MAI DAKI BOOK 1 HAUSA NOVELS BY SODANGI.docx

Author :  Hafsat C Sodangi Category :  KDP NOVELS

Chapter   3 / 7

6K to 9K   out of 19.3K words

ciro daga cikin kwai saboda

laushi da kyau.

Dama gani ba fara ba haka nan ba baka

ba. Kalar jikina ita ce tafi daukar hankali,

amma ba ya ga haka bani.da tsawo sai dai

kuma idan ba tsayuwa kusa dani kayi ba.

46

Zai vi wuya ka gane haka, don kuwa

gabo6ina suna da zubin na dogayen

mutane.

Lubabatu ce tayi sallama ta shigo ta

zauna muna gaisawa tana tambayata

shirye-shiryena, ina yi mata bayani.

Zuwa can ta ce, To ai gaskiya

Hauwa'u ni dai hakuri za kiyi ba zan samu

zuwa ba shi yasa naga da ki ga shiru ban

zo ba gara na gaya mii kawai.

Na ce, Saboda me Luba? Ta ce, TO

Yaya Abdussamad ne ya hana ni ya ce,

idan kuma nazo to zai lauki kwakkwaran

mataki a kaina.

Nayi shiru ina dan tunani a raina na

rasa abin da na yiwa Abdussamad da yake

sa shi yin irin wadannan abubuwan da

yake yi mun a wannan lokacin.

Na ce,To babu komai Luba na gode,

amma kin san wani abu? Ni fa ban san

abinda na yi wa Abdussamad ba, amma

zan shigo gidan naku dan anjima kadan.

47

Ta ce,A'a rabu da shi kawai. Ni na

riga na fahimce shi, shi a tunaninshi

sauraron shi da ki ke yi Jira yake yi ya

gama karatu kuyi aure.

Wanda Umma ma ta gaya mishi ke

mace ce ba tun yanzu ba to bai yarda ba.

Yaushe za'a ce ke kin jira shi, shi da yake

aji uku na Jami'a a yanzu ko bautar kasa

bai je ba, ballantana har ya samu aiki kuyi

aure?

Na ce, "Duk ba haka ba ne ma Luba, ni

bai taba ce mun yana sona ba, mutunci ne

kawai na dauka a tsakani."

Ta ce, "Tabdijam! Ke kenan amma

kowa ya sani."

Bayan tafiyar Luba shiru na yi ina

tunani ban san abinda ya hana ni fahimta

ba sai a yanzu ne nake fahimtar wasu

abubuwan.

To amma koda na gane hakan tun farko

ko kuma ace shi ya gaya mun da kanshi

48

zai yiwu na jira shi? na yi wa kaina

tambayar.

A take kuma na baiwa kaina amsa ba

zai yiwu ba don kuwa a yanzu ma auren

nawa ya dauro ne saboda wasu dalilai.

Da dai ace muna da wadatar da zan yi

karatuna ne ba tare da wata matsala ba to

da sai in ce zan yi ta jiran Abdussamad har

ya yi karatunshi ya gama muyi aure.

Don kuwa wane mutum na ce bana

sonshi dan gaye ne. Duk da iyayenshi ba

masu kudi ba ne Abdussamad dan gata ne.

Haka nan shi ne dan farin namiji a

gidansu. Nayi maza na cire tunaninsu shi

da kanwarshi a cikin raina, na ci gaba da

harkokina, saboda hakan shi yafi mun.

Kayatacciyar walima aka shirya ana

gobe daurin aurena. Babu abin da bai ji ba

a wurin walimar.

Ana cikin walimar ne kuma 'yan uwan

Ango suka iso da La'asar aka farata ba a

gama ba sai gab da sallar Magriba.

49

A wurin su Sadiya nake jin labarin irin

kawataccen kayan auren da aka y1 mun

kamar zan yi dokin gani sai kuma naga to

al ma nawa ne, dokin me kuma.

Na tsaya cewa Ishak ya kawata bikin

nan ma tamkar na bata ne. Nayi kwalliya

iri-iri ba a magana.

