun shinkafa da wata
leda babba baka.
Yayi sallamaya tafi. Na dade a wurin a
tsaye kafin na shiga gida.
Ummma ta zubawa kayan idanu ta ce,
"Ikon Allah! Shi kuma wannan ko waye
sai Allah. Na zauna na jawo ledar na bude,
zannuwa ne masu kyau guda biyu da
kayan shafa masu daraja.
Sai da Babana yaci abincine sannan ya
kira ni na same shi a zaune. "Ke Hauwa'u
ashe dama kin fara tsayuwa da samar1 ne
ni ban sani ba?
Naji wani iri a cikin jikina, na kuma
rasa abinda zan ce mishi. Ya ce, Ke ía
nake sauraro don ni nayi zaton shi wanan
37
yaro Abdussamad da nake ganinku da shi
ba wani abu ba ne a tsakaninku face
makwabtaka da mutunci.
To shi kuma wannan a ina ki ka same
shi?" Nayi wa Babana bayanin komai
game da mutumin, har da ranar gamuwvata
da shi da kuma abinda ya gaya mun da kan
shi ya ce "To tashi ki tafi."
Na dawo dakina na zauna bayan na kai1
wa Umma har da kayan atamfofin da
kudin wanda ta mika su ga Babana gaba
daya.
Washegari Abdussamad bai zo ba
kamar yadda ya saba, sai bayan kwana
biyu ne inda dawowa daga siyo sugan da
naje yi a shagon unguwarmu, na ganshi
tsaye kusa da shagon
Ya ce, "Hajiya Hauwa'u. Na ce Ni
din ce kuma Hajiya a yau? Ya ce Eh
mana, ba dole nace FlajIya ba, wannan irin
luntsumemiyar mota haka a1 kin san mai
niya ake cewa llajiya ba wanda yaje ba
38
Kin ga yanzu dole mu rinka yi a hankali
kenan tunda Tunku ma yasan shurin da
yake yi wa kashi.
Na ce, "Haka ne." Ban tsaya cigaba da
jin abinda yake fada ba, tunda na fahimci
so yake ya soka mun magana sai kawai
nayi gaba.
Ranar da Ishak ya ce zai zo kuwa sai
gashi ya dawo, na kuma isar da sakon
Mahaifina a gare shi ta yana son ganinshi.
Bai tsaya wani dogon bata lokaci ba ya
ce, zai jira shi ba sai yaje ya dawo ba, don
haka shigowa gida nayi na bar shi da nufin
shi na sai yaga Babana kafin ya tafi.
Hakan kuwa aka yi, ban san yadda suka
yi ba, bani kuma da damar tambaya, don
haka harkokina kawai nasa a gabana.
Na dai yi nufin tambayar Umma ko
Babana zai bani kudin nan naje na biya
kudin Makaranta dashi, sai dai na gagara
saboda nauyin da nake ji.
39
Ban yi zaton zuwanshi a washegari ba,
kwatsam sai ga shi. Ina tsaye yayin da
yake jingine jikin motarshi ya ceNa
dawo ne yau don nayi miki magana kan
al'amuran da muka tattauna da Baba.
Muyi magana da ni da ke saboda
fahimtar juna. Jiya ganin da nayi mishi ya
bani izinin turo magabatana don daidaita
maganar aure."
Cikin wani irin mummunan faduwan
gaba na dago kai na kalle shi, karo na
farko da nayi hakan a karo na uku da fara
Zuwanshi gidanmu.
Yana cikin matsakaitan mutane, shi din
ba kyakkyawa ba ne, haka nan ba za a kira
shi mummuna ba.
Shi da kanshi ya lura da canzawata, ya
ce "Shi yasa na ce zan ganki don mu
tattauna a tsakaninmu. Kina da matsala a
kan turo magabatana da zan yi?
A hankali na girgiza kaina alamar a'a,
don kuwa babu wani hukunci da Babana
40
Zai zartar na sa kafa na shure shi da sanina,
kuma ina cikin hayyacina ba.
Ya ce, To ya naga yanayinki ya
canza? Ban san dalili ba sai na samu
kaina da ce mishi "Karatu nake yi." Ya
dan yi murmushi.
Don ta wannan nayi wa Mahaifinki
alkawarin zan sa ki a Makaranta kiyi ta
karatun har ki gama, bayan wannan kuma
sai me? na ce, "Babu." Ya ce, "To ni
ranar Jumma'a zan tafi Kaduna gida wurin
iyayena, don mu zanta kan maganar.
Na ce, "To Allah ya kiyaye hanya." Ya
ce, Amin. Ya miko mun kudi a
hannunshi na karba tare da godiya.
Duk yadda na kai da daurewa da na
zauna gaban Umma zan yi mata magana
sai kawai na fashe da kuka.