Ranar Asabar da aka daura aure aka kai

ni gidan aka watse saboda wadanda suka

zo daga wasu garuruwa da za su koma a

ranar Lahadi don samun damar komawa

wuraren aikin su wadanda suka saura daga

yan biki kawai, yan uwan Umma ne da

yan uwan Babana wadanda a gidanmu

suke.

Na bude idona ina kallon dakin

shiryayyen daki na zamani irin wanda

mafarkina bai taba nuna mun shi a

matsayin nawa ba.

A takaice dai gidan yayi matukar

haduwa daidai da rayuwar 'yan boko. Bani

50

kadai ba nasan Ummana da Babana ma za

Su samu nutsuwa a yanzu.

Naci amarcina yadda ya kamata, abin

ba a cewa komai ga kuma karin nutsuwa

da na samu ta bangaren abinci da kuma

wurin zama sai abin ya hadu ya sani nan

da nan nayi wani irin canzawa, nayi kyau

ba kadan ba.

SKullum idan 'na tashi nake tsab tace

gidana na fara da abincin karyawa wanda

shayi ne da biredi wani lokaci ya ce da

kwai zai ci wani lokacin kuma ya ce da

sauran farfesun dare zai ci.

Kasancewar kusan kullum yana kawo

kaji ko kuma kifi ko nama ya dai danganta

da abin da yake so sannan na fara gyaran

dakin kwanciyarmu wanda kullum na

gyara shi sai na tsaya na kare mishi kallon

saboda sha'awar da yake bani.

Kullum kuma burina Umma tazo ne

taga inda nake kwana amma har yanzu

wajen watana daya shiru bata zo ba.

51

Sai na tsabtace toilet din da ke cikin

bedroom din na kalkale tiles din bango

zuwa na kasa yayi tas, sannan na fito falo.

Nan ma haka kafn na shiga kicin, nan

ma na gyare shi na goge tiles din shi nayi

wanke-wanke na goge cabinet sannan na

fito na wanke tsakar gidan nan tas.

Nasa sandar goge-goge nayi mopping

din ko ina. Bana gajiya saboda yadda yin

hakan yake yi mun dadi a cikin raina.

Bayan duk na gama hakanne sai kuma

na dauko kayanmu da muka cire na wanke

su na goge.

Ban cika yin abinci da rana ba saboda

baya dawowa da rana sai dare, don haka

sai kawai na sha shayi ko dan wani abu

mai sauki sai da daddare ne nake yin girki

Kullum cikin raina dai ina tsara yadda

zan rinka tafiyar da al'amuran gidana ne,

idan na koma Makaranta.

52

A yau kuma nayi nufin yi mishi

maganar tunda idan ba batan lissafi nayi

ba, to ina cikin wata na uku ne da aure.

Sai da na gabatar mishi da abincin shi

shinkafa da miya da salad na ajiye mishi

kunun zaki a gefe, sannan na koma na

zauna na ci gaba da kallon abinda ake yi a TV.

Ishak ba mutum ba ne mai hira zan iya

cewa abinda aurenmu ban sani ba ko da

can kafin auren ban lura na gane hakan ba ne.

Kullum dai idan zai dawo to ka'idarshi

zai yi guzurin Jaridar da zai karanta ta

ranar kafin zuwan shi wurin kwanciya.

Idan kuma ya kwanta ranar ba shi da

bukata ta to zai yi juyawar shi ne ya kalli

bango nima nayi tawa kwanciyar ban

kuma taba daukan hakan a matsayin wata

matsala ba.

Idan kuma ranar sati ne to kuwa haka

zai wuni yana kallon Jaridar shi ta sati,

53

idan kuma yamma tayi to zai fita ba zal

dawo ba sai sha daya ko da rabi idan ya yi

dare kuwa har sha biyun dare.

To zan iya cewa wannan ita ce babbar

matsalata da shi amma nauyinshi ya hana

ni yi mishi magana.

Sai dai maganar Makaranta ta ce a yau

nayi nufin yi mishi magana saboda tafiyar

lokaci.

Saida ya gama cin abincin shi na

kwashe kwanukan sannan na dawo na

zauna can gefe na ce mishi cikin ladabi.

"Don Allah ina so ne nayi maka wata

magana idan ba za ka damu ba." Ya dan

kawar da Jaridarshi daga kan fuskarshi ya

ce, "Uhum ina jin ki."

Na ce, Dama maganar Makaranta ta

nake so nayi maka don yanzu na kai wata

shida bana zuwa kada lokaci ya yi ta

tafiya."

Yayi shiru zuwa wani lokaci da har na

fara gundura da shirun nashi sai da ya

54

daga Jaidar ya ci gaba da dubawa sannan

ne ya ce "Ba yanzu ba."

Na ce, Na'am!" saboda yanayin da

amsar tashi tazo mun. Na ce miki ba

yanzu ko da matsala ne?"

A hankali na ce, "A'a babu." Ya ce,

To madallah." Sannan ya ci gaba da

kallon Jaridarshi. Daki na shiga na kwanta

sai dai na kasa hana kaina kukan da yazo

mun.

Ba yanzu ba sai yaushe? Sai dai ba zai

yiwu nayi mishi irin wannan tambayar ba.

To waye zai tambayan mun shi? Ai sai

daini din don kuwa ni ce nake zaune tare

da shi. Hakan ne yasa ni mikewa daga kan

gadon na fito falon na sake neman wani

wuri na zauna.

Na ce To yaushe ka ke ganin ya dace

kenan na koma Makarantar? Ya janye

Jaridar daga fuskarshi ya zuba mun ido

yana kallona.

55

"Ke! Tashi ki bani wuri, ke kuma

wacece da za ki yi mun titsiye? Shashashar

yarinya kawai.

Wadanda ya zamarwa dole ma ba su

tsaya sun ga kin yi karatun ba ballantana ni."

Mikewa na sake yi na hau gado na

kwanta. Har aka kira assalatu ban runtsa

ba, kuka kawai nake yi kukan sharbe.

Wane irin abu ne kuma haka meke

faruwa ne? Shin me Ishak yake nufi? Na

mike daga kan gadon na nufi bayan gida

nayi wanka sannan na dauro alwala.

Har yanzu barcin shi yake yi cikin

kwanciyar hankali. Nayi sallolina na nafila

raka'a biyu sau uku sannan na zauna na

dan yi karatun Kur'ani.kafin aka fara kiran

sallah.

Lokacinne ya tashi ya shiga bayan gida

yayin da ni kuma na tada sallar nafila ta

raka'atul fijri, sannan nayi sallar asubahi.

56

Na durkusa na gaishe shi kamar yadda

na saba sannan na shiga kicin don kokarin

yin abin karyawa kada ya makara.

Ba tun yauba na sha yin tunanin shiga

gidajen makwabta da muke unguwa daya

da su saboda mu'amalla da Jama'a.

Ban kuma samu damar yin hakan baa

duk kuwa da cewar su sun shigo ba sau

daya ba ba sau biyu ba. Haka nan ma

yayan su.

Baran ma dai Hindu wacce nasan ko

bata gime mun ba to zamu yi sa'a da ita

don a yanzu a SS 2 take kenan da muna

tare a Makaranta.

Don haka ko a yau da nayi nufin na sha

kunun gyada da safe sai na tashi domin na

leka sudaga nan kuma na samu wanda zai

siya mun gyada da kamu.

Ba a yi hanzarin tambayar Ishak ba

amma a a raina sai na kuduri aniyar idan ya

dawo daga wurin aiki sai na sanar da shi.

57

sNa fito na rufe ko'ina na cikin gidan

sannan na nufi gian su Hindu wanda yake

kallon namu gidan nayi kyakkyawan

sallama a tsakar gidan wanda hakan yasa

Momy mahaifiyarsu ta leko.

"A'a'a Amarya ce yau a gidan namu?

To shigo daga ciki mana." Na bita muka

shiga falon na zauna a kasa ta ce "A'a

zauna a kan kujera mana."