9T6 Menene kuma na kuka? Ta tambaye
ni fuskarta a yamutse. Na ce "Umma daga
zuwa biyu sai kawai maganar aure, ko
41
gama saninshi bamu yi ba, sannan
karatuna fa?"
Tayi shiru ta ci gaba da saka maballan
gar da na samu ta gama, an kai kamar
mintina biyar sannan ta fara yin magana.
"Babanki ba shi da halin daukar
dawainiyar Makarantarki, kema kin san da
haka. A yanzu ma da ki ke Makarantar
Secondary abin ya gagara ballantana kin
shiga wacce ki ke burin yi ta koyon jinya.
Idan da kina da zurfin tunani kema ya
kamata ace kin fahimci hakan. ke kadai ce
a cikin ku bakwai ki ke ka ratun nan,
amma a biya miki kudin Makaranta ma
abin ya gagara.
Babanku yana zuwa wurin aikin nan da
yake yi ne kawai ba wai don kudin da ake
ba shi ba tunda a yanzu ba biya ake yi ba
sai don kawai kada ya zauna a gida ba tare
da yana da abin yi ba.
Ba kuma zai yiwu ya ce takamar ke da
shi kuna son kiyi karatu ya yi ta ajiye ki a
42
gida ba, ke mace ce. Kin kai lokacin aure
tunda kuma sh1 ya ce ya yaba da kamalar
mutumin.
Ina ganin shi kenan magana ta kare, ya
kuma yi alkawarin zai tsaya yaga kin yi
karatun da ki ke son yi.
Na tashi na dawo dakina na kwanta
saboda yanayin da jikina ya yi mun, aure a
yanzu? Babu abinda ke zagaya mun
kwakwalwata irin ko wata guda ban yi da
sanin mutumin ba.
To amma tunda dai yayi alkawarin zan
yi karatu shi kenan magana ta kare, dama
burina kenan idan na samu hakan kuma
zan yi murna.
Bayan nan ban sake zuwa Makaranta ba
saboa abinda Babana ya ce kenan a jinkirta
aga yadda maganar zata kaya.
Na ci gaba da karatun a dakina. Sati
biyune kawai bayan nan iyayen Ishak suka
zo an sasanta da su har an daidaita lokacin
aure don suma suna son shi da gaggawa.
43
Sun kuma zo da kayansu na na gani ina
So. Tun daga lokacin da maganar aurena ta
yadu ban sake ganin Abdussamad na
gaishe shi ya amsa ba wani lokacin ma
yana hango ni yake kaucewa.
Ban san abinda yake nufi ba, don haka
nima sai kawai na share shi.
Shirye-shirye na nima nake yi da
iyakacin karfina tunda dai ba zance bana
son Ishak ba, kamar yadda ba zan ce ina
Son shi ba.
Babban burina dai da nake hangowa
kamar nishadi. Ishak da kanshi ya
shaidawa iyayena ba ya bukatar wata
doguwar dawainiya da ta danganci kayan
daki, shi gidanshi akwai komai.
Don haka shirin da Umma ma take yi
ya dan yi sauki kokarinta kawaina ganin ta
hada mun kayan kicin ne ta kuma saya
mun sabon Keke gau a kwalinshi.
Tunda nima ta koya mun dinki na kuma
iya daidai gwargwado. A shirye-shiryen da
44
aka yi mun a gida kuwa har da na zuwan
garin ma garin Babana Birmin Kudu, duk
kuwa da suma za su zo bikin.
An yi mun shirye-shirye masu yawa
daga gida amma duk da haka sai da Ishak
ya kawo kudi masu yawa ya kara mun.
Zan iya cewa tun da aka fara maganar
aurena da shi al'amarin da yanayin
gidanmu gaba daya ya canza, don kuwa
duk zuwan da zai yi zai kawo kudi masu
dan dama ya bani.
Haka nan ba zai rasa abin amfani da zai
sauke mana ba. Tun da farko da Babana
yana karba ya hana ni am fani da kayan da
yake bani.
Amma da aka zo magana tayi karfi sai
ya bar ni har da kayan da yake kawo mun
na zannuwa yana karba yanzu duk ya
dawo mun da su.
Ni kuma na kai an diddinke mun su, ina
ta kwalliyata gwanin sha'awa. Wani lokaci
45
sai nayi tunani na ce to a waje ma ya
wadata ni haka ina kuma ga naje gidan shi.
Kwanaki uku kawai nayi a birnin kudu
duk kuwa da yawan 'yan uwan Babana da
ke garin saboda gabatowar bukina na
gaiyato kawayena irin su Sadiya da wasu
daga cikin ajinmu da na san muna mutunci
da su.
Na kuma gayyato Lubabatu kanwar
Abdussamad da muke unguwa daya da su
gashi kuma dama tare muka tashi tunda
sa'o'i muke.
Ina zaune a dakina ina shafa mai na mai
tsada Ishak ne ya ke saya mun shi wanda a
yanzu ya mayar mun da jikina tamfar
wacce aka