Na mike na gyara zamą a kan kujerar

sannan na gaisheta cikin girmamawa ta

amsa tare da yin yar hira kadan wacce

mafi yawancinta kan al'amuran gida ne.

Na ce, Hindu bata nan ko? Ta ce, "Eh

ba su dawo daga Makaranta ba, saboda

tana tsayawa lesson."

Ban. wani tsaya bata lokaci ba na mike

don dawowa gida har kofar gida ta rako ni

da yar leda a hannunta ta miko mun nayi

godiya na nufi gida ina tunanin inda zan

samu abin da na fito nema.

58

Wanda ba zai yiwu kuma na kara yin

gaba ba. Wani abin mamaki shi ne ban

lura na hangi motar Ishak ba sai da nazo

shiga gida.

Wani irin mummunan faduwar gaba ne

ya same ni sai dai kawai sai naga to ai ba

nisa nayi ba sai nayi mishi bayani.

Na shiga dakin cikin murmushi na ce,

Lah ban yi zaton zaka dawo yanzu ba, shi

yasa... " kan na gama maganata ya ce

"Dama idan na fita yawon ki ki ke tafiya?

lye? Inà ki ka je? Na ce miki daga ina ki

ke, kaga mun shegiya 'yar matsiyata.

Raina yayi mummunan baci na ce "A'a

ni kada ka sake zagina ka hada da iyayena,

me nayi da zafi haka?"

Ya ce, "An zage su matsiyata me za ki

yi iye na ce me za ki yi idan an zage su su

din banza su din wofi."

Wannan shi ne na farko kuma na karshe

na gaya miki idan ki ka kuskura ki ka sake

59

ita na dawo gidan nan ba kya nan sai nayi

miki abinda ba ki yi zato ba."

Ya juya ya fita ina jin shi ya sakala

kwado ya rufe gidan ta baya. Na zauna a

wurin nayi kuka irin wanda ban taba yi ba

a rayuwata.

Dama haka auren yake? Na san iyayena

talakawa ne wadanda ba su da komai

amma ba haka yana nufin Ishak ya zage su

ba ne tamkar sun dauke ni sun ba shi ni

auren da ko wata biyar bai yi ba.

Tausayin Babana ya sake kama ni,

mutum mai kokari da bai taba zuwa kofar

gidan wani neman taimako ba, ya dogara

ga Allah ne da kuma dan abinda yáke

samu a wurin aikinsa.

Hakanne yasa mutanen unguwarmu har

da ma su kudin suke matukar girmama shi.

Na lallaba na mike da nufin shiga kicin

nayi girkin abincin dare. Na kuwa samu ya

kawo wani cefanen abinda a yau ya daina

birge ni.

60

Na dauko na fara rarrabawa, ina ajiye

komai a wurinshi, na zaro ledar da naji

danshi, kifi ne manya masu kyan gaske

guda uku.

Na bude frizer na ajiye guda biyu na

fara gyaran dayan da alama shi yake son ci

da daddare.

Farfesun kifi nayi mishi wanda bai yi

romo mai yawa ba, sai nayi coconut fried

ice na ajiye a food flask ganin har na

gama bai dawo ba duk kuwa da daren da

nayi sabodamakarar da nayi wajen

farawa.

Har nayi sallar Isha'i shiru bai dawo ba.

Bai saba yin dare a waje ba idan ba

kwanakin sati ba ne wato Asabar da

Lahadi.

Tun ina sa ran dawowan shi har na

hakura na hau gado na kwanta. Can cikin

dare na ji motsin shi.

Na mike na same shi tsaye yana cire

riga da niyyar canzawa don kwanciya.

61

Na fito falo na dauko abincinshi na

kawo mishi, bayan nayi mishi sannun da

ko kallona bai yi ba.

Na ajiye abincin da farfesun na koma

gefe na zauna yadda na saba yi. Ya gama

shirin shi ina tunanin zai zauna yaci

abincin ne sai kawai naga ya hau gado ya

kwanta.

Na dan daure na ce ba za ka ci abincin

ba ne? Bai ce mun komai ba duk kuwa da

nasan idonshi biyu saboda haka sai na

tattara na kai kicin na zuba cikin wani abin

na saka a fridge don gudun kada ya lalace.

Na dawo dakin na gyara na sake

kwanciya sai dai a yanzu kam ban samu

yin barcin ba.

Kan kace meye wannan sai na fara jin

saukar numfashin Ishak yau ma haka na

kwana ban yi barci ba.

Sai dai duk tsawon lokacin tunani nake

yi na ya kamata naje gida naga iyayena

62

haka nan na sanar musu da abinda yake

faruwa.

Hakanne yasa da na gama gaishe shi da

safe na roki ya bani izinin zuwa gida bai

bani amsa ba haka nan bai tsaya karyawa

ba yayi ficewarshi.

Da wani bacin ran na wuni wanda yau

duk da dadin da gyaran gidan nan yake yi

mun yau haka ya zauna sai da naga

La'asar tayi sannan na mike don shirin

abincin dare.

Shaf, na mance da abincin jiya da Ishak

bar ci ba, don haka na nufi kofar gida don

na samu yaran da zan baiwa abincin.

Sai dai a kulle na ganshi ta baya. Sai

kawai na dawo na kama aiyukana. Kamar

yadda jiya bai dawo ba sai tsakar dare

haka nan yau ma.

Sannan bai ci abincin ba ya sake

kwanciya. Gari ya waye na sake yi mishi

maganar zuwa gida yau ma bai ce mun

komai ba, ya fita ba tare da ya karya ba.

63

Na dai lura idan nace zan zauna ina

kunci da bakin ciki to zan nakasa kaina,

sai kawai na nemi samun saukin

damuwata ta wata hanyar.

Ni ba ma'abociyar kallon fim ba ce,

amma yau sai na shiga laluben drawer da

ke jikin TV stand din don neman kaset din

kallo.

s1Na yi dace da wani mai suna Why did I

get married too?' sunan shi ne ya dauki

hankalina da na saka kuma sai na samu

kaina da nutsuwa don yin kallon.

Kawaye ne guda uku sai dai kowacce

da irin matsalar aurenta. Na dan ji dadin

yin kallon don ya rage mun damuwa.

Ban ki yin abinci ba don ganin ba ya ci

kuma ina ta tara shi a fridge. Tuwo nayi

miyar kubewa bushasshiya na ajiye kamar

yadda na saba.

Ban kwanta ba zama nayi na jira

dawowarshi. Shima yau bai vi dare sosai

ba, don kuwa sha daya da kwata ya dawo.

64

Babu irin tunanin da ban vi ba amma ina

kasa sanin abin vi a kan matsalar. Zaman

auren da nayi ba mai yawa bane

ballantana har nayi wayon zama da miji.

Amma sai na kudure a raina a yau idan

ya dawo zan san abin yi akai shi ne kuma

na ba shi hakuri.

Ganina da yayi zaune a falon bai tsaya

ba wucewa yayi zuwa cikin daki yadda ya

saba.

Na bishi na sake yi mi1shi sannu, sannan

na tsugunna a gefe na ce Don Allah idan

nayi maka laiti ne ka yafe mun abinda nayi

maka. Ba kuma zan sake ba da ikon

Allah."

Wannan magiyar da nayi mishi ita ce

tasa shi ajiye rigar barcin da ya dauko zai

saka ya kalle ni.

To kenan har kin isa na zage ki ki

rama. Iye! Ke kuma wacece a cikin mata?

Duk da bacin ran da maganar tashi ta sa

ni wacce a take kuma na kasa danne

65

hawayen da suka fara zuba a idona

hakurin na ke ba shi kafin daga baya ya ce

ya wuce amma kadá ki sake ko da wasa."

Hakan bai sa yaci abincin ba, amma bai

dame ni ba. Na hau gado na kwanta.

Washegari na lura ba shi da niyyar buga

sammak0 irin

3 / 7